Showing 3001 words to 6000 words out of 40241 words
dashi me ɗaukan ido, duk da ameera kyakkyawa ce ajin karshe wannan ta fita domin idanunta sunada girma sosai gasu da shape ɗin kwai, tasa kwalli hakan yasa kara fito da kalan madara, kyakkyawan fuskanta ɗauke yake da kwalliyan fulani wanda ya bala'in yi mata kyau, tsayawa na rubuta kyawun wannan yarinyar ɓata lokaci ne, ajiyan zuciya inna da ameera suka sauke a tare, inna cikin jin haushin ta koma ta zauna, ita kuma ameera ta ɗau buta ta zuba ruwa sannan ta kai mata, karɓa tayi tace "yawwa adda meera Allah baki miji na gari me hankali kamar ke"
a takaice tace "a banɗaki kike ki daina kiran sunan Allah"
da sauri ta mari bakinta tace "kumafa hakane na daina"
saida tayi tsarki sannan ta fito tane kwance zanin gaba ɗaya, yarwa tayi a kasa sai underwear ne a jikinta, zama tayi tana haƙi kamar wacce tayi gudun shekara ɗaya, inna ta harareta tace "yanzu NAJWAH kin kyauta? kin shigo gida da gudu babu sallama kinsa mun tsorata mun gudu hakan ya miki?"
dariya tayi sosai tace "wallahi inna keda adda ameera kunada tsoro, miye abin gudu dan kunga na shigo da gudu? to ai fitsari ne ya matseni shiyasa na shigo a guje"
Ameera dake tsaye tana kallonta tace "ina shanayen?"
taɓe baki tayi kana tace "gasu can na barsu idan sunga dama su karaso da kansu idan sunga dama su kwana a wajen sune sauro zai ciza bani ba"
dafa kai ameera tayi tace "najwa ki rinƙa sanin kin girma mana, meyasa zaki bar shanaye acan bayan kin san halin baba, najwa sai yaushe zakiyi hankali?"
turo karamin bakinta tayi tace "nifa na gaji, kullum kiwo ko tallan nono bamuda lokacin hutu?"
sandan kawai ta durkusa ta ɗauka sannan tace "to kiyi hakuri yanzu tashi muje mu dawo dasu inda suke kwana kinji ƴar kanwata?"
a hankali ta tashi tace "naji"
zanin ta ɗaura bata damu daya ɗauru ko baiyi ba suka fita, can cikin daji ta bar shanun hakan yasa ameera ta fara korosu gida suna tafiya tare, wani saurayi sanye shima da kayan kiwo yazo wucewa da shanunshi, da gangan ya korosu ta wajen nasu ameera ganin ya tare musu hanya ameera ta fara kokarin canja musu hanya, kara tare gabansu yayi da nashi, ameera ta ɗan ɗaga murya kaɗan tace "dikko ka tare mana hanya ka ɗan kora shanayenku mu wuce"
rike sandan yayi yana karkaɗa kafa yana kallonsu, ta kara magana yace "ba zanyi ba"
cikin fusata najwa tace "ka janyesu kafin ranka ya ɓaci"
yace "ke kin isa ki ɓatamin rai? keda kikace bakya son kowane saurayi a wannan rugan shine zaki zauna lafiya?"
Ameera ce taje ta gaba zata fara kora shanayensu taji saukan mari, da sauri ta kalleshi a tsorace tace "me nayi maka dikko?"
