Showing 30001 words to 33000 words out of 93383 words
so ta san ma'anar kalmomin karshen da ya rubuta mai kama da farasanci da turanci.
"Lafiya ki ka ba waya hankalinki?"
Muryar Ummita ya katse mata tunani, ta isa wajenta ta miƙa mata waya. Har a sannan hausarta ba ta dawo daidai irin ta Kanawa ba.
"Ɗan fassaramin ƙarashen saƙon nan, me yake nufi?"
Ummita ta karanta tun daga farko, tun kuma somawarta take zabga murmushi don ba ƙaramin burgeta ya yi ba.
"Fatan alheri ya yi maki a wannan rana. Kai Humaira wannan mutumin akwai iya tsara kalami, ina ji a jikina kin samu mijin aure."
Guntun tsaki Humaira ta ja gami da warce wayarta tana ƴar harararta.
"Ai ke ce mijin, ni raba ni da wannan shirmen soyayyar kin ji ko. Ba ni da lokacinsu."
"Anya Humaira kalau kike kuwa? Ko dai sai an haɗa da addu'a?"
Yamutse fuska ta yi kawai ta kwashi tafarnuwar ta dauraye ta watsa a turmi ta hau daka. Ganin haka itama Ummita ta share batun.
A gefen Futuha kuwa, gaba daya ta yo kan Raihana.
"Ke! Wane Ibb din ki ke nufi ne?"
Raihana ta yi jim, ba ta son ta ce Ibb Malaminta allura ta tono garma don haka sai ta kife ta da fadin.
"Ba fa wanda kike zato ba ne, wannan wani Ibb ne Ibrahim sunansa suka hadu da ita a hanyar islamiyya."
Nannauyan ajiyar zuciya Futuha ta yi kafin ta juya ta koma gadonta tana jan tsaki.
"Toh barkanta, amma da ace Ibb da nake mutuwar so da kauna ne wallahi sai na koyamata hankali. Ke kuma wani sabon salon gulma da munafunci tun da ta wanke maki fuska da mari kike wani shakkarta har da taya ta hira. Ke kika sani."
Raihana dai ba ta tanka ba ta mime ta bar mata ɗakin. Amma ta sa a ranta babu wani abu da zai sa ta kara biye musu wurin nunawa baiwar Allah da ba ta ji ba kuma ba ta gani ba ƙiyayya kawai saboda don zuciya irin nasu.
***
Gidansu cike taf da jama'a sakamakon daurin auren Fu'ad da aka yi a ranar, haka ya dinga kutsawa ransa duk a ɓace har ya shige bangarensu, kai tsaye dakinsa ya nufa, tun daga falo ya cire hularsa ya yi jifa da ita, hakanan babbar rigarsa blue itama ya ajiye saman kujera kafin ya zauna ya shiga kokarin cire covershoe din da ke a ƙafarsa da kuma safa. A duniya Fadeel ya tsani hayaniyar jama'a, wannan ta sa kansa har wani sarawa yake yi. Ya ja guntun tsaki gami da kwantar da kai jikin kujerar ya lumshe idanu. Zafi biyu ya haɗe mishi, ga na rashin samun haɗin kan yarinyar da yake jin ta a ƙoƙon rai, ga kuma wata irin yunwa da yake ji domin ko karin kumallo bai yi ba suka fice masallaci wurin daurin aure. Kowa kuma a dangin sai ya yo kansa da tsokana a wajen, su na fadin saura kai babban yaya. Wadanda ba su da labarin dawowarsa kuwa, sai a ranar suka gan shi. A hankali ya bude lumsassun idanunsa ya murza yatsunsa suka yi ƙara, har wani zogi suke yi mishi saboda gaisuwar da ya dinga yi da jama'a. Lokaci guda kuma ya miƙe ya nufi bandaki, hannun ya wanke tas da hand sanitizer sannan ya fito rike da karamin tawul yana gogewa. Ya yi daidai da shigowar Ibb tare da wani dan uwansu Imran.
Sallamarsu ya amsa ya koma mazauninsa har da kwanciya wannan karon. Kafin Ibb ya yi magana ya riga shi.
"Wai so ku ke na mutu? Yunwa fa nake ji."
Harararsa ya yi.
