Showing 27001 words to 30000 words out of 93383 words
dawo ya tambaye ta ace ta fita alhalin ba ta da makaranta yau.
Aikuwa dai sai wuraren biyar da mintoci suka shigo gidan, ko ci kanki ba wanda ya cewa wani a cikinsu. Su Yassar dake zaune cikin abokansu a kofar gidan su ka bi su da kallo.
"Ga uwar girman kan gidannan ta dawo." Faɗin wani abokin Yassar yana nuni da Humaira. Tun ranar da ya yi gangancin kulata da sunan so ta ci mishi mutunci yake jin tsanarta. Yassar tsaki ya ja.
"Kai ka so ai dama ka ga kalar nata girman kan, amma ga mata a gari kamar ƙasa ka rasa ta kulawa sai wannan ƴar ƙauyen nijar din?"
Sauran suka yi dariya. Shi kuwa Yassar miƙewa ya yi ya bi bayansu ganin kamar Raihana na sharce hawaye, jikinsa har mazari yake don muddin ya kasance Humaira ce sila to ya rantse sai ya rama mata koda kuwa gaban Abba ne ba Mubarak ba.
***
A falon gidan suka iske su Futuha zaune, sallamar Humaira ta dakatar da Ummita daga shiga kicin, ta dawo cikin falon da sauri don ta ganewa idonta ko ita ɗin ce. Futuha da Yasmeen kuwa ido suka bi Raihama da shi ganin yadda fuskarta ta yi ja ga shatin yatsu kwance saman fuskarta.
"Ke, Raihat, me nake gani haka? Uban waye ya mareki?!" Tasleem ta faɗi da buɗaɗɗiyar murya tana kallon Humaira. Humaira da ita dinma kiris take jira ta dube ta dakyau.
"Ni ce nan, ko za ki rama mata ne?"
Aikuwa jin haka gaba daya Tasleem da Futuha suka yo kanta, ta kuwa shiga tarewa, duk wacce ta bugeta sai ta sa hannu ta rama da iyakar ƙarfinta, duk da cewar su biyu ne a kanta, ta yi iyakar kokarinta amma itama ta ji jiki. Ummita ta hau kwala ihun kiran Mami, ga Yassar a gefe da ya ƙi ya tsawatar don dama ya jima da haushin Humaira a ƙoƙon ransa. Raihana na ihun su kyaleta akan ba ita ce ta mare ta ba amma inaa dama sun jima su na dakon rana mai kamar ta yau din hakan ya sa da gayya suka yi biris da ita. Yayinda a ɓangarenta shakkar tonuwar asirinta take musamman da ya kasance Yaya Mubarak na gari, ta sani koda ace Abba bai taɓa lafiyarta ba, shi kam ban da lafiya ma, hatta da wayar da take tunƙaho da ita sai ya raba ta da shi.
Kusan a tare Abba da Mami suka shigo falon. Wata tsawa Abba ya daka da ta sa gaba daya suka saki juna, Humaira gefen kumatunta na fidda jini sakamakon yakushi da ta sha da dogayen faratan Futuha. Su kuwa daga mai riƙe baya, sai mai riƙe gefen fuska da naushin Humaira ya kumbura har ya tasa. Mami zuciyarta ta yi wani iri, ta kasa magana ta yi shiru tana kokarin hadiye abin da ke cinta. Abba ya karaso falon ya dube su gaba daya. Humaira tuni ta durkusa, ganin haka su ma suka durƙusa.
"Mene ne hakan? Wane sabon shashanci ne haka? Ke Humaira wadannan ba su girmeki ba? Ku kuma manyan wofi ba kanwarku ce ba? Duk me ya kawo rigimar ne?"
Humaira ba ta ce uffan ba, Yassar ya yi saurin sa baki.
