Showing 27001 words to 30000 words out of 40241 words
habibi school"
murmushi akan fuskanta har ta gama siyarwa cikin lokaci kaɗan ta koma gida, inna tana zaune akan tabarma tana jin rediyo, najwah tayi sallama ta shigo, inna bata amsa sallaman ba tace "Allah Allah Allah ka tsinewa wanda yake sace yara a garinnan, Allah ka tona mishi asiri a duk inda yake"
najwah zama tayi tace "inna ke dawa kike tsinuwa?"
tace "najwa kullum sai naji an sace yara dayawa, najwah abin yana tsayamin a rai"
jikinta a mace tace "gaskiya inna duk wanda yake sace yara ya kamata idan an kamashi babu wani maganan prison a kasheshi kawai domin ya cika mara imani"
sauke habibi tayi tace "sauko ɗana Allah ya tsareka da tsarewarshi"
inna tace "ameen amma ya naga yau kin dawo da wuri?"
murmushi tayi tace "inna kin san me?"
tace "a,a sai kin faɗa"
tace "gobe idan na dawo daga talla zan kai habibi school"
habib da magananshi baya fita sosai yace "mama zanje makaranta?"
tace "eh habibi kaima zaka fara zuwa kamar su hanif"
hanif yaron makotansu ne sunada mutunci akai akai suna shigowa gidansu, cikin jin daɗi ya fara tafiya yaje ya ɗauko roban wasanshi ya fara wasa, tace "inna yanzu ba a bakin kasuwa zan zauna ba a wani company zan rinƙa kai nono"
tace "to amma najwa ki kula da kanki kinga ban sanki da wani hali ba sai faɗa dan Allah ki zama me mutunci"
tace "insha Allah inna ba zanyi abinda zai zamowa habibi abin magana ba zan zama me kamun kai a duk inda naje"
tace "yawwa Allah miki albarka"
tace "ameen inna"
tun daga ranan ta zama me kawo nono a wajen, idan tasa sai me karɓa yazo ya karɓa mishi, tana ganinshi yana shiga kuma tana ganin fitanshi amma maganar fatar baki ɗaya bai taɓa shiga tsakaninsu ba, ita dai abinda ya kawota shi take yi, saide sunyi mugun sabo da masu aikin wajen.
da kanta taje ta yiwa habibi register a makaranta ya zama student, ta siya mishi uniform da lunchbox ta siya mishi karamin jaka, duk abinda ake bukata tayi, zaune yake akan cinyarta yana damunta da tambaya "mama to ina zansa ruwan idan ansa?"
cikin rashin son magana ta nuna mishi gefen basket ɗin tace "anan"
yace "to mama idan kuma ruwan ya zube fa?"
tace "sai ka cire ka rike"
yace "mama idan kuma..."
cikin gajiya tace "dan Allah habibi banson surutu zafi na damuna ga gajiya"
yace "kiyi hakuri mama"
murmushi tayi ta rungumeshi idan tayi magana kamar ranta a ɓace sai yace kiyi hakuri mama, hakan yana tuno mata da adda Ameera wacce ko ba laifinta bane idan abu ya faru saita rinƙa bada hakuri, da alama habibi ya biyota domin abu kaɗan sai yace ayi hakuri, ko shi da inna idan tayi mishi faɗa sai yace kiyi hakuri inna, har kofan gida aka kaisu, fitowa tayi ta goyashi ta shiga gidan bata kula mutanen unguwan sabida tana jin maganganu daga bakinsu na cewar cikin shege tayi ta haifi habibi, tana shiga ta kwanta a kasa tace "na gaji"
inna tace "sannu da gajiya"
tace "wallahi ɗauko habibi zai rinka gajiyar dani"
tace "to najwa me zai hana ni na rinƙa zuwa ina ɗaukanshi?"
tayi saurin cewa "no inna ba zan iya barin zuwa ɗaukoshi ba zan daure"
tace "Allah miki albarka"
"Ameen" ta amsa sannan ta tashi ta ɗibi abinci tazo tasa musu da habibin tare suka fara ci tana bashi a baki.
