Showing 30001 words to 33000 words out of 40241 words
kaine yanzu babanmu kaine zamu bawa darajan mahaifi duk da na girmeka amma wannan kannenka ne muneeb kayi aure"
ta karashe maganan tana kuka, ido ya zuba mata tunda ta fara maganan har ta gama bai ɗauke ido ba, tace "ina tausayinsu sameer musamman Azad banaso ya rasa kulawa"
shifa ba wai auren ne ba zaiyi ba, raini ne bayaso kana auren mace zata fara rainaka shi kuma shine abinda baya so, ga mata dayawa suna kawo mishi hari ɗauke kai yake daga kansu sabida bai shirya karɓan raini ba, ganin tana kuka yace "to...me....abin kuka?"
tace "dole nayi kuka muneeb baka san me yake damuna a rai ba"
yace "na..naji...zanyi auren"
tace "muneeb yaushe zaka yi? kaida ko budurwa baka yi baka kula mata, anan nana makociyarmu ta fara nuna tana sanka amma ka rinƙa yiwa yarinya shariya ko kallo bata isheka ba gashi har tayi aure"
tashi yayi yana hamma yazo ya share mata hawayen yayi mata peck a forehead yace "ki...ki...daina kuka bakida lafiya...idan lokaci yayi zanyi auren"
zatayi magana ya rufe mata baki yace "shiiii ya isa"
maganinta ya ɗauko ya ɗau goran ruwa yazo ya durkusa a gabanta yace "take"
karɓa tayi tasha ya rike hanunta yace "oya time for sleep"
kashe tv yayi su sameer da suke zaune kamar akan kaya suka tashi da sauri suka tafi, hanunta ya rike har zuwa ɗakinta, kallonshi take duk yadda taso tayi magana ya hanata, cire mata karamin hijabin yayi yace "sleep"
kwanciya tayi ya rufata da blanket yace "g...good night"
kashe mata wuta yayi ya fita, ɗakinshi yaje kasancewar ya gaji bai amsa kiran da azeez yake mishi ba ya kashe wayan ya kwanta, idan yana son hutawa baya barin waya a buɗe kuma baya sa komai a ranshi cire komai yake ya kwanta.
_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 10*
~Cikin bacci najwah sai zufa take tana girgiza kai, damƙe bedsheet ɗin tayi da mugun karfi a firgice ta tashi tace "A,aaaaaaaa"
inna tace "subhanallah" jin ihun da najwah tayi yasa ta tashi daga baccin da take, kallon najwah wacce ta dafa kirji sai zufa take, tace "menene?"
tana share zufa tace "inna wani mummunan mafarki nayi, inna wasu yara kanana na gani suna kuka a ɗauresu sannan aka rufesu a wani ɗaki me tsananin duhu, sai kuma wani mutum tsaye da baƙin kaya ya rufe fuskanshi da facemask suna rokanshi ya fitar dasu a wajen inna yana tsaye yana kallonsu yana dariya, sai Adda meerah tace naje ta ceci yaran kada na bari ya cutar dasu tana kuka take cewa najwah kije ki taimakesu na san zaki iya najwah"
inna tayi shiru ganin hankalin najwan a mugun tashe yake tace "Allah sarki watakila kinsa satan yara da ake a garinnan ne a ranki tunda kullum ina faɗa miki naji a rediyo"
ta girgiza kai tace "inna ban taɓa sawa a raina ba"
habib dake bacci yace "mama zansha ruwa"
kasa tashi tayi ta ɗibo mishi ruwan tsaban tsoron da mafarkin ya bata, inna ce ta ɗibo mishi ruwan bayan yasha ta bawa najwah tace "kisha ruwa"
karɓa tayi ta shanye tas kafin tace "na gode"
zama tayi ta kasa komawa baccin inna tace "kiyi addu'a ki kwanta insha Allah ba zaki kara mummunan mafarkin ba"
tana toshe kunne tace "inna kukan yara nake ji a kunnuwana"
inna tace "najwa mafarki fa ba gaskiya bane ki kwanta kiyi bacci"
tace "wallahi inna kukan yara nake ji"
inna addu'a ta fara mata tana tofa mata har ta samu nutsuwa ta kwanta saide bacci yaki ɗaukanta haka ta kwana ido biyu, har gari ya waye bata runtsa ba, abincin karyawa tayi musu sannan ta tashi habib tace yayi salla sallan yayi tayi mishi wanka ta shiryashi cikin uniform, yace "mama meyasa idonki a kumbure? kuka kiyayi?"
