Showing 15001 words to 18000 words out of 93383 words
ta fito. Anan kuma ta ga ta amsa waya ta yi jifa da wayar saman gado tana ɗan goge fuska. Jiki a sanyaye ta ƙarasa gareta ta zauna.
"Ummita, lafiya? Meyafaru?"
Ummita tana kallon littafin amma ta kasa karatun sai kawai ta girgiza kai tana shirin cewa ba komai amma tuni hawayenta ya zuba saman littafin. Humaira ta janye littafin.
"Don Allah meke faruwa? Anyi wani abu ne bayan fitar mu?"
Nan ma girgiza kan ta yi. Ganin haka sai kawai Humaira ta mike ta nufi sif dinta, har ta sanya kaya jiki a sanyaye Ummitan ba ta da niyyar cewa wani abu. Ganin haka sai ta ƙarasa wajenta karo na biyu.
"Na tambayeki mene ne kin kasa cewa komai, kuma kina kuka." Jin ta yi shiru ne yasa Humaira fadin.
"Toh bari na kira Mami mai yiwuwa ita za ki faɗamata."
Har ta miƙe da sauri Ummita ta riƙe hannunta. Suna haɗa idanu ta girgiza mata kai, itama Humaira tuni idanunta sun cicciko don a duniya ta tsani kukan mutum. Kuka ma irin na waɗanda ta ke yiwa ƙauna domin Allah. Duk abin da ya shafi irin mutanen nan tana jin abin a ranta tamkar ita ya shafa.
"Kar ki je, zauna na faɗamaki." Ta koma ta zauna tana mai zuba mata ido bayan ta share kwallarta.
"Yayar Mamana ce ta kira ni daga Bichi, kwanakin nan duk sun takura akan lallai sai na fiddo miji na yi aure wai karatun ya isa hakanan. Su sam hankalinsu bai kwanta da zamana a gidannan ba. Ita Babbar yayar Mamana, Anti Maijidda cewa take yi wai har mafarke-mafarke take yi a kaina don haka za su yiwa Abba magana a dakatar da karatun nan, ida n ma aure ne dai a yimin. Ni kuwa na dage akan ba zan yi aure yanzu ba, na ce musu ko zance ba na yi, sun ce ai kuwa anan da Bichi ba zan rasa mijin aure cikin ƴan uwa ba, Anti Maijidda har cewa ta yi ga babban ɗanta Yusuf nan, wai ya kammala gininsa za ta turo shi ya zo mu yi hira mu fahimci juna. Kin taɓa jin wannan irin abu don Allah Humaira? Duka-duka nawa nake da za su ce za su aurar da ni yanzu? Zangon karshe nake a Ss1 zan wuce Ss2, idan ma auren suke buri su ga na yi, ai sa bari dai shekaru biyun da suka ragemin a sakandire na kammala su. Haka kawai don wasu mafarke-mafarken da ba su da tabbas ku rushemin ginin rayuwata? Sun bi sun kafawa Mami karan tsana, ban san hawa ba ban san sauka ba, amma nima su na hantarata akan na mayar da ita tamkar uwar da ta haife ni, gani suke na fifita dangin Babana sama da su. Toh don Allah faɗamin, mutanen nan sai na je wurinsu duk shekara a can nake hutun dogon zango da ake ba mu na makaranta har ya ƙare, amma su ko sau ɗaya ba su taɓa zuwa garin nan da zummar ganina a gidan nan ba acewarsu su da Mami har abada don ba su yarda da zuciya ɗaya ta ke riƙe da ni ba. Akan Mami na sha duka a wajensu idan na je domin duk wanda ya aibata ta zan buɗe baki nace sam ba haka take ba, to fa anan sai na ɗanɗana kudata. Yanzu wannan matsalar auren da ta taso ki faɗamin Humaira, ta ina zan kashe ta ba tare da na samu matsala da su ba, nikam wallahi gaba ɗaya kaina ya ƙulle."
Humaira ta sauke ajiyar zuciya.
"Wai Allah!" Shi ne abin da ta furta don ita komai ma ya tsaya mata cak, ta rasa me za ta cewa Ummita. Mamaki take yi na yadda suke yiwa Mami kallon baibai alhalin matarnan iyakar kokari tana yi a kansu, irin kokarin da ko mahaifansu na usuli sai haka. Can kuma ta dubi Ummita.
