Showing 1 words to 3000 words out of 46126 words

Chapter 1 - TAIMIYYAH

Start ads

15 Aug 2025

299

Middle Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin

na

https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci

ko

marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi

ko

tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan

ko

sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku

dena

binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF

,TXT

da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java

ko

mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This

hausa

novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more

hausa

novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF

,TXT

or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC

those

with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng

to

download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook :

https://facebook.com/taskarnovels

Twitter :

https://twitter.com/taskarnovels

Telegram :

https://t.me/taskarnovels

[7/24, 11:03 AM] Ayshat Dansabo

😘

: *TAIMIYYAH*❤



©



Ayshat Ɗansabo Lemu✍

🏻

*MABUƊI*

*Ina me farawa da godia ga Allah subhanahu wata'ala

,da

ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna asama,ina roƙo ubangiji yayi riƙo da hannuna wajen rubuta dai-dai,ya kuma yafe kusakuran da zasu iya kasancewa aciki Ameen.*

*SADAUKARWA*

*Na sada

ukar da wannnan littafin gaba

ɗ

ayansa zuwa ga duk wata me nakasa

,especially

masu matsala irin na TAIMIYYAH,ina roƙo ubangiji yasa nakasan ta zame muku alkhairy da

ɗ

aukaka a rayuwa.*

*Page 1*

Matashiyan budurwace kwance ƙudundune cikin bargo,jikinta na

faman kakkarwa alamun zazza

ɓ

i ne yai mata kamun me kyau,daga gefenta wata dattijuwa ce wacce shekarunta ya fara nisa sosai,don a ƙalla zatai shekaru sittin da biyar zuwa sama,farace tas dattijuwan me tsagen kalangu a fuskanta hagu da dama,kyakykyawace wand

a a kallo

ɗ

aya zaka zaci cewa bafulatana ce,sai dai ba hakan bane bahaushiyace ziryan,wanda ubangiji ne kawai yai mata baiwan kyau da farin fata,hannu takai tana janye bargon da budurwan ta ƙudundune aciki,cikin muryan da ke nuni da tsananin kulawa take fa

ɗ

in "Tashi TAIMIYYAH ki ƙoƙarta kiyi wanka ko zaki daina wannan rawan sanyin,idan kin karya yanzu sai Sani yazo ku koma asibitin watakila wa

ɗ

annan magungunan ka

ɗ

ai bazasu wadatar da ke ba sai an ha

ɗ

a da alluran dai da ba'a so."

Ta ƙare maganan tana ƙarisa

yaye bargon da budurwan ta rufa dashi,nan take kyakykyawan fuskan budurwan da aka kira da TAIMIYYAH ya bayyana,tare da jikinta baki

ɗ

aya wanda take sanye da rigan bacci Ash colour me kauri sosai,kamanninta da tsohuwan daya bayyana sosai zai baka tabbacin

idan ba ƴarta bace to akwai alaƙa ta jini me ƙarfin gaske dake tsakaninta da dattijiyan matan,abinda kawai dattiyan zata nuna mata shine fuskan manyance ,amma hatta farin fatan nata irin na Dattijiyan ne,TAIMIYYAH ta yamutse kyakykyawan fuskanta tana sake

lumshe manyan idanunta,muryanta can ƙasa dake

ɗ

auke da ƴar shagwa

ɓ

a take fa

ɗ

in "Wash! Allah Iya baki ji kaina ba kaman zai cire wallahi."

Iya ta dube ta cike da tausayi da kulawa tana fa

ɗ

in "Sannu kiyi haƙury zai bari

,yanzu

tashi ki shiga wankan na ha

ɗ

a m

iki ruwan

ɗ

umi sosai da zakiji da

ɗ

insa,Allah ya baki lafiya TAIMI na."

Budurwan ta amsa da "Ameen." Tana miƙewa tsaye da ƙyar sai lokacin na kula da cewa tana da tsayi dai-dai misali wanda bai cika yawaba,sam bata da jikin ƙiba sai dai jikin a murje yake

cike da tsoka da cikan halitta me

ɗ

aukan hankali,ta sake lumshe manyan idanunta sabida ciwan da kanta keyi,kafin a hankali takai hannunta na hagu ta dafa guiwan ƙafanta na hagun tana me fara takawa zuwa toilet

ɗ

in dake

manne cikin

ɗ

akin,Dattijiya Iya tabi

bayanta da kallo ƙaunar budurwan da tausayinta na sake ratsa ilahirin jinin jikinta,tana matuƙar tausayin TAIMIYYAH sai dai ko ka