tana mamakin habib wani lokaci idan yayi tambaya kamar ba yaro ba, tace "kukan me zanyi habibi tunda kana tare dani?"
yayi murmushi yace "yawwa mama batayi kuka ba"
tana gama shiryashi tasa kaya itama ta fito suka yiwa inna sallama, har kofan school ta ajeshi kafin suka tafi, yau tazo da wuri, suna ganinta me gadi yace "kyakkyawa kin karaso yau da wuri"
murmushi tayi tace "eh baba sabida yau na kai habibi makaranta da wuri ne"
yace "Allah sarki"
shiga ciki tayi, tana zama babu jimawa motocin muneeb suka shigo, sai yau ta ganshi tunda ta fara saida nono anan bata taɓa ganinshi ba, yadda yake tafiya kamar bayason taka kasa yasa taji bata sanshi, ga wani botsarewa da yake yana shan kamshi sai taji ya kara bata haushi, bata kara tsananshi ba saida taga yana bin kowa da kallon raini da isa, duk yadda suke durkusawa suna gaisheshi bai amsa na ko mutum ɗaya ba, ɗauke kai tayi lokacin da zasu haɗa ido, saida ya juyo kafin tabi bayanshi da kallo, gwada tafiyanshi tayi yadda yake bubbuɗa hanu tace "takama kamar karuna ko dan yanada kyau da kuɗi ne yasa yake wannan cika yana batsewan, tsaki taja taci gaba da abinda yake gabanta, jim kaɗan akazo karɓan nashi zuma mishi tayi ta dama da ludayin dama sannan ta zuba madara akai kamar yadda ta saba, mika mishi tayi tace "gashi"
karɓa yayi ya kai mishi ya dawo da daidai kuɗinta ya bata, karɓa tayi har ta gama siyarwa bata burin ta kara ganinshi, makarantan su habibi taje ta ɗaukeshi, yau da suka koma gida ta shiryashi itama ta shirya cikin riga da skirt me kyau, kwalli tasa tayi masifan kyau tasa mayafi green irin kayan, takalmi tasa flat wanda ta siya a kasuwa ta riko hanun habib da yayi kyau jikin jinx na yara da riga red an rubuta MY HOPE a jikin rigan, ta kalli inna dake daka tace "inna bara na kaishi yau yasha ice cream ɗinnan da kullum yake damuna da sunanshi"
tace "to najwah Allah ya tsare hanya"
tace "ameen"
farin ciki ƙarara a fuskan habib jin an kira ice cream, inna tace "ka dawomin da nawa fa megida"
yace "to inna amma guda rabi zan kawo miki"
tace "ni dai ka kawomin"
zasu fita inna tace "najwah"
tsayawa tayi bata juyo ba sai tura baki take, tasan zata fara wannan nasihan nata ne, tace "banda faɗa, najwa ki zama me hakuri banda faɗa najwa"
tace "to inna naji"
fita sukayi suna tafiya a hankali tana bashi labarin kogi, yace "to mama addanki bata zuwa ne ita?"
tace "tana zuwa amma bata fiye zuwa ba sabida ana yawan faɗa acan, kuma ita bata son faɗa kamar kai take"
yace "Ayya da na santa da tare zan kaiku makka"
tace "addu'a zakayi mata kace Allah yaji kanta yayi mata rahama"
yace "Allah yaji kanta yayi mata rahama"
tace "ameen"
mashin suka shiga aka kaisu wajen shan ice cream, sai kallon mutanen wajen take kowa da yaranshi wajen abin ban sha'awa, murmushi take tana tunani inama ace adda meerah tana raye da tare zasu zo nan, ice cream ta siya musu da habibi suka zauna suna sha, yace zai hau lilo ta ɗaurashi tana turashi, yara suna ball yace zaije suyi tana tsaye tana kallonshi yaje suna ball da yaran, murmushi take ganin habibi yana farin ciki sai taji babu abinda take kara nema a wannan duniyan, wurga ball ɗin yayi sama faɗawa ball ɗin yayi a jikin wani dake zuwa, waro ido tayi a tsorace ganin ball ya taɓa mutum, saukewa yayi yana kallonsu cikin sakin fuska ya karaso ya durkusa ya bawa habib dake tsorace yana binshi da kallo, yace "habibi ka iya ball ne?"
