Showing 30001 words to 33000 words out of 46126 words
for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa
Transferred time: - lokacin da aka turo
Name
of bank: - sunan bankin da aka turo dashi
Deposit date: - ranar da aka turo
Sai ayi SUBMIT.
*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer
* ,
amma idan yakama babu mafita saishi tau muna
amsar:
MTN,
9Mobile
Glo
Airtel
Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na
canji(
convert) kafin kudinka yashiga Balance.
Wannan shine bayanan.
[7/24, 4:55 PM] Ayshat Dansabo
😘
: *TAIMIYY
AH*❤
️
©
️
Ayshat Ɗansabo Lemu ✍
🏻
*Page 12 to13*
*CIGABAN LABARI.*
________Kaman yadda TAIMIYYAH ta sanar da Baba Sani ran Monday za ta yin Registration,hakan ya kasance misalin ƙarfe Sha biyu da rabi na rana,ta shirya cikin Riga da zani na tamfar
Holland.Ɗinkin yai mata
ɗ
as a jiki duk da babu kwalliya akan fuskanta ta yi kyau matuƙa,manyan idanunta farare tas masu wani irin turuwan baƙin ƙwayan ciki sai haskawa su ke da ƙyallin baƙin kwalli da ta zizarawa idanun.Ta
ɗ
akko gogaggen Hijab
ɗ
inta kalan
Milk wanda ya shiga da atamfar jikinta ta sanya.Wayanta ta
ɗ
auka don neman layin Zuhurah ta ji ko ta amsa ku
ɗ
in Form
ɗ
in kafin Baba Sani yadda yace Zuhuran ta tuna masa.Wayan na fara ringing ta koma ta jinjina da jikin gadon da take zaune,ba za ta iya cewa
yaushe rabon ta da
ɗ
aga waya ta kira layin Xuhuran ba,asalima ta
ɗ
auki numbern su awayan Yah Sadeeq ne ko don watarana,kada wani abu ya sameka aso kiran layin ƴan uwanka na kusa ka ce ba ka da shi.Ba don haka ba ba ta ga anfanin ma aje number
ɗ
insu cikin
wayanba,sai ko irin wannan ranan wanda sam ba ta son shiga Sasan na su ne bare wani cin fuskan ya biyo baya,tunaninta ya katse ne a lokacin da muryan Zuhuran ya ratsa kunnuwanta,daga yadda ta amsa call
ɗ
in TAIMIYYAH ta gane ba ta da number
ɗ
inta ba ta san
waye ya kirata ba.Sabida yadda ta wani lanƙwasa murya wajen fa
ɗ
in "Hello!" TAIMIYYAH da murmushi ya kwace mata ta amsa da fa
ɗ
in "Salam Zuhurah TAIMIYYAH ce
,kin
amsa ku
ɗ
in form
ɗ
inne mu wuce tare? Don ni yanzu zan wuce shi ne na ce bari in kira ki inj......
"
Kafin ma TAIMIYYAH ta kai ƙarshen maganan ta ji
ɗ
in
ɗ
in
ɗ
in...!Zuhurah ta kashe wayan,hakan yasa TAIMIYYAH bin wayanta da kallo tana ta
ɓ
e baki,ko ka
ɗ
an abin bai ba ta haushi ba don a ganin ta Zuhurah kan ta taiwa ba ita ba,Skull
ɗ
in ma in ba ta yi ba duk
don kanta tunda ita dai ta sa ka kanta kuma za ta yin ko da Zuhuran ko ba bu,don haka sai kawai ta miƙe tana dafa ƙafanta ta fara takawa,ta isa wajen da take rataye jakunanta ta ciro wata ƙaramar jakan LV.Ta bu
ɗ
e ta cilla wayanta ciki,bayan ta tabbatar duk
ku
ɗ
a
ɗ
en da za tai anfani da su suna ciki.Wajen Drawern Bed-side na gado ta nufa ta bu
ɗ
e tana janyo ledan Sweet da na Dabino ma su kyau da ba ta rabo da ajewa sabida yawan bada sadaka da ta ke yi,ta
ɗ
iba ta watsa a jaka tana mai da Drawern ta rufe,ko da ta
