Showing 9001 words to 12000 words out of 40241 words

Chapter 4 - NI DA MUNEEB

Start ads

11 Sep 2025

59

Middle Ads

komai sugar kawai ya rage zaku siya"
fitowa sukayi zata ɗaura musu suka jiyo guɗa daga waje, dandazon mata suka gani akan mashin suna guɗa, ga kuma wata da aka rufe fuskanta da mayafi, da kallo suke binsu har suka shigo gidan, ɗaya daga cikinsu tace "mairam mun kawo miki kishiya wannan itace sabuwar matar Abdullahi jauro, gata nan ba dai ku nuna mata kyau ba itama kyakkyawa ce yadda kuke ji da kyau a garinnan itama tana dashi"
buɗe fuska amaryar tayi, inna tana tsaye kawai tana kallonsu ta kasa cewa komai, najwa tace "to ai wa wanda ya aurota zaku faɗawa ba muba"
matar tace "kece najwah daga jin wannan maganan da kikayi to bari kiji munfi karfinki mu ba sa'anninki bane duka zamuyi miki me kyau mu koya miki hankali"
matsowa tayi gabanta ta tsaya tace "to dakeni, ki dakeni idan kin isa, wallahi kikayi kuskuren taɓa najwah saina nuna miki asalin hanyan gidanku"
matar ta fara masifa kamar zata mari najwah, itama najwah cikin tsiwa take mayar mata, ameera ce ta fara jan najwah tana cewa "kiyi hakuri ki kyaleta"
tace "barni adda meera ta taɓani wallahi saina ƙona gidannan, duk kowa ya mutu a ciki, tana taɓani sai nayi mata dukan tsiya kuma basa fetur a gidan na kona naga karshen iskanci"
hayaniya ne ya kaure a gidan amarya ta ɗaura mayafi a kugu tace najwah tayi mata rashin kunya, meerah ganin zata kama najwah da faɗa ta janye najwa, duka ta kaiwa najwah, tana jin saukan hanunta a jikinta ta kwace daga rikon da ameera tayi mata, kan amaryan tayo ta shaƙeta nan take suka fara dambe, matar da take magana tasa hanu zata daki najwa ameerah dake tsaye ta rike hanun tace "karki taɓamin kanwata"
tace "idan na taɓa ta zaki rama mata ne?"
tace "eh"
ganin zata kaiwa najwah duka ta riketa da karfi, duk hakurin ameera saida suka kwashe da dambe nan take gidan ya kacame baka jin komai sai ihu da duke duke, najwa wacce ta kai amaryan kasa tana jibganta kamar ita ta haifeta, kanwar amaryar taje da gudu ta ɗau taɓarya tayo kan najwa zata kwala mata ameera da sauri ta tare, ihu tayi lokacin da taɓaryan ya sauka a kanta, najwa a firgice ta kallesu taga yarinyar da taɓaryan yake hanunta sannan ta kalli meerah da jini ya fara wanke mata fuska, wani irin kukan kura tayi ta cafko yarinyar, karɓa tayi ta fara dukanta dashi, ganin meerah tana kwance tana rike da kanta yana jini suka fara neman hanyan gudu, rufe kofan najwah tayi tana kallonsu tana haƙi tace "wallahi tallahi babu wacce zata fita daga gidannan da rai matukar adda meerah ta mutu"
duk sun fara tsorata, kitchen ta shiga ta ɗauko kalanzir ɗin dake cikin jarka ta fito dashi, zubawa tayi a tsakar gidan sannan ta ɗauko ashana inna tana rike da ameerah tana cewa "najwah kar kiyi haka, najwah kar kiyi"
ashana tasa ihu suka fara wuta ya fara ci da gidan, tana tsaye tace "tunda kuka taɓa lafiyan adda meerah sai kowa lafiyanshi ya taɓu"
kowa yana neman hanyan gudu, inna ce tayi karfin halin kwantar da Ameera taje ta ɗibo ruwa ta fara zubawa suna ganin haka suma suka fara tayata duk da zafin wutan saida suka daure suka tsayar da cin wutan, bayan komai ya lafa sum sum suka fara barin gidan sabida sunga abinda yafi karfinsu, dama labarin najwah suke ji yau sunga asalin wacece najwah, tana tsaye hanu a kugu tana jira a taɓata, amaryan a hankali ta tashi ta shige ɗakin da yake nata tayi shiru kamar munafuka, ruwa najwah ta ɗiba tazo ta wankewa ameera ciwon ya tsaya da jinin, ba wani wani ciwo babba bane hakan yasa ta ɗauko ɗankwalinta tazo ta ɗaure mata tace "sannu adda meerah"
ɗagata tayi suka koma ɗaki suka zauna, tace "sannu amma meyasa zaki taremin? ai da kin bari ya sauka kaina nasan zanfi samun kwanciyar hankali, banaso abu ya sameki"
inna wacce take zaune a gefensu tayi tagumi, tace "najwah ya zanyi dake?"