"Abba ba fa wani abu ba ne, Humaira ce ta mari Raihana har fuskarta ya yi shatin yatsu, shi ne don Tasleem ta yi magana kawai sai ta taso mata da faɗa wai ta mara ko akwai shegen da zai rama mata. Kalmar shege ya fusata su suka yi kanta da duka." Murmushi mai ciwo Humaira ta yi lokaci guda hawayen da take dannewa suka zubo samam fuskarta, zubar hawayen a inda Futuha ta mata rauni ya sa ta jin zafi amma ba ta ko damu da sharewa ba don wata azabar ta fi wata, ita daya ta san me take ji a zuciyarta. Ummita ma hawayen take na ganin yadda gaba daya Yassar ya juya magana. Ita kuwa Mami, karasowa ta yi ta ɗaga fuskar Raihana tana kallo. Tabbas mari ne, fuskar ta yi ja, ga yatsu kwance ta ko'ina a gefen fuskar.
"Mari?! Mamana dagaske ne kin mari ƴar uwarki? Me ta yi maki da zafi har haka da kika ɗau hukunci da kanki?"
Raihana nan fa ta shiga zare-zaren ido, Humaira ta kalleta na ɗan dakiku, har abada ba za ta tona mata asiri gaban iyayensu ba. Mami ta kai matsayin da ko laifin ɗiyarta ta gani za ta iya rufa mata asiri don haka dakyar ta haɗo abin fadi.
"Ka yi hakuri Abba. In sha Allah ba zan kara ba."
Nan kuma Abba ya kara fusata.
"Oh, dagasken kenan kin mare ta ko?! Wannan ai hauka ne! Kamar babu manya a gidan? Ke waye ya mare ki?"
Nan ya shiga bude mata wuta, sai da ya gama sannan ya maida hankali ga su Futuha wadanda duniyarsu ta yi dadi, ko babu komai wacce suke yiwa kallon ta fi su a wurin Abban yau ya rufe ido ya wanketa tas kamar zai kai duka. Hakan yasa ba su ji zafin nasu faɗan sosai ba. Sai da Mami ta sa baki sannan ya bar wurin. Humaira na ta kallon fuskar Mamin don ta hasaso yanayinta amma ba ta fahimci komai ba sai dai jikinta ya yi sanyi ganin ko kallonta Mamin ba ta yi ba. Hakan na nufin ba ta ji dadin hukuncin da ta yiwa Raihanan ba?
***
"Ban da abinki Humaira, duk son da Mami za ta nuna mana ai ba zai kai son ƴaƴan da ta haifa da kanta ba. Ni ba abin sa ya fi ban haushi irin yadda ba a damu da tambayar inda ku ka je ba. A jikina nake ji ba hakanan kawai za ki mari Raihana ba, akwai abin da kike ɓoyewa. Amma wace rana zai maki? Zai siya maki daraja ne a gun Raihana da yan uwanta kike zato? Babu ɗaya fa, halinsu ne ba na jin za su taɓa sauyawa."
Ummita ke zubo mata zance sa'ilin da suke kicin su na gudanar da girkin dare, awanni kusan biyu bayan afkuwar komai, Humaira wacce tuni ta yi wanka ta sauya shiga cikin riga da siket ƴan kanti ta yi murmushi daidai sadda ta motsa tukunyar miya ta rufe gami da rage wuta. Juyowa ta yi tana kallon Ummita da ta mayar da hankali tana juye farar shinkafar da ta dafa a cikin ƙaton warmer.
"Ban damu da abin da kowannensu zai ce ba, ban kuma damu ko Raihana ta sauya ba ko aa, abin da na sani shi ne, ko a gaban waye, kuma a ko'ina ne, su din ko naƙi ko na so, ƴan uwana ne na jini, ba zan taɓa ganin abin da zai cutar da su na yi shiru na zuba ido ba, sai inda karfina ya kare. Kar mu ja zancen Ummita, ni yanzu damuwata Mami, ta ina zan soma wanke kaina a wajenta? Na mari diyarta har shatin yatsuna sun bayyana ƙarara a saman fuskarta, anya kuwa za ta karɓi dukkan hanzarina? Ni dai na san soyayyar uwa akan nata, dagaske ne Mami na yi mana so na hakika, amma wace uwa ce za ta kara kallonka da ƙima alhalin ka sa hannu ka daki nata?"
"Sai ni nan, Maryam."