fito Ladi ta samu a falon,suka gaisa da TAIMIYYAH sannan ta wuce Ladi ta isa
ɗ
akin Iya.A kwance ta samu Iyan ba ta jin da
ɗ
i sosai wai kanta na ciwo ta sha magani shine ta
ɗ
an kwanta,tai mata sannu da sanar da ita zata yin Registration
ɗ
in ta dawo.Iya tai
mata fatan dawowa lafiya daga haka TAIMIYYAN ta fito daga
ɗ
akin,tana takawa a hankali cikin yanayin tafiyanta da sai ta dafe ƙafanta me lalura.Wanda yanayin tafiyan na ta bai hana a ga ne irin nutsuwan da ke tattare da ita ba,sannu-sannu ta ke takowa layin
nasu idan ta ha
ɗ
u da wanda ta sani sai ta tsaya su gaisa,a haka har ta iso bakin titi inda xa ta tari Napep ya ƙarasa da ita can gaban Congo ka
ɗ
an.Inda nan ne wajen Computer Training Center
ɗ
in yake,bata wani jima sosai ba a wajen ta gama abinda zatai ta
fito wajen.Da ƙafanta ta dinga takawa tana miƙe titi,har sai da tayi tafiya me
ɗ
an nisa kafin ta tsaida Napep ta hau,ita ka
ɗ
ai ya
ɗ
auka tunda har ƙofar gida take buƙatan ya kaita.Ku
ɗ
in da ya ambata lokacin da su ka iso ƙofar gate
ɗ
in shiga gidan ta zuge ja
ka ta ciro masa,har zata shiga gida ta hango wasu yaran almajirai biyu zasu wuce ta tsaida su.Ta ba su sadakan Sweet da Dabino,har da raguwan canjin da ke jakanta ƴan goma goma ta ba su,su ka amsa su na godia ita kuma ta nufi ƙofan shiga gate
ɗ
in gidan ta
tura ta shige,zuciyanta na tuno mata da Baba Megadi wanda Umma ce tai maƙarƙashiyan da Baba Sani ya kore sa ga shi har yanzu ba'a samo wani Sabon Megadin ba,har ta isa Sasan Iya bata ha
ɗ
u da kowa a Compound
ɗ
in gidan ba,hakan kuma ba ƙaramin da
ɗ
i yai mata
ba,tana isa ƙofan shiga falon na su ta fara jiyo muryan Maryam Salis.
Lokacin da ta sanya kanta cikin falon bayan Iya ta amsa sallaman da tayi
,idanunta
akan Maryam
ɗ
in ya fara sauka.Ta saki wani irin murmushi tana ƙarawa takunta sauri,cike da murnan ganin
Maryam
ɗ
in ta fara fa
ɗ
in "Lallai ne Maryama kin iya bazata,shi ne jiya da mu ke magana a chart ba ki sanar da ni zaki zo ba."
Ta ƙare maganan lokacin da ta ke isa kujeran da Maryam
ɗ
in ta ke zaune.Maryaman ta saki murmushi itama tana fa
ɗ
in "TAIMIYYAH kena
n ai na fi so in miki bazatan tun da ke ba'a ganinki sai dai a Chart
ɗ
in
,ai
ban jima da shigowa ba Iya ke sanar min kin je ki dawo."
"Wallahi bari kawai wani Computer Training na shiga in gaya miki
,shine
na je yin Registration zuwa next week zan fara zuwa
."
Cewan TAIMIYYAH har lokacin murmushi yaƙi barin face
ɗ
inta
,ta
waiwaya wajen Iya tana fa
ɗ
in "Iya na dawo,ya ciwan kan na ki ina fata dai ya kama gabansa?"
Iya ta murmusa tana fa
ɗ
in "Ya kama gabansa kam Alhamdulillah.Na ga ai kin yi saurin dawowa da har
na ce ko za ta kira wayanki
,tace
a barki dai muna
ɗ
an ta
ɓ
a hira kin ga gashi har kin dawo
ɗ
in."
Iya tayi maganan tana tashi don komawa
ɗ
aki
,ganin
hakan yasa TAIMIYYAH miƙewa tana cewa Maryam "Mu je
ɗ
aki Besty,gaskiya yau kin biya ni na ji da
ɗ
i sosai da w
annan ziyara."
