Showing 18001 words to 21000 words out of 93383 words
take ba.
"Sannu ƴanmata, sauko."
Ta tsinkayi ɗaya daga cikin jama'ar wurin na fadi, wasu kuwa na hayaniya su na fadin ai laifin mai motar ne. Can kuma ta ji an ce.
"Alhaji kai ne da laifi, kai ka bugi motarsu garin cin burki a kurarren lokaci."
Ta buɗe idanunta a hankali jin wani daddaɗan kamshi a gefe, a hankali ta sa hannu ta ɗauki jakarta da ta tarwatse a ƙasa, duk tarkacenta sun zubo. Wani matashi ya shiga tattara mata ita kuwa tana son ta fito a adaidaitar kamar yanda ɗan sahun ya fita ya zauna gefen kwalta, amma ina tururuwar mazan dake wurin ya sa ko motsin kirki ta kasa. Da murya irin ta manyan mutane ya amsa.
"Baba, ba abin zafi ba ne. Na sani ni keda laifi, ina mai ba da hakuri garesu. Zan kuma yi kokarin gyara ɓarnar da nayi. Ku yi hakuri don Allah."
Humaira ta juya ta kai duba ga mai maganar, daidai lokacin da shima ya ɗan rankwafo don ya yi mata sannu da kuma neman alfarma akan ta sauko su je asibiti. Kalma ɗaya ta kasa fita a bakinsa da ya yi nauyi. Ƙafafunsa suka soma ƙoƙarin kayar da shi. Zai iya rantsuwa ba kaffara son budurwar yarinyarnan yake da idan da ace Uwargidansa ta yi haihuwar wuri to fa ya ci ya yi haihuwar fari da ita. A ɓangaren Humaira kallon da ta bishi da shi bai wuce na son ganin marar hankalin da bai iya tuƙi akan ƙa'ida ba har yake shirin kai ta barzahu. Babban mutum wanda ba gigin kuruciya tattare da shi, ya sha manyan kayansa har da babbar riga da hula. Kana ganinsa dai ka ga wanda ya ba arba'in baya. Ganin yadda ya ƙuramata idanu sai nan da nan ranta ya yi masifar ɓaci, ta ja tsaki wanda ya ba Alhajin nan mamaki, ba ta jira komai ba ta sauko daga adaidaita sahun ta ɗaya ɓangaren mutane na mata sannu. Matashin da ya tattara mata kayan ta yiwa godiya ta karɓi jakarta, ba ta so dubawa ba amma da yake ya matsa sai kawai ta duba, komai nata yana nan cif ba abin da ya ɓata. Dakyar take tafiya dalilin gefen cikin da har sannan ke mata ɗan zugi.
"Sannu baiwar Allah, kiyi hakuri ba da gayya hakan ta faru ba. Direbana ne ya ɗauki waya bisa umarnina ba kuma mu ankara ba hakan ta kasance. Akwai inda ke maki ciwo sai a karasa asibiti."
Ya karashe yana kai idanunsa kan gefen cikinta da take ta faman dafewa. Ganin haka sai ta saki cikin don ba ta kaunar taimakonsa saboda irin kallon da yake jifanta da shi, kwatankwacin irin kallon Kabeer. Fuskarta a daure tamau ta amsa.
"Na ce maku babu abin da ke damuna, lafiyata kalau. Nagode da taimakon."
Daga haka ta karasa tana cije lebba ta yiwa ɗan sahun sannu kafin ta kai hannunta dake rawa don har lokacin ba ta dawo daidai daga razanin da ta shiga na hatsarin ba ta fiddo kudi za ta ba ɗan sahun na hakkinsa dake wurinta amma ta kara tsintar muryar Alhajin nan wannan karon muryarsa har ƴar rawa take yi, kirjinsa kuwa bugu yake da karfi tsabar son da ya shiga zuciyarsa farat ɗaya na yarinyar.
"Ki bar shi zan biya. A wane unguwa kike sai mu sauke ki?"
Jama'ar duk idanunsu a kansu, wadanda suka lura da yanayin mutumin ba su ga laifinsa ba don Humaira ta haɗu iyakar haɗuwa, sai dai a ganin wasunsu, girma ne zai fadi muddin ya bari ta gasa mishi magana. Aikuwa masu wannan tunanin ba su kai ga furtawa ba suka tsinkayi muryarya cike da tsiwa tana magana tana kara zaro manyan idanunta masha Allah.
