Showing 36001 words to 39000 words out of 40241 words
ne da zaku bar wannan kwalban?"
najwah dake mikawa mutumi roban jin in inan da yayi da kuma muryanshi taji kirjinta ya bada sautin dum, dara daran idanunta da suke cikin nikab ta zuba mishi tana kara tuna muryanshi, cikin tsawa yace "baaa... magana nake...muku ba?"
ras gabanta ya kara faɗuwa, tabbas wannan muryan shi taji yana cewa a kasheta, harma aka lalata mata fuska, saurin ɗauke kai tayi lokacin daya juyo ta wajenta, a ranta tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un allahumma ajjirni fi musibatin"
a fusace ya bar wajen, bin bayanshi tayi da kallo har ya shiga office, jikinta ne ya fara rawa, babu jimawa taga wasu zafafan motoci guda biyu sunyi parking, manyan mutane sanye da manyan kaya suka fito suna ɗaɗɗaga babban rigunan dake jikinsu, kana ganinsu kasan sun jiƙa da kuɗi, office nashi suka nufa direct su biyu, da kallo ta bisu har suka shiga ciki, me karɓan nonon ya kaiwa muneeb sunanshi sani yazo ya tsaya a kanta yace "malama barka da fitowa"
hankalinta a kan kofan batama san ana mata magana ba, yace "malama"
har yanzu bata jishi ba, tafa hanu yayi da ihu yace "malama"
firgigit ta dawo hayyacinta tace "sani kaine?"
yace "nine tunanin me kike? sannan meyasa kikasa nikab?"
tace "mijina ne ya hanani fita babu nikab"
yace "yanada gaskiya ko nine matata take da rabin kyaunki ba zan bari ta fita babu nikab ba"
ta fara dama furan har ta gama tace "sani ban taɓa gaisawa da ogan ku ba, ka bari mana na rinƙa kai mishi idan ba matsala"
yace "to kin san oga yanada faɗa shi abinda mutane suke so bashi yake so ba, a juye yake"
tace "ba komai zan daure kaci gaba da aikinka naga barin aiki kake kafin kazo ka kai mishi"
yace "haka ne na gode"
tashi tayi ta fara tafiya da sauri, a kofan office ɗin ta makale tana jinsu, magana suke akan miyagun kwayoyi, waro ido tayi jin muneeb ɗin yana faɗa musu riban da zasu samu akan cocain ɗin dake hanunsu ɗan kaɗan da suka raina, har suka gama suka tashi zasu tafi, a tsorace ta matsa gefe ta jingina da bango kamar zata shiga ciki, ta san idan sun san ta jisu zasu iya kasheta, har suka tafi basu ganta ba amma ita tana ganinsu, dafa kirji tayi tace "ya Allah"
ajiyan zuciya ta sauke, saida suka tafi kafin ta gyara nikab ɗin tayi knocking, amsawa yayi ta tura kofan a hankali ta shiga, ido huɗu sukayi, ta cikin nikab ɗin take kare mishi kallo, shima kallonta yayi da mamakin meya kawo mace da nikab office nashi, a hankali ta karaso inda yake, ɗan durkusawa tayi kafin ta mika mishi furan tace "ga nonon"
binta yayi da kallo sai kuma yabi furan da kallo, yace "who are you?"
sam bata game me yake nufi ba, tace "ga nonon"
kallonta ya kuma yi, dara daran idanunta masu ɗauke da dogayen eyelashes baƙi ƙirin ta zuba mishi kamar me neman wani abu a fuskanshi, yace "ɗa..ɗa..ɗaga nikab ɗinnan"
muneeb baya yadda da kowa, girgiza kai tayi tace "ba sai na ɗaga ba nice me dama maka fura a koda yaushe"
yace "so fucking what? sabida kece me dama min fura...sai...sai....saina yadda dake?"
shiru tayi, yasa hanu a drower, da mamaki taga ya ciro bindiga piston, a mugun tsorace ta zaro ido tayi baya sosai tana girgiza kai, yace "ɗaga nikab ɗin"
hanu tasa zata ɗaga sameer daya gaji da knocking ya tura kofan ya shigo, ganin babban yaya rike da bindiga gata manne da bango jikinta yana rawa ga nonon ya faɗi kasa ya zube, yace "babban yaya wannan fa ba wata bace me saida maka nono ce"
sauke bindigan yayi yace "meyasa ba zata ɗaga nikab ba?"