*Jiddah Ce....✍️*
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 9*
~Cikin sauri take tafiya ta ɗaura katon bahon da take kai nono company a ciki, hanunta rike dana habibb wanda yake sanye da uniform na makaranta, tace "habibi kullum ina faɗa maka karka kuskura wani ya kiraka kaje, idan an tashi daga makaranta ka zauna waje ɗaya inda na saba zuwa ɗaukanka karka canja waje kaji?"
cikin magananshi na yara yace "to mama"
tace "yawwa ɗan albarka idan ka girma zaka zama doctor ko kuma ka zama me tukin jirgi"
a bakin titi suka tsaya tana leka mashin taga har yanzu shiru babu mashin, yace "mama idan na zama me tuka jirgi zan kaiki makka, zan kula dake idan na girma"
murmushi tayi tace "habibi nasan zaka kula dani"
mashin ɗin daya tsaya ta faɗa mishi inda zai kaisu yace su shiga, shiga tayi ta aje nonon kafin ta ɗaga habib ta ɗaurashi a cinyarta, lunchbox nashi ta aje a kasa suka tafi, a kofan school nasu ya tsaya fitowa tayi saida ta tabbatar ya shiga ciki kafin ta shiga mashin suka nufi company, a kofa ya ajeta ta fito tana ɗauka wata me aiki a wajen sanye da uniform tazo da sauri zata tayata, tace "da kin bari zan iya"
gyara hijabin jikinta black me kyau tayi, me aikin tace "no bari zan tayaki"
murmushi tayi tace "to na gode"
shiga ciki sukayi yau tayi late sosai ba kaɗan ba sabida ta kai habibi aski da sassafe, a inda ta saba zama ta zauna sai kuma ta kalli mutanen da suke gudanar da aiki.
zaune yake akan kujeran office nashi yana jujjuyawa, yunwa yake ji sosai ga nonon da aka ya kawo mishi sha ɗaya yayi ya tufar tsami yaji sosai ga wani sugar da yayi yawa a kasa, bai san meyasa sai yasha kindirmo yake jin sauƙin yunwa ba, a kullum idan baisha nono ba baya taɓa samun nutsuwa harma ya zame mishi kamar magani idan baisha ba sai yaji kasala da rashin kuzari, yauma hakan ne sai duba lokaci yake akai akai yana jira ko zata fito a kawo mishi, tsaki yaja ya ɗau waya zai kara kira a karo na biyar kenan da yake tambaya me dama furan tazo?
knocking akayi yace "y...y..yes"
shigowa akayi aje wayan yayi, haka kawai ya tsinci kanshi da yin murmushi ganin an shigo da furan a cikin bowl me kyau, aje mishi yayi kana yace "gashi yanzu tazo"
karɓa yayi baice komai ba yasa hanu a drower ya ciro rapa ɗin dubu ɗaya dayawa ya bashi, yace "kai mata"
karɓa yayi da sauri ya kalli kuɗin sai kuma yace "to oga"
buɗe furan kawai yayi bai kara kallonshi ba ya fara sha, wani irin daɗi nonon yake mishi ga kamshin madara da yake kuma a tsaftace.
da sauri yaje inda take yace "gashi wannan inji oga"
kallon kuɗin tayi sai kuma ta kalleshi, karɓa tayi ta cire iya kuɗin nonon data dama ta bashi sauran tace "kai mishi ni iya kuɗin abinda na siyar nake karɓa"
da mamaki ya waro ido ya kalli kuɗin sannan ya kalleta yace "malama kin san nawane kuɗin kuwa?"
tace "ban sani ba tunda bani na bayar ba ka mayar mishi"
shiru yayi yana kallonta ɗauke kai tayi tana zubawa wani da yazo siya, ganin da gaske take ba zata karɓa ba ya juya jiki a mace ya koma office ɗin, ya jima yana knocking kafin ya amsa, shiga yayi yazo ya ɗan russuna kafin yace "oga yarinyar taki karɓan kuɗin tace iya kuɗin abinda ta siyar zata karɓa"
a fusace ya juyo da kujeran tunda yake a duniya bai taɓa yiwa wani kyauta akayi rejecting ba, this is the first time daya bada kyauta aka mayar mishi, cikin zafin rai yace "who the hell think she is? wacece ita da muneeb makawa zai bata kuɗi taki amsa? waye babanta a garinnan?"
yayi maganan yana tada jijiyan wuya, a tsorace yace "wallahi oga ban sani ba amma da ganinta ƴar talakawa ce domin babu alaman kuɗi a jikinta sai kyau kamar macijiya....."