Maryam ta saki murmushi tana biye da bayan TAIMIYYAN har zuwa
ɗ
akin ta,Hijab kawai TAIMIYYAH ta cire ta aje jakanta ta fito zuwa Kitchen don kawowa Maryam wani abu.Duk da ta ga Iya ma tasa Ladi aje ma Maryam
ɗ
in ruwa da lemu,amma ita tana d
a raguwan Samosa a Fridge shiyasa zata soya mata kafin Ladin ta gama abincin Lunch.Cikin minti goma ta gama soya Samosan ta juye shi a kyakykyawan mazubi,ta ƙara
ɗ
aukan ruwa da lemu ta
ɗ
aura a madaidaicin Tray ta nufo
ɗ
akin.Maryam ce tayi saurin tashi tana
amsan Tray
ɗ
in a hannun TAIMIYYAH tana fa
ɗ
in "Haba qawata shine ba zaki kirani in
ɗ
akko ba."
Ta aje Tray
ɗ
in daga saman gadon,idanunta akan TAIMIYYAH da ta saki dariya tana fa
ɗ
in "Haba dai zan iya ai, ba gashi na kawo lafiya ba,ke ni fa abubuwa da yawa b
a na jin wahalan yin su,amma ku sai kuita ganin kaman ajigace nake yi ko?"
Ta ƙare maganan cikin low voice
,manyan
idanunta akan Maryama da ta saki murmushi me fa
ɗ
i,kafin ta furta "Wallahi ni haka na ke gani TAIMIYYAH,gaskiya kina da ƙoƙari sosai kam da so
n aiki."
Daga haka suka kamo hiran Skull
,Maryam
ɗ
in na mitan yadda har yanzu babu wani labari game da janye yajin aiki,bare su samu su amsa Result ma susan madafa.Daga hiran Skull aka koma na auren Murja wacce aka sanyawa ranan aure watanni uku masu zuwa.
TAIMIYYAH ce ta dubi Maryam tana dariyan tsokana take fa
ɗ
in "Mu na gama shan bikin Murja sai kuma naki Besty,ni ba ki gaya min yanzu waye gwanin ba,tunda kin rabu da Sudais."
Harara Maryama ta zuba mata tana fa
ɗ
in "Ko kuma sai ke ba,wai TAIMIYYAH ba za ki
fito da miji mu aurar da ke ba,duk irin samarin da ke tare ki a hanya,ba ki sauraransu kar dai kice har yanzu baki kula kowa?"
"Bana kula su
ɗ
in
,kuma
ban jin zan ma fara kula sun ba,samarin da ke tare ka a titi dama na arziƙi ne Maryam? Ai duk me son ka
ya biyoka gidan ubanka ne ya gabatar da kansa
,ke
ni fa babu wani maganan aure a lassafina,inba gurgu iri na zan samu ba babu wani Namijin da zai ce yana so na in yarda da shi,ku dai lafiyayyu wanda ba ku da Nakasan da za'a goranta muku don Allah kuyi ku fi
to da Mazajen mu sha biki."
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana dariyan hararan da Maryam ke faman zabga mata
,kafin
Maryam
ɗ
in ta furta "Okey! Za ki ja da ikon Allah kenan?Don ya jarabceki a hakan shine zaki ce ke ce za ki za
ɓ
i abinda zai dace da ke ba shi zai
miki za
ɓ
in abinda yafi dacewa bako?Kina bani mamaki TAIMIYYAH don wa
ɗ
ancan shashashan suna miki gori shine ki ke ganin kowa ma goranta miki zaiyi?To bari ki ji tun wuri ki cire wannan shirmen a ranki,Allah na tuba ke har wani Nakasa ma ki kai,ga guragu na
n da ko tafiya ba sa yi sun kuma yi aure sun haihu.Kuma duk acikin wanda na sani kar ki
ɗ
auka guragu suka aura,wallahi lafiyayyun maza suka aura don haka kar ki ja da Allah,ke dai ki bar masa za
ɓ
i shi ka
ɗ
ai yasan wanda zai za
ɓ
a miki in lokaci yayi,mu dai k
awai muyi addu'a Allah yai mana za
ɓ
i mafi alkhairy,Ke
ɗ
in ma da akaiwa baiwan da mu masu ƙafafun qalau ma bamu sama ba,ko a kyawunki da cikar halitta aka tsaya TAIMIYYAH ke
ɗ
in matar manya ce sosai a hakan wallahi,bare azo
ɓ
angaren karatu wannan Brain
ɗ
in
naki ba dama ne,wallahi ki godewa Allah."