Gaba daya suka kalli bakin ƙofar shigowa kicin din, Mami ce wacce ta tsinkayi zantukan Humaira na karshe. Humaira ta zuba mata idanu tana so ta ga ko za ta fahimci yanayinta, ba ta gane komai ba sai murmushin da ta gani kwance saman fuskarta. Kicin din ta karasa shigowa sosai ta ce.
"Sai ni nan Maryam, haba Humaira, kina zaton ba ni da hankali ne? Na sani duk yadda aka yi akwai wani abu da Raihana ta yi kika yi mata wannan hukuncin. Kar ki manta tazarr fitarku ba nisa, da nayi nazari sai na ga kodai wani wurin za ta je da bai kyautu ba kika bi bayanta? Kar ki sa komai a ranki, koda ba ki faɗi komai ba ni na fahimceki kinji ko?"
Humaira ta sauke nannauyan ajiyar zuciya na samun nutsuwa. Wai mami wace iri ce acikin matan uba? Komai nata daban ne, kirkinta da kawaicinta akwai mugun yawa. Sai kunya ta lulluɓe ta, ta sunkuyar da kai.
"Kiyi hakuri Mami. Ban yi..."
"Bana buƙatar ji ko sanin komai kinji ko? Komai ya wuce. Ku hanzarta shirya kayan abinci, Abbanku na jin yunwa."
Suka amsa da toh a gaggauce suka ci gaba da aiki, Mami ta fice daga kicin din fuskarta ba yabo ba fallasa.
***
Kwance take saman gadonta tana buga game a waya, hankalinta kacokam ya tafi a game din sai ga kira ya shigo. Ta yi tsam tana duban wayar, lamba ce da ba ta da masaniya a kanta. Ganin haka sai ta katse kiran ta ci gaba da game dinta, aka kara kira, ta katse, a na uku ta ɗaga a fusace amma sai ta danne ta yi sallama. Jin muryar namiji ya amsa sallamar ya sa ta jin wani abu tun daga tsakiyar kanta har zuwa yatsun ƙafa, ba ta san ma'anr hakan ba.
"Ina mai ba da hakurin yi maki katsalandan a rayuwa. Hope ba za ki damu ba idan na ce jiya na karɓi numbernki wurin Ibb Gusau."
Shiru ya biyo baya, ita ba ta fahimci komai ba don har ga Allah ta mance da su. Jin shiru ya sa Fadeel ƙara magana a tausashe.
"Ok, ba ki gane ba ko? Jiya ni da abokina da ya ba ki numbernsa akan wannan saurayin ƙanwartaki, Musaddam nake tunanin sunansa ko?"
Nan da nan ta tuna komai, wannan me kama da aljanun ne mai shegen kallo. Ta ja guntun tsaki kaɗan.
"Uhm, na gane. Ina fatan lafiya?"
Ya yi shiru yana jin amsarta a wata kala na daban, madadin ta ba shi haushi sai kuma ya ji bai ji haushin nata ba.
"Lafiyar ce ta sa na kiraki. Suna na Fadeel, magana nake son mu yi amma ta fi ƙarfin waya, idan kin ba ni dama ko zan iya sanin kwatancen gidanku?"
Ranta ya soma ɓaci, ta ji wani abu na taso mata.
"Idan maganar ba za ka iya yinta a waya ba don Allah kada ka ƙara gangancin kirana. Hakan zai fi maka alheri, sannan ina bukatar ka goge lamba ta a wayarka, tunda ba wani muhimmin abu ne ya sa ka kira ba."
Tana kai wa nan ta katse kiran, ta yi wurgi da wayar saman gado, game din ma ya fice a kanta. Ita kaɗai ce a ɗakin, sai ga Raihana ta shigo. Ko kallonta ba ta yi ba ta mike ta faɗa banɗaki, koda ta fito ganin Raihanan zaune saman gadonnata yasa ta mamaki. Fuska a ɗaure ta ƙarasa.
"Malama lafiya?"
Jiki a sanyaye Raihana ta soma magana.
"Kiyi hakuri Humaira, na ja an maki faɗa an kuma zalunceki. Don Allah ki yi hakuri. Ina neman gafararki bisa dukkan abin da na taɓa yi maki a gidannan. Ban kara gasƙata kaunarki gareni ba sai a jiya da kika shanye faɗan Abba ba ki faɗi ainahin abin da ya faru ba. Wallahi na ji kunyarki sosai, kiyi hakuri ki yafemin."