a hankali yace "inayi a school"
yace "good boy, waya kawoka nan?"
nuna najwah dake tsaye ta harɗe hanu a kirji yayi, yace "mamana"
murmushi tayi mishi ganin yaja hanun habib zuwa wajenta, yace "ina wuni maman habibi"
tace "lafiya ƙalau yayan habibi"
yayi dariya kaɗan jin sunan data kirashi yaji daɗi, yace "nima nazo siyawa kanina Azad ice cream sabida baida lafiya"
tace "Allah sarki Allah ya bashi lafiya"
yace "ameen"
yana rike da hanun habib yaje ya siya ice cream ɗin dayawa ya kara siyawa habib, tace "amma ai yayi yawa"
yace "karki damu nasan habibi na son ice cream"
dariya tayi kaɗan tace "gaskiya mun gode yana so sosai"
fita sukayi tare suna hira habib na tsakiyansu hanunshi rike dana sameer, yace "ku shiga mana na kaiku gida tunda ba sauri nake ba"
tace "a,a karka damu zamu shiga mashin"
duk yadda yayi da ita taki yadda yace "to shikenan bara mu tari mashin ɗin tare"
tace "kar dai mu gajiyar da kai"
yace "babu komai wallahi"
saida ya tarar musu mashin ya biya kuɗin kafin ya karawa habib taso taki saida ya ɓata rai kafin tace habibi ya karɓa, idan ba itace tace ya karɓa ba baya karɓan kyauta a hanun kowa, tayi mishi godiya kafin suka tafi, shiga motarshi yayi yaga miss calls ɗin jabeer, kira yayi jabeer yace "dan Allah kayi sauri wannan Azad ɗin wallahi ya fiye shagwaɓa wai kuka yake idan baisha ice cream ba zai mutu"
tsaki yaja yace "bashi wayan"
bashi yayi cikin murya kaɗan yace "ya sameer zan mutu bansha ice cream ɗin ba"
cikin masifa yake so yayi magana sai kuma yace "ba zaka mutu ba Azad yanzu zan kawo maka ka rinƙa daure rashin lafiya kaji?"
yace "to yaya"
katse wayan yayi yace "Azad Allah ya shiryeka"
yaja motan ya tafi, yana zuwa ya bawa Azad da yake zaune ya rike pillow ya zama kalan tausayi dan dama shi haka yake idan baida lafiya.
unty batool tayi mishi alaman yazo sunada magana, saida ta tafi ya bita, ɗakinta ya shiga tana zaune akan sofa yace "gani unty batool"
ta nuna mishi gefenta tace "zauna"
zama yayi tayi shiru shima yayi shiru, sun jima a haka kafin tace "sameer ya kamata mu gano wani abin zuwa yanzu sameer ban yadda da muneeb....."
yace "dakata dan Allah unty batool"
tashi yayi ya tsaya ranshi a ɓace yace "ko sau ɗaya, ko sau ɗaya ba zakiyi tunanin meyasa Allah bai nuna mana komai akan ya muneeb ba? unty batool ya muneeb is innocent baya aikata komai mara kyau, haka Allah ya halicceshi baida son dariya kuma baya shiga harkan mutane hakan ba zaisa mu rinƙa zarginshi ba, mun jima muna zarginshi amma har yau mun kasa gano abu koda ɗaya ne wanda ya aikata mara kyau, meyasa ba zamu hakura ba? can't you trust your brother koda sau ɗaya ne? tunda fa iyayenmu suka mutu shi yake kula damu, duk da baya sake mana fuska muna matukar tsoronshi amma babu abinda baya mana, matukar ya gane muna son abu shi yake zuwa ya siya mana da kanshi, kin kula damu kamar mahaifiya shi kuma ya kula damu kamar mahaifi, haramun mu rinƙa zarginshi, ba zai taɓa yafe mana ba idan yasa muna bibiyanshi sabida muga ko yana aikata wani abu a ɓoye ba zaiji daɗi ba, zai shiga tsananin damu zai fara tunanin mu na kusa dashi muna zarginshi ina ga mutanen nesa?"
tunda ya fara magana take kallonshi har ya gama, a hankali tace "sameer...."