ɗ

an ba ta nuna mata cewa nakasan da ta samu na ƙafa yana damunta domin ita ka

ɗ

aice a kullum take ba TAIMIYYAN tabbacin haka uba

ngiji yaso ganinta,tashi tayi tana me ficewa daga

ɗ

akin mintoci ka

ɗ

an ta dawo

ɗ

akin hannunta

ɗ

auke da Mug da ta ciko da zazzafan Kunun gya

ɗ

a da yaji madara sabida sanin TAIMIYYAH na matuƙar son sa,dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga toilet,tana

ɗ

aure

da ƙaton towel da tsayinsa ya sauka har zuwa guiwanta,ƙafafunta nabi da kallo wanda na lura

ɗ

aya ya sirance

ɗ

aya kuma lafiyayye,ta yadda ruwa ke gangara a jikinta ka

ɗ

ai zai baka tabbacin Allah yai mata baiwa da sul

ɓ

in fata,taiwa Hajiya Iya kallo

ɗ

aya tana

sakin murmushi,a hankali ta ciga da dafa ƙafanta na hagu tana takowa zuwa cikin

ɗ

akin,da alamu wankan da tayo yasa ta fara jin da

ɗ

in jikinta,Iya ta

ɗ

aga kai ta dubeta tana fa

ɗ

in "Sannu kinji da

ɗ

in jikin ko?

ga

kununki nan saiki daure ki farasha kafin Lad

i ta gama soya miki dankalin."

TAIMIYYAH ta

ɗ

aga manyan idanunta masu haske ta dubi Iya

,cikin

sanyin muryanta me da

ɗ

i take fa

ɗ

in "Naji da

ɗ

i Iya nagode da kulawa,amma ina ga abar dankalin wannan

ɗ

in ka

ɗ

ai ya isa,amma zuwa anjima don Allah ki min faten tsak

i da kanki irin wanda kikeyi yayi

ɗ

an tsamin yakuwannan shi kawai nake son sha." Ta ƙare maganan da shagwa

ɓ

a sosai a muryanta."

Hajiya Iya tayi murmushi me fa

ɗ

i tana fa

ɗ

in "To shikenan baki da damuwa za'ayi insha Allah,yanzu dai sha kunun ki sha magunguna

n,sai a sake kiran Sanin ku koma asibitin,ki tafi da duka magungunan sabida su gani ki kuma bu

ɗ

e baki kiyi magana agaban likitan bana son wannan miskilancin naki idan kina ciwo ki ƙi magana."

Hajiya Iya ta ƙare maganan da mita,wanda hakan yasa murmushi me

fa

ɗ

i su

ɓ

ucewa daga face

ɗ

in TAIMIYYAH wacce ta kammala shafa mai tana ƙoƙarin saka rigan da ta ciro,ba tare da tayi magana ba har Iya ta fice ta sanya doguwan rigan atamfa Red wanda akaiwa adon zanen manyan Flawer da milk and black,yayi mata kyau sosai ta

re da haska kalan skin

ɗ

inta,bata shafa komi a face

ɗ

inta ba sai lip balm me taushi,qamshin Body mist datai anfani dashi ne ya cika

ɗ

akin baki

ɗ

aya domin ita

ɗ

in ma'abociya son qamshi ce na ajin ƙarshe,zama tayi tana

ɗ

aukan Mug

ɗ

in da Iya ta aje tana fara

shan kunun ahankali cike da nutsuwa,magungunan ta sha bayan ta shanye kunun,wani zufa ta fara ji na keto mata hakan yasa ta miƙe tana ƙara ƙarfin gudun Fan

ɗ

in dake aiki a

ɗ

akin,tsaye tayi gaban dogon mirrow

ɗ

in

ɗ

akin tana kallon fuskanta da ya rame sosai

a kwanaki biyu kacal da fara ciwan nata,sai fararen manyan idanunta ma'abota haske da

ɗ

aukan hankalin mai kallonta,domin wasu irin idanu Allah yai mata baiwansu masu

ɗ

aukan hankali,ƙirjinta ta kalla tana me waro ido waje ganin cewa ta manta bata sanya Bra

ba,gashi fita zasuyi sam bazata iya fita babu shi ba,sabida Allah yai mata baiwan cikar ƙirji,sai dai bawai irin sunyi girman da har suka rankwafa bane,kawai dai bata iya fita haka babu Bra dake tare su ajikinta,wannan sabo ne dataiwa kanta tunda ta isa sa

nya Bra

ɗ

in,don haka kai tsaye wajen da take aje su ta nufa ta

ɗ

akko tana sauke zip

ɗ

in riganta zuwa ƙasa ta sanya,wayanta dake aje bisa gado ya fara ringing,sai ta

nufa wajen don ganin me kiran,ganin sunan Sani ya bata tabbacin yazo kenan,ta

ɗ

aga wayan ta

na gaida shi tare da bashi tabbacin fitowanta yanzu.

"Iya ga Sanin can ya iso zamu wuce."