tace "inna banida laifi fa, baiga irin rashin kunyar da suka zo dashi ba? badan nayi musu haka ba zasu rinƙa yi kullum sabida haka banida laifi yawwa"
ameera tace "haba najwa inna kikewa magana kina murguɗa baki?"
tace "kiyi hakuri"
"bani zaki bawa hakuri ba itace zaki bawa"
tace "kiyi hakuri inna"
inna tace "na hakura yawan fushina akanki ba abune me kyau ba, idan ina fushi dake Allah zaiyi fushi dake, Allah ya huci zuciyarki ki zama me hakuri"
kasa kasa tace "ameen"
tareda turo ɗan karamin bakinta da yake pink amma ta maidashi baki da kwalli, dara daran idanunta ta ɗago tace "zamu je tallan ko na tafi?"
tashi ameera tayi tace "muje"
inna tace "ku bari mana zuwa gobe"
najwah tace "nono zaiyi tsami"
fita sukayi suka ɗau nonon suka tafi, a wajen zaman da suka saba zama najwa ta zauna ko kallon ƴammatan dake hararansu batayi ba, a ran ameerah tana addu'a Ubangiji Allah yasa har su koma gida kada najwa tayi faɗa da kowa, wani yazo ya siyi nono ya bawa ameerah kuɗin najwah ta ɗau leda ta zuba mishi, mika mishi tayi tace "gasi"
sam bata iya hausa ba ameerah ta fita iya hausa, karɓa yayi ya juya zai tafi ledan ya fashe nonon ya zube a kasa duka, kallonta yayi sannan ya kalli nonon cikin tsawa yace "dama kin san ledan babu kyau zaki samin a ciki?"
tace "kayi hakuri ai bani nayi ledan ba"
yace "magana zaki gayamin kenan?"
tace "bari nasa maka wani kayi hakuri"
masifa ya fara mata kamar zai daketa tace "kaga da Allah malam ya isheka haka, kaifa ba ubana bane da zaka tsaya kana gayamin magana, na baka hakuri na baka hakuri kuma har yanzu kana min tsawa ubana ne yayi ledan da zansan babu kyau?"
cikin fusata yace "ni kike gayawa wannan maganan?"
tace "an gaya maka kai waye?"
zai mareta ta rike hanun shi ta yarfar a kasa, ɗankwalin kanta ta cire ta ɗaura a kugu sannan ta tsallaka nonon tazo gabanshi tace "ka mareni, mareni mana"
ameerah cikin gajiya taje tana janta tace "haba najwah kiyi hakuri mana ki zama me hakuri da kawar da kai"
tace "adda meerah kina gani fa yana shirin marina ban mishi komai ba"
yace "shegiya me kama da ɓarayi"
tace "ai idan ma sata ne ubanka su suka koyamin saboda su suke sace kuɗin gomnati har muma muka koyi sata"
yace "how dare you da zaki zagi ubana?"
tace "kayi magana da larabci ba turanci ba hakan zaisa na tabbatar kanada ilimi"
da kyar ameera take bashi hakuri tana cewa "dan Allah kayi hakuri kaji bawan Allah bari na zuba maka wani nonon"
yace "banso"
najwa tace "kada Allah yasa kaso"
cikin fusata ta koma inda take zama, ƴammatan gefenta duk sukayi tsit suna rarraba ido dan sun san wacece najwah, ameerah bayan ya tafi ta koma gefe ta zauna shiru tana kallon najwa dake wanke robobin da suka ɓaci, saida ta gama wankewa ta juyo tana cewa "Adda meerah waɗannan ba za'a kara amfani dasu ba ko yau?"
ganin meerah tayi shiru, ta turo baki tace "to kiyi hakuri ba zan kara ba"
tace "ba komai"
tace "to kiyi murmushi mana"
murmushi tayi, tace "yawwa ko kefa yanzu naji sanyi a raina"
maganan ameerah kawai takeji, nonon ya kare da wuri suka tattara suka hau mashin sai gida, yamma ne likis suna shiga sukayi salla sukaci abinci, amaryan baba bata fito ba har yanzu tsoro take, inna ta bawa najwa abinci tace "kaiwa amaryan babanku tun ɗazu bataci komai ba"
da mamakin halin inna najwah tace "shida ya aurota me zai hana ya kawo mata abinci ko kece baiwa da za...."
marin da inna tayi mata yasa tayi shiru bata kara cewa komai ba, sai gunguni da take kasa kasa, inna tace "ameera zo ki kai mata"
karɓa ameerah tayi tace "to"
sallama tayi ta shiga, tana kwance akan gado me rumfa tayi shiru, tace "ina wuni ga abincinki"
tace "na gode"
fita tayi ta samu najwah tana shiri tace "ina zaki?"
tana shafa man baki tace "filin wasa"
murmushi tayi tace "lalle yau najwahta ce zataje filin wasa?"