Maryam ta ƙare maganan idanunta akan TAIMIYYAH da ke sakin murmushi
,kafin
TAIMIYYAN ta amsa da"Nagode masa Maryama ina kuma ƙara gode masa,Allah yai mana za
ɓ
i ni bawai ina ja da Allah bane,bazaki gane me nake ji b
ane araina a duk sanda aka min gori ko aka kirani da kalmar gurguwa,amma bakomi a rufe wannan babin a
ɗ
akko wani kawai."
Yadda tayi maganan cikin wani narke murya
,yasa
Maryama dubanta wani abu na motsa zuciyanta,tana mamakin yadda TAIMIYYAH ta iya shagwa
ɓ
a me motsa zuciyan har mata ƴan uwanta,bare kuma namiji idan tana masa wannan narkewan ai tuni zata gama da shi,ta murmusa tana duban TAIMIYYAN cikin ido take fa
ɗ
in "Na ji an bari gimbiyar Yah Deeku wai ina kuka kwana ne ko auren Zumuncin za'ai ne?"
Marya
ma ta tsokani TAIMIYYAH tana sakin dariyan ta
ɓ
ara,sabida sun san da labarin Son da Yah Sadeeq
ɗ
in ke wa TAIMIYYAN,da irin tsanan da su Zuhurah sukai mata,don zuwan Maryam na farko gidan a gaban idonta Zuhura taci fuskan TAIMIYYAH,wani harara TAIMIYYAH ta w
atsa mata kafin ta sanar da ita duk yadda suka kwashe da shi,da umurnin da Baba Sani yai musu akan fito da miji,ta ƙare maganan tana cewa "Ni kin ga Maryam tunda ba wani nake kulawa ba wallahi nafi so abar ni nayi karatu na."
Maryam ta ta
ɓ
e baki tana fa
ɗ
i
n "Ke
dai
kika sani idan Allah ya kawo mijin nan kusa sai mu gani ko zaki hana mu sha bikin."
TAIMIYYAH ta saki dariya tana ta
ɓ
e baki itama take fa
ɗ
in "Oho dai ni dai barni da karanta littafan Soyayyan muna course,wallahi kuma idan mutum yana karanta litt
afan sai yayi ta imagining ina ma kaine star
ɗ
in,ko baki jin hakan Tawan?"
TAIMIYYAH ta ƙare maganan tana sakin dariyan shaƙiyanci
,hakan
yasa Maryam itama sakin dariyan tana fa
ɗ
in "Munafuka mu je dai zuwa,dama irin ku masu gudun fa
ɗ
awa tarkon luv ai baku
iya kamuwa ba,idan lokaci yazo ni ina matuƙar son in ga wani me sa'an ne zai
ɗ
auke ki."
Itama tayi maganan cike da shaƙiyanci daga haka suka cigaba da hiransu suna baiwa juna nisha
ɗ
i,har zuwa lokacin da sukai Lunch,TAIMIYYAH na jin kaman kada Maryam ta t
afi,sai da Maryama tayi sallan la'asar sannan tayi shirin tafiya,TAIMIYYAH ta yo mata rakiya bayan Maryam
ɗ
in tayi ma Iya sallama,Iyan har da bada wani ha
ɗ
a
ɗɗ
en turare cikin wanda su Abie ke yawan kawo mata tsaraban su idan yayi tafiya ko yai mata siyayya
a manyan wajeje,sosai Maryama tayi godia TAIMIYYAH ta rako ta har bakin gate,suna cigaba da hiran da bai ƙarewa indai an ha
ɗ
u har a rabu baki bai iya shiru,sallama sukai da Maryam
ɗ
in TAIMIYYAH na bata tabbacin zata je gidan nasu insha Allah,sai dai kawai
taji ta kirata tace gata nan,lokacin da Maryam
ɗ
in ta fara takawa don barin layin,sai TAIMIYYAH ta juyo tana takawa don komawa cikin gida,zuciyanta fes da jin da
ɗ
in ziyaran da qawar nata ta kawo mata.