Najwah gyara ɗaurin zaninta tayi ta ɗaureshi gam, sandan dake hanun meera ta gani a kasa ɗauka tayi, ya ɗaga hanu zai kara mata wani marin yaji saukan sanda a hannunshi, a firgice ameera ta kalli najwa dake kwala mishi sandan, kwacewa yayi suka fara dambe dashi, najwa karfin da take dashi duk ƴammatan garin tsoron dambe suke da ita domin idan ta rike mutum dukan mutuwa take mishi, da maza kaɗai take dambe, ameera janyeta take tana cewa "ki bari najwah kada baba yaji, najwa ki kyaleshi kiyi hakuri"
cikin zafin rai tace "cikani adda meera saide koni koshi yau ɗinnan ɗaya saiya cirewa ɗaya raini"
cikin mamakin karfinta yake kallonta da kyar ameera ta jata ta riketa har gida ta kaita kafin ta dawo ta kora shanun ta kaisu inda suke kwana, shigowa tayi ta zubawa najwah wacce take zaune har yanzu tana huci ido, a hankali taje bakin tanda ta ɗibo mata ruwansu wanda baya rabuwa da sanyi, zuwa tayi ta zauna a gefenta tace "gashi sha"
a hankali ta girgiza kai, matsalanta bata hucewa da wuri idan ranta ya ɓaci, kai ruwan tayi wajen bakinta tace "kisha sabida ni"
a hankali ta buɗe baki tana sha, murmushi ameera tayi sabida tasan najwa babu abinda take so a duniya kamar ita, duk abinda takeso yana bayan ameera hakan yasa itama ameera take santa sosai, hanunta ta rike cikin sanyin murya tace "najwa a kullum ina miki nasiha ki zama me hakuri, kinga duk wannan kauyen babu wacce ta kaiki kyau, kece kyakkyawar wannan rugan, sannan babu wacce ta kaiki iya kiwo, gashi kece kike tatsar nono fiye da kowace anan rugan, shiyasa suke jin haushinki, abu ɗaya kika rasa shine hakuri, najwa baki da hakuri, najwa bakida yafiya, najwah kinada riko baki mance abu da wuri, dan Allah najwah ki daina wannan halin tun ina tare dake, najwah baki san inda zaki kare rayuwarki ba, ban sani ba ko zamu kare rayuwarmu a tare ko watarana zamu rabu, nice kaɗai nake iya baki hakuri ki hakura idan bana nan ya zai kasance? dan Allah ki koyi hakuri koda kaɗan ne kinji kanwata?"
tace "naji"
murmushi tayi taja kumatunta tace "boɗɗi ta kiyi murmushi to"
a hankali tayi kayataccen murmushi, banƙo kofar gidan akayi cikin ɗaga murya tun daga bakin kofa ya fara kiran "mairam? mairam? mairama?"
inna dake kitchen tana musu abincin dare taji muryan baba tun daga bakin kofa yana kwala mata kira, fitowa tayi jikinta yana rawa tace "na'am"
wurgar da ledan hanunshi yayi kana yace "kizo nan"
zuwa tayi ta durkusa a gabanshi tace "gani"
da yatsa ya nunata yace "sau nawa nake cemiki ki gargaɗi yarannan?"
tace "sau dayawa"
yace "me yasa baki gargaɗesu ba? meyasa kullum kike bari suna faɗa da mazan gari? gashi tsabar baƙin jininsu har yau sun gagara aure yara suna can suna aure wasu harda yara amma su suna nan da jininsu irin naki sun kasa samun miji suyi aure sai kyau da suke takama dashi za'aci kyawu ne?"
tayi shiru kanta a kasa, yace "za'aci kyawu?"
bata amsa ba sabida tasan idan ta bashi amsa a yanzu zaice ta rainashi yana magana tana magana, wani irin ball yayi da ita, faɗuwa kasa tayi, ya taka ruwan cikinta yace "ba zaki bani amsa ba?"
tana girgiza kai cikin azaban cikinta daya taka tace "A,ah"
kafan ya ɗaga zai kara takata najwah ta mike a fusace zataje inda yake, hanunta ameera ta rike tace "duk abinda zakiyi ki tuna shi ya haifemu"
cikin ɗacin rai da tsananin tsananshi tace "sabida shiya haifemu saimu bari ya kasheta?"
fizge hanunta tayi taje da gudu ta rike kafanta, janyo inna tayi ta rungumeta, ganin haka ya zaro itacen dake gefenshi ya fara dukan inna, najwah rungumeta tayi itacen yana sauka a bayanta, tana runtse ido amma duk yadda za'ayi bata bari ya samu inna, ameera kuma ta rakuɓe a gefe cikin tsoronta tana kuka tana kallonsu har ya gaji ya wurgar da itacen ya ɗau ledan dake cike da tsire ya shiga ɗaki, a hankali najwah ta zame inna daga jikinta tayi shiru kawai ta tashi daga wajen, inna ta share hawaye cikin karfin hali tace "bari na gama muku abincin kunji?"
