Showing 18001 words to 21000 words out of 40241 words

Chapter 7 - NI DA MUNEEB

Start ads

11 Sep 2025

61

Middle Ads

ciwo tace "Azad? Azada? sameer? najeeb?"
birgima take, Azad dake kwance ya ɗaura kanshi a kafar sameer yana kallon laptop na sameer ɗin ya tashi da sauri yace "na manta ban duba unty batool ba, bara naje"
sauka yayi daga gadon, jallabiya ne me taushi a jikinshi, sameer yace "to na hanun daman unty batool baka minti biyu baka ganta ba sai kaji kamar akan kaya kake"
dariya yayi yace "eh mana ya sameer ai ni kalen hanjinta ne"
fita yayi ya shiga ɗakin da sallama, kunna wutan yayi yace "unty batool banzo na dubaki...."
da gudu ya karasa ya riketa domin saura kiris ta zube a gadon, wani irin ihu yayi ya kira sunan najeeb da sameer, bubbugata yake ganin ta suma ya fara kuka yana kiran sunanta, muneeb dake shirin kwanciya bacci yaji ihun azad, babu takalmi ya fita da gudu, ɗakin batool ya nufa ganin su sameer sun shiga, bai tsaya wata wata ba ya ɗauketa cak, yace "ki buɗe ido"
bai kula da wandon jikinshi gajere da armless ba ya fita babu ko takalmi tana rungume a kirjinshi, a mota ya sata sannan suma suka shiga, da gudu ya fita da ita, guards suka shiga motarsu suka rufa musu baya, kamar kullum tsaida komai na asibitin akayi domin kula da batool makawa wacce aka buɗe asibitin sabida ita, emergency aka shiga da ita, atake masu tsaronsu suka zagaye asibitin babu me shiga babu me fita.
safa da marwa yake yana kallon kofar ɗakin, su Azad suna gefe suna addu'a, har Dr ya fito muneeb yace "ya jikin?"
girgiza kai yayi yace "babu komai karka damu zata samu sauki"
shiru sukayi, har dr ya tafi babu wanda ya kara magana.


