Showing 12001 words to 15000 words out of 40241 words
aure"
share hawaye tayi tace "na san Allah yana tare dasu babu abinda zai samesu"
teddy da Ammi ta siya mata ta ɗauka tana wasa dashi tace "last gift ɗin da Ammi ta bani kenan"
Azad ne yayi knocking yace "unty na shigo?"
tayi saurin gyara fuskanta tace "shigo baby Azad"
shigowa yayi ya zauna a kusa da ita dab, ya riketa yace "unty guess what?"
tace "ummm"
murmushi yayi yace "tomorrow is big brother's birthday"
waro ido tayi tace "really?"
yace "yes and bamu faɗa mishi ba we are going to surprise him, karki gaya mishi kinji?"
tace "bazan gaya mishi ba"
yace "thank you bari na koma muci gaba da shirya abinda zamu yi"
tace "okay nima bari na kwanta na huta"
fita yayi ya rufe mata kofan.
muneeb yayi bacci sosai kafin ya tashi yana mika, kallon time yayi yaga yace "ya Allah ashe lokaci ya tafi"
slippers yasa ya fita daga ɗakin, ɗakinsu Azad ya buɗe ya leka yaga suna bacci, shiga yayi ganin kwanciyan Azad zai sashi ciwon wuya domin kamar a zaune yayi baccin, ya zame laptop ɗin a hankali sannan ya gyara mishi kwanciyan, sameer da kanshi akan kafar jabeer ya janye kanshi ya kwantar akan pillow, murmushi yayi a ranshi yana jin sanyi, sannan ya kashe laptop ɗin ya aje akan side drower, fita yayi direct ya wuce kitchen, naɗe hanun jallabiyan yayi ya kunna gas ya fara yayyanka albasa da tattasai saida ya gama ya ɗaura mai a tukunya cikin kwarewa yake girki, ya dafa musu jellop spaghetti da kifi yaji spices sannan yasa ganyen ogwu, gefe guda yayi pepper chicken domin yana so sosai, fita yayi ya ɗauko warmer ya zuba a ciki sannan ya kai dinning ya jejjera, tunawa yayi babu kalan juice da yakeso a fridge, kitchen ɗin ya koma ya buɗe fridge ya ɗauko turmeric da citta yayi blending ya tace sannan yasa sugar da flavor ya juya sosai kafin ya ɗau glass jug yasa kankara sannan ya juye a ciki ya kai dinning ɗin, komawa ɗaki yayi sabida sai sunyi salla suke cin abinci, sallaya ya shimfiɗa bayan yayi alwala yazo ya tada salla, Azad ma sallah sukayi kafin suka fito kowa yana jin yunwa, murmushi sukayi ganin ya jera abinci ya gama kamai, Azad zaije kiran unty batool sai gashi ta fito sanye da abaya maroon tayi kyau sosai, tana ganinsu tayi murmushi duk sukaje dinning ɗin suna kallon abincin daya dafa, saukowa yayi tun daga nesa suke jiyo kamshinshi, zama yayi a kujeran kusa da batool ya janyo plate ya zuba, suma suka zuba kowa yasa daidai yadda zai iya cinyewa kafin suka fara ci, shiru wajen sabida basa magana idan muneeb yana waje, wayanshi daya aje akan table ya fara ringing, kallon sunan yayi sai kuma ya kallesu yaga kowa hankalinshi akan abinci, ɗauka yayi a hankali ya tashi zai tafi kafa batool tasa mishi faɗuwa yayi wayan ma ya faɗo gabanta, ido ta zubawa sunan da taga yana yawo a screen ɗin wayar taga Azeed, kallon sameer tayi sannan ta tura mishi wayar da kafanta so take ya ɗauki numbern, da sauri tace "sorry muneeb"
ɗagashi take yi tana cewa "sorry bakaji ciwo ba?"
girgiza kai yayi ya kalli wayarshi da sameer zai ɗauka da sauri ya ɗauke ya tashi, ya fita, da ido ta yiwa sameer alaman ya bishi, sameer ya tashi zai bishi sai yaga ya tsaya yaki tafiya da sauri ya dawo ya zauna shiru tayi ganin muneeb ɗin ya dawo shima, abinci yaci gaba da ci, ya juya fuskan wayar ta yadda ko za'a kiranshi ba za'a ga suna ba.