"Toh kodai ki yiwa Abba bayanin komai? Na tabbata zai fahimceki kuma ba zai rasa matakin ɗauka ba yadda zumuncinku ba zai taɓu ba."
Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce.
"Ko? Nima na yi wannan tunanin, wallahi maganganunsu ke hargitsa ni tun wancan satin su ke huran wuta, tun fa ina dannewa har suka soma sanya ni kuka. Amma hakan zan yi kawai, zan faɗawa Abba komai, ke nasan ma kai tsaye zai nemi Kakana wanda ya haifi Mama ya yi mishi magana. Shi kaɗai zai iya tsawatar musu, daman tsoro ne ya sa na kasa faɗa mishi, amma na tabbatar zai magancemin."
Humaira ta jinjina kai.
"Sai dai don Allah kar ki faɗawa Abba zargin da suke yiwa Mami."
Ummita ta kama baki.
"Rufamin asiri Humaira, dama me zai kai ni?"
Murmushi Humaira ta yi. Suka ɗan taɓa hira sannan ta kyale ta don ta yi karatu.
Aikuwa a daren Ummita ta samu Abban ta zayyane mishi komai, ransa ya ɓaci. Ƙarshe dai ya ce ta tashi ta wuce zai san matakin da zai ɗauka. A ranar kashe wayarta ta yi ta kuma yi alƙawarin ba za ta kunna ba har sai komai ya wuce don ta tabbata zagi ne dai za ta sha a wurin su.
***
BAYAN WATA BIYU...
Gadan-gadan Humaira ta fara zuwa koyon girki, abin da ya burge su Abba da Mami bai wuce irin hazaƙarta ba na saurin ɗaukar abu. Ita kanta Anti Laila sosai take yabawa da Humairar. A farko-farko ne dai idan aka koyar da su ta zo gida ta yi sai ya kasance bai yi dadi ba ko gishiri ya yi yawa ko dai wani abin, har su Tasleem na ci don su yi mata dariya da kuma kushe. Har su na cewa Abba ya yi asarar kuɗinsa. Amma yanzu kam duk da su na kaucewa ba su son nunawa a fili yana musu dadi, to fa a ƙasan zuciyarsu su na son su ɗanɗana idan ta yi. Amma fa ana ci ana yamutse fuska ana nuna ba laifi ya ɗan yi dadi. Ita dai ba ta tanka musu tunda har Abba da Mami da Ummita su na yabon girkinta.
A farko direba ke kai ta, daga baya kuwa Mami ta nemi ɗan sahun da zai dinga kai ta kuma ya ɗauko ta. Watarana kuwa da aka yiwa ɗan sahun rasuwa da kanta ta Mami ta sanya yaron gidan me musu wanki ya raka ta titi ya sanya ta a adaidaita, a dawowa da kanta ta dawo. Tun kuma daga nan ta soma zuwa da kanta ta dawo, a karshe kuma ya kasance koda ɗan sahun bai zo ba ita ke zuwa ta dawo. Ganin ta gane hanya ya sa Mami kawai ta sallami ɗan sahun ake ba ta kuɗin mota.
Komai idan ta koya tana samun ɗan littafin da Ummita ta bata ta rubuce tsaf da hausar ajami. Rubutunta mai ɗan karen kyau da burgewa har ya kasance Ummita ta yi ta santin handwritting din.
A bangaren Islamiyya kuwa, kusan tare suke tafiya da Ummita a aji duk kuwa da cewar a can karatunta ya zarta na su, akwai abubuwa da dama da ta sani na daga litattafan addini wanda na ajin ƴan gaba ne. Hakan ya sa idan ba sa komai ta ke zama malamar Ummita. Su yi ta karatunsu musamman yanzu da ake cikin hutun dogon zango na makarantun boko. Idan ka cire Tasleem da Futuha sai samarin, babu wanda ke zuwa makaranta. Gidan sai yake yiwa Humaira daɗi fiye da a baya.
Ranar wata Asabar da yammaci su na zaune a ɗakinsu, Humaira ke taya Ummita gyaran sif ɗinta, gaba ɗaya sun sauke kayan Ummitan saman gado. Humaira sai tsokanarta take yi akan da tuni yanzu an sanya ranar aurenta da Yusuf, ita kuwa tana kai mata bugu da ninkakkiyar rigarta. Sai kuma ta ja guntun tsaki ta zauna gefe tana murmushi.
