Showing 54001 words to 57000 words out of 93383 words
ta miƙe itama. Saƙo ta ba su a leda na ankon Dinner su je su kai can asibitin Malam wajen ƙawayenta kuma abokan karatunta da suka samu dakyar don har ta ƙare. Ta miƙawa Ummita dubu su yi kuɗin mota sai kuma lambar wayar ɗaya daga ciki, Sadiya, sun gane ta, takan rako Tasleem din gida wasu lokutan don ta dauki wani abun ko kuma ta zo takanas ziyara.
Bayan sun fito waje Humaira ta dubi sararin samaniya yanda garin ya haɗu da hadari ana cida, lokacin uku da mintoci, ta ja guntun tsakin takaici.
"Kinsan Allah, sa'ar da ta ci kawai na ganin wannan shi ne aike kusan na karshe da za ta yi mana kafin ta bar gidannan shiyasa kawai zan je, amma ban da haka wannan ke ɗin da ta ce wallahi da babu inda zan je matukar ba Mami ce ta sa baki ba."
Ummita dake kokarin cusa ƙaramar lema a jaka ta ɗago tana murmushi.
"Humaira ko rigima, rabu da ita lokaci ne ai wataran sai labari fa. Yanzu kalli, ina Anti Jannat? Ba ta yi aure ba sai dai ta zo kawai ziyara ta tafi? Toh su din ma hakan ce za ta kasance, mu ma watarana sai ki ga mun yi namu auren mun tafi mun bar gidan. Sai a dade ma kafin a ganmu."
Tsaki Humaira ta ƙara ja.
"Ke dai Ummita kina son aure na lura, magana kaɗan za a yi da ke sai kin yi zancensa."
Da mamaki Ummitan ta kalleta kafin ta amsa.
"Aure ai abin so ne saboda sunnar ma'aiki (s.a.w) ne. Ke din ma ba sunnar kika tsana ba, mazan ne. Ban kuma san laifi kwakkwara da suka yi gareki ba."
Taɓe baki Humaira ta yi daidai lokacin da suka fito babban titi.
"Mu bar wannan magana, nikam ba kya ganin lamarin Anti Jannat da ɗaure kai?"
Ummita ta yi shiru cikin nazari, tabbas da daure kai, tun bayan sadda ta zo hutun sallah lamarin nan ya afkuwa tsakaninta da ita, ba ta kara dawowa gidan ba sai yanzu. Wannan dawowar kuwa, daidai da kallon Humaira ba ta yi balle har ta jefe ta da kallon banza. Ta lura ko tana wuri Humaira ta shiga, mikewa take ta bar wurin. Haka dai tana ta kaucewa abinda zai haɗa su a inuwa guda.Har Humaira ta tarar musu abin hawa suka shiga ba ta amsa mata tambayarta ba sai da ta ƙara nanatawa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan yi murmushi.
"Na lura sosai, amma ni abin da tunanina ya ban ko dai ta sauya ne tana gudun wani abu ya ƙara haɗaku ki maimaita abin da kika yi. Kin san fa ba zai yiwu ace ta mance ba."
Dariya ta yi.
"Ikon Allah, toh ni ai na mance. Kawai dai sauyin ne ya ɗan bani mamaki. Babu kyara babu hantara, babu kirana da bare da ta saba yi ba komai. Sai na ke ganin kamar da walakin goro a miya."
"Ki yi mata kyakkyawan zato, Allah yasa sanadin abin da ya kasance ta yiwa kanta faɗa. Ni kaina idan kin lura ai ta rage ɗoramin aiki tunda wannan zuwan ta sa an nemo mata yarinya mai kula da yara. Kawai dai mun saba da yaranta ba yanda za a yi ta iya raba wannan kaunar."
Humaira ta kalle ta, zuciyar Ummita mai kyau ne, da Allah ya tashi, sai ya yi haɗa ta da mutumin kirki irinta wato Malam Sahabi. Mutum mai hakuri da kunya kamar wani mace. Amma abin mamaki duk kunyarsa idan suka ga saƙonnin soyayyar da yake turowa Ummita sai mamaki ya kusan kashe su ita da Raihana. Har rantsuwa suke kusan yi su ce ba shi ba ne waninsa ne.
Ummita ta harareta.
"Kallon fa?"
