Showing 33001 words to 36000 words out of 40241 words
ganeta"
yace "okay"
a hankali yake tafiya idonshi a kanta duk da baya ganin fuskanta sabida duhu, tsayar da motan yayi ya fito kamar yana gyara, najwah da sauri ta ɓuya bayan wani bishiyan tunfafiya, ɗayan dake motan a hankali ya buɗe marfin a kwanta a kasa, cikin sanɗa yake tafiya har yazo inda take bata sani ba, ji tayi an rike kafafunta, ihu ta kwala ta fara janye kafarta tana cewa "ka sakeni ka sakeni nikam"
damketa yayi sosai ta yadda ba zata iya kwacewa ba, azeez ya karaso da gudu yace "me yasa kike binmu?"
tace "ku sakeni"
kwace kanta take, yace "babu wanda zai sakeki sai boss yaji"
wayarshi ya kira layin boss ta cikin bluetooth biyu dake kunnenshi yace "boss ga wata nan ta ganmu harma ta biyomu daji"
kwace kanta tayi zata gudu yasa mata kafa, faɗuwa tayi shima ya faɗi domin taja ƙafarshi, bluetooth ɗaya ya faɗi da sauri ta ɗauka tasa a kunne, bai ankara ba ya zaci a kasa ya faɗi, tana ji yace "ku...ku...ku watsa mata acid a idanunta ta yadda ba zata iya ganin komai ba"
yace "an gama boss"
a mugun tsorace ta fara jan kanta daga wajensu, ɗaya ya riketa ɗaya yaje mota, wani abu ta gani a karamin gora yazo inda take, tace "dan Allah kada ku ɓatamin fuska dan Allah kuyi hakuri"
yace "kinga sirrin boss ba zaiyi mu barki da ido ba duk wanda ya shiga gonan boss baya fita saida illa"
danneta sukayi cikin ihu ta ɗaga murya tace "ku gudu"
tayi magana ne ganin yaran sun fito, ta kara cewa "ku gudu kada ku yadda ku tsaya"
yara sun kai goma suka fito daga motan suna fara gudu cikin duhun, azeez ganin haka ya watsa mata acid ɗin a fuska, ihu tayi jin azaban daya ziyarci fuskanta, tana ji fuskanta yana konewa tace "wayyo Allah na mutu"
azeez yace "ka gama da ita zanje na kamo yaran banda fyaɗe kasan boss ya hana"
yace "to"
birgima take a kasa, taji yana shirin rabata da kayan jikinta wani dutse da taji kusa da hanunta ta rarumo ta kwala mishi aka, faɗuwa yayi a wajen da gudu ta bar wajen tana kukan azaba ta rufe ido bata ganin komai, banda azaban zafi babu abinda takeji, bata san ina take zuwa ba ita dai kawai tana tafiya ne, azeez wanda ya kasa ganin yara ko ɗaya ne ya dawo a wahale yace "banga kowa bafa sun riga sun gudu ina take?"
yayi tambayan yana kallonshi, yace "ta gudu"
yace "what? garin ya ka barta ta gudu?"
yace "dutse ta kwalamin"
wayarshi aka kira yaga boss, ɗauka yayi yace "boss akwai matsala fa yarannan sun gudu"
cikin fusata yace "ina...take...yarinyar?"
kallon na gefenshi yayi sannan yace "mun kasheta gashi yanzu zamu binneta anan"
yace "good tunda kun kasheta, da..da...da baku kasheta ba ni zan kasheku"
katse wayan yayi, yace "me yasa kayi mishi karya?"
yace "sabida idan mukace ta tsira ba zai barmu ba"
yace "kumafa hakane"
_Na kusa gama free pages masu son complete akwaishi kina biyan ₦400 zaki samu complete babu ɓata lokaci, account 6037523268 hauwa shuaibumapi keystone, sai a turo katin shaidan biya ta nan 08144818849_
_Jiddah Ce.....✍️_
[20/08, 2:11 am] Shuraihu Usman: 🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*NI DA MUNEEB*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
Na
*Jiddah S Mapi*
*Chapter 11*
~Gudun ceton rai take, yaran ma kowa yayi ta kanshi batasan ina take ba tayi nisa sosai kuma ta tabbatar ta bar inda suke, faɗuwa zatayi a galabaice taji an riketa, baki ta buɗe zatayi ihu aka rufe bakin, muryan mace taji tace "baiwar Allah ina zakije?"