tana dariyanta me kyau kuruciyanta ya kara fitowa sosai tace "kwarai kuwa nayi kyau?"
tace "kinyi kyau amma dan Allah dan Allah najwa kimin alkawari"
tace "na me?"
tayi maganan tana sa takalmi, tace "ba zakiyi faɗa da kowa ba har kije ki dawo?"
tace "na miki"
"yawwa nasan kina girmama alkawari saikin dawo"
tafiya tayi da sanda a hanunta tana wasa dashi har ta isa dandali, mutane sun taru wasu na gasa nama wasu na dama fura ga kuma kiɗa da akasa, ana ganinta aka fara rububi domin ta iya rawa"
tana murmushi tace "asa min waka"
sa mata akayi ta fara rawa, samaran wajen suka fara mata liƙi da naira goma goma, ƴammatan sai harara suke mata, aiko ta tara kuɗi dayawa sannan ta koma gefe ta siyi tsire ta zauna akan dutse tana ci tana bin kowa da kallo, saida tayi nak ta koshi kafin ta tashi tana hamma, dare yayi sosai ta siyawa Adda meerah da inna tsire da duka kuɗin ta kama hanyan tafiya abinta, wani yaron me gari da ake kira musa duk ƴammatan garin suna sonshi sabida yana zuwa birni yayi karatu, biyota yayi yana kiran sunanta, bata tsaya ba taci gaba da tafiya saida ya dameta da kira kafin ta tsaya tana kallonshi har ya karaso tace "me?"
yace "haba najwah kullum sai nayi miki magana bakya kulani wallahi aurenki nake son yi"
kallonshi tayi wai a haka ɗan me gari ga tsayi kamar fatalwa ga uban tsiranta kamar me cutan tamuwa, tace "musa kafin na zagi halittanka ka matsa min na wuce"
yace "haba najwah"
tsaki taja ta barshi a wajen, tana rike da ledan tana waka har ta isa kofar gidansu, muryan baba taji yana masifa kuma da alama wa adda meerah yake yi, a hankali ta shiga babu sallama ta tsaya tana kallonshi, meerah durkushe a gabanshi yace "wallahi gobe kika kuskura Arɗo yazo wajenki baki fita ba wallahi saina kasheki da duka, ba zaku zauna min a gida ku kasa auruwa sabida bakin jininku ba, ai itama najwah zan nema mata miji domin ganinki da takeyi yasa bata kawo miji ba, sai shegen kyau kamar ƴaƴan macizai waya sani ma ko macizan ne ku"
meerah kanta a kasa yace "tashi ki bani waje sati ɗaya zansa aurenku da arɗo"
najwah tace "amma baba kafi kowa sanin halin Arɗo kowa yasan halin ƴan gidansu da mugunta da rashin imani meyasa zaka ɗauki adda meerah ka bashi? meyasa zaka ɗauki shiru shiru wacce bata magana kuma kasan tabbas ba zata iya maka musu ba kaci zalinta ka haɗata aure da mashayi masu satan shanayen mutane kuma su hanasu magana"
yace "eh lalle najwa wuyanki ya kai yanka, yau ni kike gayawa magana? ni kikasa a gaba kina gayawa wannan maganan?"
tace "baba gaskiya nake faɗa kuma kasan ko waye bana shaƙƙun faɗa mishi gaskiya...."
katako ya ɗauka yayo kanta dashi, dukanta ya fara kamar zai kasheta, ihu take tana cewa "wallahi ba zan fasa faɗa ba cutar da ita zakayi"
da gudu ameerah tazo tana kwatanta, baba dukanta yake ganin bakinta yaki shiru ya ture meerah, tace "baba kayi hakuri ka kyaleta dan girman Allah baba ka kyaleta wallahi zan aureshi"
tsayawa yayi da dukan yace "banza mara hankali ke ba rashin kunya ne aikinki ba? zan shiga kafar wando ɗaya dake a gidannan"
kuka take tana kallon jikinta duk da akwai duhu tasan jini yana fita, inna tana ɗaki bata fito ba ta gaji da sha'anin najwa wallahi ta gaji, ameerah ce ta riketa suka shiga ɗaki, shi kuma baba ya shiga ɗakin amaryanshi, zama tayi a bakin gado tace "adda meerah ko kasheki za'ayi karki kuskura ki auri Arɗo domin zakiyi dana sani, idan ta kama ki gudu ki bar garinnan...."
marin bakinta inna tayi tace "wallahi najwah zan ji miki ciwo, wani irin shawara kike bata? taya zakice ta gudu ta barmu kenan?"
shiru tayi batayi magana ba, ameerah kam dama ba magana take yawan yi ba, ganin najwah tayi shiru kawai tazo ta rungumeta tayi shiru, inna tana kallonta tana share hawaye tasan za'a cutar da ameera amma tasan halin baba idan yayi magana babu me hanashi Allah dai ya tsare mata yaranta.