juya baya najwah tayi tana share hawaye, a kullum sai inna tasha tsinannen duk a wajen baba, tun suna kanana har izuwa yanzu da suka girma bai daina dukanta ba, tasha wahala fiye da yadda ake tsammani, ya wulakantata kuma yana kan wulakantata sabida yaga batada iyaye, iyayenta sun rasu kuma batada tsayayyun ƴan uwa, a hankali suka zauna kan tabarman sukayi shiru inda sabo sun saba amma kullum abin yana damunsu, ameerah ganin najwa tayi shiru ta matso kusa da ita, tace "kawo na kwance miki kanki na kara miki sabon kitso wannan ya fara tsufa"
shiru tayi har ta fara kwance mata kan, saida ta gama ta leƙo fuskanta tace "wani irin style kikeso?"
babu dariya akan fuskanta tace "kowanne"
jikin ameera a sanyaye ta fara mata kitson, bata son ganin najwa a wannan halin na rashin dariya, sabida a kullum najwa itace kawarta abokiyar hiranta, basa rabuwa ko wajen tallan nono watarana watarana ne najwa bata zuwa amma kullum suna tare.
*Jiddah Ce....✍️*
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 2*
~Suna zaune a asibiti babu wanda yayi bacci, duk suna ganin idan sun rufe ido zasu rasa yayarsu, gani suke zata mutu da zaran sun rufe idonsu, Azad ne ya fara gyangyaɗi domin baya jure wahala, kanshi ya ɗaura a kafaɗan jabeer ya rungumeshi zai fara bacci jabeer yace "kaga zaka fara ɗauramin nauyinka ko? zaka fara baccinka da baka tashi da wuri"
hamma yayi yace "ya jabeer please"
daga nan yaci gaba da baccin, ture kanshi jabeer yayi yace "ka matsa min, wannan cin da kake dashi shiyasa kake nauyi, jibi duk kafi kowa kiba anan"
tsaki yaja ya kalli unty batool dake kallonsu tana lumshe ido tana murmushi tashi yayi yaje inda take yace "unty batool ki ɗan matsa na kwanta a gafenki"
a hankali ta matsa mishi ya kwanta ya rungumeta, harara muneeb yake mishi amma ya rufe ido dan wallahi yana jin bacci, cikin mintuna kaɗan bacci ya ɗaukeshi, ido ta zuba mishi hawaye yana wanke mata fuska duk tafi jin tausayinshi shine karami duk da ya kai 20years amma tana tausayinshi sabida bai samu gatan mahaifiya ba, shafa kanshi tayi kana tayi mishi peck a goshi sannan ta juya itama ta rufe ido zata fara bacci, wayan dake aljihun jallabiyan muneeb ya fara ringing, da sauri ya ɗauka yana dubawa, tashi yayi ya fita suka bishi da kallo ciki harda unty batool data rufe ido, kallonta sameer yayi tayi mishi alama ya bishi, gyaɗa kai yayi sannan ya tashi cikin sanɗa yabi bayan muneeb, saida yayi nesa da kowa kafin ya amsa call ɗin, cikin kasa da murya ta yadda ba za'a jishi sosai ba yace "ka..ka...ka isa?"
sai kuma yayi shiru yana saurara, yace "to..to...ka karka kuskura a samu matsala, idan.. idan...idan aka samu matsala kafi kowa sanin abinda...zaiii.faru"
daga nan ya katse wayan ya juya yaga babu me kallonshi, sameer da sauri ya mannu da jikin bango har muneeb ya wuce ya koma ciki kafin shima ya fito, saida ya ɓata lokaci kafin ya koma ciki, kallonshi muneeb yayi kallon daga ina kake?
kanshi kasa yace "naje dubaka ne"
a fusace yace "ni yaro ne? zan..zan...ɓata ne?"
girgiza kai yayi yace "sorry"
tsaki yaja, duk sukayi shiru suna zaune har gari ya waye basu samu isasshen bacci ba, duk sukayi alwala a cikin masallacin asibitin sukayi salla, da Azad da sameer da jabeer tare suka shigo, ta tashi ta zauna tana ganinsu ta fara murmushi zama Azad yayi a gefenta ya rike hanunta yace "good morning unty batool"
tace "ya kake, baby Azad?"
yace "am fine ya jikin?"
tace "da sauki baby Azad"
sameer da yake hamma yace "good morning unty"
tace "ya kake?"
