Showing 6001 words to 9000 words out of 40241 words
zan kara ganin mamana da abbana ba?"
janye ƙafarshi yayi bai kalleta ba ya fita daga wajen yana jinta tana cewa "yaya ka cewa mamana zan dawo na zama likita"
shiru yayi ya kulle kofan yasa chain sannan ya kalli wanda ya kawo abincin yace "Azeez gobe za'a fita da kaya, wanda suke can an gama ka zama cikin shiri"
yace "an gama boss"
tafiya yayi ya fita daga gidan gaba ɗaya, shiga motarshi yayi sannan ya zauna, duk bodyguards ɗin suka shiga motar suka kara yin convoy suka tafi, wannan karon a cikin gari suka nufi wani katafaren waje me matukar kyau da ɗaukan ido, da alama wannan shine c.e.o ɗin company domin gateman yana ganinsu yayi gudun buɗe gate, fitowa yayi bayan ya cire facemask ɗin sannan yasa glasses ɗin ya fara tafiya, cikin isa da izza da nuna shi ɗin daga family ɗin makawa yake tafiya, masu aiki uniform nasu suit ne bakake da riga fari ta ciki, harda matan duka sanye suke da suit bakake, office nashi da yafi aljannan duniya kyau ya shiga, zama yayi akan tamfatsetsen kujeranshi, cire hulan yayi yana jin sanyin ac yana ratsa shi, kanshi ya ɗaga sama ya fara juyi da kujeran, knocking akayi bai amsa ba yana ji ana knocking saida yaga dama kafin yace "yes"
ɗaya daga cikin ma'aikatan ne ya shigo cikin girmamawa yace "oga an tura kaya kasar paris yau sannan custom sunsa hanu kaya ya wuce"
kallonshi yayi da tsumammun idanunshi kafin yace "ba..ba..babu custom daya...isa ya tare kayana"
cikin girmamawa yace "hakane oga amma fa hankalinmu ya tashi sabida munsa koken a kasan kayan kuma tabbas zamu samu ƙazamin riba"
murmushi yayi ai kuwa murmushi ya mishi kyau da ace yana yinshi a koda yaushe da yafi haka kyau, yace "good"
tashi yayi yace "ga takaddun"
nuna mishi inda zai aje yayi sannan ya cigaba da juyinshi akan kujeran, ajewa yayi ya fita, wayarshi ne ta fara ringing ya kalli sunan yaga baby Azad, amsawa yayi yace "ina...ina...jinka"
ya faɗi hakane sabida shirun da yaji baby Azad ɗin yayi, ji yayi Azad ɗin yana magana kasa kasa yace "sameer kayi magana"
sameer ɗin yace "A,a jabeer ne zaiyi magana"
musu suke a tsakaninsu ya daka musu tsawan da yasa suka nutsu a take, Azad wanda su sameer suka gudu suka barshi rike da wayan kamar zaiyi kuka yace "dama babban yaya kuɗin hanunmu ne ya kare kuma munason zuwa shopping"
tsaki yaja kana ya kashe wayan, transfer na kuɗi yayi musu a account ɗin Azad, ganin alart ya shigo na makudan kuɗi Azad ya waro manyan idanunshi yace "1 billion?"
wani irin tsalle ya daka sannan ya fita da gudu ya sauka kasa, har sun dawo falo suna game sun ma manta sun barshi a masifa eh masifa mana babban yaya ai masifa ne, rungumesu yayi da karfi yace "babban yaya ya tura mana billion ɗaya"
duk suka kalli alart ɗin, tsalle suka fara a ɗakin, batool data fito tana tafiya a hankali daga bacci ta tashi hakan yasa batada karfi ko kaɗan, dafe da bango ta karaso inda suke, Azad ne yazo da gudu ya rungumeta, ciza baki tayi cikin ciwo itama ta rungumeshi tace "baby Azad murnan me kuke?"