"Kai dai an yi ɗan iska, muna can Alhaji ya sa mu nemoka ku gaisa da abokansa ashe kai nan ka yo? To sai ka tashi ka shirya muje idan ya so kafin mu dawo na yiwa Anti Amarya magana a kawo mana abinci."
Fadeel ya lumshe idanu.
"Kasan Allah ba zan iya fita ko'ina ba, ni fa ji nake idan ma na kara sa ƙafa na fita cikin wannan ranar hanjin cikina za su fito waje."
Imran ya kwashe da dariya, shi kuwa Ibb kamar ya shaƙo amininnasa haka yake ji. Yana niyyar magana kuma sai ga kiran Alhaji karo na uku. Ya ɗaga ya mishi bayani, dama bai tsammaci faɗan Alhajin ba, cewa ya yi babu komai maza ya yi waya a kawomusu abinci. Da wannan suka yi sallama shi kuma a nan take ya yi kiran Anti Amarya ya sanar da ita.
A bangaren Anti Amarya wacce ta ci ado cikin arnen leshi ruwan toka da ya sha adon stones, ga ƙunshi ta yi sai baza ƙamshi take, jin wayar Ibb ya sa da rawar jiki ta amsa ta ba ɗaya daga cikin hadiman gidan Larai umarnin haɗawa Fadeel da abokansa abinci za ta turo a kai musu. Ta shiga falonta inda yan uwanta hudu ke zaune su na shan hira. Uku a cikinsu matan aure ne, ɗaya yayarta sai sauran gaba daya ƙannenta. Ƙanwarta Murja dake kwance tana danna waya ta kai wa duka a ƙafa. Ba shiri ta mike zaune.
"Ke tashi maza ga dama ta samu, jeki wurin Larai na sa ta haɗa abincin su Fadeel ki kai musu, kika sani ko Allah zai sa a dace ko cikin abokansa wani ma ya ce yana so?"
Jin haka babbar yayarta Saddika ta amshe.
"Ke wallahi hakane kam, tashi Murja, Allah ya ɗora ki akan su."
Murja ta haɗe girar sama da ƙasa.
"Nikam wallahi Fadeel nake so. Shi dai za ku taya ni addu'a ya ce yana sona."
"Kin ji wawiya, ke kanki kinsan kaf abokansa ma babu na yar wa musamman Ibb. Ai dai kinga irin jama'arsa da suka kawo masa ziyara muna nan dake a gidannan tun zuwansa ko?"
Murja wacce ta zo hutun makaranta gidan ƴar uwarta ta, ta mike tana gyara zaman ɗaurin dankwalinta.
"Nidai kam shi nake so, ai duk kyawunsu ba su kai shi ba. Malam ga aji na musamman. Kiga fa ko sadda su Sholy suka zo gidannan ko kallo basu ishe shi balle su ga haƙoransa. Nima din ba.."
"Ki yi zaman hira har sai ya gaji ya turo wani ya karɓar musu abincin. Shashasha marar wayo kawai. Ana kai ki kina ƙin zuwa. Ke kika sani. Zauna har ki yi biyu babu."
Jin haka da sauri ta fice daga falon tana dariyar maganar Zuwaira, mai bi wa Anti Amarya.
A kwando ta ga Larai ta haɗa komai har da cokula da farantai, ta kinkima ta yi gaba inda ta tsallake yan uwan Alhaji da suka zo daga ƙauye ko kallo ba su ishe ta ba ballantana ta yi tunanin gaishe su. Su kam suna hau gulmarta da harshen fulatanci. A ƙasan ranta ta ja Allah ya isa.
Tana zuwa ƙofar ta kwankwasa, Ibb ya ba da umarnin a shigo. Lokacin dukkansu har Imran sun cire babbar riga ana shan iskar fanka ana hira, sun zama su biyar a ɗakin sakamakon shigowar abokan Ibb biyu, Saifullahi da Idris. Da sallama a bakinta ta shiga, kasancewar Fadeel ne a saitin ƙofa ya bi ta da kallo ɗaya ya kauda kai ya maida saman kwandon dake hannunta. Dama abin da yake jira kenan, ita kuwa kusan zaucewa ta kusa yi sakamakon kwayar idanun Fadeel da suka haɗu da nata, gaba daya ta ji ta ƙara narkewa a tekun sonsa. A ranta tana ayyana ba gudu ba ja baya shi din dai ranta ke so. Babu wani abokinsa da ta ga ya burge ta, gwara ma Ibb don a baya tana mishi kallon hadadden saurayi duk sadda suka hadu ya zo gaida Alhaji, ita kuma ta zo gidan, yanzu kuwa ta fahimci Fadeel ya kere shi.