"Baba ina mutunta furfurarka hakan yasa nake gargadinka akan ka fita a hanyata wallahi tun ban gasamaka wacce za ta hanaka bacci ba. Haba! Wannan ai shiga sharo ba shanu ne, ka kusan kaimu lahira na maka uzuri yanzu kuma me ya shafeka da kudin da zan bayar? Da kai ke biyamin kudin motar? Ina ruwanka da ni?" Daga haka ta ja dogon tsaki ta miƙawa ɗan sahun dubun gaba daya na motarta zuwa da komawa ba tare da ta jira chanji ba, daga haka ta juya daidai sadda wannan matashin ya kara miƙo mata ledar da shaf ta mance da batunsa, saƙon Mami zuwa ga Anti Laila. Sai lokacin ta ga ashe ma leshi ne sai atamfa. Godiya ta yiwa matashin a fusace ta bar wurin tana huci, ga cikinta inda ta ɗan bugu bai bar raɗaɗi ba. Kunya da tarin bakin ciki suka lulluɓe Alhajin, bai taɓa zaton yarinyar ba ta da kunya ba da tuni ya ɓoye zalamarsa a kanta.
"Sai hakuri Alhaji, yaran yanzu ba su da kunya."
Ya basar da zancen yana maida duba ga Ɗan sahun nan da ba da umarnin ya tashi su karasa asibiti ko kuwa dai ya sallame shi yanzun a nan, ɗan sahun ya aminta da hakan, nan take ya ba shi kuɗaɗe masu ɗan kauri gami da ƙara ba shi hakuri. Daga haka ya juya zuwa motarsa har lokacin bai daina jin kunya da ɓacin rai ba su sake shi ba. Ya kuma ƙudurta a ransa idan har haka yaran zamani su ke, to ya yi Allah wadai da ire irenta, ba kuma ya jin zai kara kallonta da sunan wata da ya taɓa gani har ya ji kaunarta cikin ransa.
***
A ɓangaren Humaira dakyar ta karasa gidan Anti Laila, ita sai da suka yi nisa ma ta tuno ba ta da chanjin da za ta sallami mai adaidaitan don haka ta ce ya jira ta kawo mishi. Wajen Anti Laila ta karɓa bayan ta mata bayanin hatsarin da suka yi, nan kowa ya hau ta da sannu. Anti Laila da kanta ta kira Mami ta shaida mata, hankali tashe ko mintuna talatin ba a yi ba sai ga Mamin da direban Abba. Daukarta ta yi suka nufi asibiti, koda likita ya duba ta ya tabbatar kawai buguwa ce. Magunguna ya ba ta sannan suka wuce gida. Maganin ta sha bayan ta ci abinci ta kwanta.
Abba har ɗakinsu ya shigo ya duba ta, ganin da sauki bacci ma take ya sanya shi fita.
Sai da ta yi kwanaki uku ba ta leƙa ko farfajiyar gidan ba a rana ta hudu ta koma zuwa koyon girke-girke abin ta.
***
Rayuwar ta ci gaba da tafiya yau dadi gobe babu, rashin dadin a wajen Humaira bai wuce na yadda su Tasleem ke kara nuna mata kiyayya a fili ba. Har ta kai da an wayi gari watarana sun yi mata sharrin sata, domin an tashi Mami tana neman kudin har dubi ashirin da ta ajiye ƙasan filo, gaba daya ran Mami a ɓace yake, sannan ma ita Humaira ba ta nan kuma ita ce ta gyara ɗakin kafin ta fice gidan Laila. Ganin an duba ko'ina sai Futuha da su Yassar suka ba da shawarar a duba ɗakunansu. Mami a farko ta ƙi, sai da Ladidi ta ce ya kamata a duba ko'ina tunda dai nema ake kuma abin da yasa Ladidin faɗin haka ganin su na neman ɗorawa yarinyar kirki Humaira ita kuwa tana da yaƙinin idan har Humaira ce ba za a sami ko sisi na wani a kayanta ba. Tasleem da ta dage tunda Humaira ce ta yi gyaran ɗakin a soma duba kayanta ya sa Ummita cike da kwarin gwuiwar sanin wace ce Humaira ta shiga fiddo kayan Humairar daga sif dinta. Sai dai tun kan ta yi nisa Futuha ta zura hannu ta jawo wata doguwar riga.