yace "haka take da nikab kullum amma ai ni na santa"
yace "ta...ta....ta share office ɗinnan duk inda ya ɓaci ta gyara"
sameer zaiyi magana tace "to"
fita tayi ta ɗauko abin shara tazo ta fara sharewa har tayi mopping sannan taje ta kara dama sabon fura ta kawo mishi, saman desk ya nuna mata, ta aje, zata fita yace "ina sani?"
tace "naga saiya bar aikinshi yake kawo maka shine nace ya bari zan rinƙa kawo maka kullum"
bai amsata ba kawai yaci gaba da aikinshi"
tana fita ta zauna a karkashin bishiya, tace "me hakan yake nufi? yana harkan miyagun kwayoyi sannan me alakanshi da waɗanda suka sato yara?"
tashi tayi tana kallon kofan tace "ya Allah wannan shi ɗin wanene?"
dafa kirji tayi tace "ko dai shine boss?"
_Kuyi payment ₦400 ba zai rageki da komai ba, ki biya ki samu complete kiyi karatunki hankali kwance, account number 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, evidence via 08144818849_
*Jiddah Ce....✍️*
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 12*
_Last free pages anan na kawo karshen free pages akwai complete account details yana kasa duk wanda yayi payment zai samu complete_
~Har aka tashi yau idonta akan office na muneeb da masu shiga da masu fita duk tana ankare dasu, koda ta ɗauki habibi ta koma gida tunanin abin bai bar kanta ba, hasalima tana cin abincin rana kwanciya tayi, yi tayi kamar tana bacci hakan yasa basu dameta da surutu ba, naina da habibi suna zaune suna karatu naina tana kara koya mishi yadda zaiyi karatu sosai ta kware a turanci tanada ilimi ba kaɗan ba, najwah dake kwance tace "to wannan muneeb ɗin kenan shine boss da yake sa su sace yara?"
sai kuma tace "no watakila fa bashi bane kawai de muryan ne kala ɗaya, kuma ai bashi kaɗaine me in ina a duniya ba"
tace "to amma yana saida mugayen kwaya ya akayi haka?"
lissafinta ya dagule ta rasa me take tunani, har Allah Allah take gari ya waye domin taje ta kara tabbatar da abinda take zargi, washe gari ta gama komai suka tafi da habibi, a kofan school ta ajeshi yace "mama baki bani kuɗi ba"
tace "gashi amma idan ka siya abu ka ajemin canji"
yace "to mama canjin nawa?"
cikin innocent voice yake magana, tace "ɗari"
yace "thank you mama, sai kinzo, Allah kawo kasuwa"
tace "ameen yarona Allah maka albarka"
yace "ameen"
saida ya shiga ta tabbatar kafin ta koma mashin suka tafi, shima a lokacin ya shigo, kallo ta bishi dashi ta cikin nikab ɗinta, yana tafiya ne cike da izza, a ranta taji tsananshi ya ɗarsu a ranta fiye da da, ta rasa meyasa kowane kallo ɗaya idan ta mishi sai taji tana kara tsananshi, dama furanshi ta fara sannan ta tashi ta fara tafiya, knocking tayi ya amsa shiga tayi ta aje mishi a gabanshi sannan ta juya zata tafi, ji tayi an kira wayarshi ya ɗaga, a hankali ta juyo ta dawo tayi kamar bata jinshi tace "laa na manta bansa sugar ba"
harara yake mata hankalinsa akan wayan yace "ka tabbatar yau kayi aiki sabida babu kaya a tare damu kuma za'a fita"
shiru yayi, tana zuba sugar har ta gama wayan yana kunnenshi yana sauraro baiyi magana ba, sai kuma yace "a..a...a kofan school kada ka barsu yau"
katse wayan yayi ta fita tana maimaita kalman a kofan school?
me zai faru a kofan school ɗin?