Murmushi Humaira ta yi mai kyau da ya fiddo wushiryarta.
"Kawai kina bani mamaki da kike kokarin kare wadannan mutanen da ba su taɓa kaunarmu ba koyaushe."
"Uzurin kenan Humaira. Aure fa zasu yi su bar mu yanzu. Mu ma kuma..."
"Toh naji ya ishe ni hakanan Malama matar Sahabi."
Ummita ta sa dariyar jin abinda ya fito bakinta, ita din ma taya ta ta yi. Har suka isa ƙofar asibitin su na hira abinsu ana iska kaɗan kaɗan mai daɗi.
Ibb ne tsaye tare da masoyiyarsa Dr Salma, yayinda Fadeel ke zaune cikin mota yana jira su yi sallama. Mahaifiyarta ce kwamce a asibitin inda anan take aiki, suka zo dubiya ta yo musu rakiya har gaban mota. Bayan sallama da Fadeel ya koma mota yayinda suke hirarsu da Ibb tamkar kada su rabu, shi kuwa Fadeel kansa ya kwantar jikin kujera yana ɗan kallonsu yana murmushi. Shakka babu sun dace dari bisa dari. Dogaye ne su duka biyun don zasu kusan yin kai ɗaya, Dakta Salma baƙa ce, kwayoyin idanunta da haƙora ne kawai idan ta bude masu haske a fuskarta. Tana da kyau, ba ta da jiki sosai amma ba za ka kirata da siririya ba. Tana da diri masha Allah, sanya take da doguwar riga sai coat na likitoci da ta sanya saman kayan, sai kuwa mayafi ƙarami da ta yi rolling kanta da shi. Hannunta cikin aljihun rigar, gaba daya hankalinsu ba ya kan Fadeel da ya lula duniyar tunani da jin inama ace shi da Humaira ke wannan hirar ta nishaɗi. Allah kaɗai yasan yanda zai ji a lokacin. Ya soma gajiya, hakurinsa ya soma kai wa karshe amma yana dannewa gudun ɓacin ranta. Ya horu da rashin ganinta ido da ido ba hoto ba, ya sha zuwa ya tsaya a nesa kaɗan da gidansu ko zai ga wulkawarta sai dai ko mai kama da ita Allah bai taɓa ba shi ikon gani ba. Tabbas Raihana na kokari gurin aikamasa hotunanta wasu lokutan ma ba ta san ana ɗaukarta ba. Hatta da karamin video sadda take aikin snacks sai da ta ɗauka ta aikamasa. Yakan ji inama yana da iko da ita, inama matarsa ce yana kusa ya riƙo ƙugunta ya sanya ta a jikinsa ya bayyana mata irin yanda soyayyarta ke cin zuciyarsa sai dai kuma babu hali. Azabar da bidiyon ke sanya shi ciki ne ya sanya shi dakatar da Raihana daga turo bidiyo face hotuna.
Ya ja dogon numfashi ya furzar gami da kallon gefe guda yana mai kauda kai daga kan lovebirds. Hango wata ya yi kamar Humaira, ya ɗan yi tsai da idanu don so ya tantance abinda yake gani, sai kuma ya kauda kai. Ya fi tunanin gizo Humaira ta soma yi mishi, sai kuma ya kara kallo. Wannan karon ita ce tabbas, tana sanye da doguwar riga na material mai mayafi Jajaye. Yanayin kalar da garin ya yi, sai ya ba wa hasken fuskarta damar sheƙi musamman da ya kasance tana cikin annashuwa da kwanciyar hankali da alama babu wani abu dake damunta. Sai hira suke da abokiyar tafiyarta wadda ya gane ta, Ummita ce. Ya ganta a hoto don ba hoton Humaira kaɗai ba, hatta da ƴan gidan sai da Raihana ta turamishi hotunansu da kuma bayanin alaƙarsu. Har ya kama murfin mota zai fito ya tuna alƙawarin shekara da ya ɗaukar mata kawai ya fasa ya cigaba da kallonta. Dab da motar suka tsaya suna kalle-kalle kasancewar gilasanta tinted ya sa basu ganshi ba, shi kuwa Ibb shalelan Juliet, bai ma gansu ba ya lula wata duniyar sai buɗe haƙora yake yi kamar gonar auduga.