_*ni da muneeb littafin kuɗi ne ₦400 ta account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, katin shaidan biya ta nan 08144818849*_
*Jiddah Ce....✍️*
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 4*
~Najwah tana zaune tayi tagumi tana kallon ameera dake kuka, inna kuma tana cikin ɗaki itama kukan take, baba wanda ya gama dukan inna wai sabida taki bashi aron kuɗi ya fito yana huci yace "zanga abinda zai hana wannan auren ranan juma'a"
amaryarshi ta fito tana rangwaɗa ta ɓata fuska da kwalliya taje gabanshi tace "Allah kiyaye hanya mijina Allah ya baka abinda kake so"
ya washe haƙora yace "ameen amaryata"
har kofa ta rakashi, najwah wacce har jikinta yana rawa tsaban ɓacin rai tayi shirune sabida baba yace idan ta kara sa baki a wannan maganan zai tsine mata hakan yasa bata magana, saide tana jin zafin abinda baba yake yi, tunda amaryan tazo gidan wulaƙanci yake yiwa inna fiye dana da, kullum duka da zagi tana ji tana gani ba zata iya magana ba zaice zai tsine mata, Ameera ta kalleta cike da tausayi ta rike hanunta tace "najwa ta ki daina damuwa da halin da muke ciki, ni na yadda zan auri Arɗo domin idan naki kece baba zai aurawa shi, kuma zece zai tsine miki idan baki yadda ba, kinga gara ni nasha wahalan da ke kisha, kin san ina sanki sosai najwah dan Allah kada soyayyan da kike min ya ragu idan nayi aure kinji?"
murmushi tayi tace "adda meera koda me zai faru ba zan taɓa rage son da nake miki ba, adda ameera idan na kalleki ina jin sanyi a raina gashi baba zai rabamu..."
kuka ta fashe dashi, rungumeta meerah tayi tana shafa bayanta hankali tace "ya isa kanwata ya isa ƴar kyakkyawan gidanmu addanki tana tare dake koda yaushe kinji?"
a hankali ta share hawayen tace "to"
shiru sukayi kowacce tana jin babu daɗi a ranta, basu taso cikin soyayyan mahaifi ba kullum tsawa kullum duka wasu da innarsu duka bai bari ba, hakan yasa najwa bata tsoron faɗa sabida ta saba a gida, arɗo ne yayi sallama najwah wacce taji muryanshi kamar saukan aradu ta rufe ido tsaban bakin ciki, shigowa yayi ya tsaya a kansu yace "amaryata inata sallama baki amsa ba"
a harzuƙe najwah tace "kuma dan bata amsa ba saika shigowa mutane gida babu neman izini? banda jahilci...."
rufe bakinta meerah tayi ta girgiza mata kai, kallon arɗo tayi tace "ka jirani a waje ina zuwa"
fita yayi, najwah tace "da kin barni na gaggaya mishi magana ko zai rage wauta ɗan kauyen banza ɓarayin shanu"
murmushi kawai tayi tafi najwa jin zafin wannan auren tafi najwah tsanan arɗo amma bataso ta nuna tashin hankalin da take ciki a fili sabida najwah zata iya yin komai dan ganin ta samu farin ciki hakan yasa take daurewa sabida kada baba ya tabbatar da tsinuwa akan najwah, fita tayi ta zauna a nesa dashi, ya washe hakoranshi da suke yellow shar yace "yawwa amaryata dama nazo ne naji ko akwai abinda kike buƙata tunda gobe za'a sa lalle"
tace "babu komai ba abinda nake bukata"
yace "kin tabbata?"
jijjiga kai tayi, yace "to zan wuce can dandali ƴammata sun taru sai gobe"
kawai tace "Allah kaimu"
Ameera batada matsala batada damuwa komai tana yinshi a hankali ne ko magana bata yi da karfi cikin sanyin murya take yinshi, tafiya yayi cikin nutsuwanta ta shiga gida, najwa tace "ya tafi?"