"Ba sai kin zuba ba, bar shi za mu yi serving da juna." Fadin Ibb fuska a sake ganin ta sauke kwandon ta hau fito da kayayyakin tana shirin buɗe warmer.
Ta kalle shi kadan tana dan murmushi.
"Lah ba komai, bari na zubamaku, wannan ai aikinmu ne mata."
Bai kara magana ba sai mayar da hankali ya yi ga Imran dake nuna mishi wani hoto a waya. Shi kansa Ibb ba mai yawan zance ba ne sai ta kama, don haka bai hanata ba. Shi kuwa gogan kallonta bai kara ba, sai Idris da ya zuba mata ido kamar ya haɗiye ta. Shi dai kam lokaci guda ya ji ta kwanta masa a ƙoƙon rai. Don haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya dubi Fadeel.
"Wannan ƙanwarmu ce?"
Tsaf Fadeel ya karance shi, don haka ya gyada kai kawai fuska ɗaure. Ita kuwa da rawar jiki ta miƙa kwanon abinci ga Fadeel. Madadin ya karɓa sai ya dube ta. Ta ji kallon tun daga tsakar kanta har tafukan sawayenta.
"No, ki fara ba su tukunna."
"Kai Malam, idan za ka karɓa ka soma ci ka karɓa. Tun ɗazu ka ke mana raki da kukan yunwa kamar wanda ya shekara bai ci ba. Wannan ta ya ya kake azumtar watan Ramadan?"
Jin haka ya ja filo ya jefawa Imran a fuska, gaba daya aka sa dariya shi kuwa ya shafi sumar kansa yana mai lumshe idanu lokaci daya ya bude su akan Murja, wannan karon sai da ta ji miyan bakinta ya sarƙe ta sai ga shi ta soma tari ba ƙakƙautawa. Idris da sauri ya miƙa mata ruwan roba dake gefensa saman kafet. Ta karba ta sha tana satar kallon Fadeel da bai ƙara dubanta ba sai waya da ya ke faman dannawa. A haka da rawar jiki ta zuba kowa ta miƙa mishi. Friedrice ne da hadin coslow sai chicken pepper. Ta bude firij ta ciro musu lemuka ta ajiye. Daga haka ta sa kai ta fita. Tana fita Idris ya gyara zama ya shiga rantse musu akan ya ga matar aure shi dai yana sonta idan za'a ba shi. Fadeel ba ya fahimtar komai ban da ta cikinsa da ya ke yi, ganin duk da fankar da ke busawa yana gumi kawai sai ya mike ya cire rigarsa daga shi sai dogon wandon shadda da vest ya koma ya zauna. Sai da ya tashi da abincin tas kafin ya ɗauki ruwa ya kora ya dubesu. Kowannensu bai kai ga kammala ci ba, suka kwashe masa da dariya, shi kansa murmushi da tsaki ya yi lokaci guda kuma yana sa hankicif ya goge fuska.
"Ku na da matsala wallahi, ba za ku gane illar da yunwa ke min ba. Yanzu sai ta tayarmin da ulcer."
"Ai mun gane komai ranka ya daɗe. Ko za ka ƙara?"
Saifullah ya faɗi da zolaya. Fadeel ya ɗan harareshi.
"Saboda na zama rumbu ko?"
Haka suka yi ta zolayarsa shi kuwa tuni ya maida kai kan wayarsa yana kiran abu na biyu da ya tsaya mishi a ƙoƙon rai amma har ta kammala ringing ba a ɗaga ba. Haka ya kira har sau uku, sai a na huɗun, aka ɗaga. Kafin ya kai ga cewa komai ta soma faɗa.