Taɓe baki Humaira ta yi tana fadin.
"Ya wuce. Kar ki damu."
"Dagaske kike?"
Ta tambaya da sauri kamar za ta yi kuka don muryarta ta karye, Humaira ta zauna a gefe.
"Ni ban taɓa binku da kallon maƙiyana ba, kallon da nake maku na ƴan uwana ya bambanta da irin wanda ku ke yimin. Sai dai dukkan wannan ba zai sa na ga abin da zai cutar da ku na kasa magana ba. Idan na yi hakan na ci amanar kaunar da Mami ke nunamin. Raihana mutunci da darajar mace ya fi gaban ta tsaya ta siyarwa wani ƙaton banza a waje. Musaddam da kike gani wallahi ba zai taɓa aurenki ba matuƙar kika yarda kika ba shi kanki a waje, ke koda ba ki bayar ba, yaron ba aure ne a ransa ba face iskanci. Idan kuma dagasken auren yake sonki da shi, meyasa bai taɓa zuwa nan ƙofar gidanku da sunan zance ba, kema kin san karya ne kawai. Tun wuri ki yiwa kanki faɗa ki rabu da shi zai fiye maki alheri."
Raihana da tuni ta soma hawaye ta kamo hannun Humaira.
"Toh naji Humaira, amma wallahi ina sonsa, wani irin so ne da ban san yanda zan fara yakice shi ba a rai. So ne da ya rufemin ido naji ko me Musaddam zai nema a wurina zan iya yi mishi."
Sai kuma tausayinta ya lulluɓe ta, tana kuma godewa Allah da bai ɗora mata son kowane ɗa namiji ba balle har ya wahalar da ita.
"Wannan son za ki yaƙa, domin halaka ne a wajenki. Musaddam ba sonki yake yi ba muna nan da ke watarana za ki ban labari. Ki kai kukanki wurin Allah sannan ki shagaltar da kanki wajen duk abin da kika san zai dauke maki hankali daga tunaninsa. Nima kuma zan tayaki addu'a har sai Allah ya amsa, ya rabaki da wannan makahon son. Ke ina kika hango dacewarki da shi wai? Wallahi ta ko'ina ke din ba ajinsa ba ce, ban da ma dai shi son da kike ikrari bai san inda zai je ba, ai sawun giwa ya shafe na raƙumi."
Murmushi Raihana ta yi cikin jin salama, sai kuma hira ta buɗe tsakaninsu, tana ba ta labarin ainahin yanda aka yi ta hadu da Musaddam din. Humaira ta gefen ido na kallon wayarta da ke silent tana ta haske alamar shigowar waya amma ta yi biris da ita. Su na a haka Futuha ta dawo daga makaranta ta iske su, mamaki ya dabaibayeta, ta cire facemask din da ta sa don ɓoye kumburin gefen bakinta da Humaira ta daka, ba ta cewa Raihanan komai ba sai zama da ta yi gefen nata gadon tana ci gaba da kallon ikon Allah. Ita kuwa Humaira ko ta nuna ta san da wanzuwar wata a dakin bayan su. Can kuma Raihana na juyawa tana yiwa Futuha magana ta ga hasken wayar Humaira ta jawo.
"Lah, kinga fa kiranki ake ta yi. Lamba ce. Kodai Ibb ne?"
Jin sunan da ya fito bakin Raihana ya sa Futuha zaro ido waje a razane. Ita kuwa Humaira fuska ta yamutse.
"Waya sani, tun dazu ya kira wai wani kwatancen gidanmu."
"Wane Ibb din kika nufi Raihana?"
Suka dube ta, sam Raihana ta mance, yanzu me za ta ce idan Futuha ta dage akan son sanin komai? Kada dai allura ta tono garma. Ita kuwa Humaira sai a sannan ta tuno ashe fa a hirarsu tana jin Futuha na yawan maganar son da take yiwa Ibb Gusau da haduwarsa. Kodai shi ne Ibb din da take magana?
"Ibb Gusau wanda kika sani."