har ta gama saida nonon tana maimaita kalman, fitowa yayi da waya a kunne yana magana amma bata jinshi, da ido ta bishi har ya shiga mota suka tafi, jiki a mace ta shiga mashin zuwa school ɗinsu habibi, an jima da tashi musu saide taga babu kowa a kofan school ɗin, fita tayi a mashin ɗin ta shiga cikin school ɗin, mutanen data gani maƙil a ciki, wasu na kuka wasu suna ihu yasa ta tsaya ta kasa karasawa, ga malaman suma kuka suke, da kyar taja kafarta ta karasa, har wani jiri take ji ta samu wani malamin da yake zaune baya kuka amma ya dafa kanshi yayi shiru yana zufa, a tsorace tace "ina habibi?"
yace "saide kiyi hakuri an sace ɗaliban makarantar nan duka...."
kuka ya fashe dashi, duhu jiri ciwon kai duk suka haɗu mata a lokaci ɗaya, bakinta yana rawa kamar yadda jikinta yake rawa, batasan lokacin data ɗaga nikab ɗin ba, duk suka fara kallonta da mamakin rabin fuskanta da yake a kone babu kyaun gani ya zama abin kyama, cikin tashin hankali ta zauna daram a kasa ta kasa kuka ta kasa cewa komai sai bin kowa take da ido, wata mata data shigo yanzu a haukace babu hijabi tana ihu tace "yarana biyar, wallahi yarana biyar duk an kwashesu saikun biyamin yarana wallahi sai an biyani"
rirriketa akayi, najwah sai yanzu ta samu bakinta ya buɗe tace "habibi kar muyi haka da kai, habibi kada ka tafi ka bar mamanka, habibi!!!! habibi!!! habibi!!!!"
da karfi take kiranshi ta tashi a razane tana ihu tana kiranshi, atake wajen ya rikiɗe, rike najwah akayi ta fizge tana kara ihu, hanu ta ɗaura a kanta tace "ya Allah bazan iya rashin habibi ba wallahi ba zan iya ba ku tashi muje mu nemosu"
duk suka tashi ganin nata sun haukace akan yaransu matar da yaranta biyar sai suma take, fita najwa tayi duk suka bita a kofan makarantar suka tsaya suna ihu, take ƴan sanda suka zagaye school ɗin, rahoto ya tafi wa kowa a gari, najwah tsaban ihu har muryanta ya dashe, banda rarraba jajayen idanunta babu abinda take yi, wata mata da taji tausayinta sosai tazo ta riketa tace "ki rinƙa numfashi baiwar Allah kada ki haɗi zuciya"
shiru tayi bata amsa mata ba, matar ta kara cewa "kiyi nunfashi me kyau"
a hankali taja nunfashi, sai kuma tace "shi kaɗai nake gani naji sanyi, shi kaɗai ne abin alfaharina"
tace "mu rungumi ƙaddara haka Allah ya ƙaddara"
share hawaye tayi tace "ba haka Allah ya ƙaddara ba tabbas mutum ne ya tsara wannan abin kuma na rantse matuƙar ina raye babu abinda zai samu habibi, koma waya saceshi na rantse da Allah saina zame musu matsala a rayuwarsu, babu abinda zai samu habibi nayi alkawarin hakan"
tashi tayi ta karkaɗe jikinta da yayi datti, batasa nikab ɗin ba kawai ta tafi ta har komai ciki harda kuɗi da kwanukan nonon, mutane sai binta suke da kallo da rabin fuska a kone, bata damu ba yanzu damuwanta ɗaya yadda zata nemo ɗanta, da haka ta ida gida, inna tana ganinta a haka saida ta zauna sabida jiri, naina ce ta zo da gudu ta riketa ganin zata faɗi, a jikin nainan ta faɗi wani irin ihu ta kwala har makota zasu iya jinta, cikin ihu tace tace "ya sace habibi sun sace shi"
naina tace "innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
inna hanu ta ɗaura aka ta kwala wani uban ihu, tace "na shiga uku na lalace"
naina wacce zaman da tayi kaɗan dasu ta shaƙu da habibi ta saki najwah ta zauna kasa daram tana salati
najwah ihu take tana birgima a kasa, tace "ya sace shi wallahi ina zargin muneeb ne, wallahi muneeb ne ya saceshi"
tashi tayi a gigice zata fita naina ta riketa tace "ina zakije najwah?" tace "muneeb saiya bani ɗana wallahi saiya dawo da habibi"
rungumeta naina tayi ganin ta zauce tace "ki nutsu najwa kada kiyi abinda zaisa a kamaki da laifi mubi komai a hankali"
kuka kawai take yi a jikin naina.