ta rirriketa sosai tace "gida gida zanje wajen innata dan Allah ki kaini gida fuskana yana raɗaɗi"
ta riketa tace "sannu amma nima gudu nakeso nayi saide ba zan iya gudu na barki ba a wannan halin da kike ciki"
najwah tace "dan Allah ki taimakeni fuskana yana raɗaɗi"
tace "to"
riketa tayi suka fara tafiya, tace "ya sunanki?"
tace "sunana najwah"
tace "ni kuma NAINA"
tace "amma meya fito dake?"
tace "gudu nakeso nayi sabida an auramin wani tsoho wanda ya kasance mugu shiyasa nakeso na gudu iyayena sun rasu matar babana wacce nake hanunta ce ta aurar dani wa shi"
najwah cikin azaba tace "Allah sarki"
har suka shiga cikin gari najwah tayi mata kwatancen gidansu, har gida ta kaita suna shiga inna da habib wanda yaki cin abinci sabida mamanshi bata dawo ba suka taso da sauri, inna ta dafa kirji tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un najwah meya sameki? me a fuskanki ya koma baƙi haka najwah?"
matsowa tayi a tsorace tayi baya ganin fuskan a kone tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga uku, na shiga uku na lalace, mugun gani nayi yau, najwa meya sameki? baiwar Allah meya samu ƴata"
naina wacce take kyakkyawa sosai tace "a daji na ganta tana gudu nima gudun nake sai naji na rike mutum ban san komai akan abinda ya samu fuskanta ba"
inna ta ɗaura hannu aka kamar zata kurma ihu, najwah banda kuka babu abinda take yi, habib ya rungume kafafunta yace "mama meya samu fuskanki?"
tace "na kone habibi acid aka watsamin a fuska"
inna tace "wani azzalumin ne yayi miki haka? wani azzalumi ne baya son ganin kyakkyawan fuskanka najwah ya ƙona miki?"
tace "inna ban sansu ba"
labarin abinda ya faru ta basu, inna ta riketa ta kaita ɗaki ta zauna a bakin katifa tace naina ta shigo, shigowa tayi inna tace "ki buɗe ido ki kalleni"
a hankali ta fara buɗe ido, kallon inna tayi sannan ta kalli naina, inna tayi tagumi ta kasa cewa komai sai godewa Allah take da yasa idanunta suna nan lafiya ƙalau, naina tace "zan tafi"
inna tace "ina zaki da dare haka ƴata?"
kuka ta fashe dashi ta fara basu labarin mutuwan mahaifinta wanda yake da bala'in kuɗi, bayan iyayenta sun rasu a hatsarin mota shine kishiyar mamanta ta aurar da ita wa wani attajirin ɗan siyasa, abinda ya bata tsoro ta gudu shine taji yana waya da uwargidansa tana tambaya yaushe malam yace ya fara taɓa ta da sunan aure? yace malam bai bashi time ba, ta gano shi ɗin babban matsafi ne kuma bakinsu ɗaya da matarshi hakan yasa ta gudu sabida ta tsira da ranta da lafiya, inna cikin kuka tace "ki daina kuka idan zaki iya zama damu mu zauna"
tace "zan iya, idan ma nace ba zan iya ba babu inda zanje, banida kowa"
najwah tayi shiru banda hawaye babu abinda take yi, madubi ta kalla rabin fuskanta a ƙone yake yayi baƙi ƙirin rabi kuma fari.
habib ya sata a gaba shima yana kuka, da kyar inna ta lallashesu, a ranan sun kwana cikin bakin ciki.
washe gari, sauri yake yana kallon agogon hanunshi, yayi bala'in kyau cikin maroon dress, cikin sauri ya isa compound motocin da zasu fita duk suka zama ready, shiga wanda aka buɗe mishi yayi ya ɗau jarida ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya yana karatu, har suka isa company ya fito yana rike da jaridan ya wuce cikin office nashi, minti kaɗan da zamanshi akayi knocking yace "come in"
azeez da yake sanye da black dress ya shigo, ɗan russuna yayi yace "good morning boss"
harara kawai yake aika mishi bai amsa ba, jaridan ya wurga mishi yace "karanta"
karatu ya fara, a firgice ya kalli muneeb ɗin, gira ya ɗaga mishi alaman yes, yace "boss yaushe wannan labarin yaje musu?"