"Kambu! Dama yarinyar nan ita ta ɗaukarmin wannan rigar? Tasleem ku dubi rigar da nake tunanin ta ɓata a wajen wanki?"
Mami ta kalle su, ta yi shiru da mamaki. Can kuma sai ga ɗan kunne da sarƙa sun faɗo. Raihana ta zaro ido tana ɗauka.
"Innalillahi, ku ga sarƙata da nake nema kwanaki? Ashe ita ta ɗauka?"
Kai kamar wasa jikin Ummita na sanyi da wannan sharrin, ba ta yi aune ba ta kai hannu kan takardun kuɗi, tsabar razanar da ta yi ya sa ta fiddowa da sauri. Ladidi ce ta karɓa tana salati ta ƙirga, aikuwa dubu ashirin cif ne wanda Mami ke cigiya, Ummita kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin.
"Wallahi Mami wannan sharri ne, Humaira ba ɓarauniya ba ce. Ko kwandalar mutum ta gani idan tana aiki ajiyesu take a wurin da ta gan su."
Mami dai ba ta iya magana ba domin kanta ya ƙulle, a sanyaye ta sa hannu ta karɓi kuɗin ta fice a ɗakin tana ji su Yassar na yiwa Ummita masifa wai sai ta faɗi wa ke mata sharrin amma ba ta ko iya tankawa ba. Ita kanta ta sani sata ba ya daga halayyar Humaira don ta sha ajiye kuɗin da suka fi waɗannan kauri ba ta taɓa su ba, amma ta sani mutum ka iya sauyawa. Bare ma a irin gidan nan na Alhaji Isuhu da ba a facaka da kuɗi.
Humaira ba ta dawo gidan ba sai yammaci bayan la'asar, da murnarta ta tura kyauren gate ta shigo bayan ta gaida Baba dattijo dake zaune a benci yana siyan rogo a wurin ƴar tallah. Farin cikin bai wuce na yadda suka yi snacks har biyu a yau ba, samosa da springroll kuma cikin ikon Allah ta yi ya yi kyau a ido ya kuma yi daɗi a baki har a foilpaper ta nannaɗe ta kawo don Mami ta ci ta ji. Muryar Ƙasim ta tsinta a kanta.
"Ɓarauniya ta dawo."
Kallonsa ta yi gabanta ya faɗi, a duk irin wulakanci da jefa-jefan mugayen sunaye da suke mata, babu wani cinikinsu a ya taɓa kiranta da ɓarauniya wannan ya sa ta ji wani irin sanyi har ta kasa mayar masa da martani yadda ta saba idan ya jefe ta da marar dadi. Ya ɗan ɗaga gira.
"Oh, bakin ta kanwa ya yi la'asar kenan saboda kin sani kin sata shiyasa. Dama ustazancin ashe na ƙarya ne, toh yau asirinki ya tonu. Ɗan adam butulu."
Ta dafa kirji idanunta da suka cicciko da kwalla tun soma maganarsa ta kafa mishi.
"Yaya Ƙasim sata fa ka ce? Ni na yi satar?"
Ya harareta ya wuce kawai ba tare da ya ce komai ba. Ta bishi da kallo har ya shige gidan, itama a hankali ta soma taka ƙafafuwanta da suka yi mata nauyi saboda mutuwar da jikinta ya yi ta yi cikin gidan kirjinta na harbawa.
***
Ma sha Allah, Alhamdulillah. Sai kuma bayan sallah in sha Allah. Allah ya karbi ibadunmu, a sanya ni a addu'a ina bararta don Allah. 🤲🤲 Fatan alheri.
07
Tasleem, Dawud, Yassar da Futuha ne zaune cikin falon sai dai ba ta sha mamakin ƙin amsa sallamarta da suka yi ba, dama ya lafiyar giwa ballantana kuma an jefe ta da kashi? Su na ganinta Tasleem ta miƙe ta yi kerere gabanta hannuwa a ƙugu ta ce.