ganin yadda yake hararanshi yasa yayi shiru, cikin fushin daya saba a koda yaushe yace "ka...ka..ka...ka"
rufe ido yayi jin maganan yaki fita sai huci yake, da kyar yace "kace ta bar nan daga yau kakkakkkarta kara zuwa"
yace "okay sir"
tafiya yayi zai buɗe kofa sai yayi wani tunani yau kaɗai da baisha nonon ba har wani kala yake ji, idan ta tafi aina zai rinka siya?"
da sauri yace "wait"
tsayawa yayi, yace "forget about her"
yace "okay sir"
kasan zuciyarshi haushi yake ji yaji ya tsani halinta.
tana gama saida nonon ta tattara ta shiga mashin domin ɗaukan habib a school, an jima da tashi musu tun daga nesa take hangoshi ya zauna yayi shiru yana kallon yaran da suke tafiya, ya rungume jakanshi, tausayi taji ya bata dan habib yanada ruwan shiru shiru a duk sanda ta ganshi saita tuna yayarta ameerah wacce ta kula da ita sosai, hakan yasa take jin son yaron a ranta kullum yana karuwa, bataso taga yana kuka a hankali ta sauka a mashin ɗin tun daga nesa ta fara cewa "habibi? habibi?"
yana ganinta yayi wani kyakkyawan smiling da gudu ya tashi yaje ya faɗa jikinta, sama ta ɗagashi tana juyi dashi, cikin so da kaunarshi tace "habibi yi hakuri banzo da wuri ba ko?"
yace "mama ai kuɗi kikaje nema sabida ki biyamin kuɗin makaranta kuma ki siyamin indomie"
murmushi tayi tace "habibin mama me wayo"
saukeshi tayi ta rike hanunshi suka shiga mashin ɗin, tafiya suka fara yace "mama yau kin san me akayi?"
tace "a,a habibi saika faɗa"
yace "karatu akasa nayi kuma na karanta ban ɓata ba shine malamanmu ta bani biscuit harma na rage miki naki"
buɗe jakanshi yayi ya ciro mata ragowan biscuit guda biyu yace "ga naki"
karɓa tayi tace "habibi na gode amma wannan biscuit ɗin ai yayi kaɗan na bar maka ka cinye"
ya shagwaɓe fuska kamar zaiyi kuka yace "wa ke fa na ragewa"
tace "to na gode"
cinyewa tayi yace "good mama"
da mamaki tace "har ka fara koyan turanci?"
gyaɗa kai yayi irin na yara yace "harda karatu malama tace nafi su hanin ilimi"
tace "Allah maka albarka yasa ka zama me ilimi sosai"
yace "ameen"
har suka isa gida suna hira sosai, wanka tayi mishi tasa mishi jallabiya baki na yara sabo dal ta siya mishi, subhanallah harshenshi ne kaɗai yake nuna shi ba balarabe bane amma sak ɗan larabawa ya zama, tace "kayi kyau"
inna tace "wannan angon nawa kowane kaya kyau yake mishi"
yace "inna nifa ba zan aureki ba"
ta rike haɓa tace "iye to wa zaka aura?"
yace "mama zan aura"
yayi magana yana nuna najwa dake juye taliya daga kan wuta, tace "sabida me zaka aureta?"
yace "sabida ina sonta"
share hawaye najwa tayi ba tareda ta bari sun gani ba, a hankali ta mike ta ɗau plate zata zuba musu taga manja ya kare, rike kwankwaso tayi tace "hande min boni lalashewa"
inna tace "ɗume?"
cikin gajiya tace "manja timmi fa inna"
inna tace "laaa ai na manta babu ko kaɗan?"
cikin iya fulatancin ta kuma cewa "wala ko seɗɗa"
tayi maganan tana juya roban manjan, shiga ɗaki tayi ta ɗauko kuɗi tazo tace "habibi jeka maƙotanmu ka siyo manja"
ya karɓi kuɗin yace "to mama"
fita yayi ta zauna akan turmin data daka yaji, gashinta daya addabeta ta kameshi waje ɗaya ta dumbuza a cikin hula, inna tana ganinta tana tura baki sabida ta tsani kitso ko tsifa yanzu wannan kan yafi wata biyu a kitse, tun suna jiran habib har ta gaji tace "wai dan Allah meyasa idan na aiki habibi makota siyan abu bai dawowa da wuri ne?"