yace "babban yaya ya turo mana 1 billion zamuje shopping"
da mamaki ta kalli sameer shima kallonta yayi sai kuma tace "masha Allah sai kuyi mishi godiya"
Azad cikin jin daɗi ya saketa yace "bari naje na shirya yanzu zamu tafi"
jabeer ma yace "nima yanzu zan shirya yau akwai wash"
yabi bayan Azad, sameer ya juya zai bisu ta rike hanunshi, tsayawa yayi yana kallonta itama kallonshi take, tace "sameer a kullum kai kaɗai nake faɗawa abu sabida kaine babba kafi su Azad hankali da tunani, sameer mu kara sa ido akan muneeb"
cikin mutuwan jiki yace "unty batool wallahi duk wani sa ido daya kamata nayi, saida na yiwa ya muneeb to amma har yanzu na kasa gano komai may be he's innocent shiyasa bamu ga komai ba"
girgiza kai tayi ta zauna akan sofa tace "zuciyata taki yadda da muneeb innocent ne, na kasa yadda sameer, a kullum ina rokon Allah ya ciremin shaƙƙu akan muneeb amma har yanzu na kasa dainawa sameer gaskiya ina tsoron mutuwa na barku tare dashi, muneeb ɗan uwanane na jini kamar ku, amma ina tsoron barinku a hanunshi haka kawai na kasa yadda dashi, sannan nasan dole zan mutu domin ciwon cancer a ciki baya sauki"
durkusawa yayi a gabanta ya riko hannayenta yayi mata kiss a hanu sannan yace "insha Allah ba zaki mutu ki barmu ba muna tare dake, babu abinda zai rabamu"
murmushi tayi mishi, shafa fuskanshi tayi tace "ina fatan koda na mutu zaka kula da kannenka harma dashi muneeb ɗin"
yace "insha Allah ba zan karya alkawari ba"
Azad wanda yaci gayu kamar ba gobe ya sauko daga stair, wani bala'in kyau yayi cikin riga red da wando black, yasa black facing cap, agogon da ya muneeb ya bashi ranan birthday ɗinshi tsadadde yasa black, kamshi yake sosai, a gaban batool ya tsaya yace "ya? nayi kyau?"
murmushi tayi me sauti sannan tace "kayi kyau baby Azad kamar wanda zaije wajen budurwa"
rufe fuskanshi yayi da tafin hanunshi cikin kunya yace "kai unty"
jabeer ne ya fito shima yayi kyau cikin yadi milk color yasa hula milk yayi kyau sosai yana kamshi yazo yana gyara zaman agogon hanunshi, yace "sameer idan bakaje ka shirya ka fito da wuri ba wallahi zamu tafi mu barka"
harara sameer ya aika mishi sannan yace "kaida ka gagara tambayan kuɗin saida baby Azad ya tambaya shine zaka zo kana gayamin maganan banza?"
yace "kaima ai ka gagara tambaya duk ɗaya muke"
ganin sun fara musu Azad ya nuna musu atm yace "wallahi zan tafi na barku ku duka sabida kun san nine da magana akan kuɗin"
sanin halinshi sukace "Allah baka hakuri"
sameer ne ya shiga domin shiri Azad ya zauna gefen batool yace "me dame dame kikeso mu kawo miki?"
tace "koma mai inaso"
yace "karki damu yau saina huce haushina aka chocolate"
dariya sukayi, sameer ne ya fito yayi matukar kyau cikin riga orange da hula orange sai bakin wando, kamasu da muneeb ya fito sosai, ganin suna kallonshi yace "ya akayi?"
jabeer yace "gaskiya ban yadda ba duk kun fini kyau wallahi sai naje na canja kaya"
ganin da gaske yake suka kama hanyan tafiya yasan halinsu badan yaso ba kawai ya bisu yana ɓata rai, dariya batool tayi suna fita kuma dariyan ya koma kuka, masu gadinsu suna ganin sun fito suka tashi buɗe musu mota akayi suka shiga, binsu a baya sukayi domin basu tsaro na musamman, basa taɓa fita babu masu tsaro tun basa so har sun saba, tsadaddun motoci ne kuma kowane da sunan family ɗinsu akai wato makawa, duk wani motan da yake wucewa idan motocin gidansu sunzo wucewa tsayawa suke, hakan kuwa akayi yauma motocin sun tsaya a gefe, Azad ne yace "nifa gaskiya na tsani wannan ɗabi'an babban yaya wai sai kowa ya jira mun wuce kafin ya wuce? to idan sunada uzuri fa? wani fa sauri yake zai kai matarshi ko ƴarshi asibiti meyasa za'a tsayar dasu?"