________
Tunda suka fito daga gida gabanta ke cigaba d
a fa
ɗ
uwa,ta kai dubanta kan A.Maleek
ɗ
in wanda yake gefenta,ya bala'in ha
ɗ
e face yana faman danna wayansa,sai ta sake manne masa tana me
ɗ
aura kanta bisa kafa
ɗ
ansa,abinda ya janyo hankalinsa har ya
ɗ
ago daga latsa wayan nasa yana sauke manyan idanunsa akan
ta,yana son jin tausayinta amma yana hana kansa hakan,don yana lura tun safe da ya tabbatar mata zasu je wajen wani Babban likitan mata,take faman kuka amma sai bai nuna damuwansa akan kukan nata ba,ya
ɗ
auke kai a yanzu
ɗ
in ma yana sake mayar da hankalinsa
akan Chart da yake da wani manager
ɗ
insa me kula masa da harkan gidajen gonansa dake Kaduna,Yusuf Driver
ɗ
insa ne ke tuƙa su shi da Suhailah suna baya,har suka iso gidan Doctor Saiff Suhailah bata da wani nutsuwa,kallo
ɗ
aya zakaiwa face
ɗ
inta kasan a ru
ɗ
e
take,waya Maleek Ado ya
ɗ
aga ya shiga kiran layin Dr.Saiff
ɗ
in,bugu biyu ya
ɗ
aga Maleek
ɗ
in ya furta "Ga mu daga bakin gate
ɗ
in mun iso."
Ko mintu biyu baiyi da sauke wayan daga kunni ba
,megadin
gidan ya bu
ɗ
e musu gate suka danna hancin motan ciki,daga c
an tsaye suka hangi Doctor Saiff
ɗ
in yana jiran shigowansu,ya nufo motan cikin sauri yana kai hannu ya ƙarisa bu
ɗ
ewa Maleek murfin motan,yana fa
ɗ
in "Ran Chairman ya da
ɗ
e,barka da ƙarisowa Bismillah mu shiga daga ciki."
A.Maleek ya miƙama Dr.Saiff hannu su
kai musabaha
,dai
-dai lokacin da Suhailah ta fito,Dr.Saiff ya dubeta yana fa
ɗ
in "Ran Madam ya da
ɗ
e Bismillah mu je daga ciki." Daga haka yai musu jagora zuwa babban falon gidan nasa,ya
ɗ
aga waya yai kiran matansa me suna Sumayyah ta fito,cikin sakin fuska t
akewa Suhailah barka da zuwa don ya sanar mata da zuwan su,ta risina ka
ɗ
an tana gaida A.Maleek ya amsa a taƙaice lokacin da yake zama cikin kujera,daga haka ta janye Suhailah zuwa
ɗ
aya falon,tana komawa ta ha
ɗ
o lemu da ruwa ta kawo mata,suka sake gaisawa c
ikin rashin sabo da sanin juna,shiyasa daga gaisuwan sai shiru ya ratsa,bada jimawa ba sai wayan Sumayyan ya sake
ɗ
aukan ki
ɗ
a,ta
ɗ
aga wayan tare da yin shiru kafin ta furta "Okey tuh." Ta sauke wayan tana duban Suhailah da sam bata da walwala ta sanar mata
Daktan na jiran ta a falon da suka baro,cikin mutuwan jiki Suhailah ta nufi falon,tana samun kusa da Maleek
ɗ
in ta zauna,tambayoyi Doctor Saiff yai mata ta sanar dashi komi tun daga lokacin da ta fara shan Pills na planing
ɗ
in har zuwa lokacin da ta dain
a,shekara
ɗ
aya kenan ya tsura mata ido kawai yana jinjina hauka da shirme irin na wasu matan,don shi baisan wani irin wauta ne zai kai mace fara yin planing alhali bata ta
ɓ
a ko haihuwan fari ba,sai dai laifinta ka
ɗ
an ya gani akan na daƙiƙin likitan da ya b
ata go ahead
ɗ
in fara tafka kuskuren da tayin,ya kai dubansa kan Maleek Ibrahim Ado wanda ya
ɗ
auke kai tamkar baisan me suke tattaunawa ba,sai