"Wai Malam kai din maye ne?! Na ce ka bar kirana ka ƙi! Dole ne zuwanka gidan namu? Haba, wannan jaraba da naci har ina wai? Mtsw."
Daga haka kit, aka kashe kiran, nan da nan kansa ya yi wata irin sarawa, dama ga ciwon kan da tun ɗazun yake ji. Gumi ya karyo masa saboda tsananin ɓacin rai, idanunsa tuni suka kaɗa. Sauyawar yanayinsa ya sa Ibb ƙuramasa idanu. Sai dai bai ce komai ba ganin ba su kaɗai ne a falon ba. Sai bayan da gaba daya suka fice don gaisawa da Alhaji sannan Ibb ya dube shi, lokacin ya mayar da kai jikin kujera ya lumshe idanu don har su Imran suka fita sun yi zaton bacci ne ya kwashe shi su na mishi tsiya. Shi kuwa duk yana jin su ba shi dai da karfin biyewa shirmensu.
"Fadeel, wai meke faruwa haka?"
Jin muryar Ibb yasa shi bude idanun, ya mike zaune sosai.
"Yarinyarnan nema take ta kashe ni, daga ranar da na gan ta har zuwa yau ban huta ba."
Cikin rashin fahimta Ibb ya dan wurga hannu.
"Wace yarinya ce haka? A rayuwarka har ta hanaka sakat? Wace ce?" Tsakaninsa da Allah ya yi furucin don shi gaba ɗaya ma ya manta da wata Humaira.
"Wacce muka haɗu da su tare da wannan ɗan iskan yaron."
Shiru Ibb ya yi cikin nazari sannan ya dube shi a hanzarce.
"Are you serious? Kana nufin ka kira ta?"
Cikin ido Fadeel ya dube shi.
"Yes, mun yi waya, amma duka ba masu dadi ba ne."
Ya kora mishi bayanin duk abin da ya faru, Ibb ransa ya ɓaci.
"Unbelievable! Yanzu akan mace ne ka shiga wannan yanayin? Fadeel kai ne dagaske dai wanda na sani? Mutumin da gaisuwar kirki abu ne mai wuya a ganka kana yi da wacce ba muharramarka ba, kai ne yau da bakinka ka ke faɗin cin kashin da wata shashasha can take maka? Kuma har ka ke tolerating in the name of love? Is this love or madness?"
A fusace Fadeel ya soma magana, tun da Ibb ya jefi Humaira da kalmar shashasha ya ji ransa ya yi masifar zafi.
"Oho! Idan ma haukan ne naji ni na jefa kaina ai ba da sa hannunka ba ko? Ban damu da duk wani tunani da za ka yi ba. Ina sonta, ka zo gabana kana kiranta da shashasha ba zan iya jura ba Ibb! Ina haɗa ka da Allah, idan har ba goyamin baya za ka yi ba toh kada ka kara kuskuren zaginta a gabana. Kawai dai ina ji a jikina wataran za ta gane ni din masoyinta ne na gaskiya."
Yana kaiwa nan ya mike ya nufi hanyar ɗaki, Ibb kuwa baki a wangale yake binsa da kallo har ya ɓace masa. Meke damun Fadeel? Ya jefawa zuciyarsa tambaya, a take kuwa amsar ta zo masa, Soyayya ce. A fili ya ce.
"Idan kuwa har wannan ita ake kira da soyayya, ina nemawa kaina tsari da ita. Kai kuma Fadeel ina roƙon Allah ya yayemaka wannan haukan son."
Daga haka ya mike ya fita a dakin domin shi har ga Allah ba ya fatan wannan rashin hankalin da mace za ta zage shi ya kasa daukar mataki a kanta. Ko ƴar uban wace ce ba zai ƙara yi mata kallon wata abar so ba, ballantana har ta ci galabar yi mishi son ranta.
***
Humaira na kwance a yammacin ranar juma'a ta ji ihun ƴan matan gidan ya karaɗe falo, ta mike zaune tana mutsistsiƙa idanu. Hayaniyar ta mene ne? Kafin bacci ya gama wartsake mata sai ga Ummita ta shiga fuska ba yabo ba fallasa.
"Wai hayaniyar me ake yi?" Fadin Humaira. Tsaki Ummita ta ja haɗi da taɓe baki.