gyaɗa kai tayi kawai ta riko hanun najwan suka shiga ɗaki, zaunar da ita tayi ta ɗauko abin yankan farce ta fara gyara mata farcen, ido ta zuba mata tana ganin yadda take yanke mata farcen cike da santa tace "adda meerah"
bata ɗago kai ba tace "na'am najwahta"
tace "ina sanki sosai"
murmushi tayi tace "nima haka"
tace "banso ki auri ɗan wannan rugan ba, naso ki auri ɗan birni me hankali wanda zai kula dake wanda zaki zauna a gidanshi kiji daɗi ki kara yin kyau sosai kifi haka kyau"
murmushi tayi kana tace "idan da rai da rabo hakan zai kasance insha Allah"
tace "adda meerah ina tsoron aurenki da arɗo babu Alkhairi fa"
tace "ba komai zan daure kada baba ya tsine mini kamar yadda yayi ikirari"
shiru tayi tana kallonta, addanta kyakkyawa ce, gashi bata magana ga yawan murmushi sannan kuma tana tsananin sonta, batada faɗa domin ko tallan nono sukaje tun suna yara sai ayi mata duka a rana yafi sau a irga, banda kuka ba abinda take yi saita share hawaye tayi shiru, saide idan najwa tana wajen take rama mata, batada kawaye haka kuma bata yawo amma najwa idan ta fita saide aje a nemota, share hawaye tayi kawai ta ɗauke kanta tana tausayin halin da zata shiga idan tayi aure wannan arɗo mara hankali kannenshi mata da maza duk ba hankaline dasu ba.
washe gari mutanen unguwa suka cika gidan domin gobe ne auren arɗo da ameerah, shanu aka yanka ana aiki saide najwah ta tafi tallan nono ranta babu daɗi, yau kaɗai ta zama shiru bata kula kowa ba duk da suna tsokananta bata kulasu harta dawo gida yamma likis, an yiwa adda meera lalle ja da baƙi, kyaun fatarta sosai ya haska lallen, kanta kuma anyi mata kananan kitso, a gefe najwah ta tsaya ta jingina da karan dake kewaye a gidansu tayi shiru tana kallonta, a hankali ta ɗago kai suka haɗa ido, murmushi tayi mata sannan tayi mata alaman tazo, zuwa tayi ta zauna a gefenta tayi shiru, meerah tace "boɗɗi kin dawo?"
tace "eh"
shiru tayi tana kallon lallen da haka har akazo akayi sakun lalle, naman shanun ake soyawa ga kuma nono da ake haɗawa na biki me kyau, ga madaran shanu da aka tanada mai yawa, da dare suna kwance a ɗaki meera ta kasa bacci itama najwah haka, dukkanninsu suna tunanin rabuwa, sun saba da junansu suna kaunar junansu, meerah ce tace "boɗɗi?"
a hankali tace "na'am"
tace "bakiyi bacci bane?"
tace "a'a"
"me yasa?"
tace "bazan iya ba ina tunanin rabuwa dake"
tace "nima haka boɗɗi amma babu yadda muka iya haka Allah ya tsara, amma ina neman wani alfarma a wajenki, dan Allah idan na tafi kada ki rinƙa sa kanki a damuwa ki zama me hakuri da kawaici ki zama me yafiya da mantuwa kinji boɗɗi na?"
share hawaye tayi tace "to adda"
da haka ransu babu daɗi har bacci ya ɗaukesu, washe gari mutanen rugan gaba ɗaya suna shagalin biki, duk da kananan magana da ake bai hana sunyi shagali me kyau ba, nono da shinkafa da dambu ga naman shanun da suka yanka a gidan amarya dana ɓangaren ango, me dj aka ɗauko daga gidansu ango, najwah ɓuya tayi a banɗaki tana kuka kamar ranta zai fita, ita kuma ameera kuka take a fili sabida damuwan ya taru yayi mata yawa, da haka har lokacin da akazo da mashina mai kafa biyu domin ɗaukanta, an cika kofan pam sai wasan mashin ake, ameerah kuka ta fara kamar ranta zai fita tana kiran najwah, a lokacin najwah ta fara kukan gaske, tana tuna duk wani rayuwan wahala dana jindaɗin da sukayi tare, har aka fita da ita inna taki fitowa daga ɗaki, da haka har aka kaita gidansu arɗo wanda aka gyara mata ɗakin taɓo me kyau akayi mata jere da samiru da kwanuka masu ado na fulani, a ɗakin aka shigar da ita, me dj aka ɗauko yazo da manyan speakers aka kunna waƙa sai tikan rawa ango da abokanshi da kannen ango suke yi, najwa tana ɗaki taki fitowa ameerah ta riketa sabida tasan idan ta fita zatayi faɗa da mutane, shagali akayi sosai kafin kowa ya watse aka bar amarya da angonta, jikin najwa a sanyaye ta shiga gida, inna tana kwance akan gado taci kuka ta koshi, itama kwanciya tayi a gefen innan tayi shiru tana hawaye.