"Ke nifa ina da mijin aure a hannu, kawai dai bai taɓa zuwa gidannan ba, ba na so kowa ya sani sai na kammala karatu."
Humaira ta zaro ido da wani irin zumuɗi ta ce.
"Don Allah dagaske? Waye wannan mai sa'ar?"
Ummita ta ɗan harareta sai kuma ta miƙe ta ci gaba da ninkin da take yi.
"Oho, idan ta yi wari kya ji."
Duk irin magiyar Humaira dai ba ta samu Ummita ta furta komai ba, da ta ga hakan ba mai ɓulla bane sai ta sauya ta ce.
"Toh abu ɗaya za ki faɗamin, Allah kuwan daga shi ba zan ƙara tambaya ba. Na san shi, na taɓa ganinsa? Eh ko aa?"
Dariya Ummita ta yi.
"Wai ni za ki yiwa wayo ko me?"
Itama dariyar ta yi.
"Allah ba wayo ba, kawai ina son sani."
Ummita ta ɗan yi shiru, ta sani idan har ta ce mata ta san shi to za ta ƙara damuwa da son ji ita kuwa duk data yarda da Humaira ba ta shirya kowa ya ji yanzu ba. Sai ta girgiza kai.
"A'a toh."
Jin haka Humaira ta taɓe baki.
"Toh shikenan, idan ta yi wari ma ji."
Kafin Ummita ta tanka sai ga Muhsin ya shigo a guje.
"Adda Humaira, ki zo inji Mami za ku gaisa da Yaya Kabeer."
Humaira ta ji kanta ya yi wani dum, wani irin ɓacin rai da bakin ciki na taso mata da ba ta san silarsa ba. Nan da nan ta haɗe fuska tamau kamar ba ita ke dariya yanzu ba.
"Ka ce gatanan zuwa." Ummita ta amsa jin ba ta da niyyar amsawar. Ta sani Humaira ta tsani Kabeer, tun ganin da ya yi mata a gidansu tare da Mami yake bibiyarta. Amma yadda fuskarta ta sauya ita kam ba ta taɓa ganinta cikin wannan yanayin ba.
"Ke lafiya? Daga ance maki Kabeer ya zo?"
Tsaki ta ja ta miƙe a fusace cike da wata iriyar tsiwar da ita kanta Ummita ba ta san ta da ita ba ta ce.
"Aikin banza da wofi, na tsani naci da takura wallahi. Mutum sai shegen naci, itama Mami ta biyemishi har da wani aikowa a yi kirana." Ta kara jan tsaki. Maganarta na karshe kan kunnen Raihana da ta shigo ɗakin tana danna waya, baki buɗe take kallonta.
"Ke, Mami za ki yiwa rashin kunya? Har da tsaki?"
Ko kallonta ba ta yi ba ta juya ta ci gaba da ninkin kayan da alama ba ta da ko niyyar tashi balle ta je. Ummita ta kalli Raihana itama ta dube ta, a fusace Raihana ta karaso ta fisge rigar dake hannun Humaira ta yi jifa da shi. Humaira ta mike a zuciye ta ce.
"Malama na fada! Nace na fada! Kabeer din banza da wofi! Ba zan je ba din akwai abin da za ki iya yi? Ko waye ya tilasta ni shiga lamarinsa sai na gasa mishi maganganun da zai yi dana sani!"
Raihana gaba daya ta tsorata, kamar dai Humaira kamar ba ita ba. Kawai sai ta gifta ta fice daga ɗakin ba tare da ta tanka ba don dama Raihana akwai tsoro. Ummita ta mike ta kama hannun Humaira a sanyaye.
"Humaira, lafiyarki kuwa? Me ya yi zafi?"
Ba ta ce komai ba kawai ta zare hannunta a cikin na Ummita, zama ta yi ta yi shiru sai huci ga gumi na tsastsafo mata. A haka Mami ta shigo dakin, Raihana duk ta ba ta labarin abin da ya faru, kallon Humaira take yi a nutse, sai kuma ta karasa ta zauna gefenta. A hankali ta dafe hannunta. Humaira ta kalleta, kawai sai ga mamakinsu ta fashe da kuka.
"Mami don Allah kiyi hakuri, wallahi na tsane shi, ki ganinsa bana son yi. Kiyi hakuri don Allah ki janye batun zuwa mu gaisa da shi."