zaune suke suna kallo Azad yana rike da ledan popcorn yana ci yace "unty batool maganinki na yamma baki sha ba"
tace "baby Azad na gaji da shan magani, wallahi wari maganin yake min"
tashi yayi yaje fridge ya ɗau maganin sannan ya dawo ya fara ɓarewa yana mika mata da ruwan, tace "ba zansha ba"
kamar zaiyi kuka yace "unty batool lafiyanki shine kwanciyar hankalinmu dan Allah ki daure kisha"
tace "Baby Azad ba zan taɓa warkewa ba likita ya tabbatar da hakan"
hawaye ya fara, ta share mishi tace "zansha"
karɓa tayi tasha sannan tasha ruwan tace "na haɗe"
murmushi yayi ya rungumeta, sameer ya ɗauke kai daga kallonsu dan tausayi ya cika mishi rai, jabeer ya canja channel duk suka kalli tv jin labarin da ake badawa wanda kullum sai an sanar da ɓatan yara masu yawa a garin, jikinsu a mace suke kallon tv, me news ɗin ya nuna hoton kyakkyawar yarinyar da take sanye da uniform yace "wannan tana cikin yara goma da aka sace na makarantar m.u academy, kamar yadda iyayen yarinyar suka sanar bayan an tashi daga makaranta basu samu daman zuwa da wuri ba bayan sunzo sun tarar da iyayen yara guda tara suna neman yaransu, saide basu samesu ba ciki harda ƴarsu, an tabbatar musu wani baƙin mota ne ya tsaya da wani me sanye da bakaken kaya kuma ya rufe fuskashi da facemask ya sacesu, matar da take soya kosai a gefen titin itace ta bada wannan shaidan, kafin ta fara ihu ta tara mutane motar har yayi nisa, ba yau wannan abin ya fara faruwa a wannan garin ba, an jima ana sace yara kanana harma da manya to amma wanene yake wannan satan? meyasa yake sacesu? ina yake kaisu? wannan shine tambayan da yake damun kowa, sannan bayan sacesu da kwana kaɗan sai aga gawarsu a cikin gari wannan wani irin rashin imani ne? me yara kanana sukayi?"
shiru su batool sukayi duk jikinsu a mace, hoton yaran ake nunawa, a hankali ya turo kofan, sameer yace "ya Allah duk wanda yake wannan aikin ya Allah kada ka barshi ya zauna lafiya a duniya, ya Allah ka sakawa waɗanda aka zalunta"
jabeer yace "wallahi jikina yayi sanyi ka dubi yara kanana ka kalli kukan da iyayensu suke wani irin mara imani ne Allah ya tsinewa...."
kit ya kashe tv yana kallon sameer, shiru yayi wani irin harara yake mishi sannan yace "ku...ku....tashi anan"
duk suka tashi, Azad ya kwashe duk abinda ya barbaza a wajen suka nufi ɗakinsu, batool ta bishi da kallo saida gabanshi ya faɗi, kau da kai yayi, ya zauna a gefenta yayi shiru, tace "muneeb meyasa ka koresu? meyasa ka katse musu hiransu? meyasa baka bari sun tsinewa wanda yake aikata wannan mummunan abin ba?"
cikin in ina yace "sabida inason...magana...dake"
gyara zama tayi tace "ina jinka"
yace "a cikin....dukiyan...Abba....akwai...wani....agogon...gold...dana gani....bayan ....na kai...kasuwa akace zasu siya miliyan ɗari uku, shine nake neman....shawaranki na siyar?"
murmushi tayi tace "naji daɗi daka nemi shawarata muneeb amma ai kaine kake tafiyar da komai, ni ba lafiya ne dani ba kayi kokari kawai kai kam ka kula da dukiyan marayu, sannan muneeb zanso kayi aure kafin na mutu, kaga matar da zaka aura zata maye gurbina idan na mutu, zata kula dasu idan tanada hankali zata zama itace me kulawa dasu Azad, zanso na bata amana kafin na mutu"
ɓata rai yayi, a duk lokacin da akayi mishi maganan aure saiya ɓata rai yaki magana, tace "muneeb ka fahimceni aurenka shine mafi alkhairi, kayi aure mu samu mace kaga ni kaɗaice mace zanso...."
wayarshi ce tayi ringing tashi yayi ya fita kafin ya amsa wayan, ya jima sosai yana waya sannan ya dawo, ɗakinshi ya wuce, su sameer suna zaune akan katon gadonsu, sameer yana kwance ya ɗaura kanshi akan kafar jabeer yana game a wayanshi, azad kuma yana zaune akan drower ɗin dake kusa da gadon ya ɗaura kafanshi akan drower ɗin, yace "sameer jabeer kun san wani abu?"
sukace "no"
ya gyara zama yace "gobe da birthday ɗin babban yaya kuma da alama shima bai sani ba, ya kamata muyi mishi surprise kamar yadda yake mana surprise wani lokacin shima muyi mishi ko zamu sashi murmushi koda sau ɗaya ne a shekara"
sameer yace "shawara me kyau gaskiya kaine karami amma kaine me tunani kafi wannan gaɓon"
yayi magana yana marin kafar jabeer, tsaki jabeer yaja yace "kaima ai naga ba tunanin ne da kai ba"
yace "amma na fika"