"Ɓarauniyar banza da wofi, kin dawo kina wani sum-sum kamar munafuka. Koda dai dama munafukar ce, Mamin da ta daukake ki tana maki kallon kamar wata waliyya ai gashinan kin watsa mata ƙasa a ido. Ke ni ba wannan ba ma, earpiece dina da na jima ina nema idan kinsan ke ce ɓarauniyarsa wallahi tun wuri ki fiddomin abina. Atoh, bari ma Abba ya shigo gidan, ko Mami ba ta faɗamasa ba sai mun faɗa."
Humaira wacce ta kasa tsaida hawayenta, kallon Tasleem din kawai take har ta kai aya, lebbanta na rawa amma ko harafi guda ta kasa fitarwa tsabar baƙin ciki. Wannan wace irin baƙar rana ce a wajenta haka da za a wayi gari da yi mata ƙazafin sata? Ta kasa motsawa, haka Futuha ma ta taso da nata kalar rashin mutuncin, su Yassar na taya ta. Ba ta iya cewa uffan ba sai kukan da ta ke rusawa kamar ranta zai fice. Tsawar da ta ji an daka musu ya sa ta kallon hanya, ruwan hawaye ya sa ganinta komawa dishi-dishi, sai a hankali bayan ta ɗan runtse idanu sun ɗan zuba ne sannan ta lura ashe Mami ce. Ƙarasowa ta yi fuskarta a ɗaure, sai ta koma mata Mamin da ta fara cin karo da ita a ranar farko na zuwanta gidan. Kirjin Humaira ya hau dukan tara-tara, ta runtse idanu saboda ta gama hasaso abin da zai afku, wato mari za ta sha a wajen Mami, sai dai ga mamakinta ta ji akalar faɗan sam ba a kanta yake ba, su Tasleem ta shiga yiwa tamkar za ta ari baki.
"Ashe rashin mutuncin naku ya kai har haka? Raini ne wannan ku ka yimin ko mene? Ban hana ɗayanku yiwa Humaira maganar abin da ya faru ba? Ina ce har ɗaki ke Futuha kin biyo ni akan sai an ɗauki mataki na ba ki saƙo ga ƴan uwanki cewar na kashe maganar kada wanda ya tayar? Oh saboda ku nunamin ni banza ce wurinku, hukuncina ma na banza ne shi ne dalilinku na yin watsi da zancena a kwandon shara ko?! Toh wallahi ku fita idona tun wuri, kuma daga rana irin ta yau ku ka ƙara tada wannan batu sai na saɓamaku kamanni."
Tana kai wa nan ta ja hannun Humaira zuwa ɗakinta. Ta bar yarannata a tsaye tamkar su haɗiyi zuciya su mutu don haushi, Yassar ne ya soma jan wani dogon tsaki kafin ya sa kai ya bar falon, Dawud ya mara mishi baya. Tasleem kuwa ƙwafa ta yi.
"Innalillahi, ke Futuha na soma tsoro, na yarda dagaske ne da ake cewa ƴan ƙasarsu na da asirai, anya wannan shu'umar yarinyar da Kawunta hakanan suka bar mana uwa? Anya ba sai da suka shuka tsiyarsu sannan ta dawo wajenmu ba?"
Futuha da ta kasa magana kawai sai ta ja tsakin itama ta ɗauki wayarta ta wuce sashen Anna idanunta cike da kwallar baƙin ciki.
***
A gefen Mami kuwa, su na shiga ɗakinta ta rungume hannuwanta a kirji ta daure fuska tamau har sai da Humaira ta sha jinin jikinta.
"Zauna." Ba musu ta zauna a saman kafet, ita kuwa ta hakimce a gefen gado.
"Na tsawatarwa yarannan saboda na riga da nasan takun saƙar da ke tsakaninku, ba na son a samu fuskar da za su ƙara ɗora maki karan tsana a matsayinki na yar uwarsu ta jini. Wannan ɗin ma da suke gwada maki fatana su daina na kashe shi gaba ɗaya. Amma meyasa haka Humaira? Har yanzun ina kokwanto akan kin aikata wannan laifin na ɗaukar kudi a ɗakina, amma idan na tuna ganin da na yiwa kuɗin a cikin kayanki sai zuciyata ta tsinke. Ki faɗamin iyakar gaskiyarki, kamar yanda idan na ci karo da ɗaya cikin su Tasleem sun aikatamin laifi zan hukunta su, kema matuƙar da zuciya ɗaya nake zaune da ke ya zama wajibi na dauki mataki idan kin yi ba daidai ba."
