Showing 39001 words to 40241 words out of 40241 words

Chapter 14 - NI DA MUNEEB

Start ads

11 Sep 2025

67

Middle Ads

wayar ya buɗu, bata san kan waya ba kawai ta fara taɓe taɓe, hotuna ta fara gani, wayan ya kusa faɗuwa lokacin da taga hotunan yara cikin harda na habibi, jiri takeji tasa hanu a baki tana zaro ido ta kasa rufe bakin, knocking akayi da sauri ta wurgar da wayan ta ɓuya a bayan fridge, Azeez ne ya shigo sanye da baƙin kaya ya cire facemask ɗin, kallonshi take a tsorace tana ɓoye a bayan fridge, tashin muneeb ya fara, ganin baya hayyacinshi ya kalli maganin dake gabanshi, ɗauka yayi taga ya ciro wani abu a aljihu yasa akan maganin yana kallo, da sauri ya aje ya fara bubbuga muneeb da karfi, yace "oh my god oga yasha wannan maganin"
gani tayi ya buɗe drower ya ɗauko wani abu a farin roba karami, sa mishi yayi a hanci yana shaƙa sau uku ya buɗe ido, kallon azeez yayi kanshi yana sarawa yace "a...azeez yaushe kazo?"
yace "tun ɗazu amma boss meyasa kasha maganin?"
yace "bansha....komai ba"
yace "kasha mana boss"
ya kalleshi sannan ya kalli office ɗin, yace "oga ka tuna kasha"
kallon wayarshi dake kasa yayi, sannan yace "ruwa kawai nasha"
ruwan ya kalla sannan suka duba ruwan, zaro ido yayi yace "samin akayi"
yace "kuma boss na kiraka ka ɗauka amma kayi shiru har na gama maganan"
yace "ban amsa call ba"
yace "ka amsa mana boss"
kallon cikin office ɗin yayi yace "akwai wanda ya shigo kuma akwai me bibiyana ya zama dole mu nemo ko waye domin tabbas yaji abinda muke yi kuma ya gane"
yace "me kawo min nono ce kawai ta shigo kuma bana zarginta dan muguwar ƴar kauye ce kazama ba zata iya plan da wasu ba"
azeez yace "koma menene ya zama dole mu zargeta"
jikinta yana rawa tana kallonsu, tari ne yazo mata ta rasa yadda zatayi ta cusa kanta a hijabi dan kyar ta hana kanta yin tarin, tare suka fita, da rarrafe ta shige toilet ɗinshi ta rufe, har suka gama searching basu ga komai ba kuma sunga robobin amma bata nan, komawa office yayi tana zaune a toilet sai zufa take, har dare kafin ya fita salla, cikin sanɗa ta fito, kwanukan ta kwashe ta fita da sauri ta koma gida, naina wacce hankalinta yake a tashe tace "najwah ina kika shiga? hankalinmu duk a tashe?"
cikin razanan da take ciki tace "naina akwai matsala"
ta riketa ta zaunar da ita akan tabarman tace "matsalan me?"
tace "ina inna?"
tace "taje gaisuwa makota anyi musu rasuwa"
hanun naina ta rike tace "zaki taimakeni?"
tace "zan taimaka akan komai sabida yanzu mun riga mun zama yaya da kanwa"
tace "na gode naina, na samo wanda yake sace yara a garinnan"
da mamaki tace "ko dai kanki ya taɓu ne najwah?"
tace "wallahi lafiya kala nake"
fara gaya mata komai tayi, naina ta dafa kirji tace "Innalillahi yanzu ya zamuyi kada su cutar da habibi?"
tace "shine taimakon da nakeso kimin"
tace "to najwa ta yaya zan iya taimaka miki?"
tace "ta hanyan tsohon mijinki"
manyan idanunta ta kara warowa waje, cike da tsoro tace "Alhaji kike nufi?"
tace "kwarai shi"
jikinta ya fara rawa tace "najwah idan son zama da ni ne bakya yi ki faɗamin, wallahi zan tafi zan barki"
tace "naina ki fahimceni kin riga kin zama ƴar uwata naina habibi shine kaɗai nake gani naji kamar ina tare da yayata"
tace "yayarki kuma?"
cikin kuka tace "kwarai adda meerah"
labarinsu ta fara bata, har zuwa wannan lokacin da take rike da habib wato ɗan adda meera, hawaye naina ta share sannan tace "na yadda zan taimakeki koda zan rasa rayuwata, na yadda"
share hawaye tayi da bayan hanunta sannan tace "kince alhaji yanada kuɗi sosai?"
tace "eh yana dashi"
tace "kin san inda yake ajewa?"
gyaɗa kai tayi tace "na sani amma najwah kuɗin tsafi bai kamata mu taɓa ba"
tace "naina ya zama dole mu taɓa sabida dole saina wanke wannan tabon dake fuskana kafin zamu iya tsiratar da rayuwar yara ƙanana, kin taɓa cewa a India ana plastic surgery ko me kikace?"
tace "eh surgery"
tace "yawwa to shi nakeso nayi sabida fuskana ya dawo kamar da, kuma kin san dole saida kuɗi"
tace "eh hakane amma ta yaya zan kara komawa gidan Alhaji?"
tace "tare zamu koma kuma da dare zamuje nasan kin san ko ina a cikin gidan kuma kin san lokacin baccinsu, sata zamuyi"
tace "najwah idan suka kamamu fa?"
tace "kisa a ranki ba zasu kama mu ba, naina ya zama dole ta kowane hanya na tseratar da ɗana, sannan muneeb ba zan barshi ba, wannan shine zai zama karshe a satan da yake"
tace "kina ganin hakan shine mafita?"
tace "eh sabida muneeb zasuyi saurin ganeni da wannan tabon na fuskana"
tace "to shikenan zamuje kuma zamuyi sata amma fa ta bayan gidan zamu shiga"
tace "naina ko ta inane sai mun shiga gidan Alhaji saleh"

*Anan na kawo karshen free pages akwai complete ₦400 kina tura receipt zan tura miki complete Insha Allah, account number 6037523268 Hauwa shuaibumapi keystone, sai a turo evidence ta nan 08144818849*

_jiddah Ce....✍️_
08144818849
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login