Humaira ta ɗan yamutse fuska tana gyara gyalenta da iska ke kaɗawa.
"Nikam asibitin nan juyar da kai gareshi, don Allah ƙara kiranta ki ce bamu gane wajen da ta ce ba kinga garin yana kara haɗewa."
Itama Ummita duk ta damu ganin hadari ta fiddo waya ta dannawa Sadiya. Nan ta ce su tsaya inda suke ta gansu.
Suka ja kuwa suka tsaya, Humaira ta zubawa mutanen dake ta shawagi a wurin idanu tana godiya ga Allah a ranta idan ta ga an wuce da marasa lafiya dayake suna daidai Emergency. Ba su wani jima ba sai ga Sadiyar ta iso, bayan sun gaisa ta karɓa ta yi musu godiya suka juya suka kama hanyar fita.
Fadeel kamar wanda aka tsikarawa allura haka ya zabura ya fito daga motar ya dubi Ibb.
"Malam ka zo mu tafi ba ka ganin yanda garin ke haɗewa wai?"
Suka dubeshi, Dakta Salma ta yi murmushi.
"We are sorry Amininmu. Bari na kyale shi haka. Nagode sosai ku gaida gida."
Bai ko kalleta ba ya amsa da toh don shi gaba daya hankalinsa na ga su Humaira yana fatan Allah ya sa su amince su sauke su a gida. Ibb ganin an soma yayyafi ya yi mata sallama ya shiga motar ya tayar.
"Please and please ka yi sauri kada su hau abin hawa, so nake ko yaya ka yimin kokari ta amince mu kai su gida."
Ya tayar da motar ya soma tafiya sannan ya dubi Fadeel cikin rashin fahimta ya ce.
"Wa kenan kake magana a kai?"
Fadeel da idanunsa ke kan su Humaira wadanda suka kara ɗaga ƙafa ganin ruwa ya soma sauka bai ce komai ba face nuni da ya yi mishi da hannu. Sam bai ga fuskokinsu ba sai baya, kafin ya yi magana Fadeel ya sake tarar numfashinsa.
"Humaira ce."
"Ohh." Abin da kawai Ibb ya ce kenan.
Yana zuwa daidai saitin inda suke ya tsaya har yana tare musu hanya, Humaira dake saitin wurin ta kalli motar ranta a ɓace don a ganinta ko waye yana sane ya sha gabansu. Ta bude baki da zummar magana Ibb ya sauke gilashi suka kalli juna. A gaggauce ta gaishe shi, itama Ummita haka, ta gane shi saboda tana ganin hotunansa a wayar Raihana, shi ne dai wanda y taimaki Raihanar.
"Gida ku ka nufa ne? Ku shiga na sauke ku don yanzu idan ku ka shiga napep jiƙewa zaku yi."
Ruwan sosai ya ƙara ƙarfi, Humaira ta buɗe baki za ta ja musu Ummita ta dafe hannun da sauri ta amsa.
"Toh mungode." Ta kalli Humaira, a hankali kuma a gaggauce ta ce.
"Muje Humaira, yanzu ba lokacin jan musu ba ne, wallahi nidai ina mura kin sani, ruwannan ya dake ni kuma lafkewa zan yi da bikin nan."
Jin haka Humaira ta amince suka shiga, ita ta soma shigewa sai Ummita. Motar sanyi sakamakon Ac dake aiki. Sai a lokacin ta lura da wanda ke zaune a gefen Ibb din, ji ta yi kirjinta ya buga dam, ta rasa dalilin bugawar kamar yanda ta kasa dauke idanu a kansa. Shi ɗinma ita yake kallo babu ƙakƙautawa har bai iya ya amsa gaisuwar Ummita ba. A bangaren Humaira ji ta yi idan ta cigaba da kallonsa ranta zai iya fita saboda wani irin zafi da take ji a kirjinta ga kanta dake faman sarawa don haka da sauri ta kauda kai ta matsa ta maƙure a kujerar bayansa tana jingina da kofar motar. A hankali Ibb ya dan bubbuga kafaɗar Fadeel, firgigit ya dawo hayyacinsa ya gyara zama, gilashinsa ya zaro a aljihu ya rufe kwayoyin idanun da so da tsananin kauna ga kewa suka haɗu suka galabaitar. Dakyar Humaira ta iya gaida Ibb sannan ta gaida Fadeel din ba tare da ambaton suna ba. Shi ma amsawa ya yi can ƙasa.