hanu biyu ya haɗa yace "dan Allah unty batool mu rufe wannan maganan anan, daga yau idan maganan zargin babban yaya zaki min dan girman Allah kada ki sake kirana, ni bazan iya zama ina zarginshi ba"
tace "sameer nima na fara wannan tunanin wallahi nima kunya nake ji ace wai nice nake zargin kanina da aikata ba daidai ba, nima banason hakan yanzu sameer"
yace "da hakan yafi unty batool"
tace "to ka saki fuska mana"
sakin fuska yayi
tace "mu koma falo"
tafiya sukayi kamar babu maganan da sukayi, jabeer yace Azad fa lafiyansa lau banda ciye ciye babu abinda yake yi"
cikin kakkausan muryanshi ya shigo sanye da bakin suit, yayi masifan kyau kamar balarabe yace "wa...wawwaye ba lafiya?"
Azad yace "nine"
da sauri yace "kaga Dr?"
yace "no yaya yanzu na samu lafiya...."
kafin ya karasa ya ciro waya ya kira dr mansoor, yace yazo akwai mara lafiya, rarraba ido Azad ya fara domin harga Allah ya warke rigima ne kawai da rashin son zuwa school da babban yaya yace zai fara, jabeer yace "yawwa idan akayi maka allura zaka warke"
kamar zaiyi fitsari a wando jin allura, jabeer juyar da kai yayi yana dariya kamar zai mutu, har dr mansoor ya shigo ya fara dubashi allura ya ciro tana hawaye yace "wallahi na warke babban yaya wallahi lafiyata ƙalau"
cikin rashin fara'anshi yace "sai anyi maka ko lafiya kake"
su jabeer ne suka danneshi aka mishi alluran ihu yake har aka gama, tsaki muneeb yaja ya bar wajen, Azad saida yayi kuka sosai kamar karamin yaro kafin bacci ya ɗaukeshi.
koda suka koma gida inna tayi godiya da ice cream ɗin da suka kawo mata, cikin dare zaune take ta haɗa kai da gwiwa duk yadda taso tayi bacci yau ta kasa, data rufe ido adda meerah take gani rike da yaran tana kuka, sannan tana cewa taje ta taimakesu, hankalinta tashi yake idan tayi wannan mafarkin, ta rasa abinyi sai sharan zuwa take tana cewa "Allah me yake faruwa ne? wasu yara ne wannan a kulle?"
tayi shiru sabida babu amsa, inna ta tashi itama ta zauna, tace "najwah ya kamata ki manta wannan mafarke mafarken da kike ki rinƙa samun bacci tunda da rana ba hutu kike samu ba, ki daina hana kanki bacci"
bata ɗago kanta ba tace "inna ina ganin idan ban gano menene wannan mafarkin yake nufi ba ba zan kara samun isasshen bacci ba a rayuwata"
shiru inna tayi, tace "inna bayan nayi mafarkin na farka kukan yara baya barina, ya zama dole na fara gano me hakan yake nufi"
inna tace "to Allah ya baki sa'a amma kibi komai a hankali"
tace "to inna"
a daren sai bacci ɓarawo ne ya saceta shima bata yishi cikin daɗi ba.
washe gari, zaune take a karkashin bishiya inda ta saba zama tana zuba nono a bowl hankalinta baya jikinta mafarkin da tayi yana kara yawo a ƙwaƙwalwanta ta kasa samun nutsuwan ƙwaƙwalwa, da sauri yace "malama kina zubar da nonon fa"
firgigit tayi ta dawo hayyacinta ta zuba sannan ta mika mishi, zama tayi ta zabga tagumi a ranan ta saida nonon babu walwala a tare da ita, har habib yana tambayanta da taje ɗaukanshi cewa kawai tayi babu komai habibi, koda ta koma gida ta irga kuɗin dake hanunta sun taru da yawa, gani tayi basada kayan abinci dayawa ta fara lissafi har ta gama tace "inna anjima da yamma zanje kasuwa"
inna tace "to najwah Allah ya kaimu"
tace "ameen"
habib yazo da ball ɗin fata siya mishi a hanu yace "mama tashi mu buga ball"
tace "habibi ina mata suka iya ball?"