*Jiddah Ce...✍️*
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 6*


~Najwah ce zaune a kusada Adda meerah, cikine babba a jikin adda meerah haihuwa yau ko gobe, yanzu najwah ta daina zuwa tallan nono saboda kula da adda meerah wacce bata samun kulawa sam sam a wajen kannen mijin da surukarta, ɗaure take da guntun zani ta ɗaura ɗankwali siriri, gashinta da kullum yake a kitse guda biyu ya sauka har bayanta, wuta take hurawa hayaki ya dameta sosai sai tsaki take ja kamar tayi kuka, Ameerah dake zaune akan kujera tana kallonta tace "boɗɗi kibar wannan wutan kawai idan zai dameki"
tace "a,a Adda ya zama dole ne na hura dan banso ki rinƙa shan ruwan sanyi zai saki mura"
murmushi tayi tace "to boɗɗi na gode, gani nayi wai hayaki yana damar min ke"
tace "ba komai"
da kyar wutan ya kama ta girka tukunyar ruwa kafin ta fara share cikin gidan, kallonta kawai Ameerah take, a hankali ta juyo domin zubar da shara ido suka haɗa, Ameerah tayi murmushi, tace "adda wai meyasa kike yawan kallona ne a kwanannan?"
tace "ba komai najwah kawai bana miki fatan kiyi aure a wannan rugan, ina miki fatan ki samu miji me hankali me kuɗi wanda ba zai wulakantaki ba, Inaso kiyi karatu ki zama wani abu a rayuwa, kar kiyi aure ki karashe rayuwarki cikin wahala irin wanda nake ciki yanzu"
murmushi tayi tace "adda kenan"
daga nan bata kara cewa komai ba, amma can kasan zuciyanta wani irin tausayin ameera take ji, da kuma haushin mazan kauyen da tsanansu ciki harda baba, har ruwan yayi zafi kafin ta ɗauko flask ta juye a ciki, shiga ɗakin tayi ta aje kana ta ɗauko cup ta zuba mata kaɗan ta kai mata, karɓa tayi tana sha Arɗo yayi sallama, ɗauke kai najwa tayi tana cigaba da aikin gabanta, kallonta yayi sai kuma ya kalli ameera yace "ina abincina?"
tace "yanzu najwa zata girka"
tsaki yaja yace "ni ba zanci abincin da zata girka ba sabida kece matata ke nakeso ki girka idan kuma kin barmin ita yau ta zama matata to saiki bamu ɗaki ki koma cikin gida"
najwah dake rike da tukunya batasan lokacin da tukunyan ya faɗi ba jin maganan banza da arɗo yake yi, bata kulashi ba kawai taje tasa takalminta ta gyara mayafinta tace "adda na tafi"
tafiya tayi har taje bakin kofa taji ihun adda, da gudu ta dawo dan ganin meke faruwa, gani tayi yana janta a kasa zuwa bakin murhu, rufe ido tayi tace "Arɗo ka saketa bakaga ciki a jikinta ba?"
cigaba da janta yayi tace "Arɗo ka saketa nace"
ganin ba zai saketa ba taje da gudu ta fara janshi, cikin zafin rai ya juyo zai mareta ta rike hanun gam, tace "wallahi idan ka kara taɓa adda meerah zanyi maka abinda ba zaka taɓa mantawa ba"
Ameerah tace "najwa ki tafi"
sakin hanunshi tayi kawai ta fita daga gidan, ranta yana suya, wani irin baƙin ciki ne ya cika mata zuciya, batasan lokacin data fashe da kuka ba, har ta isa gida kuka take, a kofa ta tsaya ta share hawayenta sannan tayi sallama ta shiga, inna tana kan tabarma tayi tagumi sabida yanzu baba ya gama zagin iyayenta, tana ganin najwah tace "kin dawo? ya kika baro Addanki?"
a hankali ta zauna kusa da inna tace "tana lafiya"
kwanciya tayi akan tabarman ta ɗaura kanta akan kafar innan tace "inna bana farin cikin zaman adda ameera a gidan arɗo meyasa bakwa buɗe baki kuyi magana ku kwaci ƴancinku? nifa ko za'a kaaheni ba zanyi aure a wannan rugan ba"
shiru inna tayi itama bata fatan najwah tayi aure a wannan rugan, shiru sukayi kowa yana tunani a ranshi.
cikin dare Ameerah ta fara naƙuda duk yadda tayi arɗo ya kira mata mutane su taimaka mata yaki, tsaki ma yaja yace "sauran matan da suke haihuwa da kansu su kaɗai ba mutane bane?"
kuka take yi sosai tace "arɗo dan Allah ka kiramin innata ko najwah dan Allah kaji?"
pillow yaja ya kara gyara kwanciyarshi yana bacci, bayanta sarawa yake sosai ga wani irin azaban ishin ruwa da take ji, tana birgima a wajen tana cewa "cikina wayyo bayana, wayyo Allah zan mutu jama'a ku taimakeni, najwah? najwah? najwah?"
ta galabaita sosai kafin ta samu ta haihu batama san ko mace ko namiji ta haifa ba sabida tsananin duhun dake ɗakin Ita dai tana jin sautin kukan jariri sama sama domin bata san inda take ba.

