Showing 15001 words to 18000 words out of 40241 words
yace sai an bashi dubu biyu, inna tace "bawan Allah dubu ɗaya ake zuwa"
zagin inna yayi najwah ta fizge jikinta ta kwasheshi da kokawa, subhanallah inna tace "najwa zaki kasheni ne? najwah so kike ƴan rugan nan suci gaba da zaginki?"
ganin ta kasa rabawa tace "hande min boni minkam, najwah idan baki sakeshi ba zan ɓata miki rai"
ganin abin yafi karfinta ta ƙwalawa amaryan baba kira tace "sa'ade kizo ki tayani"
fitowa tayi tazo itama babu takalmi ta fara jan najwah da kyar suka shigar da ita gida, tana huci tana mayar mishi da zagin da yake mata, kamar zata fito ta saman gidan domin inna ta kulle kofa, da kyar ya karɓi dubu ɗaya ya tafi, inna ta shigo da sauran kayan, tana shiga ta kalli najwa ta ɗaga hanu sama tace "ina rokon Allah ya shiryamin ke najwa, Allah ya shirkeyi, najwah kinaso ki ɗauramin ciwon zuciya? kuyi koyi da yayarki mana najwah, ki zama me hakuri kamar ita amma kullum kina janyomin abin faɗa a gari?"
shiru tayi batayi magana ba har inna ta gama sannan ta shiga ciki, shiri tayi ta fito tace "bari naje gidan adda na dubata"
tace "to amma dan Allah kar kiyi faɗa ki zama me hakuri najwah"
tace "naji"
shiga ɗaki inna tayi ta ɗauko kayan miya masu yawa su daddawa dasu barkono da sauran ganyen data busar tace "gashi ki kai mata kice ina gaisheta tayi hakuri ta maida komai ba komai ba"
tace "to inna"
tafiya tayi bata haɗu da kowa ba har ta isa gidan, a kofa tayi sallama, jin hayaniya yasa tayi saurin shiga, waro ido tayi ganin uwar mijin meerah da kanwarta sun sata a gaba suna zaginta uwa da uba, ita kuma tana durkushe tana hawaye, ganin kanwar ta zunguri kan meerah batasan lokacin data shigo tace "ke nafise karki kara taɓamin adda ta idan uwarku ce zata mata faɗa to ku kada kusa baki domin ba baiwarku bace"
ameerah da sauri ta tashi ta rike najwa tace "boɗɗi kinzo? kin kini bakya zuwa boɗɗi nayi kewarki"
tace "haba adda me zaisa na rinƙa zuwa gidan ɓarayin shanu, wannan bakin cikin da zan tarar na cin mutuncin da zasu miki shi nake gujewa"
murmushi tayi tace "ba komai fa boɗɗi ina zaman lafiya dasu yau akasi aka samu"
tace "wallahi hankalinki ba'a kwance yake ba adda ki duba yadda kika rame? kalli yadda kika zama kamar bakya cin abinci?"
nafise dake tsaye tace "ai ba gidan yunwa kuka kawo ta ba"
tace "yunwa kam na nawa? ai kinsan ba haka muka kawota ba gidanmu dai yafi karfin abinci saide wani abin"
tace "eh amma bama dukanta kamar yadda ubanku yake dukan uwarku..."
ai kafin ta rufe baki najwah ta shaƙo wuyanta domin bata ɗaukan zagin inna, uwar mijin tazo zata ja najwah tureta tayi ta fara dukan nafise kamar an aikota, ameerah cikin tashin hankali take jan najwa, nafise ihu ta fara, meerah cikin ɓacin rai tace "najwah idan kika kara dukanta ba zan kara kulaki ba wallahi"
cak ta tsaya da dukan tana huci, nafise kuka take bakinta ya fashe, meerah cikin ɓacin rai tace "me tayi miki da zaki daketa?"