yaja hanunta yace "mama zan koya miki"
tace "habibi ban iya ba"
ganin zaiyi kuka ta tashi ta tsaya tace "to muyi"
murmushi yayi ya naɗe ƙafan wandonshi black tana kallonshi kamar wani babba yace "let's go"
farawa sukayi yanata ci sai tayi tafi shi kuma yana murna har ya gaji dan kanshi yace an gama, yace "na cinye mama"
ta kwaɓe fuska tace "ai ban iya ba"
dariya yayi yace "ko kin iya na fiki iyawa"
kallon farcenshi tayi tace "ɗauko reza akan window"
tashi yayi ya ɗauko reza ta kamo hanunshi ta fara yanke mishi farce, saida ta gama tace "yawwa hanun habibi ya kara kyau"
yace "mama ai hanuna irin naki ne kinga wannan bakin ɗigo karami kema gashi a naki"
kallo tayi tana mamaki wayon yaron, wannan tabon itada adda meerah suna dashi bata taɓa lura yana dashi ba sai yau daya faɗa, tace "gaskiya habibi kanada wayo da tunani"
murmushin yara yayi, ta shafa suman kanshi da take mishi gyara sosai tace "Allah maka albarka"
yace "ameen"
shiru sukayi, yace "mama wannan daya siya mana ice cream ɗin me sunanshi?"
kashe mishi ido ta fara tana rufe bakinta alaman yayi shiru, inna caraf take kallonta, sai kuma tace "laifi ne dan yayi tambaya? waye yake magana akai?"
tace "inna masu saida ice cream ɗinne fa ɗaya daga cikin ya siya mishi"
tace "to ya gode"
habib zaiyi magana tace "tashi kaje ka ɗauko takaddu muyi karatu"
yace "to"
yazo dashi sukayi karatu, sai yamma likis kafin ta shirya tasa hijabi dogo da makalmi flat ta ɗau kuɗin ta fita, mashin ta tara da sauri sabida kada tayi dare, a bakin kasuwa ya sauketa ta gama siyayya ta fito da manyan ledoji a hanunta sun mata nauyi sosai ta tsaya a bakin titi tana jiran mashin, yau kam da alama zata jima bata samu ba sabida shiru har yanzu babu ko kan mashi, tafiya ta fara da kafa sunada nisa sosai da zata tafi kawai hakan yasa take ɗan tsayawa idan tayi tafiya, ta gaji sosai hakan yasa ta zauna a gindin bishiya tayi shiru tana kallon motocin dake wucewa ɗaya ɗaya basu da yawa, har duhu ya fara sosai babu mashin, tsaki ta fara ja sabida ta gaji, wani zazzafan mota jeep baki da bakin tinted glass yazo wucewa da gudu, tsayawa motan yayi ya kasa tafiya, tana kallo me motan yana jan motan amma yaki tafiya da alama matsala aka samu, buɗe motan yayi ya fito sanye yake da baƙaƙen kaya ya rufe fuska da facemask ga kuma safan hanu da yasa, ba zaka iya ganin komai a jikinshi ba sai idanunshi, gabanta ne yayi mummunan faɗuwa, da sauri ta ɗauke kai kamar bata kallonshi lokacin da yake gyaran motan, tsaki yaja taga ya ciro waya yayi kira, sai kuma ya katse yana cigaba da gyarawa, a hankali taga an sauke glass ɗin wata yarinyar ƴar karama ta leƙo suka haɗa ido, da sauri yazo ya shiga motan yaja glass ɗin sama, tada motan yayi, sai kuma motan ya tashi, tafiya ya fara amma wannan karon a hankali yake tafiya, zubawa motan ido tayi, gani tayi kamar akwai mutum a booth, tashi tayi tana kallon yarinyar data ciro hanunta ta waje tana kiranta, aje ledan tayi a wajen ta fara binsu, bata san meyasa take binsu ba amma taji a ranta tanason ganin su waye a wannan motar, gani tayi ya nufi hanyan daji gashi duhu yayi binsu take ganin sun ɗan fara gudu itama ta fara gudu, azeez dake driving ganin sun shiga daji ya ciro wayarshi ya haska, zaici gaba da driving yaga kamar ana binshi, da sauri ya kashe wayan sannan ya kalli madubin ci gaba yayi da tafiya amma idonshi a baya, gani yayi da gaske ana binsu, kallon na gefenshi yayi yace "ana binmu"
da sauri ya juya yace "waye?"
yace "gata can ka kalleta karta gane mun