najwah dake kwance akan gadon inna bacci take inna na gefenta itama tana bacci, a firgice ta tashi tace "Adda Ameerah?"
kallon cikin ɗakinsu dake ɗauke da duhu tayi, taɓa goshinta tayi taji zufa sosai ya wanke mata fuska, dafa kirji tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un adda meerah?"
inna dake bacci ta buɗe ido a hankali tana kallon najwah cikin duhun ɗakin, tashi tayi ta ɗauko fitila ta kunna nan take haske ya gauraye ɗakin, ganin najwah dafe da goshi cikin razana tazo da sauri ta riketa, rungumeta najwah tayi, inna tace "mummunan mafarki kikayi ko?"
tace "inna nayi mafarkin dada tazo ta ɗauki adda ameera sun tafi wani waje kuma basu kara dawowa ba"
Dada itace ta haifi inna kuma ta jima da rasuwa, inna gabanta yayi mummunan faɗuwa jikinta yana rawa tace "karki damu insha Allah babu abinda zai samu Ameerah"
tace "inna amma ance idan kayi mafarkin mamaci ya ɗauki wani to mutuwa za'ayi"
shiru inna tayi, da sauri najwah ta saketa, dira tayi daga kan gadon babu ko tsayawa neman mayafi tayi hanyan waje da fitilan a hanunta, inna tace "ina zaki najwah?"
tace "zanje gidan adda meerah"
tace "najwah karfe ukun dare fa ya kusa"
tace "inna bazan iya zama ba koda na zauna hankalina ba zai zauna ba"
buɗe kofan tayi tasa takalmi, tana jin baba yana cewa "waye? waye?"
bata kulashi ba ta fita daga gidan, cikin duhun daren take tafiya tanasa kafanta a duk inda fitila ya haska, da haka har ta isa gidan adda, da sallama ta shiga cikin sanɗa take tafiya, kowa yana bacci a wajen hakan yasa ta nufi ɗakinsu adda, a hankali ta tura kofan tasa kanta tana lekawa, da sauri ta haske fitila a inda take ganin mutum kwance, shiga ciki tayi, idanunta kamar zasu fito lokacin da taji ta taka mutum, hasakawa tayi taga adda meerah kwance a jariri yana gefenta shima a kwance, jikinta ne ya fara rawa kasa yin komai tayi, fitilan dake hanunta ya faɗi kasa, idanunta sun kara girma, da kyar ta daure ta durkusa kasa ta bubbuga ameerah a hankali tace "adda meerah? Adda meerah?"
jin shiru ta fara bubbugata da karfi tana cewa "Adda meerah? dan Allah ki tashi bamuyi haka dake ba, ki tashi bamuyi haka dake ba adda, kar kimin haka"
jaririn ne yayi kuka, ido ta kai kan jaririn jin yana tsala ihu ta ɗaukeshi cikin jinin ta rungumeshi, wani irin ihu tayi saida duk mutanen gidan suka tashi, kofan ɗakin suka zo domin ganin abinda ke faruwa, arɗo dake bacci ya tashi da sauri jin ihu yace "wani shegen ne yake mana ihu a tsakar dare haka?"
mamanshi rike take da fitila haskawa tayi taga Ameerah kwance cikin jini bata motsi ga najwah rungume da jariri yana ihu, salati suka fara, tace "meya sameta?"
kasa amsawa najwa tayi banda ihu babu abinda take yi sai kara kanƙame jaririn take, a cikin daren aka tara mutanen unguwa ciki harda inna wacce har rugansu akaje kiransu, tace "dan Allah kar ku cemin abinda najwah tayi mafarki ya faru, bamuyi haka da ameera ba dan Allah"
tana zuwa ta tarar da Ameerah kwance an rufeta da zani har fuskanta, ga najwa kanƙame da jariri ta zama kamar a zauce, shiru inna tayi tazo ta buɗe fuskan taga Ameerah ido rufe fuska ɗauke da murmushi, tace "Ameera haka mukayi dake? haka mukayi dake Ameerah zaki tafi ki barni? zaki tafi ki barni Ameera?"
kuka ta fashe dashi ta ɗaura kanta akan Ameerah tana kuka me cin rai, har gari yayi haske babu wanda ya runtsa arɗo sai rarraba ido yake mamanshi kuma tasa mayafi ta zauna daram a kasa.