yace "ina zan sani? kullum ina faɗa maka ka rinƙa taka tsantsan ka rinƙa sanin inda zaka haɗu da mutane kafin ka basu sako, yanzu gashi nan har hoto shi lokacin da kake mika musu cocain, ba...ba...ba dan ka..rufe fuska da mask ba da an kamamu"
yace "sorry boss na saba haɗuwa dasu a bakin teku sabida can ne yafi sirri amma wannan karon sunce helicopter ɗinsu ba zai tsaya a bakin kogi ba"
cikin harara yace "shiyasa kayi taking risk? ka...ka...kakkasan bana taɓa taking risk a rayuwata ko? kasan koda yaushe....a ankare nake da kowa, azeez wannan harkan namu yanada haɗari sosai, har batool zargina take amma na rufe duk wani kofan zargi, ina sane takesa sameer ya samin ido, tunda...gida...suna zargi inaga mutanen waje?"
yayi shiru kanshi kasa, yace "be very careful azeez"
yace "insha Allah boss"
ya nuna mishi wajen zama yace "seat"
zama yayi, yace "jiya da...da...dare ya kukayi da yarinyar?"
yace "boss kawai gani mukayi tana binmu saida muka shiga tsakar daji muka kasheta amma yaran sun gudu"
yace "ka tabbata ta mutu? kasan fa muneeb baya barin evidence binnewa yake kota yaya"
yace "boss na tabbata ta mutu"
yace "good job"
tashi yayi yace "zan wuce"
yace "okay"
fita yayi, muneeb ya kalli time yaga basu kawo mishi fura ba yau, yunwa yake ji sosai yakeson sha, waya ya ɗaga ya kira akace bata fito ba, jim kaɗan ya kara kira aka tabbatar mishi bata fito ba, shiru yayi ya rasa abinyi, wayar sameer ya kira, sameer dake shirin fita yaga kiran babban yaya da sauri ya ɗaga yace "hello babban yaya good morning"
yace "sameer bata fito ba kuma inason nono"
yace "to gaskiya idan ta kai wannan lokacin bata fito ba akwai matsala, bari naje na dubata a bakin kasuwan"
yace "kayi...sassa... sauri"
yace "to"
motarshi ya shiga ya hana kowa binshi dan baison wannan masu gadin, bakin kasuwa yaje yana dubata a inda ya saba ganinta, bai ganta ba, da mamakinshi yaga babban yaya yana kara kiranshi, ɗauka yayi yace "babban yaya bata nan fa...."
"ka nemi gidansu"
shine abinda ya faɗa mishi kafin ya katse kiran, bin wayan yayi da kallo yace "gidansu kuma? is ya muneeb okay?"
kallon mutanen wajen yayi baima san waye zai fara tambaya ba, a hankali yaje wajen wata mata dake gefe ya gaisheta sannan yace "dan Allah wata bafulatana da take saida nono anan nake nema"
matar tace "okay maman habib?"
yace "eh ita dan Allah ko akwai wanda yake da number ɗinta?"
tace "ai maman habib batada waya"
yace "kash"
tace "amma na san gidansu dan akwai ranan da muka haɗa mashin saida aka ajeta kafin aka wuce dani"
da sauri yace "dan Allah kimin kwatance"
tace "to"
kwatance tayi mishi yayi godiya ya ciro kuɗi dayawa ya bata, karɓa tayi tana godiya, motarshi ya shiga yaja da sauri, daɗi yakeji a ranshi sabida baison babban yaya ya nemi abu a wajenshi bai samu yayi mishi ba, tafiya yayi da nisa har ya shiga unguwansu, kofan gidan data mishi kwatance ya tsaya, fitowa yayi ya tsaya a kofan yayi sallama, najwa da inna da habib suna zaune akan tabarma naina kuma tana musu girki sukaji sallama, idanu naina ta zaro domin a matukar tsorace take ta san Alhaji ba zai taɓa barinta ba, duk inda take saiya nemota hakan yasa jikinta ya fara rawa, najwah da rabin fuskanta ya koma baƙi ƙirin babu kyaun gani tayi karfin halin cewa "habibi leka waye ne"
da sauri ya tashi ya fita babu takalmi ya leka cike da wayo bai fito ba, murmushi sameer yayi mishi yace "habibi yau baka je school ba?"
da sauri ya koma ciki bai bashi amsa ba, a gaban najwah ya tsaya yace "mama wancan mutumin daya siya mana ice cream ne yazo"
tace "sameer?"
