Showing 24001 words to 27000 words out of 40241 words

Chapter 9 - NI DA MUNEEB

Start ads

11 Sep 2025

62

Middle Ads

komai yana lissafa musu duk yaransu da school ɗin da suke, a hankali suka tashi yace "kowannenku inada voice nashi da video ɗinshi idan kunga dama kuje ku tona asirin muneeb idan kunga dama ku bari'
sum sum suka juya zasu tafi kowanne bai kara magana ba, suna fita ya koma ya zauna wayarshi ya ɗaga ya buɗe data, ganin sameer yasa hoton Azad a status ya buɗe yana kallo, murmushi yayi ganin yayi kyau ya kashe datan.
kiran layin azeez yayi, yana ɗagawa yace "ina video da voice ɗin suke?"
azeez yace "boss ai duk na tura maka cikin memory ɗin da muke aje kowane sirrinmu kuma kasa a cikin agogon"
yace "okay na aje a gida ya zama dole mu shirya komai domin su Alhaji sale sun fara min barazana ya zama dole na kula da wannan memory yanzu nakeso na turawa Alhaji lawan voice da video ɗaya sabida su san ba barazana nake musu ba"
yace "okay boss"
katse wayan yayi da sauri ya fita ya rufe office ɗin, da hanu ya yiwa guards alaman zasu tafi, buɗe mishi mota akayi ya shiga ba ɓata lokaci suka bar company, motoci sun kai biyar suka rufa mishi baya, Bluetooth yasa a kunneshi yayi shiru yana kallon hanya, har suka isa gida aka buɗe mishi ya fito, da sauri ya shiga ciki domin yanzu zai fito su koma, su batool suna falo suna kallo sun maida hankali kan tv suna kallon film da alama ya musu kyau, da sauri suka kalleshi lokacin daya shigo, kallo ɗaya yayi musu, batool tace "lafiya?"
yace "abu nazo ɗauka"
daga nan ya haura sama da ɗan gudunshi yake taka stair case, shiga ɗakinshi yayi yaje direct inda yasan ya ɓoye agogon, dubawa ya fara, bai gani ba, da sauri ya cire drower gaba ɗaya yana dubawa, gabanshi ya faɗi ganin babu agogon, gashi komai daya shafi sirrinshi yana ciki, haukacewa yayi a ɗakin yana watsi da komai yana duba agogon, zufa ya fara ganin ya duba ko ina lungu da sako har gadonshi saida ya ɗaga bai gani ba, zama yayi a kasa yace "na...na...na shiga uku"
Azeez ne ya kirashi ya ɗauka jikinshi yana rawa yace "azeez the agogo is not with me anymore"
azeez yace "what??? boss kasan me a cikin wannan agogon kuwa? boss idan agogon nan ya ɓata mun shiga uku, wallahi boss guduwa zanyi na bar kasar nan"
yana yamutsa gashin kanshi da ihu yace "is not here an sace azeez"
cikin tashin hankali azeez yace "mun mutu boss wallahi sunanmu gawa"
wurgi yayi da wayan ya fara marin kanshi a birkice yace "ina ka aje muneeb? aina ka aje wannan agogon?...m..mu..
muneeb kai wani irin wawa ne?"
idanunshi sunyi jajur jijiyoyin kanshi sun tashi sosai banda safa da marwa babu abinda yake yi a ɗakin, flower ves ɗin dake gefenshi ya ɗauka yayi wurgi dashi, karan da sukaji duk suka kalli sama, batool ta dafa kirji sameer ya kashe tv duk suka kalli sama, kwalaben turaren yayi watsi dashi, toshe kunne batool tayi jin karan fashewan kwalaben, idanu a waje tace "sameer meya samu yayanku?"
sameer yace "ban sani ba unty"
da ihu yace "nooooooo"
har stair saida sukaji yana girgiza, duk sun kasa zuwa inda yake, dafa kai yayi da sauri ya samu waje ya zauna, kasa zaman yayi kawai ya fita kamar zaki, kallonsu yayi da idanunshi jajur yace "waye ya ɗau agogo a ɗakina?"
shiru sukayi suna kallon juna, a tsawace yace "waye?"
shiru sukayi, yace "ba....ba...bab....."
marin kanshi yayi jin maganan yaki fitowa yace "ba...bab...bab..."
kuka ya fashe dashi kawai yana kallonsu, jikinsu yayi sanyi musamman batool, rikeshi tayi cikin kwantar mishi da hankali ta zaunar dashi akan sofa, kallon sameer tayi da alaman ya bata ruwa, ruwan sanyi ya ɗauko mishi ya tsiyaya a glass cup, karɓa tayi ta kai bakinshi, kallonta yayi da idanunsa da sukayi jajur ga hawaye daya jiƙa dogayen eyelashes nashi, sai ya zama kamar wani ƙaramin innocent baby boy, lips nashi pinkish sunyi jajur, ya girgiza mata kai, tasa hanu a suman kanshi dake a hargitse ta shafa sannan tace "sha ruwa muneeb"
a hankali ya buɗe baki yasha ruwan, yaji yana sauka kaɗan daga tsananin fushin da yake ciki, a hankali ya ɗaura kanshi a cinyarta yayi shiru, shafa kanshi take a hankali, su sameer suka zauna suna sukayi shiru, duk zuciyansu yana tsinkewa suna tsoron ya gane Azad ne ya ɗauka.