sameer dake karanta jarida yace "to ai kasan ba zamu iya karya wannan dokan ba dole haka zamu hakura"
jabeer kam danna wayarshi yake bai kulasu ba, da haka har suka isa mall ɗin, babban mall ne parking sukayi suka fito a tare suke tafiya masu tsaronsu suna binsu a baya, kowanne rike da bindigan kariya da kuma bakin kaya a jikinsu, duk masu siyayya aka fitar dasu waje domin makawa's zasuyi siyayya ba'a bari kowa ya zauna a mall ɗin, Azad cikin jin haushin fita da mutane sukeyi idan zasuyi shopping yayi tsaki kawai yasan koda yayi magana umarnin babban yaya ne a cewarshi babu abinda yafi mishi kannenshi muhimmanci shiyasa yake basu masu tsaro kwararru na musamman, duk abinda suke so ɗauka suke suna sawa a basket, da haka har suka gama aka ɗauka har mota aka kai musu, Azad ne rike da karamin leda a hanu suna tafiya suna hira, biyan kuɗin sukayi kana suka koma mota, sai a lokacin aka kyale mutane suka shiga.
lokacin da suka hau titi kowane mota tsayawa yayi, wani driver da yake sabo ya kalli motocin da suka wuce sannan yace "wai meyasa a kullum idan waɗannan sunzo wucewa sai ace kowa ya tsaya su ɗin su waye ne?"
murmushi na kusa dashi yayi sannan yace "waɗannan sune family ɗin makawa, yayansu muneeb makawa attajirin me kuɗi ne yana ɗaya daga cikin manyan mutane uku masu kuɗi na nigeria, ance su marayu ne babu uwa babu uba shi yasa yake son kannenshi kamar ranshi, da abu ya samu kannenshi ya gwammace ya sameshi koda wani irin masifa ne, hakan yasa duk inda zasu je suna tare da masu basu tsaro, bai yadda da kowa ba shiyasa yake basu tsaro na musamman"
driver yace "gaskiya alamu sun nuna yana sansu irin wannan kulawa haka?"
yace "kaɗan ka gani daga cikin soyayyan da yake nuna musu, saima kaje siyan abu idan sunzo dole ka hakura sai an gama dasu kafin a juyo kanka"
yace "to Allah ya kyauta"
a tsakiyan falo suka barbaza kayan kowa yana zaɓan bashi, batool wacce take kuka tunda suka tafi har saida taji dawowansu kafin ta share hawaye tana kallonsu suna raba kayan.
Najwah durkushe take a gaban shanu tana tatsan nono, sanye take da kayan fulani fari tayi adonsu me kyau ta fenta bakinta da bakin kwalli, gashinta da Adda meera ta kitse mata ta barshi babu ɗankwali sai adon data kame gashin dashi kamar ribbon, murmushi take yi tana waƙa da harshen fulatanci tana cikin nishaɗi a duk lokacin da zata tatsi nono, adda meerah ce ta karaso wajen hanunta rike da samira itama tayi kyau sosai cikin riga da zani na atamfa, da ado sosai a fuskanta ta ɗaga murya tace "najwa kizo muci abinci kin gaji saiki huta ni zanyi sauran"
jin an ambaci abinci tayi saurin tashi domin bata jure yunwa, da sauri taje ta zauna karkashin bishiyan da Adda meera ta zauna, abincin ta buɗe shinkafa da wake ne yaji man shanu da barkono, murmushi tayi tace "wayyo Allah kamar inna ta san abinda nake so a raina"
tace "ba inna bace nice na dafa sabida nasan kinfi so"
murmushi tayi tace "gaskiya naji daɗi"
wanke hanunta tayi tasa suka fara cin abincin, daɗi yake mata sai murmushi take, meerah tace "najwah?"
tace "na'am adda meera"
tace "kin san duk duniya babu wacce nake so kamar ke ko?"