ɗakinshi ya shiga kayan jikinshi ya cire sannan ya ɗaura towel ya waist nashi, shiga toilet yayi ya tara ruwa a bathtub yasa sabulai sunfi kala goma masu kamshi, kumfata ruwan ya fara saida yayi kumfa sosai kafin ya kwance towel ɗin ya shiga cikin kumfa me kamshin, lumshe ido yayi yana jin nutsuwa, a duk lokacin daya gaji ko yake cikin damuwa idan ya shiga bathtub yana samun nutsuwa, saida ya jima kafin ya kunna shower ya lumshe ido yana jin daɗin ruwan, da haka har ya gama wankan ya fito ya ɗaura towel ɗinshi ya ɗau karami yana tsane gashin kanshi ya fito, a gaban mirror ya ɗau wayarshi dake ringing cikin fusata yace "wai Azeez ba nace kada ka rinƙa kirana idan ina gida ba? me...me...me...?"
kasa karasawa yayi, marin fuskanshi yayi yace "me..me..."
Azeez yace "me nake so?"
yace "yes"
azeez yace "yara biyu fa sun mutu boss"
yayi shiru, kana yace "to...to.... so kake nazo na cinyesu?"
shiru yayi, katse wayan yayi ya aje, zama yayi ya shafa mashi me kamshi sannan yasa jallabiya me taushi, kwanciya yayi akan gadonshi me taushi ya rufu da blanket cikin nutsuwa ya fara bacci, batool a hankali ta bar bakin kofan ta fara tafiya, a ranta tana juya maganan tace "to meyasa bayaso a kirashi idan yana gida? su waye yake magana akai?"
tace "ya Allah na kasa yadda da muneeb"
ɗakinta ta shiga ta kwanta akan gadonta me kyau, kallon hoton dake manne a bangon ɗaki tayi, dukansu ne a hoton ciki harda Abbansu da Ammi, share hawaye tayi tace "Allah yaji kanku Allah yasa kun huta, Allah yasa kuna tare da mala'ikun rahama"
tace "nima na kusa zuwa na sameku zamu bar kannena babu mace a wajensu, babu mace a kusa dasu su kaɗai maza zasu zauna tunda muneeb yaki

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login