_*Paid book ₦400 ta account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, evidence of payment via 08144818849*_


_Jiddah Ce....✍️_
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 8*


~Yana kwance bai ɗago kai ba kuma ba bacci yake ba, firgigit ya tashi da sauri yana kallonta, yace "wait...ina Azad?"
ba sameer ba harda ita saida sukaji hantar cikinsu ya kaɗa, yace "sameer bani wayarka"
jikin sameer yana rawa ya mika mishi karɓa yayi ya fara duba status ɗin da yasa, kallon hanun Azad yayi sannan ya kallesu yace "ina Azad?"
sukayi shiru, tsawa ya daka musu "i..i...ina Azad?"
atare sukace "yaje birthday party ɗin abokinshi"
cewar jabeer, kallonsu yayi yace "kenan kuna sane ya ɗauki agogona?"
shiru sukayi, yace "kun...sane?"
suka jijiga kai alaman A,a,, kiran wayan Azad ɗin ya fara babu kakkautawa, ganin bai ɗaga ba yace "aina yaje?"
sukayi shiru dan basu sani ba, yace "aina!!!"
ssmeer a tsorace yace "wallahi bamu san aina suke yi ba"
yace "motoci nawa ya tafi dashi"
jabeer yace "takwas"
tashi yayi ya ɗau wayarshi yana cigaba da kiran wayan Azad ɗin, tsoronshi kada Azad ya taɓa wani abu agogon ya fara magana, kira yake har yanzu bai ɗaga ba, yace "Az...Azad ka ɗauka mana"
yasan wautan Azad zai iya careless da agogon koma ya kyautar idan yaga dama, tsaki yaja yana kara kira.
Azad yana tsakiyan fili da birthday boy suna tikan rawa, yasa wayarshi a silent sabida bai son damuwan yayunshi a cewarshi, shine ya zaka idon gani a wajen komai sai an kira sunanshi, kuɗin hanunshi duka ya gama a wajen, sai dare suka tashi daga wajen kallon agogo yayi yaga karfe 8 na dare, dafa kirji yayi yace "na shiga uku Allah yasa na riga babban yaya zuwa gida"
shiga mota yayi yana kallon agogon daya kara mishi daraja a wajen, kowa so yake yayi hoto dashi saiya nuna agogon a cikin hoton hankalinshi yake kwanciya, gabanshi ya fara faɗuwa lokacin da suka kusa gida, yace "ya Allah ka taimaki bawanka Azad kasa ya riga ya muneeb zuwa gida ameen, ya Allah ni maraya ne kaga banada mama banada baba kaji tausayina banason bulala"
ana yin parking ya fito yana hamma yana mika ya gaji sosai ga bacci da yake ji, cikinshi ne ya ɗibi ruwa ganin motar babban yaya a cikin gida alama ya dawo, "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga uku"
tafiya ya fara da kyar, s hankali ya tsaya a bakin main parlour, takalminshi ya cire ya rike a hanu, cikin sanɗa ya buɗe kofan, ganin duhu a ɗakin yayi hamdala cikin sanɗa yake tafiya baison kowa yasan ya shiga, hanyan stair ya nufa zai fara takawa aka kunna wutan, saida ya kusa faɗuwa garin juyowa, ido huɗu sukayi da ya muneeb dake zaune akan sofa ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya yana girgiza kafa yana kallonshi, gefe kuma su ssmeer ne unty batool tayi shiru, ɓoye hanunshi me ɗauke da agogon yayi yace "babban yaya ina wuni ya gajiya?"
kallon da yake mishi yasa ya haɗa hannu biyu yace "dan girman Allah kayi hakuri wallahi tallahi kuskure ne"
da hanu yayi mishi alaman yazo, jikinshi yana rawa yazo ya tsaya nesa dashi, yace "gani"
yace "karaso"
zuwa yayi yana hawaye yace "gani"
tashi yayi, a tsorace yayi baya zai gudu, rikeshi yayi, yace "wallahi zan cire maka agogon banyi komai dashi ba hoto kawai nayi"
cire agogon yayi ya mika mishi bai karɓa ba kuma bai daina kallonshi ba, yace "unty batool ki tainakeni karki bari ya dakeni, ya sameer ya jabeer kuce kar ya dakeni bana son duka, babban yaya kaga ni maraya ne banida mama banida baba dan Allah karka dakeni...."
janyoshi yayi jikinshi ya kankameshi, shiru yayi yana kallon bayanshi so yake ya tabbatar da gaske wannan ya muneeb ne?
duk suka kalleshi harda batool, cikin sanyin murya yace "me..me..meyasa baka tambayeni ba ka ɗauka?"
yace "kayi hakuri ba zan kara ba"
shiru yayi yana jin son yaron a ranshi, yayi niyan yayi mishi duka amma kalman maraya daya kira yasa jikinshi yayi sanyi, ya tuna mishi da abubuwa dayawa da suka faru a rayuwarshi, a hankali yace "karka kara"
yace "to babban yaya na gode"
zameshi yayi ya fara share mishi hawayen, ya kalli dressing ɗin da yayi yace "je kayi wanka ka rama sallolin da ake binka"
yace "to na gode"
a hankali yake tafiya yana juyowa a zatonshi ba da gaske ya yafe mishi ba, koda ya shiga ɗaki rufe kofan yayi da key dan har yanzu bai yadda ba zai mishi komai ba, kallon agogon yayi sannan yasa a aljihu kawai ya fita daga gidan yana kiran wayan Azeez, murmushi batool tayi taga jabeer da ssmeer sun sauke nannauyan ajiyan zuciya.