inna da kanta ta yiwa Ameerah wanka aka shiryata domin kaita gidan gaskiya, najwah wurgi tayi da jaririn inna ce ta rikeshi lokacin da zai faɗi, rike Ameera tayi ta hanasu fita da ita, da kyar aka taru aka riketa suka fita da ita, silalewa tayi kasa ta faɗi a sume, ruwa aka ɗiba aka shafa mata a fuska, ba ita ta farka ba saida masu jana'iza suka dawo, tana zaune a wajen inna tayi shiru idonta akan jaririn da ba'a mishi wanka ba har yanzu, inna taki bata jaririn sabida a zatonta najwah ta samu taɓin hankali duba da yadda take bin mutane da kallo da yadda take yin abu kamar ba daidai take ba, arɗo ne ya shigo ya durkusa kasa mamanshi ce tace yaje ya gaishesu sabida kada ayi zarginshi, kamar da gaske ya fara kuka yace "inna ya hakuri?"
shiru inna tayi mishi, yace "najwah ya hakuri?"
shiru tayi tana kallonshi, yace "duk abinda ya faru Allah ne ya tsara...."
wani irin kukan kura da tayi ta damko riganta da iya karfin da Allah ya bata, cizo ta fara kai mishi daga nan ya fara kwatan kanshi, sakinshi tayi ta ɗauko katon kataton dake gefe ta rinƙa kwala mishi, mutanen dake wajen kowa ya tsorata suka fara ja baya sabida sunyi zaton mahaukaciya ce, inna ta kwantar da jariri a kasa tazo tana jan najwah, fizgan jikinta take tana kuka da hawaye tana dukanshi da katakon, kanwarshi dake zaune tace "ya isheki haka taya zaki rinƙa dukanshi shiya kasheta ne?"
juyo dara daran idanunta tayi, sun rikiɗe sun koma jajur, fuskanta ma ya koma jajur daga yellow, batasan lokacin data janyo kanwar tashi suka fara dambe ba, ranta yana tafasa ji take zata iya komai a yanzu, inna tana cewa "najwa kiyi hakuri ki bari, najwah ki kyalesu"
kin barinsu tayi katakon ta ɗaga zata maka mata jaririn ya fara kuka, ajewa tayi da sauri taje inda yake ta ɗaukeshi ta rungumeshi, kallon inna tayi tace "mu tafi"
da sauri inna ta ɗauko mata takalminta kin sawa tayi tsaban zafin zuciya kawai ta fita da yaron a rungume babu takalmi, duk cikinsu babu wanda ya iya hanata tafiya da jaririn suna tsoron yi mata magana ma, share hawaye tayi a hanya tana jin son yaron yana ratsa jiki da jininta, inna tayi shiru tana so tace ta sassauta rikon data yiwa yaron tana jin tsoro domin har ita yau tana tsoron najwah, suna shiga gida tana rike dashi taje bakin murhu ta hura wuta ta girka ruwan zafi, saida yayi zafi sosai kafin ta juye a baho, shiga ɗaki tayi da ruwan ta ɗauko klin da soso, gyara ɗaurin zanin tayi sannan ta yanke cibiyan ta fara mishi wanka, yana kuka tana cewa "ka daina kuka kaji insha Allah ba zaka taɓa kuka ba matukar ina raye"
saida ta gama mishi wanka ta sashi a sabon zaninta ta rungumeshi, kuka yake yi sosai, ta gane yunwa yake ji, goyashi tayi ta fita, wajen shanunsu taje ta fara tatsan madara, saida ta tatsi dayawa kafin ta koma gida, saukeshi tayi ta fara bashi madaran, sha ya fara tana kallonshi kamar tana kallon meerah kama suke sosai da meerah, saida ya koshi kafin yayi shiru bacci ya ɗaukeshi, akan gadon inna ta kwantar dashi sannan ta kwanta a gefenshi ta kasa koda kyafta ido ne kallonshi kawai take tana tuna tun lokacin da suke yara da Adda meerah har zuwa yanzu da take mafarkin ta mutu domin har yanzu bata yadda da gaske adda meerah bata raye ba, inna ce tayi sallama da abinci a hannu, ajewa tayi a hankali tace "najwah sauko kici abinci kinga tun jiya rabinki da abinci"
girgiza kai tayi, tana jin ciwon kai tace "a'a inna bana jin yunwa"
shiru inna tayi, ta zauna kawai a kasa, baba ne ya banko kofar gidan ya shigo, ɗaga murya yayi yana kiran sunan inna, a hankali ta fito daga ɗakin ta durkusa, da yatsa ya nunata yace "Allah ya isa tsakanina dake safiya Allah ya isa ban yafe ba, kuma kije sai Allah ya saka min"
kallonshi tayi da mamaki tace "me nayi maka?"
yace "safiya Allah ya isa ban yafe ba, safiya abinda kika koyawa yarannan kenan? Ashe zina kike koya musu safiya? yanzu har ameera da take da aure bata daina zina ba, gashi nan arɗo ya irgamin komai yace tunda ya aureta bai taɓata ba, to aina ta samu cikin wannan jaririn da kuka shigomin gida dashi?"