yace "fine"
jabeer ma ya gaisheta, tana amsawa sukaji sallaman muneeb kasa kasa, amsawa sukayi da basketa a hanunshi da katon flask a ciki, ajewa yayi da flask na tea yace "ga breakfast"
tun kafin suyi magana ya fita, Azad ne ya sauko ya janyo basket ɗin, plate ya jejjera a ciki guda huɗu ya cire sannan ya buɗe abincin, kamshi ne ya karaɗe ɗakin, jallof rice ne wanda yaji vegetables da pepper chicken, serving spoon ɗin ya ɗauko ya fara ya fara zubawa kowa, tashi yayi ya bawa sameer da jabeer nasu, shi kuma yasa nashi dana batool a plate ɗaya, bata ya fara a baki a hankali take ci badan tana jin daɗinshi ba sai dan bataso suga rashin samun saukinta, shima yana ci haka har suka gama, maida plate yayi a cikin basket ɗin, batool tace "ku kaini gida banason zaman asibiti"
duk suka amsa da "to"
riketa sukayi ba tareda sun tambayi Dr ba sabida dama basa zama a asibitin sosai, tana tsaye amma bata iya mikewa, tafiya take a hankali suka fita, security suna ganinsu suka buɗe musu mota shiga sukayi, suma duk masu gadinsu suka shiga motarsu tare suka fita daga hospital ɗin, hakan yasa asibitin ya zama free yanzu sabida family ɗin makawa sun tafi, koda suka isa gida ma riketa sameer da jabeer sukayi Azad kuma ya ɗauko basket ɗin yana binsu a baya, masu aiki suka zo da gudu cikin girmamawa suka karɓi basket ɗin daga hanunshi, a falo suka yada zango, ta kwanta akan sofa su kuma suka shiga ciki domin yin wanka, koda sukayi wanka fitowa sukayi Azad yayi kyau cikin gajeren wando da rigan armless, zama yayi ya kunna tv ya kamo tashan cartoon ya fara kallo, jabeer kuma ya kwanta shima sanye da kayan shan iska yana latsa waya, kallon sameer tayi sannan tayi mishi alaman yazo kusa da ita, tashi yayi ya koma kusa da ita, kasa da murya tayi tace "ya ake ciki?"
yace "gaskiya ban gano komai ba har yanzu, sabida yayi nesa kafin yayi wayan banji komai ba, a ankare yake gaskiya"
dafa goshi tayi tace "oh my god sameer tabbas akwai gagarumin abinda muneeb yake aikatawa kuma ina zargin ba abu me kyau bane, sameer aina muneeb yake samun waɗannan maƙudan kuɗin? iyayenmu masu kuɗi ne tun kafin su mutu to amma sameer munfi kowa sanin muneeb yanada kuɗin daya wuce misali kuma duk mun san ba'a wannan company yake samu ba, wallahi sameer na jima ina zargin muneeb anya ba tsa...."
rufe bakinta yayi yace "dan girman Allah unty batool karki furta wannan kalman, zuciyata ba zata jure jin wannan kalman akan babban yaya ba, eh nima na yadda akwai abinda yake yi a ɓoye amma inada tabbacin ba wannan mummunan abin bane"
ido ta zuba mishi na tsawon mintuna kafin tace "sameer ina tsoron wani abu yazo ya sameku bayan na mutu sameer ina tsoron muneeb wallahi ina tsoronshi"
shiru yayi kanshi kasa yace "unty batool addu'a zamu dage dashi babu abinda zai...."
turo kofan da akayi yasa yayi tsit bai kara ko tari ba, ita kuma batool ta rufe ido kamar me bacci, shigowa yayi fuska a murtuƙe sanye yake da farin shadda yayi bala'in kyau, ga wani kamshi da yake yi me daɗi, agogon rolex me tsadan ne ɗaure a hanunshi sannan yasa hula akan tulin gashinshi dake sheƙi kamar na mata, sajenshi a gyare idan ba magana yayi akaji harshenshi ba zaka rantse balarabe ne, idanunshi masu rikita mutum ya zubawa sameer sannan ya kalli Azad da jabeer wanda hankalinsu baya kanshi yayi gyaran murya, duk suka gyara zamansu suka nutsu, kallon batool yayi wacce ta buɗe ido yace "zan fita me zan kawo miki?"