zatayi magana tace "kimin shiru, Idan kinsan faɗa zai kawoki gidana karki kara zuwa"
cikin ɓacin rai tace "sabida ke ba zaki iya magana ba suna cutar dake dan zan rama miki shine zaki ce karna kara zuwa? to idan anyi duniya Dan manzo babu ni babu kara zuwa wannan gidan"
wurga mata kayan miyan tayi a fusace ta fita ta bar gidan, ameerah kuka ta fara ta shiga ɗaki tana kuka sosai, najwah bakin rafi ta tafi ta tsinko mangoro dayawa kafin ta dawo gida, bata nunawa inna komai ba ta shimfiɗa tabarma ta cire mayafin kanta, datti kanta yayi sosai amma bata damu ba, ta fara shan mangoronta, saida ta shanye tass kafin ta tashi ta wanke hanu, baba ne ya shigo da sauri taje ta karɓi ledan hanunshi, yana zama amarya ta fito ta fara kirga mishi faɗan da najwah tayi itada me mashin, bulala me tsayi ya ɗauko daya riƙe najwa saida inna ta fito karɓanta, har fitsari saida tayi a wando tsaban zafin dukan, jikinta a farfashe ta koma ɗaki ta kwanta akan gadon inna tana raira kuka, inna tace "banji zafi ba, daidai gara ya rinƙa dukanki ko Allah zai sa kiyi hankali"
tana cikin kuka ameerah ta shigo, ta kasa zama sabida abinda najwah ta faɗa, ba zata iya bari najwah tayi nesa da ita ba, shiyasa ta zauna a bakin gadon tana jinta tana kuka, a hankali tace "kinga abinda kike janyowa kanki ko? kullum ina ce miki ki zama me hakuri bakya ji najwah, yanzu idan kikayi aure haka zakici gaba da zama mara hakuri? idan ma bakiyi aure ba idan na haife yarana saisu rinka jin mamansu tana dambe da mutane? kin ganin kin kyauta? najwah ki rinƙa sanin kin girma, kin san ina sanki ba zan iya ganinki kina kuka hankalina ya kwanta ba koda kece da laifi, dan Allah ki daina kinji?"
cikin kuka tace "ba kince kada na kara zuwa gidanki ba?"
tace "haba boɗɗi ta me zaisa na hanaki zuwa inda nake? cikin ɓacin rai nayi maganan shiyasa ma na biyo bayanki, kiyi hakuri ba zan kara miki tsawa ba kinji?"
tace "to"
Ameerah tace "tashi to ki rakani sabida dare bayi"
tace "to dama ban kaiwa shanu ruwa ba"
tashi tayi tace "amma kanki yayi datti boɗɗi har tsami yake"
turo baki tayi tace "banson kitso nikam"
tace "to muje na wanke miki kafin na tafi"
zatayi magana taja hanunta tace "muje banson musu"
ruwan sanyi ta ɗiba sannan ta haɗa dana zafin da inna ta girka, omo ta kumfata ta fara wanke mata gashin, saida ta tabbatar babu datti sannan tace "boɗɗi ki rinƙa wanke kanki"
tace "to"
ruwan ta ɗiba dayawa a babban roba suka tafi wajen shanayensu ta aje musu ta duba lafiyansu kafin ta raka Ameerah har kusa da gida sannan ta juya tana wasa da kara a hanunta tana waka har ta isa gida, kwanciya tayi ta fara bacci domin ta gaji, inna salla tayi tayita addu'a Allah ya shirya najwah yasa ta daina wannan halin na faɗa da kowa.
*Jiddah Ce....✍️*
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 5*
~Har dare suna zaune shiru ba karamin haushi sukaji ba da babban yaya ya ɓata wannan cake da shagalin, batool wacce take karfin hali sabida ba lafiyane da ita ba, tace musu "kunga muneeb ba wanda zaku rinƙa yiwa gwaninta bane, shi mutum ne wanda yake a juye ba zaku taɓa gane inane alkiblanshi ba, kada ku kara mishi surprise"
sameer yace "amma ai shi yana mana"
tace "dashi daku ba daya ba, kunfi kowa sanin halin yayanku"
shiru sukayi Azad banda tsaki ba abinda yake yi, jabeer tsaban haushi ya kasa cewa komai, kawai yace "ni zan tafi school ba zan tsaya haushi ya kasheni ba"
shiga ɗaki yayi ya ɗauko katon jakanshi na baya ya rataya ya rike laptop ya kalli sameer da yake kallonshi yace "zaka je ne ko na tafi?"
tashi yayi yace "bara na ɗauko jakata nima"
ɗauka yayi ya fito yana jan zip ɗin, sukace "Azad ka kula da unty batool sai dare zamu dawo"
yace "sai kun dawo"
fita sukayi suka shiga zazzafar motarsu driver ya jasu da guards suka bi bayansu, tsaki jabeer yaja yace "wallahi babban yaya mugun ɗan iska ne"
sameer yace "ai yafi karfin ɗan iska ma saide ɗan guguwa"
dariya jabeer yayi, wayanshi ne yayi kara da sauri ya duba yaga babban yaya ɗauka yayi jikinshi na rawa yace "hello"
cikin rashin fara'a yace "nono zaku siyamin na fridge ɗina ya kare banda me...me..tsami"
yace "to babban yaya"
kallon sameer yayi yace "mu juya mu tafi kasuwa"
yace "me kuma?"