Ibb ke tambayar Ummita abin da ya kawo su asibiti.
"Kuna da marar lafiya ne?"
"Aa, aiko mu dai Anti Tasleem ta yi. Ita ɗin ɗaliba ce a nan. Nursing take karantawa ne."
Dan jinjina kai Ibb ya yi.
"Ok, na fahimta."
Jin motar ta ɗauki shiru sai rediyo dake aiki sai ko ruwa da ke jiƙa gilasan motar yana sauka a guje saboda karfin da ya yi. Ummita ta dubi Humaira.
"Wai, da tuni yanzu fa mun jiƙe."
"Uhm." Shi ne amsar da ta ba ta. Fadeel kuwa lumshe idanun ya yi ya ji sautin Uhm din har tsakar kansa, gaba ɗaya sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi. Kamar kuma haɗin baki sai ga gidan rediyon sun saki waƙar Breaker mai taken Kalmar So. Humaira sam hankalinta ba ya jikinta, ji take kamar ta buɗe motar ta dira a cikinta. Gaba daya koina a jikin rawa yake, Ac ke kaɗawa a motar amma ita zufa take. Ta tuna da ambaton Allah ba shiri ta shiga ambata a ƙasan ranta a hankali ta soma dawowa cikin nutsuwarta.
A bangaren Ummita da Ibb, hira suke ɗam taɓawa kaɗan, shi kuwa Gogan da Humaira ba ka jin komai daga bakinsu, babu kamar Fadeel da yake jin waƙar ta zo daidai da yanayin da yake ciki. So yake ya tambayi ya take? Ya lamuran rayuwa? Ba ta hakura ba har yanzu? Ba ta amince ya turo iyayensa ba? Sai yaushe? Amma ina! Babu ko kalma ɗaya da yake jin zai iya furtawa, ba ya fatan rabin shekarar da ya kusan cinyewa ya tashi a banza balle ya ga shekarar ida da rai da lafiya, wannan ya sa yake takatsantsan ya kuma jure bai ƙara kallonta ba tunda ko ya kalli side mirror ba ya ganin komai face danshin ruwan dake kwarara sai ko hasken fitilun motocin dake saman titi.
Har suka iso gidan ba ka jin uffan daga Fadeel, shi kansa Ibb sanin halin mutumin ya sanya bai takale shi da hira ba ko sau ɗaya. Ya dai san yau Humaira ta fama mishi inda yake mai ƙaiƙaiyi.
"Ko mu karasa da ku har cikin farfajiyar?"
Wannan kalmar ya sa Fadeel cire gilashin idonsa, ya dubi gidan su Humaira, wato har an iso kenan.
"Aa, mungode sosai. Bari mu karasa ciki."
Cewar Ummita. Humaira kuwa har ta kama ƙofar ta bude, amma ina, iska mai karfi da ruwan da ya fesomata ya sa dole ta koma ta rufe. Fadeel ganin haka ya juya bayan, sai a sannan ya kara kallonta ido cikin ido, da sauri ya dauke idanunsa ya dan kai hannu baya ya dauko lemar dake ajiye a wurin. Fitowa ya yi ya buɗe lemar, babba ce don ta fi ta Ummita girma, Ummita kam tuni ta fita itama ta bude nata lemar da ba zai ishe su ba su biyu koda a dazun ne. Kofar Humaira ya bude gami da miƙamata lemar. A sanyaye take dubansa.
"Karɓa mana Humaira." Ibb ya furta, ta kalleshi.
"Mungode sosai, Allah ya kiyaye hanya." Daga nan ta fita, sai ya kasance su biyun a ƙasan lemar. Kan Fadeel a ƙasa ba ya son kallonta gudun ɓarowa kansa aiki, ta sa hannu ta karɓa sannan ta dan ja baya kaɗan.
"Idan na shiga zan aiko a kawo."
Murmushi ya yi mai kyau har a sannan bai kalleta ba ya amsa da toh. Daga haka ya fice ya koma cikin motar ya rufe. Ita ma ta nufi kofar da gudu-gudu.
"Muje."
Ba musu Ibb ya yi reverse ya juya kan motar suka bar layin. Ƴar dariya ya yi.