Inna na zaune tana tsifa ita kuma najwah tana bakin murhu tana girki, ta rame sosai sabida yawan tunani, ta kara zama fara dal, gashinta ta kame ta dunbuza waje ɗaya sannan taci gaba da gyara wutan, habib ne ya tashi daga bacci kuka ya fara, da sauri ta wurgar da abin gyaran wutan ta shiga ɗakin da gudu, ɗagashi tayi tace "habibi ka tashi?"
madaran shanu data tanada mishi ta ɗauko ta fara bashi, sha yake tana murmushi tace "yawwa habibi shanye duka"
saida ya shanye ta cire kayan jikinshi ta ɗibi ruwa a flask tayi mishi wanka sannan ta canja mishi kaya baby oil data siya mishi ta shafa mishi, goyashi tayi ta koma tana cigaba da aikin, inna tace "najwah kawoshi na rikeshi tunda kina girki"
tace "a,a inna banson yayi kuka, idan yana wajenki kuka yake"
tasan bataso ana rabata dashi shiyasa tayi shiru tana cigaba da tsifan, yana bayanta har ta gama girkin ta juye a kula, ajewa tayi a kusa da inna tace "bari naje kasuwa yanzu na san nayi latti amma banson ina fasa zuwa"
inna tace "to najwah Allah ya bada kasuwa"
tace "ameen"
hijabi tasa green tasa takalmi me ɗan kyau data siya sannan ta gyara kwanciyan habib a bayanta ta ɗau kwanon nonon da sauran robobin da zata buƙata, fita tayi daga gidan tana tafiya cikin sabawa da tallan ta nufi bakin titin, kashin ta tara sannan ta shiga ta zauna bayan ta faɗi bakin kasuwa zai kaita, tana zama habib ya fara kuka, tace "yi hakuri habibi yanzu zamu isa yi hakuri"
me mashin yace "ɗanki baison zama"
tace "wallahi haka yake bayason na zauna wai saide muyi ta tsayuwa"
yace "Allah sarki"
tafiya sukayi me nisa kafin suka isa bakin kasuwa, fitowa tayi ta biyashi kuɗinshi kafin ta sauke nonon ta kai inda ta saba ajewa, gaisawa tayi da sauran matan dake wajen suna saida kayan miya da kuma masu saida dankali, sauke habib tayi ta rikeshi a hanu ta fara siyar da nonon cikin kwarewa, sameer wanda yazo tun ɗazu yana zaune a mota yana jiran ko zata zo, sabida babban yaya yace kada su kara siya mishi nono me tsami kuma nata babu tsami, ya lura duk lokacin da suka siya nono a wajenta baya zama da tsami kuma babban yaya yana enjoying sha, murmushi yayi lokacin da yaga tazo, yazo ya gaisheta amsawa tayi tace "yau ka zo da wuri"
yace "ai idan banzo da wuri ba kina siyarwa ki tafi bakya jira"
tace "ɗana ne baya son rana shiyasa idan rana ya fito nake tafiya ko ban gama siyarwa ba"
kallon yaron yayi masha Allah kamar ɗan larabawa yace "amma ke balarabiya ce ko?"