"wai nono yake so nashi ya kare"
da sauri suka cewa driver ya juya zuwa kasuwa, a inda suka saba siya mishi suka siyo babu tsami ko kaɗan, ansa musu a babban leda sameer yana rike dashi jabeer kuma yana rike da wayarshi, sameer yana juyawa yayi karo da mutum, najwa wacce nonon yake kanta faɗuwa yayi ya wanke mata fuska da jikinta, waro ido sameer yayi ya tsaya yana kallonta, wani irin huci take yi tana kallonshi da dara daran idanunta, ya kasa magana ita kuma tana tafasa jin baice mata ko sannu ba saima kallonta da yake, cikin masifa tace "bakaga abinda kamin ba?"
yace "sorry"
wani tukukin bakin ciki ne ya tsaya mata a wuya jin da turanci ma yake mata magana, ta ɗau nonon dake gefenta batasan ko na waye ba ta watsa mishi shima jikinshi ya ɓaci, waro ido jabeer yayi da sauri yazo yace "ke bakida hankali ne? zaki watsa mishi nono?"
tace "shi hankalin ne dashi daya bige nawa?"
hayaniya suka fara guards nasu sukazo da sauri, ɗaya ya daka mata tsawa itama a fitsare ta juya zata mayar mishi taga bindiga a hanunshi, tsit tayi bata kara cewa komai ba sai rawan da jikinta yake yi, da sauri ta kalli sameer tace "dan Allah kayi hakuri kace ya ɗauke wannan bindigan daga kaina"
sameer yayi mishi alaman ya ɗauke, ɗaukewa yayi kawai ya ɗauki na ledan yaja hanun jabeer suka tafi, ajiyan zuciya ta sauke ganin sun tafi tace "wayyo najwah yau da an harbeki ya inna zatayi? Allah ne ya yiki da nisan kwana"
juyawa tayi zata tafi da sabida babu nonon da zata siyar, baya tayi zatayi ihu ganin sameer tsaye yana kallonta, hanu yasa a aljihu ya ciro kuɗi sabbi dal ya bata, kallonshi take da mamaki, tace "na me?"
yace "na wanda nayi miki asaranshi, kiyi hakuri bada sanina bane"
jikinta yayi sanyi, tace "karka damu idan nono ne muna dashi dayawa duk ruganmu babu wanda ya kai babana yawan shanu, ko sau goma zaka ɓarar zan tatso wanda ya fishi"
murmushi yayi yace "kiyi hakuri ki karɓa sabida nasa mun dawo ne domin na baki"
tace "karka damu, inna idan taga wannan kuɗin zata ce aina na samu, kuɗin sun min yawa gaskiya dama dubu ɗaya ce zan karɓa"
yace "dan Allah ki karɓa"
karɓa tayi ta cire dubu ɗaya kawai sannan tasa mishi a aljihu tace "na gode"
barinshi tayi a wajen ta tafi, binta yayi da kallo har ta shiga mashin ta tafi.
jabeer daya jima da zuwa yace "sai muje ai tunda ta tafi"
binshi yayi suka koma mota suka tafi.
