Showing 1 words to 3000 words out of 40241 words

Chapter 1 - NI DA MUNEEB

Start ads

11 Sep 2025

53

Middle Ads


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 1*


~Karfe ɗaya da rabi na dare a lokacin da kowa yake bacci cikin garin melang a daidai wannan lokacin suke tsaye cikin tashin hankali, da kaga fuskokinsu zaka san ba karamin tashin hankali suke ciki ba, maza ne su uku samarai, kowannensu yana safa da marwa cikin rashin sanin abinyi, kyawawa ne ajin karshe farare ne sal kamar ka taɓasu jini ya fito, saide wanda yake tsaye ya jingina bayanshi da jikin kofa da alama shine karaminsu ya fisu fari sabida shi ya zama yellow, gashin kansu idan ka gani kamar na larabawa, jikinsu kuma kana gani kaga gidan da suke ciki zaka san ba karamin daula suke ciki ba, ɗaya daga cikinsu ya kallesu yace "yanzu ya zamuyi? mu kira babban yaya?"
shiru sukayi domin duk suna tsoron kiran babban yaya a wannan lokacin, yace "AZAD ya kamata ka kirashi ka sanar dashi halin da ake ciki kaga kaine karami yafi jin tausayinka kuma yafi sonka"
shiru wanda aka kira da Azad ɗin yayi, sai kuma ya kalli na gefenshi yace "JABEER kai ka kirashi mana"
jabeer ɗin yayi shiru yana kallonshi sai kuma ya kalli wanda yake goge zufan goshinshi yace "SAMEER kai ka kirashi mana"
da sauri ya girgiza kai yace "no no I can't kaide ka kirashi"
musu suka fara tsakaninsu kowa yana cewa saide ɗan uwanshi ya kira, tarin da sukaji daga sama yasa suka kalli saman dukansu, har rige rige suke wajen hawa upstair, ɗakin da suka ji tarin suka nufa Azad ne yayi saurin zuwa ya hau makeken gadon dake ɗakin, yaye blanket ɗin yayi duk suka yo kan kyakkyawar dake kwance akan gadon, tana kama dasu sosai farace sal, a hankali ta buɗe manyan idanunta wanda suke a lumshe murmushi tayi musu ganin yadda suke cikin damuwa sabida ciwonta, ta mika musu hanunta, atare suka ɗaura hannayensu akan nata, cikin zafin ciwo tace "baby Azad ka daina kuka, banson ganin ɗan autanmu yana kuka kaji?"
baima san yana hawaye ba, a hankali ya share hawayen ya sunkuyar da kanshi, buɗe baki tayi zatayi magana tari ta fara sosai, hanunta dake cikin nasu ta damƙe, waro ido sukayi a tare ganin ta suma, jabeer wanda ke tsaye baisan time ɗin daya fara bubbugata yana cewa "unty BATOOL ki buɗe ido, unty batool karki rufe ido kinji? zamu kaiki asibiti yanzu"
kokarin buɗe idon take sabida kada hankalinsu ya tashi sosai, saide ta kasa ciwon ya tsananta, sameer bai san time ɗin daya fita da gudu ba, ɗakinsu ya shiga da gudu ya hau makeken gadonsu na alfarma ya ɗau wayarshi dake saman gadon, numbern da yayi saving da babban yaya ya kira, kusan sau uku kafin aka ɗauka, cikin tashin hankali yace "ya MUNEEB jikin unty batool ya tashi, ya muneeb kazo da sauri zata mutu"
wurgar da wayar yayi ya koma ɗakin bai jira amsan muneeb ɗin ba, yana shiga yaga jabeer yana sawa unty batool kaya, taimaka mishi sukayi yasa mata riga dogo, bai tsaya sa mata hula ba kawai ya kame tulin gashin ya ɗaure sabida babu lokacin kitso, ɗagata yayi sama ya fita da ita, su Azad suna binsu a baya, dukansu basu ma kula da kayan bacci bane a jikinsu, sauka yake da ita akan stir suna biye dasu da gudu domin kaita asibiti, turo kofan akayi gaba ɗaya suka zuba mishi ido, sanye yake da jallabiya yayi bala'in kyau da fuskanshi wanda kana gani kasan daga bacci ya tashi, yana kama sosai dasu amma ya fisu kyau nesa ba kusa