dafa kirji tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un arɗo ba zaiga Annabi ba, arɗo sai Allah ya tsine mishi tunda ya yiwa gawa sharri"
yace "kece Allah zai tsine miki, safiya Allah ya tsine miki albarka keda yaran da kika haifa da wacce ta mutu da wacce take raye dama yaron da aka haifa duk Allah kwashe muku albarka"
najwah dake ɗaki tayi shiru tana jin wani abu me nauyi a kirjinta, duk maganan da baba yake faɗa sai taji kamar an ɗaura mata dutse mafi nauyi a kirji, sai hawaye take, inna tashi tayi zata tafi yace "dakata safiya, kin san ba zan zauna da ɗan zina ba, ba zan reni shege ba, sannan yarannan na fara zargin ba yarana bane, musamman najwah harma da ita Ameeran, sabida haka na sakeki saki uku"
hawaye masu zafi suna wanke mata fuska tace "usman tunda nake ban taɓa zina ba, sannan ƴaƴana basu taɓa zina ba, idan har na taɓa zina Allah ya saka maka da Alkhairi, idan kuma ban taɓa yiba Allah ya sakamin da Alkhairi ya fara nuna maka sakayya tun a duniya, Allah yabi min haƙƙina dana ƴaƴana, ƴata ta rasu usman shine zaka sakamin da wannan mugayen kalaman? ina bukatan rarrashi da hutun zuciya ina jin zafin mutuwan ƴata shine zaki bini da wannan sharrin? ban yafe ba"
shiga ɗaki tayi ta kwanta akan gadon tana kuka, najwah wacce taji komai tace "inna zama a garinnan bai kamamu ba, tashi zakiyi mu shirya mu bar garinnan"
inna tace "na yadda najwah na yadda mu bar garinnan wallahi nima ba zan iya zama ba"
tashi tayi ta fara shirya kayansu a boro, inna ta tattara duk wani abu me amfani ta zuba a katon ghana most go, najwah ta ɗaga bakin tabarma ta ciro kuɗi masu yawa sannan tace "ga wannan na tallana ne da nake ɓoyewa"
karɓa inna tayi tace "Allah miki albarka amma yanzu ki jirani zanje gidan rabi dilalliya tazo ta faɗi nawa zata siya sauran kayan ɗakin duka"
tace "to inna"
mayafi inna tasa sannan ta fita zuwa gidan dilalliya, baba ya shigo ɗakin ya kalli najwa wacce taki kallon inda yake, takadda ya wurga mata yace "ga takaddan sakin uwarku sai kuje kuyi ta bin maza kuna zina kuna samun kuɗi idan kunga dama ku tara duniya da abinda ke cikinta idan kunga dama kubi mazan duniya haka dai zaku kare a wahale a tsiyace"
fita yayi daga ɗakin ta kalli takaddan da larabci aka rubuta hakan yasa ta gane me a ciki, sawa tayi a jakan inna sannan ta kalli yaron dake bacci, murmushi tayi, inna suka shigo da dilalliya ta duba kayan duka sannan tace "to gaskiya safiya kayanki basuda wani kyau, kinga tsofin yayi ne amma naga halin da kuke ciki zan siya da daraja"
inna tace "na gode sosai Allah ya saka da Alkhairi"
tace "ameen"
kuɗi ta ciro masu ɗan kauri ta irga ta bata, karɓa tayi da godiya, bayan ta tafi inna ta kalli najwah tace "wani suna zamu sawa yaron?"
shiru najwa tayi da ace macece da zasu sa mata ameerah, inna tace "ko nasa sunan babana?"
tace "eh inna"
a hankali ta fara raɗa mishi suna yadda akeyi, murmushi tayi tace "sunanshi HABIB"
najwah ta kalleshi tace "a wajena kuma sunanshi HABIBI"
inna tace "Allah ya raya habib da albarka yasa ya zama ɗa na gari"
tace "ameen inna"
goyashi tayi a bayanta tasa mayafi sannan inna ma ta tattara kayansu ta rike suka fita, kuka ya fara tana girgizashi tace "habibi yi hakuri yi shiru habibi"
tafiya sukayi najwah bata kara juya baya ta kalli gidan ba, haka kuwa tayi lokacin da sukazo barin garin bata kara kallon garin ba, mashin suka hau aka tafi dasu can cikin gari nesa da garinsu sosai, murmushi tayi lokacin da suka shigo cikin birni ta kalli inna wacce bata saba da birni ba, tace "karki damu inna komai zai zama da sauki"
tace "to najwah"
tace "me mashin taimako nake nema"
yace "ina jinki"
tace "dan Allah ina zamu samu

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login