cikin motan da aka sasu kuka suke musamman habib wanda yake jin tsoro sosai dama yanada tsoro sosai, azeez dake sanye da bakaken kaya ya rufe fuskanshi da hanunshi da komai na jikinshi ya juyo cikin tsawa yace "idan bakuyi shiru ba zan zubar daku ku mutu"
tsit sukayi babu wanda ya kara magana, cikin daji yake tafiya dasu saida suka isa gidan, ya kalli na gefenshi yace "mu rufe musu ido dokan boss ne haka"
tsayawa yayi da motar suka fara ɗaura musu bakin kyalle ta yadda ba zasuga gidan da zasu kaisu ba, habibi da suka fara tafiya kasa yayi da kyallenshi yana bin ko ina da kallo har cikin gidan aka shiga dasu, kallon mutanen gidan yake a tsorace, lokacin da zasu fara fita dasu yayi saurin rufe fuska da kyallen kamar baiga komai ba, wani ɗaki suka kaisu bayan sun basu uniform sun sa, sannan suka ciccire nasu suka ƙona, saida aka shiga dasu kafin aka kwance musu kyallen su duka, kuka sukeyi kowa yana kiran mama ciki harda habib wanda yama gaji da kukan sai ajiyan zuciya yake saukewa, kwanciya yayi a kasa ya fara bacci.
najwa yadda taga rana haka taga dare, baccin ma koda yake ɓarawo yau ya kasa ɗaukanta, har gari yayi haske tayi salla ta rinƙa addu'a Allah ya tseratar da habibi da sauran wanda aka sace, tuni aka fara yaɗawa a gidan jaridu da gidajen tv da rediyo, shiri tayi ta ɗau nonon ta ɗaura a kanta yau batasa nikab ba haka ta tafi, koda taje company kowa binta yake da kallo bata damu ba, idonta akan kofa zuciyanta yana tafasa jira take taga shigowan muneeb sabida ta tabbatar da zarginta matukar ta tabbatar muneeb ne yake yin haka ta rantse da Allahn daya halicci sammai da kassai saita lalata rayuwar muneeb, saita hanashi jin daɗin duniya, sai muneeb ya nemi mutuwa da kanshi, bashi kaɗai ba har family ɗinshi saita zame musu bala'i da masifa, sai sunji sun tsani koda irin sunanta ne, idan ya tabbata shine sai yayi nadaman taɓa abinda tafi so akan komai wato habibi.
Kallo suke amma duk jikinsu a mace, fitowa yayi sanye da suit yayi kyau sosai yana waya, da kallo ya bisu sannan ya katse wayan har ya karaso basu sani ba, kallon tv yayi yaga hotunan yaran da aka sace ake nunawa ga iyayensu sai kuka suke suna cewa a tayasu da addu'a, kashe tv yayi, duk suka kalleshi, ya ɓata rai yace "breakfast"
jiki a mace suka tashi, duk cikinsu babu wanda ya iya cin abincin sai jujjuya cokala suke, binsu yake da kallo, sunada tausayi duk wanda yaga yadda iyayen yaran suke kuka matukar yanada imani sai yayi kuka, Azad yace "unty batool kenan kashe yaran za'ayi?"
cikin mutuwan jiki tace "wallahi ban sani ba baby Azad, ban san meyasa ake sacesu ba, ko kashesu za'ayi ko kuɗi zasuyi dasu oho, amma abin yayi muni, abin ya wuce misali Azad wani irin rashin imani ne zaisa a rinƙa sace yara kanana waɗanda basu san komai ba? Allah ba zai taɓa barin wanda yake wannan abin ba kuma kullum idan nayi salla ina addu'a Allah ya tona asirin...."