ta jijjiga kai tana cigaba da cin abincin, tace "to Inaso kiji duk maganan da zan miki kin san dai ba zan cutar dake ba"
tace "um"
tace "najwa ki koyi hakuri, dan Allah kada ki kara faɗa da kowa a wannan rugan, najwa ki daina biyewa mutane kina faɗa da mata da maza"
haɗiye abincin tayi sannan tace "ai bana faɗa da mata duka nake yiwa duk macen fata tsokaneni kuma kinfi kowa sanin ƴan rugannan basu da kunya kuma ni bana neman tsokana kin sani, saide duk wanda ya tsokaneni ko shine me garinmu saina rama"
kullum idan tana mata nasiha bata yadda hakan yasa tayi shiru kawai tasan da gaske bata neman tsokana amma batada hakuri, da haka har suka cinye abincin ta koma ta gama tatse nonon kafin ta ɗaura katon kwaryan a kanta tace "mu tafi adda meerah zanje wanki a bakin kogi"
ɗaukan samiran tayi sannan ta ɗau goran ruwan da sandanta ta rike suka jera suna tafiya suna hira kamar kawaye da haka har suka isa gida, najwa ce ta shiga ɗaki ta ɗauko tulin wankin da suka tara tace "na tafi bakin kogi"
inna dake banɗaki tayi saurin fitowa tace *
"najwah banda faɗa, kiwa Allah kiwa Annabi kada kiyi faɗa da kowa, najwah kinfi kowa sanin yadda nake shan zagi a garinnan a kanki cewa ake kun kasa auruwa sabida rashin kunyarki har yayarki ana tsoron auranta, gori iri iri babu wanda ba'a yimin amma ni nasan lokacinku ne baiyi ba, dan Allah najwah ki barni da abinda yake damuna har babanku bai daina zagina akanku ba yace kun kasa aure dan Allah ki fita harkan kowa"
tace "to inna naji"
kundura tasa fari sannan ta ɗaura wankin a kanta ta ɗau baho da omo tace "adda ameera idan kin gama yiwa inna kitson zaki zo da wuri ko?"
tace "eh ba zamu jima ba yanzu zan gama mata ina bayanki"
tace "to"
tafiya ta fara ita kaɗai tana waƙa bata kallon kowa gabanta kawai take kallo, daurewa tayi da tsokanan da ake mata har ta isa bakin kogi, sabida batason fitina yasa ta koma can gefe ta aje kayanta karkashin bishiya taje ta ɗibo ruwa bata kula ƴammatan da suke zaune suna wanki ba, ta kai ruwan ta aje da omo sannan tace "bari naje na tsinko mangoro kafin nazo na fara wankin"
can cikin bishiyoyin ta shiga cikin rashin tsoro duk da kukan tsuntsaye da take ji bai tsoratata ba sabida ta saba, naɗe zaninta tayi ta hau bishiyan ta fara tsinko nunannu tana sawa a cikin riganta data ɗaga, saida ta cika ɓam kafin ta diro daga bishiyan, murmushi tayi tace "harda Adda meera na tsinkawa"
tafiya ta fara domin komawa wajen wankin yadda ta bar ruwanta da kayan haka ta tarar, dutse ne yaja kafarta ta faɗi kasa mangoro suka zube, gangara suka fara ta tashi da sauri tana tsinewa, ɗaya daga cikin ƴammatan ta tashi da sauri ta fara ɗauka, najwa data gama kwashewa ta kalli yarinyar sannan tace "bani mangoro na"
yarinyar tace "a kasa na tsinta"
cike da tsiwa tayi maganan, idanunta masu kama da madara tace "bani mangoro na tun kafin a jimu"
tace "ba zan bayar ba tunda ba a hanunki na kwata ba, kema ai satowa kikayi"
a fusace tace "na miki kama da ɓarauniya? ko a gaya miki halin da kuke yi kowa ma shi yake yi? ki bani mangorona nace"
ci ta fara, cikin fusata ta zubar dana hanunta tayo kan yarinyar, itama ganin haka ta wurgar dana hanunta suka fara dambe, duka najwa take mata tun tana iya ramawa har najwa ta haɗa hanunta duka biyu ta rike, dukan kawo wuƙa take mata yarinyar tana ihu, ƴammatan suna rabasu ganin kawarsu tana dakuwa suka shiga mata, dukan najwa suka fara, ganin haka ta riko ɗaya a cikinsu ta jata suka faɗa kogin, dukanta take a cikin ruwan tana tsoma kanta tana fitowa dashi, ɗaya daga cikinsu ta waro ido ganin najwah zata kashe Altine da wani irin gudu ta kwasa ta ɗaga zaninta kamar zata kife kasa ta nufi gidansu najwah, a guje ta shiga ta faɗi ƙasa tana haƙi, Ameera dake yiwa inna kitso ta saki kan da sauri ta mike tana dafa kirji a tsorace tace "meya faru?"