Humaira ta ja majina tana kallon Mami. Girgiza kai ta soma cikin muryar kuka ta ke magana.
"Wallahi Mami, Allah ɗaya, ba zan yi wasa da Ubangijina wurin yi maki ƙarya ba, ban taɓa ɗaukar ko abin sakacen haƙori a ɗakinki ba tare da izninki ba ballantana kuma kudin da ba nawa ba. Mene ne bakya kokarin yimin a gidannan da zan yi maki sakayya da hakan? Kina yimin kyautatawar da ko na rayu da mahaifiyata abin da za ta yimin kenan. Toh a wane dalili zan zama butulu har na ɗauka daga asusunki? Mami wallahi ban ɗauka ba, ba ni kuma da masaniyar yanda aka yi kudin suka je cikin kayana, nidai na san na maki gyaran ɗaki, na kuma adana su a inda na gansu, na fita zuwa gidan Anti Laila."
Mami ta yi shiru tana nazarinta, duk kushen mai kushe ba zai taɓa zama da Humaira ya ji ta masa karya ko sau ɗaya ba. Toh wannan dabi'a ce ta mahaifiyarta, ta sani sarai mahaifiyar Humaira haka take da faɗar gaskiya. Ta san kuma ko a gaban Abban maganar ba za ta chanja zani ba. Sai ta yi nufin kasheta a yanzu ta hanyar numfasawa ta dafa kan Humairar cikin taushin murya ta ce.
"Ya isa hakanan, bari kukan kar ya ja maki ciwon kai. Na yarda dake ai dama, sai dai kin san kudi ba zai kai kansa cikin kayanki ba ko? Koda ace ba ke kika kai ba akwai yadda aka haihu a ragaya, kin ga kuwa dole na bincika matsayina na matar gida ko?"
Humaira ta gyaɗa kai har sannan tana sauke hardadden numfashi irin na wanda ya ci kuka ya ƙoshi. Mami ta dora da fadin.
"Toh don haka kar ki fahimce ni baibai don na tuhumeki, ya zama dole na aikata hakan ne ko don sauke hakki, yanzu kuma da ya kasance ba ke ba ce, zan bincika a sannu gaskiya za ta yi halinta. Tashi ki je ki ci abinci ki huta."
Humaira ta gyada kai kawai ta mike ta fita. Har sannan jikinta bai bar ɓari ba, sharri ya fi komai ɗaga mata hankali, ta tsani sharri, ta kuma ci alwashin ita kanta za ta dage da addu'a har sai gaskiya ta yi halinta don a yanzu kam ba ta da amsar ba su Tasleem sai lokacin da komai zai bayyana muraran.
A can ɗaki ma Ummita ta tarar tana nata hawayen, sai ya zamana ita ce mamai rarrashin Ummitan da nuna mata ai Mami ta fahimce ta. Ummita ta labarta mata yadda komai ya faru. Ta kara da fadin.
"Ba ni da tabbaci akan ko su Tasleem ne da aikata hakan, amma shakka babu ina zarginsu."
Murmushi Humaira ta yi.
"Kar ki damu yar uwa, idan ma su ne ina mai tabbatar maki wataran gaskiya za ta bayyana."
Daga haka suka bar zancen, koda Abba ya zo, babu wanda ya tunkareshi da zancen don ba karamin gargadi da jan kunne Mami ta yi musu ba, koda Anna ta hau faɗa, sai Mami ta sanyayar mata da jiki da faɗin abin da ta fi tunanin akan sharrin da aka yiwa Humairar. Dole itama Anna ta lallaɓa su akan zanceya mutu. Daga ranar kuwa ba a kara tayarwa ba kuma basu fasa kiran Humaira da wannan sabon suna na ɓarauniya da suka laƙaba mata ba. Wanda hakan ya fi komai yi mata zafi, duk kuwa da