girgiza kai tayi tace "mi fullo me ka gani?"
yace "ɗanki ne kamar balarabe"
murmushi tayi ta kalli yaron yana kallonta tace "habibi wai kayi kama da balarabe?"
murmushi yayi jin sunan data kira yaron dashi, yace "habibi sunanshi?"
tace "habib sunanshi inace mishi habibi sabida ina sanshi sosai"
yace "Allah sarki"
sa mishi tayi dayawa ya mika mata kuɗin ta karɓa tace "to sai kuma ka dawo"
yace "to maman habibi"
ya kalli habib yayi murmushi yace "habibi sai anjima"
murmushi tayi har fararen haƙoranta suka bayyana, idan kanaso ku shirya da ita to kaso habib idan taga kana son habib ko baka sonta bata damu ba, Ita dai aso ɗanta, idan kuma ka ki habib tofa tsanan duniya zata ɗauka ta ɗaura maka, saida ta siyar duka kafin ta goyashi ta tattara kayan ta yiwa sauran sallama sannan ta tafi, tana shiga gida ta saukeshi ta bashi madara sannan taci abinci ta kwantar dashi gefe ta shiga banɗaki tayi wanka fitowa tayi tasa riga baƙi me kyau ta zauna kusa dashi tana kallon inna dake tsifa, tace "wai har yanzu inna baki gama wannan tsifan ba?"
tace "ina ruwanki tunda ba tayani zakiyi ba? da Ameerah ce data gama har tamin kitso"
jikinta yayi sanyi jin sunan ameerah, hawaye ya cika mata ido ta sunkuyar da kai, itama inna saida tayi maganan sai kuma taji sanyin jiki itama, najwah tace "inna ba zan taɓa yafewa mutanen rugan mu ba, bazan taɓa yafe musu ba"
ɗaukan yaron tayi tace "ba zan taɓa bari habibi ya sansu ba, kuma kullum Allah ya isa zan rinƙa musu har sai naji labarin rugan ya kama da wuta babu wanda ya fita da rai a cikinsu, sannan habibi zan bashi duk wani gata da ɗa yake samu a wajen uwa harma dana uban zan haɗa, ba zai taɓa wulaƙanta ba matukar ina raye saide idan na mutu, ba zan taɓa bari jinin adda Ameera yasha wahala ba kamar yadda ita tasha"
kuka take yi sosai, itama inna kukan take har suka gashi sukayi shiru, ta kudura a ranta zata kula da ɗanta sosai.
haka akayi tana bashi kulawa koda yaushe a bayanta yake bata yadda ya rabu da ita, idan sun rabu saide salla ko alwala da haka har ya fara girma ya fara wayo, mama shine sunan da yake kiranta, ta bashi kulawan da ko wani me gatan bai samu ba, yanzu haka tana tara kuɗin da zata kaishi school ne saide abin yayi yawa kuɗin yaki haɗuwa gashi ya fara wayo tafi so ya fara karatu tun yanzu, duk wani ɗawainiyansu yana kan wannan tallan nonon shiyasa kuɗin basa isa.