meerah tana zaune a bakin gado kanta rufe da mayafi arɗo ya shigo, gabanta ya faɗi jin muryanshi, cire babban rigan yayi sannan ya washe baki ya hauro saman gadon, rungumeta zaiyi tayi saurin matsawa jin wani irin wari da yake, tanada tabbacin yafi sati baiyi wanka ba, da mamaki yace "me haka? niba mijinki bane?"
kanta kasa tace "banki ba amma kayi wanka kafin ka taɓani"
cikin tsawa yace "zaki fara nunamin wannan banzan halin gidanku ɗin ko? to wallahi tallahi ba zakimin na karɓa ba, dan na taimaka na aureki kinyi kwantai a gidanku, duk rugan nan babu me kulaku shine zaki tsiro da rashin kunya?"
kanta kasa tayi shiru, saida ya gama tace "kayi hakuri dan Allah"
tsaki yaja yace "zaki gane kuskurenki ne a wajena".
Sameer dasu Azad sunata shirya birthday party ɗin muneeb ba tareda ya sani ba, gidan yayi kyau sunyi decorating komai ya kammala, banda murmushi babu abinda batool take yi, har suka fito sanye da kaya iri ɗaya maroon da hula baki, cake ɗin sunyi baki, Azad ne ya fito da kaya a hanunshi yayi bala'in kyau yazo wajen unty batool yace "unty wannan suit ɗin zai yiwa babban yaya kyau?"
kallo tayi sannan ta kalleshi tace "baby Azad baka taɓa zaben abu marar kyau ba, wannan kayan shine kalan cake ɗinshi kuma nasan muneeb zaiyi masifan kyau a ciki, inada tabbacin yau ƴammata sai sun kawo mishi hari fiye da dubu"
dariya me kyau yayi sannan yace "dama babban yaya akwai farin jini gashi yau zai kara yin kyau, yanzu komai ya kammala saura kiranshi kawai"
tace "to kirashi"
wayarshi kiran iphone16 ya ciro ya kira numbern daya saving da babban yaya saide bai ɗaga ba.
safa da marwa yake a cikin office ɗin hanunshi dafe da kanshi akai akai yake share zufa, knocking akayi yace "wa..waye?"
"Azeez ne"
da sauri yace "come in"
turo kofan azeez yayi kanshi kasa yace "boss gaskiya yaron ya gudu kuma mun nemeshi sama da kasa bamu ganshi ba, lokacin da yake gudun munso mu kamashi amma ya gudu"
wani irin tsawa kamar zai fasa office ɗin yayi jikinshi yana rawa "how dare you da zaka barshi ya gudu?"
kanshi kasa cikin girmamawa kamar zai durkusa kasa yace "boss wallahi bada sonmu bane..."
ɗaga rigan azeez ɗin yayi ya ciro piston ya ɗaga kamar zai harbeshi, zaro ido yayi yace "dan Allah boss kayi hakuri karka kasheni"
yace "me amfanin...wannan? me amfanin bindiga da bazaka harbeshi dashi ba....?"
kasa ya durkusa yace "am sorry boss wallahi nama manta akwai bindiga a jikina"
wayar azeez ɗin ne ya fara ringing da sauri ya ɗaga yace "hello kasim ya akayi?"
shiru yayi yana saurara sai kuma ya kashe ya kalli muneeb da sauri yace "boss muje an ganshi amma ya kuɓuce musu kuma babu bindiga a wajensu"
bashi bindiga yayi da gudu suka buɗe kofan suka fita, muneeb ne ya shiga motarshi ya zauna, shima azeez ya shiga, guards nashi sukazo da gudu suka shiga motarsu, da kanshi yake driving da wani irin gudu yake tafiya, azeez addu'a yake a ranshi Allah ya kaisu lafiya, sun hau tsakiyan titi aka fara kiran wayar muneeb babu kakkautawa tsaki yayi ya duba sunan, ganin sunan baby Azad yana yawo da sauri ya amsa ya kara a kunne, baby Azad da yake kallonsu sameer yace "hello babban yaya ka dawo gida yanzu jikin unty batool ya tashi"
tsayawa yayi ba shiri, azeez daya tsorata yace "innalillahi"
a zatonshi accident sukayi, kallon muneeb ɗin yayi, da sauri muneeb yace "ya zama dole na koma gida, f..fi...fita ka koma motan guards zan koma gida yanzu"
da mamaki azeez yace "amma boss inda zamuje yafi komawanka gida ka manta..."