inna tace "ai baya jin magana ne kullum saina mishi faɗa baya ji zai dawo ya sameni ne ai saina mareshi"
ɓata rai tayi domin ta tsani ace za'a mishi faɗa bale mari, murmushi inna tayi domin da gangan ta faɗi hakan, tace "inna me yayi na faɗa da har zaki ce zaki mareshi watakila mutane dayawa sukaje siyan abu shiyasa bai dawo da wuri ba"
shiru kawai tayi mata, shigowa yayi yana shesheƙan kuka, da kallo ta bishi direct wajenta yazo ya faɗa kanta yana kuka, tace "meya sameka?"
yace "halima ce ta mareni"
tashi tayi wuf tace "ta mareka?"
hijabi ta zaro daga kan igiyan tasa babu ko takalmi a kafarta ta rike hanunshi zasu fita inna tace "najwah? najwah? ki dakata ki tambayeshi me yayi mata ta mareshi?"
cikin masifa tana tafiya kamar zata kife tace "koma me yayi meyasa zata mareshi?"
kafin inna tayi magana ta fita, babu sallama ta shiga gidan, maman halima na zaune tana kulla kuɓewa taga mutum a kanta, da sauri tace "subhanallah baiwar Allah ya zaki shigo mana gida babu sallama?"
tace "wacece halima?"
halima ta fito daga ɗaki budurwa ce tace "nice halima me ya faru?"
nuna habib dake ɓuya a bayanta yana share hawaye tayi, tace "me yayi miki kika mareshi?"
tace "ki tambayeshi mana shi da ya kai miki kara"
tace "habibi me kayi mata?"
yace "ban mata komai ba"
ta kalleta da idanunda da suka kara girma tace "yace bai miki komai ba, meyasa kika mareshi"
ganin sun fara tashin hankali matar tace "baiwar Allah manja ya fasa mata"
tace "shiyasa zata mareshi sabida ya fasa manja? bata san tsautsayi bane? wallahi idan ta kara taɓashi koda laifinshi ne saina koya mata hankali"
cikin tsiwa halima tace "wallahi saina mareshi naga abinda kika isa kiyi, idan kinaji kinada ɗanyen kai to wallahi inada yaya ɗan taurin kai ne kamar ke"
hijabin jikinta ta cire ta ɗaura a kwankwaso taja hanun habib tace "habibi tsaya anan"
tsayawa yayi, tace "idan ba zina akayi aka haifeki ba ki taɓashi"
"dan girman Allah kiyi hakuri baiwar Allah"
cewar maman halima, najwah tace "a,a mama bari dai ta gwada rashin kunyarta ni najwah zan nuna mata karamin hauka take dashi"
halima tazo ta ɗaureshi da mari, rike kunci yayi yace "wayyo fuskata"
najwah data janyo halima zaka rantse itace ta haifeta, maman halima tana ihu ganin najwah akan ruwan cikin ƴarta tana duka kamar an aikota, tuni makota suka fara taruwa jin hayaniya da ihu a cikin gidan, inna babu shiri tazo, jan najwah suka fara, ranta tafasa yake so take ta lahanta halima ko ranta zaiyi sanyi, sallama akayi wani mashayi ya shigo gidan yace "wai me yake faruwa yau a gidanmu aka taru?"
maman halima tace "yauwa audu kazo ka taimaki ƴar uwarka wannan yarinyar batada kunya"
a fusace yazo zai mari najwah, hanunshi ta rike da karfi tana kallonshi tace "babu abinda ya saka"
yace "kanwata kika daka? yau zan kasheki a gidannan"
ganin zai fara dukanta inna tace "dan Allah kayi hakuri bawan Allah wallahi..."
kafin ta karasa najwa ta kwasheshi da dambe, matan wajen duk sun tsorata ganin tana rama duk dukan da yayi mata jan kafafunshi tayi ya zube kasa tim, duka take kai mishi, habib yazo yana janta yana cewa "mama ki barsu mu tafi"
inna tace "najwah ɗanki fa ke miki magana ba zakiji magananshi ki hakura ba?"
tace "kin manta da nasihan Ameerah?"
cak ta tsaya daga faɗan, hanun habib ta rike suka fita daga gidan, inna ta rinƙa basu hakuri musamman mamansu ta basu hakuri sosai saida sukace sun hakura kafin ta fita, matan unguwa sai mamakin karfin najwah suke, tana zuwa gida tace "habibi jirani naje na siyo mana manja"
yace "to mama amma karki kara zuwa faɗa dasu"
tace "insha Allah ba zan kara ba"
hijabin tasa zata fita yace "mama wacece ameerah?"