sameer dake zaune kasa yace "yaya wallahi na dubata ban sameta may be batada lafiya ne shiyasa ban siya a wajenta ba"
tsaki yaja ya aje nonon dake da bala'in tsami yace "ka koma...I...idan ka ganta a company zata rinƙa kai mana kullum"
yace "to amma fa tanada aure anya mijinta zai bari?"
yace "ba...ban...ban damu da aurenta ba kaje kawai"
yace "to"
tafiya yayi ya koma bakin kasuwa, hamdala yayi tareda godewa Allah ganin yanzu take sauka a mashin, da sauri yaje ya karɓi habib dake hanunta, murmushi tayi data ganshi tace "kaine?"
gyaɗa kai yayi yace "eh nine"
kayan ta ciccire ta kai wajen zaman yana wasa da habib yace "habibi ya kake?"
ta zauna tace "bani shi karya gajiyar da kai"
yace "a,a karki damu dama magana nakeso muyi"
tace "to ina jinka"
ya zauna akan roban dake gefe yace "dama Inaso nayi miki wata tambaya ne amma dan Allah kada ranki ya ɓaci"
tace "to ina jinka Allah yasa na san amsa"
yace "kinada aure?"
murmushi tayi kawai ta girgiza kai, yace "okay kun rabu da mijinki?"
murmushi tayi ta kuma girgiza kai, yace "to habibi ba ɗanki bane?"
tace "ɗana ne"
yayi shiru sai kuma yace "dama kindirmo mukeso ki fara kaiwa a company ɗin su babban yayanmu"
kallonshi tayi tace "wani company?"
yace "zan kaiki ko yanzu amma sai idan kin amince amma ina tabbatar miki zakifi samun ciniki saide dole kiyi hakuri domin babban yaya sam sam baida alkibla wani irin mutum ne a juye"
murmushi tayi tace "ban damu ba abinda ya kaini shi zanyi"
yace "to zamu iya tafiya yanzu?"
tace "to ba damuwa"
a ranta tace "Allah yasa lokacin shiga school na habibi ne yayi domin tana jin zata iya jure kowane wulaƙanci ne domin ganin tasa habibi a school, motarshi ya buɗe mata da sauri ta girgiza kai tace "a,a zan shiga mashin sai yabi bayanka"
yace "to ba damuwa"
mashin ta shiga shi kuma ya shiga motan suka fara tafiya, suna bin bayanshi habibi na bayanta tana bin titi da kallo, har zuwa katafaren company ɗin ya shiga kuma aka bar mashin nasu ya shiga sameer ne yace a bari, suna shiga ta fara kallon wajen, data fita ta kalli sameer tace "anya zan iya saida nono anan?"
yace "karki damu zaki iya komai ai koya ake"
tace "amma ya sunanka?"
yace "sameer"
tace "ni kuma najwa"
yace "to yace idan kin yadda ga can inda zaki rinƙa zama"
kallon wajen tayi me kyau amma a waje waje daban dana masu aiki s wajen, a hankali tace "to"
ya tayata ɗauka ta komar wajen, yace "to daga yau kin zama me aiki a company ɗin makawa"
murmushi tayi tace "to na gode"
yace "bari na shiga ki dama min wanda zan kai mishi"
a hankali ta fara damawa cikin tsafta ya karɓa ya tafi office na ya muneeb, knocking yayi yana zaune suna magana da wani, jin bai amsa ba ya tura kofan ya shiga, da sauri muneeb yayi kasa da ledan dake gabansu, yace "kai sameer...za...za ..zaka shigo mana babu knocking?"
yace "am sorry"
nonon ta aje mishi yace "ta yadda da aikin yanzu haka tana cikin company"
gyaɗa kai kawai yayi, ssmeer zai tafi yace "i...i...ina fatan ka faɗa mata iya limit nata?"
yace "eh na faɗa mata"
fita yayi, muneeb ya sauke ajiyan zuciya kafin yace "back to business"
littafi suka fara aka ɗanka mishi kuɗi cash kafin suka gaisa mutumin ya tafi, nonon ya ɗauka ya buɗe fari sal, murmushi yayi bai san meyasa Allah ya ɗaura mishi son nono ba, kullum idan baisha bama sai yaji kamar baida lafiya, a hankali ya tashi ya ciro kankara a fridge yazo ya zuba a ciki, sha ya fara hankali kwance.
najwah bin masu aiki take da ido yanayin da suke aiwatar da komai cikin tsari ya birgeta,sameer yazo yayi mata sallama kafin ya tafi, ta zama shiru saide masu aikin sun karɓeta hanu bibbiyu kowa yana siyan nonon a wajenta, taji sanyi a ranta, taji daɗin zata kai habibi school, a ranta tace "da yaddan Allah zan jure komai matukar zan rinƙa samun kuɗi haka na kai

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login