wani irin tsawa ya daka mishi yace "Are mad? ba..ba...bakasan family ɗina sunfi min komai ba?...zan..zan...zan iya rasa komai hadda rayuwata amma banda family ɗina nonsense"
buɗe marfin yayi yace "sorry boss"
a tsawace yace "out"
fita yayi da gudu ya juya motan domin tafiya guda, azeez shiga motan ɗaya daga cikin guards ɗin yayi, gudu muneeb yake akan titi matsa mishi ake domin sun san koda ya bige mutum to ya bige banza, domin ko mutuwa kayi saide ya bawa iyayenka diyyan maƙudan kuɗaɗe idan kace zaka yi case dashi ba za'a kara ganinka ba, wani irin hon yayi da gudu gateman ya buɗe, yana shiga ya fito da sauri ya shiga cikin ɗakin, turus ya tsaya lokacin da yaga suna tsaye duka harda batool ɗin sunyi bala'in yin kyau ga kuma cake da aka rubuta happy birthday babban yaya a jiki, wani irin ɓata rai yayi kana ya bisu da kallo, yana huci ya karaso yace "waye ba lafiya?"
shiru sukayi ganin fuskanshi babu ko alaman walwala, tsawan daya daka musu saida jikinsu ya fara rawa harda batool dake rike da cake saida cake ɗin ya kusa faɗuwa, yace "waye ba lafiya?"
kallon Azad yayi a tsorace Azad ya koma bayan batool ya riketa, yace "ku...ku....ku wasu irin marasa hankali ne?"
shiru sukayi, kallon cake ɗin yayi yace "sa...sa...sabida wannan kuka kirani kunsan aikin dana bari.. nazo?"
shiru sukayi, ya kara daka musu tsawa yace "kun sani?"
karɓan cake ɗin yayi daga hanun batool ya buga da kasa, take cake ɗin ya tarwatse a kasa, waro ido sukayi suna kallon yadda yake tattaka cake ɗin da takalminshi, tsaki yaja yace "useless...."
fita yayi daga ɗakin yana kiran azeez, duk suna tsaye sun kasa yin komai, Azad wanda yake kallon cake ɗin kamar zaiyi kuka yace "wai wannan wani irin mutum ne?"
batool zama tayi akan kujera ta sauke numfashi tareda dafa kanta, sameer zama yayi a kasa shi kuma jabeer ya zauna a gefen batool yayi tagumi.
Najwah tsaye take tana rike da kwanukan tallan nono, ta gama siyarwa tun ɗazu amma bata samu abin hawa ba, tsaki takeja sabida zafin rana da yake damun fuskanta, yau sati ɗaya kenan da auren ameera bata je gidanta ba so take taje ta dubata, wani mashin ne ya tsaya ta tara sannan ta shiga ta ɗaura kayan a cinya sannan suka tafi, har kofan gida ya kaita sauke kayan tayi sannan ta sauka, tace "nawa?"
yace "dubu biyu"
wani kallo ta mishi kallon ka rainamin hankali, tace "dubu biyu daga saudiya ka ɗaukoni ne?"
yace "ban gane daga saudiya na ɗaukoki ba, dama nawa kike tunanin zaki bani?"
tace "idan ka karɓi ɗari biyar to ka tsira idan baka karɓi ɗari biyar ba wallahi ba zan kara ko sisi akai ba"
sauka yayi daga mashin ɗin yace "idan kinaji kinada hauka to na fiki hauka wallahi zanci uwarki anan..."
ta daka tsalle tace "ba uwata ba saide uwarka..."
marinta zaiyi ta rike hanun, kallonta yayi jin karfinta, da hanu ɗaya ta cire mayafin kanta ɗaura kugu tayi tace "ka taɓani idan ka isa"
yace baiji abinshi haka ba hayaniya suka fara, inna dake salla tana idarwa bata jira tayi addu'a ba ta fito ba takalmi, ganin zasu kwashi dambe taje ta rike najwa, hakuri ta fara bawa me mashin ɗin,