ba, sannan ya fisu yawan gashi, gashinshi kamar na mata domin baya aski, sai gyara yake yiwa gashin, wani lokaci har kitsawa yake, da gudu ya hauro stir ɗin ya karɓeta daga hanun jabeer sannan ya fita suka bishi a baya, babban compound na gidan ya nufa, gidan kamar rana tsabar hasken glove daya ƙayata kamar a saudiya, motocin dake compound ɗin sunfi goma zafafa masu tsada, tsadadden mota kiran g-wagon ya nufa, suka buɗe mishi ya shiga da ita ya kwantar da ita a ciki kafin ya shiga, duk suka shiga suma bai hanasu ba yayi hon gateman ya buɗe musu, security na gidan dama idan zasu fita suna binsu a baya hakan yasa suka ɗauki motoci biyar suka bisu a baya, wani irin gudu yake da motar kamar zai tashi sama, Allah ne ya kaisu asibitin lafiya, kerarren hospital ne ana ganin motocin gidansu ne aka buɗe musu gate da gudu ya shiga bai tsaya parking me kyau ba ya fito, ɗaukanta yayi keken da ake ɗaura marasa lafiya likitoci suka fito dashi da sauri sabida sanin waɗanda suka shigo hospital ɗin, sun saba zuwa kuma sun san ciwon dake damunta hakan yasa direct suka fara turata zuwa ɗakin kula da marasa lafiya, gaba ɗaya hanunsu akan keken ciki harda babban yaya, time da za'a shiga da ita ɗakin likitocin suka dakatar dasu, shiga akayi da ita suka tsaya a bakin kofan, Azad ya jingina kanshi jikin kofan shi kuma babban yaya ya fara safa da marwa, jabeer kam kasa tsayuwan yayi waje ya samu a gefen ɗakin ya zauna yayi tagumi, sameer ma yana tsaye ya jingina da jikin bangon ɗakin, kana ganinsu ba sai an faɗa maka ba zaka san waɗannan suna cikin gagarumin damuwa, sun jima sosai a ciki kafin suka fito, har rige rige suke wajen tambayan dr ya ake ciki?
ya gyara siririn glasses na idonshi sannan yace "Alhmdllh munyi nasaran lafar da ciwon, amma kamar kullum yauma magana ɗaya ne lafawa ciwonta yayi ba sauki ba, gaskiya yayarku batool tana shan wahala ban taɓa ganin wacce take da juriya kamar yayarku ba, amma ciwon yana cin jikinta ina tsoron kada ta rasa....."
muneeb ne yayi saurin rufe mishi baki, girgiza mishi kai yayi cikin zafin rai da rashin dariya daya saba bale ya haɗu da wannan ciwon da yake samun yayarshi yace "ka...ka...ka... iya bakinka...ba...ba...ba abinda zai sameta....yayata ba...abinda zai...zai..zai...zai..zai"
marin fuskanshi yayi cikin tsananin in inan da yake yi yace "ba......ba..."
kara marin kanshi zaiyi jabeer yayi karfin halin rike hanun, kallonshi yayi da manyan idanunshi da suka rikiɗe suka koma jajur, jabeer yace "ya muneeb bafa kai ka ɗaurawa kanka rashin magana me kyau ba, Allah ne ya yika me stammering babu yadda zakayi saide kayi hakuri ba wai ka hukunta kanka ba"
shiru yayi a hankali ya zame hanunshi ya kalli dr wanda yake kallonsu da tsananin tausayin MAKAWA FAMILY duk inda ake maganan arziki to idan an ambaci makawa's tofa anzo karshe, duk abinda ake mallaka na more rayuwan duniya to familyn makawa sun mallaka kyau, kuɗi, ilimi, suna, duk suna dashi saide abu ɗaya suka rasa shine farin ciki, a kullum cikin damuwa suke sabida rashin lafiyan yayarsu wacce sukafi sonta fiye da komai na duniya, a cikinsu da akwai wanda za'a iya mayar da ciwonta kanshi tabbas da sun daɗe da karɓe mata ciwon, duk wani kasa da akace ana samun maganin ciwonta sunje amma basu dace ba, hakan yasa babban yaya yasa aka gina asibiti ya ɗibo kwararrun likitoci sabida su rinƙa kula da ita a lokacin da ciwonta ya tashi.