tsayawa tayi ta kasa tafiyan, a hankali ta juyo tace "yayata ce amma ta rasu"
yace "Allah yaji kanta"
tace "ameen"
fita zatayi inna tace "koma koma koma nace"
komawa tayi, tace "bafa can zanje ba inna manja zanje siyowa a kasuwa"
tace "kawo kuɗin ki zauna a gida ni zanje na siyo"
zatayi magana inna tace "kimin shiru ki koma ki zauna ko kofa kika fita ban yafe ba, har sai naje na dawo mara hakuri kawai"
kuɗin ta karɓa tasa takalmi ta tafi domin babu takalmi ma taje raba faɗan, komawa tayi ta zauna tace "habibi kawo takaddunka muyi karatu"
ɗaki ya shiga ya kawo takaddun suka fara karatu, inna ta dawo da manja kafin sukaci abinci, har dare babu inda taje, kayan habib ta cire mishi sannan tasa mishi vest da gajeren wando na yara, ita kuma tasa kayan da take bacci dashi mara nauyi ta hau katifan inna ta jima da bacci, habibi ya rungumeta sabida haka ya saba bacci, addu'a tayi mishi ta shafa mishi sannan ta shafa suka fara bacci.
ya tashi daga aiki yau da wuri, su Azad suna falo suna aikin kallo, ya hararesu duk a nitse suke yace "ina unty batool?"
tare sukace "tana ɗaki"
ya mikawa Azad ledan yace "kai mata"
da sauri ya tashi ya karɓa, ɗaki ya shiga yayi freshup kafin ya fito yasa kaya mara nauyi ya ɗau laptop ya fito, Azad ya kai sakon harma ya dawo domin kallon film ɗin da yake so akeyi, zamanshi keda wuya suka jiyo sautin tafiyan babban yaya, kallon juna sukayi, yazo ya zauna a ɗaya daga cikin sofan ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya yasa glasses kafin ya fara duba laptop ɗin, tsit suka zauna ko tari babu me yi a cikinsu suna kallon ma basa gane me akeyi a tv, kallonsu yayi ɗaya bayan ɗaya kafin ya kara cigaba da aikinshi, azad ne ya tashi a hankali yace "bari naje na duba abu"
gyaran murya muneeb yayi yace "dawo"
dawowa yayi, yace "zauna babu inda zakaje"
yana magana ne kamar zaki, a hankali ya zauna, sameer yana kunshe dariya a ɓoye, azad ya ɓata rai, unty batool wacce take zaune akan gado, kamar ta san meke faruwa a kasa, ta tashi tasa karamin hijabi akan riga da wandon jikinta, wayarta a hanu ta fito tana dudduba wayan, zama tayi a kusa da Azad ta kalleshi tace "baby Azad kana lafiya?"
a ranshi yace "ina lafiya wannan mugun na nan"
a fili kuma yace "kaina ke ɗan ciwo Inaso nasha magani"
da sauri tace "ciwon kai? yaushe? meyasa bakasha magani ba?"
yayi shiru, ta kalli muneeb da yake kallo tace "tashi kaje kasha magani"
wuf ya tashi yana kallon sameer, da sauri ya nufi sama ɗakinsu ya shige ya ɗau wayarshi ya fara duba chart da akayi a group nasu, kanshi ya ɗaura akan pillow ya ɗau sweet nashi yana sha, batool tace "muneeb inaso muyi magana kuma so nake ka bani duk hankalinka"
aje laptop yayi ya juyo yana kallonta yace "i..ina jinki"
tace "muneeb ya kamata kayi aure, lokaci yana kurewa muneeb, bai kamata muyi ta zama haka a gidannan babu ci gaba ba, ya kamata ace kayi aure ka haifi ƴaƴa muma mu kara yawa a family ɗinmu, ka san dai ni bazan iya aure ba muneeb banida isashen lafiya nan gaba kaɗan zan nemi taimako sabida jikina ba sauki nake samu ba kara ciwo nake ji, ya kamata ka samu mace me hankali wacce zata kula da kai, idan nayi sa'a ka samu me hankali nima zata kula dani da sauran kannenmu amma baka tunanin aure ma muneeb baka damu ba naga bakada niya, iyeyenmu nasa raye