"Fadeel kana son Humaira."
Fadeel bai iya kallonsa ba ballantana ya samu amsa. Ya kara cewa.
"And you know what? Kun dace sosai."
Nan ma bai kalleshi ba sai dai ya yi murmushi. Ganin ba ya son magana ne ya sa Ibb rabuwa da shi.
***
A can kuwa Humaira na shiga ta bada lemar a miƙa musu, ɗan aike ya dawo ya ce babu kowa a wajen, ta karɓa a sanyaye ta shige ɗakinsu da shi. Madadin ta karasa ciki sai ta ajiyeshi a ɗan gefen don ya sha iska. Suka sauya kayan jikinsu saboda jiƙewar da suka ɗan yi. Ummita ta ɗauro alwala sannan itama ta ɗauro, koda ta idar da sallah kwanciya ta yi saman dardumar don kanta har lokacin sarawa yake yi kamar jijiyoyin kan nata za su tsinke. Tuna Fadeel kaɗai yana haifar mata da rawar jiki da ciwon kai, daga haka kuma sai ta ji kamar ana mata ihu a kunne. Kafin ka ce wannan sai ga Humaira ta soma kuka sosai. Ummita da ke kwashe jiƙaƙƙun kayansu ta juya da sauri ta juyo. Allah ya taimaka su kaɗai ne a ɗakin ta roƙi yanmatan akan su fita ta gyara don sun yi kaca-kaca da shi. Tuni ta fahimci matsalar jinnunta ne, ta sha mamaki ma da bai tashi a mota ta yiwa su Fadeel rashin mutunci ba.
Da sauri ta fice zuwa kicin, can baya ta zagaya inda ake dora babban tukunya a icce saboda yawan da aka yi. Garwashi ta zuba cikin kasko ta dauka da sauri gudu-gudu ta nufi dakinsu. Mami dake kokarin shiga kicin don ganin kwandunan kayan miyan da Abba ya ce an kawo na girki ta tsaya cak hankalinta ya yi kan Ummita wacce ke tafiya kamar wani abu ya faru. Da sauri ta bi bayanta.
Ita kuwa Ummita, tun cikin babbar sallah da ta je Bichi ta karɓowa Humaira hayaƙi a wurin ɗan uwan mahaifiyarta hakan yasa Humaira na fara kuka ta yi niyyar turara mata. Abin mamaki har ta isa yanayin kukan Humairar bai sauya ba. Ta ciro maganin ta barbaɗa cikin kaskon ta ajiyeshi kusa da Humaira. Nan da nan kanta ya soma juyawa. Daidai lokacin Mami ta faɗo ɗakin. Abin da ta gani ne ya sanya ta kallon Ummita,
"Lafiya? Meke faruwa da Humairar? Wannan wane irin hayaki ne kuma?"
Ummita ta sha jinin jikinta don gaba daya ba ta sanar da Mami ta karɓowa Humaira hayaƙi ba.
"Ba komai Mami, kukan nan ta soma wanda take yi idan aljanunta suka tashi shi ne.."
Mami ta daka mata tsawa.
"Shi ne me?! Shi ne kike yi mata hayaƙi ba tare da kin sanar da ni ba? Haba Ummita, yanzu idan Abbanta ya ji wa zai yiwa faɗa? Maza ɗauke hayaƙin nan."
Ummita ta dauka ta fitar zuwa bandaki ta kashe, ta sani ta yi kuskure amma kuma cikin ikon Allah Humaira ta yi shiru sai gumi take haɗawa da alama kuma bacci ya ɗauketa.
Ummita ta kai duba ga Mami, zuwa lokacin tana zaune gefen gado.
"Ki yi hakuri Mami."
Girgiza kai Mami ta yi.
"Ba laifi kika aikata ba Ummita, na sani kulawa ce da yar uwarki, amma ko mene ne ya dace na sani saboda nima ina nawa kokarin a kanta don har na yiwa Abbanku maganar wani mai bada magani zan kai ta wurinsa bayan biki ya ga mece ce matsalarta."
Gyaɗa kai Ummita ta yi tana murmushin farin ciki. Ba ta da fatan da ya wuce ta ga Humaira ta samu lafiya ta amince da auren mai kaunarta irin Fadeel.
"Toh Mami. Allah ya sa a dace."
Mamin da murmushi ta