Humaira ta furta da murmushi saman fuskarta, ta karbi wayarta a hannun Raihana ta katse kiran amma sai ta sa a kunnenta kamar gaske ta hau fadin.
"Assalamu Alaikum, ina neman afuwa ka kira bana kusa. Fatan ka karasa gida lafiya?" Tana kaiwa nan ta sa kai ta fice daga dakin, sai da ta isa falo sannan ta kwashe da dariyar ganin yanda Futuha ta cika tayi tam har gefen bakinta da ya kumbura sumtum yana kyalli. Ta dai san ta harba mata bomb a zuciya.
10
Dariya take yi har ta shiga kicin ɗin, Ummita dake amsa waya tana lumshe idanu ta yi azamar katsewa tana dubanta. Humaira kuwa ganin haka ta karasa fuska dauke da walwala tana bin ta da kallon tsokana.
"Waya kike amsawa ko? Shi ne ina shigowa kika yi saurin katsewa. Nidai ya kamata zuwa yanzu na san waye wannan majnun ɗin naki."
Ummita dai ba ta tanka mata ba sai maida hankalin da ta yi wajen ɓarar tafarnuwa tana murmushi, sai kuma ta share zancen da hanyar fadin.
"Wai dariyar me kike yi ne?"
Sai a sannan ta tuna abin da ta yiwa Futuha, dariyar ta kuma taso mata. Ta fayyacewa Ummita labarin, baki buɗe take kallonta.
"Ke kuma ina kika samu lambar shi?"
Ita shaf ta mance Ummita ba ta da labarin komai, ta yi ajiyar zuciya. Labarin da ba ta so bayarwa ba amma ya zama dole ta sanarwa Ummita don ba ta da yar uwa kuma aminiya sama da ita. Ta labarta mata duk abin da ya faru da sanadiyyar marin Raihana ta kara da jan tsaki da fadin.
"Shi ne wannan mayen ya takuramin da kira fa, toh ita Raihana ta yi zaton ma Ibb din ne. Ni kuma don na shaƙawa ƴar banza shi ne na sa wayar a kunne ina wayar gangan na soyayya."
Ummita da iyakar burgewa yar uwar ta burgeta sai ta shiga murmushi kawai da mamakin kaifin hankali da tunaninta, ta sani ko ita ba lallai ta iya shiru a irin wannan gaɓar ba. Amma ta gwammace kowa ya yi mata kallon rashin kyautatawa akan dai ta bayyana gaskiyar abin da Raihana ta aikata. Sai kuma karar wayar Ummitan ya katse tunaninta. Da sauri har su na rige-rigen ɗauka ita da Humairar, sai dai a karshe wayar ta faɗa hannun Humaira tana dariya, ga nata wayar ta na ta haske shaidar faɗowar saƙo amma ko a jikinta.
"Ki yiwa girman Allah kada ki ɗaga." Gwalo ta yi mata suka hau zagaye a kicin din.
"Sai kin rantse cewar za ki fadamin ko wane ne mai kiran."
Da sauri ta amsa.
"Eh wallahi zan fadamaki, yanzu dai ban wayar."
Ba musu ta ba ta tana dariya, ta ja kujera ƴar tsugunno ta zauna tana duba nata wayar da saƙon ya faɗo tun ɗazun.
_*Kar ki yi tunanin akwai abin da zai sa Fadeel ja baya ko tsoro. Ki tambayi wadanda suka san waye shi, yana da naci akan abun da zuciya da gangar jikinsa suka yi na'am da shi. Ba shi da saurin karaya, ba kuma ya jin zai soma daga kan ɗiya mace. Ina kuma farin ciki shaida maki ke ce halittar farko a mata da na ji zuciyata ta yi na'am da kasancewarta rabin jiki kuma abokiyar rayuwata. Nasara tana tare da wanda ya miƙa lamarinsa ga Allah. Have a nice day.*_
Ta karanta har da karkata kai kusan sau uku, sai ta ji ma abin kamar irin a fina-finan da ake haskowa a tashar Hausa da su Tasleem ke kunnawa. Ranta na wani irin huci da zafi, a gefe guda kuma duk da wannan radadin wai sai ta ji tana