"Aunty Jannat ce ta zo, kanwar Mami."
Humaira ta zaro ido, ba ta taba zama da ita ba amma ta sha jin labarinta a bakin Ummita na irin uƙubar da ta sha a wajenta sadda tana rayuwa a gidan.
"Dagaske? Ki ce mun shiga uku."
Ganin ruɗewae Humairar har ya so ya fi nata ne yasa ta dariyar dole wanda ba ta shirya masa ba.
"Ke da ba ki taɓa zama wuri guda da ita ba? Ba lallai ki fuskanci matsalar da na fuskanta ba ai."
Ita dai Humaira ta ji ne kawai ba don ya zauna a kwakwalwarta ba.
*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
Suna nan zaune Humaira na cewa ita kam za ta so ganin ya wannan Jannat din take mai shegen son mulki sai ga Muhsin da Waleed sun faɗo ɗakin a guje. Kira ne daga Mami akan su fito a gaisa da Jannat. Ummita ta dafe kirji, yayinda Humaira mikewa ta dube ta.
"Wai ya haka, kinsan fa yarannan akwai daukar zance yanzun sai su fasalta musu yanayinki."
Ummita sai ta maze ta mike. Suka kama hanyar falon, tun kafin ma su kai ga ƙarasa shiga ta hange ta. Kamanninta sak da Mahaifiyarsu wato Anna. Kusan har ta so ta fi Mamin hasken fata, siririya ce ba ta da tsawo duk kuwa da cewar tana daga zaune ne. Yaranta ƴan biyu tamkar an tsaga kara an karya, ba su wuce sa'o'in Muhsin ba. Wato shekaru goma a duniya. Riga da wando ne a jikinta sai abaya dake ajiye a hannun kujera wanda ga dukkan alamu cire ta ta yi. Gashinta ya sha kananun kalba an tufke a tsakiyar kan ya yi kamar ta sa ribos din acuci. Gaba daya iyalan Mami na falon ciki kuwa har da Anna wacce ba kasafai ta fiye fitowa ba. Humaira ita kanta sai da ta sha jinin jikinta ganin Anna a falon, sai da itama ta ji kamar ta ja hannun Ummitan su juya. Aikuwa su na ganinsu Anna ta tamke fuska gami da juya harshe zuwa buzanci. Ko me ta fadi oho, gaba daya suka kalli su Humaira, matasan suka gimtse dariyarsu sakamakon Mubarak dake zaune, sun tabbata muddin suka ce fiddo shi waje to fa kashinsu ya bushe wurinsa. Hatta da Raihana ba ta ji dadin zancen Anna ba domin har ga Allah yanzu ba ta da matsala da su, ta riƙe su ƴan uwan na gaske kuwa.
Ita kuwa Jannat kallon Humaira ta ke yi kamar wacce ta ga kashi. A yatsine ta amsa gaisuwarta, Ummita kuwa gaisuwar ma ba ta samu ba sai harara da ta watsa mata ta ja tsaki.
"Wai Anti Jannat har yanzu wato kina nan yadda na sanki."
Mubarak ya fadi ransa duk ba dadi, tun daga kalmar agolar da Anna ta kira Humaira da shi har zuwa yanda Jannat ta karɓi gaisuwarsu. Rai a ɓace ta amsa.
"Toh ko za ka sa hannu ka buge ni ne? Dama ai kai na faɗa can dai dangin uba ka biyo ba mu ba."
Zai yi magana da sauri Mami ta ɗaga mishi hannu, aikuwa abin da take gudu shi ya afku domin Anna faɗa ta hau yi kamar ta ari baki wai laifin na uwarsa ce da ta fifita bare a kan nata. Ganin dai abu ya ƙi ƙarewa Humaira ta miƙe tana mai jan hannun Ummita, itama ba shiri ta miƙe sun kama hanya tana ji Jannat ta kwalawa Ummita kira tana ba ta umarnin ta ja Hassan da Hussein ɗakin su Muhsin ta musu wanka. Ita dai Humaira a fusace ma ta karasa ɗakin don ta matsu ta daina jin muryar tsohuwarnan da ma Jannat din wacce ta ji tsanarta lokaci guda ya rufe ta. Me ake da wanda bai san daraja ta