murmushi tayi mishi sannan tace "koma me zaka kawomin Indai na halak ne Inaso"
ido ya zuba mata itama tasa idonta a nashi tana kallonshi, da sauri ya ɗauke kai kawai ya fita daga ɗakin, kallonta Azad yayi yace "unty batool meyasa kike yiwa babban yaya haka?"
shiru tayi bata bashi amsa ba, da alama shima jabeer baiji daɗi ba kawai yaci gaba da pressing wayarshi, tsadadden motarshi g-wagon fari dal ya shiga sannan ya kalli bodyguards nashi kosassu masu murɗaɗɗen jiki irin na ƴa wrestling, sai kuma yaga security's ɗinshi wanda suke sanye da baƙaƙen coat da hanu yayi musu alaman su shiga mota akwai inda zasu je, shiga motan sukayi yana zaune a baya aka buɗe gate nasu na alfarma, convoy sukayi har suka hau titi saida kowane mota ya tsaya suka wuce, haka dama kullum idan sunyi convoy to babu motan da zai kara wucewa sai motocin gidan makawa sun gama wucewa, sunyi tafiya me nisa kamar zasu bar garin wani daji suka shiga banda bishiyoyi babu abinda suke wucewa har suka isa tsakiyan dajin wani gida ɗaya a tsakar dajin me tsananin masifan kyau suka tsaya a kofan, buɗe mishi kofa akayi ya fito fuska ba annuri ya kalli security dake zagaye dashi yayi musu alaman su zagaye kofan da yatsu biyu kawai yayi musu alaman, shiga ciki yayi yasa bakin glasses a idonshi sannan yasa facemask ta yadda babu me iya ganeshi, masu aikin gidan duk suna sanye da uniform kala ɗaya pink na yadi ne riga da wando, maza ne yawanci masu aikin sai mata kaɗan basu da yawa, kana ganin matan zaka san suna cikin baƙar wahala domin duk fuskansu yayi baƙi ƙirin ga datti da suke fama dashi, suna ganinshi suka far durkusawa kasa basa tashi har sai ya wucesu, wani ɗaki ya nufa wanda yake nesa da gidan, tun daga bakin kofa yake jiyo kukan wasu kananan yara, toshe kunne yayi jikinshi ya fara rawa, jingina yayi da jikin bango sannan ya rufe ido yana so yayi relax kafin ya ɗan samu nutsuwa shiga ciki yayi ya ciro makulli a aljihunshi sannan ya buɗe kofan ɗakin da aka rufe harda chain, shiga yayi ya goya hannayenshi a baya, subhanallahi ƙananan yara ne a wajen suna ɗaɗɗaure da chain a hannayensu, wasu suna kwance a gefe kamar basa da rai, yunwa da alama yana ɗawainiya dasu, ga wani irin wari da ɗakin yake yi, kallonsu yake ta cikin glasses ɗin, wani yaro da ba zai wuce 12years ba yana kwance cikin wahala bakinshi ya bushe yana kuka yace "yaya dan Allah ka fitar damu daga nan, yaya kayi hakuri idan laifi mukayi maka ka yafe mana"
shiru yayi yana kallon yaron, sai kuma yayi murmushi ya ciro waya daga aljihu, cikin sanyin murya yace "ka..ka...kawo abinci"
katse wayan yayi, babu jimawa akayi knocking buɗewa yayi da kanshi, wani matashi wanda yake sa'a dashi dan ba zai wuce 31years ba ya shigo da wasu mata suma da uniform a jikinsu, hanunsu rike da manya manyan kulolin abinci suka shigo dashi suka aje a gabanshi, yayi musu alama da hanu, jikinsu yana rawa suka fara sa abincin akan plate, bawa yaran suka fara sannan yace "ru...ruwa fa"
jikin babban matar yana rawa ta tashi da sauri taje suka shigo da ruwan gora, fara bawa yaran sukayi kamar sunyi shekara basuci komai ba haka suke karɓan abincin wasu harda wanda ya zube a kasa suke ɗiba suna ci, saida ya tabbatar sun gama basu kafin ya juya zai tafi yaji an rike ƙafarshi, bai juyo ba kuma bai janye kafar ba, wata kyakkyawar yarinya ce fara sal tace "yaya nifa kaga banida lafiya kullum sai mamana ta bani magani amma yau kwana goma bansha ba kuma banje school ba, kuma abbana yace idan na girma zama doctor sabida nice kaɗai suka haifa, to yanzu ina nan yaya kenan ba