zaune yake akan sofa me alfarma dake cikin gidanshi wanda gidan yake na sirri ne, babu wanda ya sanshi da gidan sai shi sai azeez da guards nashi, sai kuma wanda idan an kawo gidan, saide da zaran ka shiga gidan fitanka da rai saide idan Allah ne ya yika da tsananin nisan kwana, gida ɗaya ne tal a cikin daji, ga masu tsaron gidan da mugayen makamai, bindigun dake hanunsu ko manyan sojoji basa rikewa, duk wani abin more rayuwa akwaishi a gidan, saide wannan gidan sunanshi gidan mutuwa, duk wasu yara da za'a sace a garin tofa dasa hanun muneer, wani lokaci da kanshi yake zuwa yayi satan, kallon laptop ɗin yayi yana sanye da kayan shan iska, farin riga ne ya buɗe boturan rigan kirjinshi me ɗauke da kwantaccen gashi a waje, gajeren wando ne fari mara nauyi a jikinshi ya ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya wannan shine zaman daya saba a koda yaushe, crossing leg yake yi, laptop ya zubawa ido yana kallon jaridan daya buga da kanshi na sace yara hamsin da akayi a cikin kwana uku, a hankali ya taɓa wajen share yayi sharing ta yadda duk duniya zasu gani, muneeb yanada tarin mabiya a shafukanshi na sada zumunta, harkan magani yake hakan yasa ya zama babban dealer ɗin magani wanda yayi kaurin suna a ko ina, mutane suna bibiyanshi a social media sabida yadda yake ɗaukan mutane aiki, murmushin gefen baki yayi lokacin da yaga labarin ya fara watsuwa a duniya, kanshi ya jingina da jikin sofan yana kallon yadda ake share na labarin daya posting a second ɗaya, wine ɗin dake cikin glass cup na gabanshi ya ɗauka yayi sipping kaɗan ya mayar, knocking akayi yace "yes"
azeez ne ya shigo yace "boss an samo yara goma"
murmushi yayi yace "a cire duk kayansu a kona a basu uniform susa sannan a tabbatar an rufe fuskansu da baƙin kyalle ta yadda ba zasu gane inda aka kawosu ba koda sun gudu"
yace "okay boss"
tashi yayi zai tafi
yace "az....azeez"
yace "yes boss"
tashi yayi daga zaunen yazo gabanshi yace "ka..ka...kasan haɗarin aikinmu, abi a hankali"
yace "na sani boss"
waya ya ɗauka ya kira numbern da yayi saving da Alhaji sahabi, karawa yayi a kunne yace "ha...ha...hallo, an samu....yara... guda...goma sabbi"
shiru yayi sai kuma yace "da...da...safe a zubar da gawansu cikin gari"
katse wayan yayi yace "duk waɗanda...aka...kai.ba.a dace ba, dole a kai wasu....da safe....jirginsu zai tashi a basu uniform....su...zama cikin shiri"
yace "okay boss"
fita yayi yaja yaran da suke ɗaure da bakin kyalle a ido suna kuka da ihu, bindiga ya ciro yayi harbi yace "idan bakuyi shiru ba zan kasheku da wannan bindigan"
shiru sukayi ya shiga dasu ɗakin da wasu suke kwance a ciki, ya cire musu kyallen sannan ya kira matan dake aiki yasa suka canja musu kaya daga nan aka ɗauresu a wajen fita yayi bayan yace a basu abinci.
yana zaune yana kallon duk abinda yake faruwa a ɗakin, kwanciya yayi akan sofan ya lumshe ido, a hankali bacci ya ɗaukeshi bai farka ba sai azahar, shiga ciki yayi yayi wanka sannan yasa kayan daya cire ya fito yana waya, da hanu yawa security's alaman zasu tafi, mota aka buɗe mishi ya shiga, da kanshi zaiyi driving hakan yasa shi kaɗai ne a motar, fita sukayi suna binshi a baya da zasu motar, company ya nufa domin yanada baƙi, an shirya musu zama, yana zuwa kawai ya wuce inda zasuyi zaman, a high table ya zauna sannan ya fara musu bayanin yadda samun maganin ciwon hanta da za'a fara aiki dashi zai kasance, sun fahimta domin shi ɗin kwararre ne yanada ilimi sosai yasan kuma duk abinda zaiyi domin ya amfanar da marasa lafiya da maganin daya kawo, sun gama zama lafiya ya tashi ya koma office domin duba meke tafiya a cikin company, yana tsaka da dube dube a laptop yaga komai normal, knocking akayi yace "yes"
shigowa akayi me kawo mishi coffee ne sanye da uniform amma babban mutum ne, da cup ɗin a hanunshi ya durkusa yace "yallaɓai ga coffee"
kallonshi yayi kallon daya saba da raini da rashin sanin darajan kowa da kuma wulakanci, ya karɓi coffee ɗin ya kai baki, wani irin zafi ne ya ziyarci bakinshi da sauri ya zubar dana bakinshi, cikin tsoro mutumin yace "yallaɓai kayi hakuri wallahi....."