glass jug na juice ne ya faɗi daga hanun muneeb, atare suka kalleshi, fashewa glass ɗin yayi ya durkusa zai kwashe jabeer yace "ka bari yaya zan kwashe"
hanu yasa zai kwashe siririn glass ya yanki karamin yatsanshi
"Ash"
ya faɗa cikin jin zafi, da sauri unty batool ta riko hanun tace azad ya ɗauko first aid box tashi yayi domin ɗaukowa murmushi yayi ganin ya kawar da maganan, tashi yayi yace "na tafi"
fita yayi ya barsu a wajen, kamar kullum convoy sukayi da zafafan motoci har suka isa company, yana fitowa a mota ta bishi da ido ko kyaftawa batayi, har ya shiga office kafin tayi sauri ta fara haɗa mishi furan, saida ta gama ta nufi office ɗin, ji tayi yana waya da sauri ta dakata da knocking ɗin batayi ba, cikin in ina yake cewa "an gama gashi maganin a hanuna da yamma zan bada a kawo maka a airport duk karfin jinin mutum idan yasha wannan maganin ɗaya saiya bugar dashi ya sashi bacci kamar ya zama gawa"
dariya yayi sannan yace "an gama"
tana ji ya aje wayan tayi knocking, amsawa yayi ta tura kofan ta shiga, bai kalleta ba dan yasan itace, a gabanshi ta aje nonon idonta akan maganin dake kan table da alama shine maganin da yake magana akai, juyawa tayi zata tafi ta taka kafarshi a firgice ta juyo zubewa tayi akan table ɗin, idanu a waje cikin tsoro ta kalli hanunshi daya riketa dasu, kallon fuskanta daya bashi kyama yayi, sakinta yayi ya kalli nonon daya zube a jikinta, jikinta yana rawa tace "kayi hakuri wallahi bada"
wurgi yayi da ita ta faɗi akan tiles, yace "out"
jiki yana rawa tace "bari na haɗa maka wani nonon"
tsaki yaja ya nuna fuskanta yace "da nasan...haka...haka fuskanki yake abin iyama da ban taɓa sha ba"
shiru tayi kanta a kasa tace "shikenan zan daina dama maka gobe zan kawo maka madaran sai kasha"
abin mopping ta ɗauko zata fara goge inda ta ɓata yaja tsaki ya shiga toilet, da sauri buɗe goran ruwan dake kan table ɗin yasha kaɗan, maganin data ɗauka ɗaya ta jefa a ruwan, girgizawa tayi sannan ta maida ruwan, abin mamaki bai canja kalan ruwan ba, fitowa yayi yace "out"
fita tayi, tsaki yaja yana dana sanin shan nonon da yayi na tsawon rayuwarshi, sai yaji ya tsani nonon ma, ko mutuwa zaiyi ba zai kara sha ba, murmushi tayi bayan ta fita, sai kuma ta samu waje ta zauna tana aikinta kamar batayi komai ba, can taga sani ta ɗaga mishi hanu, yazo suka gaisa tace "sani tambayi oganku a kawo masa nono?"
yace "dama baki kai mishi ba?"
tace "shi yace sai an tambaya za'a kawo"
yace "bari na tambaya"
direct office ɗin ya wuce, knocking ya rinƙa yi bai amsa ba, tura kofan yayi ya shiga gani yayi yana bacci kamar zai faɗi akan table, da sauri ya juya ya fita, tace "akai mishi?"
yace "bacci yake amma nayi mamaki oga na bacci a office bai taɓa yin haka ba"
tace "Allah sarki bari na bari to idan ya tashi"
yace "to"
tafiya yayi, tayi murmushin da ita kaɗai tasan dalilin yi, saida ta tabbatar sani ya tafi kafin ta tashi da roba a hanu kamar zata kai mishi, shiga tayi batayi knocking ba, ganin yana bacci tayi saurin aje roban taje inda yake, bincike ta fara tana buɗe duk wani abinda tasan za'a iya ɓoye abu a ciki, bata samu komai ba, wayarshi ta gani, zata ɗauka taji ya fara ringing da sauri tayi received sannan ta kara a kunnenta, ji tayi yace "oga mun gama komai mun cire musu uniform kuma munsa musu uniform namu, yanzu saura kawai a gama cinki kafin mu fitar dasu a gama aiki"
gabanta yayi mummunan faɗuwa aje wayan tayi jikinta yana rawa, gani tayi ya katse wayan, kallon fuskan muneeb take babu ko kyaftawa, a razane take kallonshi kenan shine ya sace su habibi?
hanunshi tasa akan tunprint na wayar take