ya gyaɗa kai yace "eh shine"
tashi tayi da sauri ta shiga ɗaki, hijabi tasa sannan ta ɗauko nikab ta rufe fuskanta dashi, fitowa tayi tace "sameer sannu da zuwa"
murmushi yace "yawwa maman habibi"
gaisawa sukayi idonta kawai yake iya gani, yace "dama yayane ya aikoni yace bakizo yau ba shine na fara neman gidanku wata wacce kuke zama tare a bakin kasuwa tamin kwatance"
tace "Allah sarki dama bana jin daɗi ne shiyasa banje ba, amma gobe insha Allah zan fita"
yace "to idan ba damuwa zan iya tafiya mishi dana yau?"
tace "ba komai ka jirani ina zuwa"
yace "to mun gode sosai"
shiga ciki tayi naina dake zaune akan turmi da gudu ta tashi zata shige ɗaki a tsorace, najwah tace "tsaya mana ba komai costomer ɗina ne"
komawa tayi tana dafa kirji tace "thank god"
najwa nono ta ɗauko ta fara haɗa mishi saida ta gama tasa a leda ta fito ta mika mishi, karɓa yayi ya ciro kuɗin ya bata, tace "karka damu kyauta na baka"
yace "kika bashi dai sabida ni bana sha"
tace "ban sanshi ba kai na sani kai na bawa"
yace "to na gode"
zata shiga gida yace "amma meyasa kikasa nikab?"
tace "ba komai dama ina sawa bari nayi amma yanzu zanci gaba da sawa"
yace "to na gode sosai"
tace "ba komai" kawai ta shiga gida, motarshi ya shiga ya kama hanyan company, kiran muneeb ya shigo ya ɗaga yace "gashi nan na samo gidansu kuma ta bani wanda zan kawo maka"
baiyi magana ba ya katse wayan, kwafa sameer yayi sannan ya fesar da iska yace "Allah na godema dana samo ta"
koda ya isa knocking yayi, ba ɓata lokaci yace "yes"
shigowa yayi da leda a hanu yazo ya durkusa ya mika mishi, karɓa yayi yace "buɗe fridge.....ɗau...ɗau...ɗau..."
marin fuskashi yayi, da sauri sameer ya rike hanunshi yace "dan Allah yaya ka daina haka"
yana huci yace "ɗauko bowl da ice a fridge"
a hankali ya saki hanunshi zuciyanshi cike da tausayin yayanshi, bowl ya ɗauko da spoon wanda ya aje musamman dan shan nono, kankara yasa a ciki kafin ya kawo mishi, juyewa yayi a ciki yana tsaye yana kallonshi yadda yake juyawa cikin tsafta yake yin komai, ɗago kai yayi sukayi ido huɗu da sauri ya ɗauke kai yace "babban yaya zan tafi"
kai kawai ya ɗaga mishi ya fara sha, fita yayi.
najwah suna zaune suna cin abinci itada naina da habib tace "inna dole na rinƙa fita zuwa saida nono zan rinƙa sa nikab sabida idan anga fuskata zasuyi saurin gane ni"
inna tace "a,a najwah ki bari ni na rinƙa kai nonon can kada watarana kiyi kuskuren ɗaga nikab ɗin suzo su kashemin ke"
tayi maganan tana hawaye, naina tace "me zai hana ni na rinƙa kaiwa"
ta girgiza kai tace "A,a kema Alhaji ba zai daina nemanki ba, idan sun ganki zasu kasheki"
sukayi shiru, najwa tace "insha Allah babu me kara ganin fuskata inna saide idan ina gida amma ba zan taɓa kuskuren ɗaga nikab ba"
inna tace "to najwah na yadda ba zaki ɗaga ba kuma insha Allah addu'ata tana tare dake, babu abinda zai sameki"
tace "to inna na gode"
bayan sun gama cin abincin tasa nikab ta fita daga gidan, madara ta siyo ta dawo ta fara haɗa nonon da zata fita dashi gobe, naina tana kallonta yadda take yin abu cikin kwarewa tace "amma kinyi zaman ruga ko?"
gyaɗa kai tayi taci gaba da haɗawa, kallon tulin gashinta naina tayi sannan ta kalli fuskanta rabi da bai kone ba, tace "amma gaskiya najwah ke kyakkyawa ce"
murmushi tayi kawai batayi magana ba, naina tanada yawan tambaya ita kuma najwa bata son yawan tambaya, tace "amma habibi ɗanki ne?"