watsa mishi yayi a fuska, cikin jin raɗaɗi ya fara goge fuskanshi ya nuna mishi hanyan waje yace "f..f...fita"
tashi yayi yana jin azaban zafi a fuskanshi yaje wajen ruwa yana wanke fuskan, har fuskan ya ɗaye, yana kuka sosai wata daga cikin masu aikin tazo tace "baba meya sameka?"
yace "yallaɓai ne ya watsamin coffee a fuska"
rufe ido tayi ganin fuskan ya ɗaye tace "Innalillahi sannu baba gaskiya yallaɓai baida imani Allah ya saka maka"
yace "ameen".
muneeb cigaba yayi da abinda yake gabanshi, waya ya kira yace a tara duk masu aikin su jirashi a hall na meeting, cikin mintuna kaɗan suka hallara gaba ɗaya masu aikin, kowa ya zauna a kujerun da aka tanada domin meeting, sun surutu tsakaninsu kowa yana addu'a Allah yasa ba laifi sukayi ba, cikin tafiyan isa da izza, babu alaman fara'a ko kaɗan ya shigo, tsit sukayi babu wanda ya kara ko numfashi me nauyi bale tari, tsayawa yayi ya goya hanu a baya yana binsu da kallo, da kakkausan muryanshi yace "waye cleaner?"
da sauri cleaner tace "gani yallaɓai"
yace "i....i...ina ɗayar?"
tace "batada lafiya bata zoba"
yace "na..na..koreta a aiki ke kuma kizo nan"
gabanta yana faɗuwa tazo ta ɗan durkusa tace "gani yallaɓai"
ya nuna mata waje da hanunshi yace "ɗa..ɗa..ɗauko wancan roban"
fita tayi da sauri taje waje can da nisa ta ɗauko roban da suke mopping dashi, tazo dashi tace "gashi nan yallaɓai"
ya karɓa yace "da..dama ba ɓaci roban yayi ba yau kika kasa mopping...me kyau?"
jikinta yana rawa tace "am sorry yallaɓai"
hanu ya zuba a aljihu yace "jeki saman... stair"
waro ido tayi zatayi magana yace "jeki...mana"
da sauri ta fita taje saman stir ta tsaya, yace "diro"
ba ita kaɗai ba har sauran mutanen saida cikinsu ya ɗuri ruwa, duk idanunsu a waje ganin yadda yayi maganan ba wasa, kuka ta fara tace "na tuba yallaɓai wallahi ba zan kara ba na tuba"
yace "i..idan..baki diro ba na koreki"
tace "ina tareda kannena marayu da wannan aikin nake kula dasu, idan na bar wannan aikin ban san yadda zanyi dasu ba"
yace "ina ruwana?"
tana kuka tace "yallaɓai na tuba"
tsaki yaja ya kalli sauran mutanen yace "daga..yau..duk wanda bai aikinshi daidai ya bar aikin anan"
tafiya yayi ya barsu, hamdala tayi tana godewa Allah.
bacci yayi sosai a cikin office baima san lokaci yaja har anyi sallan Isha ba, kallon agogo yayi yana yamutsa fuska, da sauri ya tashi ya shiga yayi alwala yayi salla sannan ya fito ya rufe office ɗin, duk masu aikin suna nan, domin idan bai tashi ba babu wanda ya isa ya tafi, duk jimawan da sukayi babu wanda ya isa ya shigo haka suka hakura suna zaune koda kwana zaiyi to saide suma su kwana wannan dokan muneeb ne, suna ganinshi sukayi hamdala bai kulasu ba ya wuce wajen mota domin tafiya gida, suna ganin ya tafi suka tashi kowa ya kama hanyan tafiya, yana zuwa gida ya kalli falo yaga babu kowa, kallon dinning yayi yaga sunci abinci, zama yayi yaci abinci shima sosai kafin ya tashi, har zai wuce ɗakinsu sai kuma ya dawo da baya, ji yayi suna hira Azad na basu labari, buɗe kofan yayi ya shiga, kowa ya kwanta suka rufe ido kamar masu bacci, murmushi yayi ya maida kofan rufe, tafiya ɗakinshi yayi, azad ne ya buɗe ido yace "ya tafi"
duk suka tashi kowa yaci gaba da hiranshi, batool tana ɗaki tasha maganinta amma fa tana jin ciwon yana damunta sosai yau, ta daure sosai sabida batason ɗaga hankalin kannenta saide duk yadda taso ciwon yaci karfinta, numfashi take ja da kyar tana birgima, waya take kokarin ɗauka ta kasa, hawaye ta fara na azaba cikin