TAIMIYYAH ta fa

ɗ

i hakan tana kallon Hajiya Iya dake zaune saman

ɗ

aya daga cikin kujerun da suke qawataccen falon nata

,Iya

ta

ɗ

aga kai tana sauke ganinta akan

TAIMIYYAH da ke sanye da dogon Hijab kalan Red da yai mata kyau sosai,ta saki murmushi tana fa

ɗ

in "To sai kun dawo ki kula ki kuma bu

ɗ

i baki agaban likitan bana son wannan miskilancin naki,kice ma Sanin idan kun dawo ya shigo ina son ganin sa."

TAIMIYYAH

ta amsawa Iya tana miƙewa hannunta

ɗ

aya riƙe da ƙaramin hand bag da ta sanya magungunan da aka

ɗ

aurata akai,

ɗ

aya hannun na dafe da guiwan ƙafanta na hagu,wanda ke bada tabbacin sai da taimakon dafa guiwan shanyayyen ƙafan take iya takawa tana tafiya,a dukk

anin cikar halittan ta babu inda ke da naƙasu sai wannan ƙafan na hagu daya shanye ya silance,kyakykyawace da ta mallaki duk wani cikan halitta me

ɗ

aukan hankali,ahaka ta dinga takawa har ta fice daga falon Hajiya tayo waje,idanunta suka shiga ƙarewa harab

an sasan Iya kallo kaman me son gano wani abu,kafin ta cigaba da takawa bisa tsarin yadda ubangiji yaso tafiyan nata ya zamo ahaka har ta fito daga sashin Iya baki

ɗ

aya,ta iso ainihin haraban gidan me

ɗ

auke da part guda biyu duk da na Hajiya Iya ne cikon n

a ukun,tafiya ta cigaba dayi zuciyanta na karyewa a lokacin da idanunta ke hango mata matar da ta fito daga

ɗ

aya part

ɗ

in,bayan matan wani matashi ne ke biye da ita riƙeda da wata ƙatuwar leda a hannunsa,TAIMIYYAH tayi saurin yin ƙasa da kanta tana cigaba

da tafiya har ta iso dai-dai inda Hajiya Shuwa suke tahowa,hakan yasa TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyan tana jiran ƙarisowan Hajiya Shuwan wacce suke kira da Umma,matar wan mahaifinta ne wacce taiwa TAIMIYYAN wata irin muguwan tsana.

"Ina kwana Umma."

Sune

kalmomin da suka fito daga bakin TAIMIYYAH a lokacin da su Umman suka iso suna shirin gitta ta su wuce

,sai

dai gaisuwan da ta aikawa Umman yasa Umman dakatawa tana zubawa TAIMIYYAH ƙananun idanunta,fuskanta babu

ɗ

igon fara'a ko ka

ɗ

an,tai mata wani malalac

in kallo memakon ta amsa gaisuwan TAIMIYYAN sai cewa tayi "Ikon Allah su gurguwa kenan ance baki da lafiya,ke kuma haka Allah ya yoki irin jaraba ga nakasa ga yawan ciwo da wanne za'aji?

kuma

a hakan ake so wani yazo yace zai kwashi jaraba,ga gurgunta ga y

awan cuta kaman sikila,to mu dai kurwan mu kur kada arasa me so ace wataran za'a cinnama lafiyayyun ƴaƴan mu gurguwa raguwan cuta."

Ta ƙare maganan da jan tsaki tana yin gaba abinta bayan ta kalli

ɗ

an lelen

ɗ

an nata ta maka masa harara tare da yi masa sig

n da ido alamun ya shige gabanta,ba tare da ta kuma kallon TAIMIYYAH da tai ƙasa da kai zuciyanta na shiga wani irin ƙunci mara misaltuwa ba,manyan idanunta tuni sun fara tara hawaye, ciwan kan da take riritawa taji ya dawo sabo,cikin

ɗ

an hanzari ta dafa ƙ

afanta me laluran ta fara cigaba da tafiya,sai dai taku biyu tayi taji sassanyan qamshin turaren BENTLEY na isowa hancinta,kaman yadda kafin tayi wani yinƙuri yayi saurin tare gabanta,manyan idanunsa masu kama da nata ya sauke akanta,wani abu na yawatawa c

ikin maƙoshinsa,cak! TAIMIYYAH ta tsaya still bata

ɗ

ago face

ɗ

inta ba don qamshinsa ya

gama

bata tabbacin ko waye domin kaf gidan shi ka

ɗ

ai ne mamallakin irin wannan turaren me qamshin da ke kashe jikinta, amon muryansa me cike da ginshira taji cikin kunnu

wanta yana fa

ɗ

in "Kiyi haƙury Sis da halin Umma please!

watarana

sai labari ko ka

ɗ

an bana so kisa wani damuwa a zuciyanki haka Allah ya halicceki kuma yaso ya ganki, mu da ita babu me halitta haka kuma babu wanda isa ya sauya halittan wani face wanda yayis

a,ya jikin naki?"

Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya

,hakan

yasa TAIMIYYAH yin jarumtan maida ƙwallan da suka cika idanunta,sai dai duk yadda ta so

ɓ

oye halin da zuciyanta ke ciki ƙaramar zazzaƙan muryanta dake rawa ya fallasata,cikin sanyin muryan da ke

kashe zuciyansa take fa

ɗ

in "Naji sauƙi Yah Sadeeq zazza

ɓ

in ne yaƙi tafiya shine yanzu zamu koma wajen ganin likita,ina kwana dafatan mun tashi lafiya."

Ta ƙare maganan da gaida shi tana me

ɗ

ago manyan idanunta ta sauke akan face

ɗ

insa

,sai

dai ganin ita

ɗ

in yake kallo yasa ta sake ƙasa da kanta,tana jin yadda idanunsa ke cigaba da yawo akanta,kafin ya furta "Okey! Allah ƙara lafiya yi maza kije tunda yana jiranki zuwa anjima zan shigo sasan Iya sai muyi magana

,take

care Angle."

Ya ƙare maganan da wani kar

yayyen sauti daya motsa zuciyan TAIMIYYAH

,hakan

yasa ta gya

ɗ

a kanta tana lumshe idanunta da bu

ɗ

esu lokaci guda ta cigaba da takawa zuwa parking space inda take hango motan Sani,ya bi bayanta da kallo tausayinta da matsananciyan ƙaunarta na sake kassara zuc

iyansa.

Ko da TAIMIYYAH ta isa wajen motan Sani baya ta bu

ɗ

e ta shiga don tana buƙatan kwanciyane sabida yadda kanta ke sarawa,sam baiyi ƙorafi ba domin matsayin driver yake bashi da damuwan duk inda zata zauna

ɗ

in,sannu yai mata yana tada motan bayan TAI

MIYYAH tayi ƙarfin halin amsa masa,zuciyanta na mata bitan baƙaƙen maganganun Umma wanda inda sabo yaci ace ta saba da yadda Umma ke kyaran halittan ta da kushe nakasanta tamkar itace tayo kanta a hakan,ba haka Allah yaso ganinta ba, hawaye masu

ɗ

umi suka

silalo mata ta kai hannu ta share tana son ƙarfafa zuciyanta kaman ko yaushe,don ganin maganganun basuyi tasiri a zuciyanta sosai ba,sai dai har suka isa asibitin ABU da ke zaria zuciyanta babu da

ɗ

i,zuciyanta ya sake nauyi tana tambayan kanta wai har sai y

aushe ne zata daina fuskanta gorin halitta

da cin fuska daga wasu cikin ahalinta akan yadda Allah ya yota?

da

ƙyar ta lallashi kanta ta samu ƙwarin guiwan shiga cikin asibitin don ganawa da likita.

A ƙalla ta shafe kusan awa guda kafin ta fito tana faman

liliya inda akai mata alluran,domin bayan dukkanin bayanai da taiwa likitan sai ya sanar da ita dole ta amshi allura guda uku wanda zaa jera yi kullum guda

ɗ

aya,ba don rai yaso ba ta amince domin allura na daga cikin abinda family

ɗ

inta suka tsana akira z

a'aiwa ƴaƴansu tun bayan laluran data samu TAIMIYYAN wanda ta sanadin allurance ta samu wannan nakasan na shanyewan ƙafa

ɗ

aya,wanda hausawa ke kira da shan inna wanda kuma take fuskantan ƙalubale me tarin yawa daga ƴan uwanta da wasu baren daban ma,kai kac

e itace ta janyowa kanta laluran da kanta ba Allah ne ya

ɗ

auro mata ba.......

Hello! my people gani da sabon salo sabon tafiya irin wanda Ɗansabo bata ta

ɓ

a zuwa dashi ba

,labarin

TAIMIYYAH labari ne mai cike da ban tausayi, ha

ɗ

i da darasi me tarin yawa g

a zallan ƙauna da soyayya me motsa zukata,kada ki bari abaki labari a wannan karon kowa ta ƙoƙarta ta mallaki nata akan fara shi me sauƙi da zan fa

ɗ

i nan gaba ka

ɗ

an,ku dai ku cigaba da bibiyata a shafukan da zasu biyo baya don jin ya rayuwan TAIMIYYAH zai

kasance.

#Ɗansabo

ce

#

[7/24, 11:03 AM] Ayshat Dansabo

😘

: *TAIMIYYAH* ❤



©



Ayshat Ɗansabo Lemu ✍

🏻

*Page 2*

Lokacin da TAIMIYYAH suka dawo gida daga asibitin ana ta kiraye-kirayen sallan zuhur ne,hakan yasa Sani wuce

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login