tana nuna waje da hanu tace "najwa..najwa zata kashe Altine a bakin kogi"
ba shiri inna da ameera suka fita bama su tsaya sa takalmi ba, itama yarinyar ta bisu a baya, gudu inna da ameera suke kamar ba zasu iso ba, waro ido inna tayi ganin najwah ta tsoma kan yarinya a ruwa tana jibganta kamar ita ta haifeta, da ihu tace "najwah ki saketa"
ameera ce ta shiga cikin ruwan ta fara jan najwa, inna ma ta shigo suka riketa da kyar suka janyeta, tana fizgewa suka riketa ameera ta kwashe wankin sai gida.
*Jiddah Ce....✍️*
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 3*
~Suna shiga gida inna tace "haba najwah kinaso ki kasheni ne? meyasa bakya jin magana ne? meyasa?"
tana huci tace "inna mangorona..."
dukan data kai mata yasa tayi shiru, bulala ta ɗauka ta fara dukanta dashi cikin jin haushi tana haɗawa da hanu, Ameera ce tayi sauri tare dukan tace "ki barta mana haka inna dukan ai yayi yawa"
cikin haushi tace "matsa min ameera idan ban zane najwah yadda raina yake so ba yau sai bakin ciki ya kasheni, anan fa kina ji ina mata gargaɗi banda faɗa amma tana zuwa zata tsokano faɗa?"
tsintsiya ta ɗauka ta fara bugunta dashi, ihu take tana ɓuya a bayan ameerah sabida ta tsani bulala, ganin inna zata kara mata ameera ta rike bulalan tace "ki gudu"
gudu tayi ta shiga ɗaki ta rufe kanta a ciki, inna wani irin haushi ameerah ta bata, bulalan ta fara yimata tace "saiki karɓa mata tunda kin fini sonta, saiki karɓa mata ja'ira mara wayo"
saida ta huce haushin akan ameera sannan ta wurgar ta shiga kitchen ta fara girki, ameerah zama tayi akan tabarman kitson da basuyi ba kenan, har dare taki buɗe kofan sabida tsoron duka, saida aka kira salla kafin cikin sanɗa ta buɗe tana lekawa, ganin babu inna a cikin gida ta fita da sauri tayi alwala zata koma inna tace "kika sake rufe mana kofa saina kakkaryaki"
rakuɓewa tayi a jikin kofan ta shiga tasa hijabi ta fara sallanta wanda babu karatun kirki da take yi sai dungurawa, da sauri ta idar ta zauna a gefe tayi shiru ameera ce ta shigo itama tayi sallan, inna data idar tace "sai kije ki ɗauko muku abinci"
tashi tayi taje ta ɗauko abincin ta aje a gaban adda meerah, ci suka fara tuwo da miyan rama ne me daɗi, har suka gama ci kafin Ameera ta kalli inna tace "kiyi hakuri inna insha Allah hakan ba zai kara faruwa ba"
tace "shikenan ya wuce"
tace "bari na karasa miki kitson"
najwah saida taga inna ta saki jiki kafin ta fara hira itama adda ameera tana karasa kitson, har suka gama baba be dawo ba, ganin haka suka rufe kofan suka kwanta sabida sun saba watarana zaiyi kwana uku ma bai dawo ba, najwah tafi jin daɗi ma idan baya nan, washe gari tunda sukayi salla suka fara shirya nonon da zasu tafi talla dashi, gari yana yin haske sukayi wanka suka fara shiri, najwa ce zaune adda meera tana musu kwalliyansu na fulani, har ta gama mata, tace "masha Allah kanwata tafi kowa kyau a garinnan"
murmushi tayi tace "ban fiki kyau ba inji inna"
tace "gaskiya kin fini kyau"
gashinta shima tayi mishi adon fari fari kaɗan, tayi kyau kamar ka saceta ka gudu, addu'a ta tofa mata sannan tace "Allah ya kareki da sharrin ido da baki"
murmushi tayi tace "ameen"
itama shiri tayi mama dake cikin gida tana shirya musu tace "na gama