Dr yace "zaku iya shiga sabida tana ta kiran sunanku"
atare suka shiga muneeb yaja stool ya zauna kusa da ita ya zubawa fuskanta ido, tana tsananin kama da mahaifiyarsu a duk lokacin da yaga fuskanta babu wacce yake gani sai Amminsu wanda a yanzu bata raye, batool itace take kula dasu itace ta zama musu mahaifiya, tunda Amminsu ta rasu itace take kula dasu, tun Azad yana karami itace take kula dashi, Azad baisan Ammi ba ya girma ne kawai ya ganshi tare da batool wacce kullum suke tare, ada yana gaya mata mama batool amma da yayi wayo suka sanar dashi mutuwa Amminsu tayi shine ya fara kiranta unty batool, tunda Ammi ta rasu basu taɓa kewanta ba sabida batool tana tare dasu, kwatsam ciwo ya sameta wanda aka rasa gane takamaiman ciwon na menene wasu suce ciwon sugar wasu suce hawan jini wasu suce ciwon hanta, babu irin ciwon da ba'a faɗa musu, saida suka fita kasar India kafin suka gane cancer na ciki ke damunta, a ranan data fara jinya muneeb duk da karfin halinshi saida ya rufe kanshi a ɗaki yayi ta kuka, da za'ace kuɗi yana siyo lafiya babu abinda zai hanashi siya mata lafiya koda na biliyan nawa ne, saita zama itace mace mafi lafiya a duniya, saide kuɗinsu ya kasa sama mata lafiya, cikin karfin hali ya ɗago kai yana kallon kannenshi da suke zaune jugum kowanne yayi shiru, ba kamar da lokacin da take da lafiya zakaje gidansu ka tarar suna hira cikin nishaɗi musamman Azad zaka tarar suna game, sameer da jabeer sunyi karatu a kasar Cyprus shiyasa Azad ya fisu tsananin shaƙuwa da ita, hararansu yayi kana cikin in inanshi yace "tun...tun...tunda yaushe ya tashi mata?"
rarraba ido suka fara a tsorace suna kallon juna sabida kada suyi karya ya ganosu, idan bakinsu baizo ɗaya ba sun san halinshi sun san me zai biyo baya, tsawa ya daka musu yace "yaushe nace?"
Azad yana murza yatsa yace "tunda karfe sha...."
sameer yayi saurin cewa "da minti sha biyu"
cikin rashin dariyan daya zame mishi ɗabi'a yace "ka..kak..kakkarfe nawa?"
yace "karfe ɗaya da minti sha biyu"
karewa sameer ɗin kallo yayi ganin yana kallon jabeer alaman duk suce karfe ɗaya, zaiyi magana batool ta buɗe ido a hankali tace "muneeb..."
juyowa yayi da sauri ya rike hanunta yana murzawa yace "kin tashi? ya jikinki? ya yake miki yanzu?"
a hankali ta gyaɗa kai cikin sanyin murya irin na marasa lafiya tace "da sauƙi muneeb"
kallon Azad tayi sannan tayi mishi alaman yazo, a hankali yazo ya tsaya a gabanta ya sunkuyar da kanshi, kare mishi kallo take hawaye yana cika mata idanu, sam batason abinda zai rabata da kannenta batason wannan ciwon amma Allah ya ɗaura mata, murmushi tayi sannan ta rike hanunshi tace "baby Azad kaine karami kaine kullum nake yawan yimaka nasiha, duk da nasan ko bana nan yayunka zasu kula da kai, amma nasan duk kulawan da zasu baka ba zai taɓa kai wanda zan baka ba, domin akwai banbanci tsakanin kulawan mace dana maza, abinda nakeso da kai shine ka zama me hakuri kabi yayunka sahu da kafa domin yanzu sune iyayenka, wannan ciwon nawa nasan bana tashi bane, sameer da jabeer ku kula da kaninku sosai ku bashi kulawa wannan amana nake baku shi kamar yadda Ammi ta bani amananshi kuma ina baku amana, sannan muneeb ban cireka ba duk da bakada lokaci kullum kana cikin aiki amma kada hakan yasa ka mance da amanan kannenka"
shiru sukayi duk cikinsu babu wanda baya hawaye, a kullum idan ciwonta ya tashi saita rinƙa musu nasiha tace su kula da kaninsu ganin tana son Azad sosai yasa suke sonshi suma kamar su haɗeshi, basa son abinda zai taɓa Azad ko rashin lafiya yake sai suma sun zama kamar marasa lafiya, ganin suna hawaye ta juyar da kanta ta yadda ba zata kallesu ba, tace "ku rinƙa sani a addu'a idan na mutu kada ku manta dani, karku manta da ammi ku rinƙa mata addu'a dan Allah"
security ne zagaye da Asibitin basu bari a shiga kuma wasu bari a fita hakan yasa sukayi niyan kwana a asibitin dan sun san a tsare suke, musamman shi muneeb yafi samun kwanciyar hankali ne idan yana tare da masu tsaronshi.