tace "bakiga munyi kama bane?"
tace "eh to ai bansan asalin fuskanki ba"
murmushi tayi tace "ɗana ne mana"
tace "to amma..."
hanu ta ɗaga mata tace "naina idan kinaso mu zauna lafiya kada ki karamin tambaya akan habibi ko abinda ya shafeshi, yawan tambaya ma banso"
tace "to insha Allah"
tayata ta fara suka gama, najwa ta fara shara ita kuma naina tayi musu goge goge, duk sanda ta tuna abinda ya faru da ita sai gabanta ya faɗi, tana wanke kwanuka taji ihun yara a kunnenta sakin kwanon tayi ta kwala ihu, inna dake cikin ɗaki ta fito zaninta har yana shirin faɗuwa, tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un najwah me yake damunki?"
kanta ta rike tana toshe kunne kamar wacce ta zauce tace "inna bana gane hankalina inna ban san me yake faruwa ba, yara basa barina na huta ihu suke min a kunne"
naina ce ta riketa tana tofa mata addu'a, saida ta ɗan nutsu kafin ta riketa a hankali zuwa ɗaki, a bakin katifa ta zauna tace "naina na rasa me yasa nake jin ihun yara ko bacci nake sai sunzo min, naina banyi cikin shege na zubar ba bale ace yaran dana zubar suke damuna"
hanunta naina ta rike tace "najwa akwai abinda yasa kike jin wannan ihun, haka kawai Allah ba zaisa kiji babu dalili ba, amma sanin dalilin shine aiki, kiyi addu'a sosai, koni lokacin da nake gidan Alhaji kullum bana iya bacci mugayen mafarkai nake yi wani ma idan na tashi bana iya motsi jikina duk yana ciwo, ashe Allah ne yake nunamin Alhaji matsafi ne a mafarki, dana dage da addu'a ba gashi Allah ya nunamin a fili kuma na tsira da rayuwata ba?"
tayi shiru, ta kara matsa hanunta cikin son bata karfin gwiwa tace "addu'a zaki dage dayi babu dare babu rana kada ki fasa addu'a kinji?"
tace "to"
tace "idan ma wani abin ne kiyi addu'a Allah ya bayyana miki cikin sauki"
tace "amma naina da Allah ya nunamin wannan mutumin daya sace yara kinga garin taimakonsu na rasa rabin fuskata, naina haka zan kare rayuwa da fuska rabi? naina ko habibi na lura tsoron kallona yake, to inaga wasu mutane da zasu kalleni?"
tace "haka Allah ya ƙaddara kuma insha Allah zakiyi nasara a kansu"
tace "Allah yasa"
tana zaune tana bata karfin gwiwa.
washe gari ta shirya habibi kamar kullum ta shirya nonon sannan ta ɗaura a kanta, nikab tasa sannan ta rike hanunshi suka tafi, mashin suka shiga ta kaishi har kofa sannan ta bashi kuɗin break da abincinshi ya shiga har ciki kafin suka tafi, a kofan company ta fito tana ɗaukan katon roban ta shiga dashi ta kwashe komai kafin ta biyashi kuɗinshi, bala megadi yace "kyakkyawa yau da nikab kuma kikazo?"
tace "eh baba mijina ne yace na rinƙa sa nikab kada na bari wasu mazan su kalleni"
yace "yayi gaskiya domin barin mata kyawawa irinku suna yawo haka ba nikab zai kawo wani abin a cikin al'umma"
murmushi tayi kawai ta wuce ciki ta zuba mishi furan da take kawo mishi kyauta a kullum, ya karɓa yana godiya yana sa mata albarka, komawa tayi yau da alama ta riga wanna ɗan jiji da kan ogan nasu zuwa, tana zaune a wajen motocinsu suka shigo, ɗauke kai tayi lokacin daya fito cikin farin kaya, yayi kyau sosai ga kamshin turarenshi dake isowa har wajenta, zuba nono tayi a wani roba tana haɗawa wani dake tsaye a kusa da ita, tafiya yake cike da izza har yazo bakin kofan shiga asalin wajen, runtse ido yayi jin ya taka abu a ƙafarshi, a hankali ya buɗe idon yaga kwalba ya taka kuma kafar har ya fara jini kaɗan kaɗan, a tsawace ya kira masu shara, da sauri sukazo suka durkusa gabanshi, nuna musu yayi yace "ku...ku...ku.....ku makafi