Kauyen sangu shine karamin kauyen da fulani suke zama, anan sukayi bukkokinsu sannan sukayi ruga, kowane ɗan kauyen yanada shanayensa da yake kiwo, kowane akwai ruga da yake dashi hakan yasa kansu yake a haɗe suka ɗauki kansu kamar ƴan uwa, saide duk mutuncin da yake tsakaninka da mutum idan ka taɓa mishi shanu zaku iya rabuwa, kyakkyawar yarinyar ce bafulatana ta fito ɗaure da nono a kanta, kayan fulanin dake jikinta fari ne tayi ado a fuskanta ta kitse gashinta me yawan gaske ta barshi a bayanta babu ɗankwali a kanta sai kundura da tasa a kafarta, kana ganinta kaga asalin bafulatana ga wani murmushi da yake kan fuskanta wanda yake kara mata kyau, cikin ɗaga murya tayi magana da hausanta wanda baya fita sosai tace "inna na tafi"
daga cikin gidan aka amsa da "Allah waddu lumo"
tace "ameen inna"
tafiya ta fara a hankali take tafiya cikin natsuwa, daga nan zuwa inda take saida nono yanada nisa hakan yasa ta ɗan ɗaga kafa domin kada tayi late, can cikin gari inda mutane suke zuwa siyan kayan miya ta samu gefe ta aje nonon ta zauna akan wani dutse tayi shiru tana kallon mutanen dake wajen, kowa yana harkanshi, ƴammatan dake wajen suma suna saida nono tsaki suka fara ja kowacce tana aika mata harara, bata kulasu ba, da haka har aka fara zuwa siyan nono, abin mamaki wajenta kawai ake zuwa su kuma babu me kulasu, tsaki sukeja cike da tsana da jin haushinta, ɗaya daga cikinsu ta kasa daurewa ta tashi cikin masifa tace "ke AMEERA bafa tsoronki mukeji ba da zaki rinƙa zuwa kullum kina hana mana kasuwa ba ki gaggauta tashi anan kafin na ɓarar da nonon"
a hankali tace "safiya am me nayi miki? saida nono fa kawai nake kinga da nazo ma ban muku magana ba sabida bakwa amsa gaisuwana kuma ku ƴan uwana ne...."
a tsawace tace "dakata babu ƴar uwarki anan, karki kara kiranmu da ƴan uwanki, yadda kike muguwa mara imani ki kwace mana samarai sannan ki kara kwace mana sana'a shine zaki ce mu ƴan uwanki? muguwa me kyawun ɗan maciji sai kyau amma babu tausayi"
shiru tayi ganin ta hau, saida ta gama tace "kiyi hakuri safiya ki kawo nonon naki zan siyar miki..."
"ki siyarmin? tunda nice uwar bakin jini ba zan iya saidawa ba sai kin sa hanu? to kafin na fara cin ubanki anan ki tashi"
zatayi magana ɗayan dake gefe tace "ba zaki tashi bane?"
a hankali tace "indo bafa nice..."
a fusace ta tashi tace "idan baki tashi ba wallahi zamu ɓarar da nonon"
sum sum ta tashi cikin tsoro ta ɗau nonon ta ɗaura a kanta, gefe dasu can taje zata zauna sukace ta bar wajen duka, a hankali ta ɗau nonon ta tafi gida, a hanya tana share hawaye har ta isa rugansu, tana shiga inna wacce take zaune akan tabarma tana dama fura tace "lafiya ameera?"
ajewa tayi tana hawaye tace "sun koreni wai kada na kara zuwa wajen"
inna ta kare mata kallo kafin tace "wai ameera yaushe zaki daina tsoro? yaushe zaki zaka mara tsoro ne ameera?"
kanta kasa tace "kiyi hakuri...."
da wani irin gudu ta shigo gidan tayi wurgi da sandan kiwon dake hanunta ta wurgar da goran ruwan, inna da ameera sun tashi da gudu suma suka shige ɗaki, zanin data ɗaura na dark blue ɗin kayan fulani dake jikinta me ado me tsananin kyau ta ɗaga, fararen cinyoyinta da suke sheƙi kamar wacce take skin care routine suka bayyana, babu ɗankwali a kanta saide gashinta da aka kitse mata guda biyu sun sauko har zuwa hips nata, wani irin tsantsi gashinta ke dashi gashi baƙi ƙirin, da gudu ta shiga banɗaki ta fara fitsari, saida ta gama ta ɗaga murya cikin gurɓataccen hausanta wanda har yafi na yayarta tace "Adda meera kawomin buta mana dan Allah zanyi tsarki"
subhanallah wani irin zazzaƙan murya Allah ya bata, ga wani wutar kyau da take

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login