Wani irin kuka ne da sheshsheƙa tamkar wacce ake kokarin raba ta da numfashinta. Mami da Ummita wacce duk ta firgice suka dubi juna sai kuma ta rungumo Humaira.
"Kar ki damu, ya tafi ya bar gidan ma. Kuma na yi maki alƙawari Kabeer ba zai ƙara takura maki ba. Kin ji ko?"
Sai a sannan ta gyaɗa kai ta bar kukan, lokaci guda kuma ta fara dawowa hayyacinta. Ita dai Ummita ikon Allah ta zubawa ido tana kallo. Abin dai kamar a wasan kwaikwayo.
06
Dare ne misalin karfe ɗaya da mintoci, ɗakin ya yi shiru ban da munsharin Tasleem ba abin da kan addabesu kullum ba abin da ke motsi. Humaira wacce abu biyu suka hana ta sukunin bacci, ta zubawa tagar ɗakin ido tana kallon farin wata da ya hasko har cikin ɗakin nasu. Garin babu zafi sai iska dake kaɗawa kaɗan kaɗan hakan yasa rashin wutar bai hana mutanen gidan sukuni ba. Ta ja guntun tsaki ta miƙe zaune gami da runtse idanunta.
_'Humaira ba ki kyautata kalamai ga Mami ba. An sani maganar Kabeer kika tsana, sai dai yanayin da kika yiwa Mami magana kamar wata Humairar aka chanja ba ke ba. Idan kin yiwa Raihana wannan dama abokiyar yinki ce, amma ga Mami, kin yi kuskure.'_
Ta tuno kalaman Ummita, wannan na daga cikin abin da ya damu zuciyarta, Mami fa, matar da ta ke ba ta kulawa da zuciya ɗaya. Ta maye mata gurbin Dada da Mamarta wacce ba ta buɗi ido ta gani ba. Ta kuma zame mata abokiyar hira a lokuta da dama idan tana zaune ita kaɗai a gidan. Hakan za ta dinga ba ta labarin Nijar itama ta ba ta na ainahin garin iyayenta wato Agadez su yi ta nishaɗi.
Abu na biyu da ya tsaya mata a rai bai wuce na mamaki da tunanin abin da ta yi ɗin ba. Eh ta san ba ta son Kabeer, ta tsani ma ganinsa, amma tsanar har ta yi yawan da za ta kasa ɓoyewa har haka? Ita kam abin ya sha mata kai.
Tana nan zaune dai ganin ɓatawa kanta lokaci da tunani take yi da b zai magance mata komai ba sai kawai ta maida kai filo a hankali bacci ya sure ra. Duka wannan zaman da ta yi har zuwa kwanciyarta akan idanun Raihana wacce munsharin Tasleem ya hana ta sukunin bacci. Tsoron yarinyar ya ƙaru a zuciyarta, ta kasa kwakkwarar motsi ga fitsari cike fal a mararta amma ina, ga ni take ai tana miƙewa Humaira za ta tashi ta shaƙe ta don ta gama ba zuciyarta cewar iskokai ne da Humairar. A wannan daren dai bacci ɓarawo ne ya sace Raihana.
***
Ta kammala shirinta tsaf kamar koyaushe za ta wuce wurin koyon girki, ta fito falon. Ummita na zaune tare da su Muhsin a falon, Raihana kuwa na gefe ɗaya ta hakimce tana abin da ta saba, latse-latsen waya. Ganin Humaira yasa ta kalle ta sau ɗaya ba ta ƙara ba don ita ba ta so ma su haɗa ido, har ga Allah tun can tana tsoron mai aljanu. Tana kuma shakkar yi musu rashin kunya tun wataran tana jss 2 da wata abokiyar karatunta ta shaƙe ta akan ta zauna a kujerarta ta kuma yi magana amma ta ƙi tashi. Da ta fusata ta shaƙo wuyanta sai da malaminsu ya kwace ta. Abba har makarantar ya je, iyayen yarinyar suka ba da hakuri aka kuma sauya musu aji. Tun daga nan ta ke tsoron duk abin da zai danganta ta da mai iskokai. Ko kusa da su ba ta raɓa.
"Har kin fito kenan?" Ummita ta tambaya tana kallonta fuska a sake. Itama murmushin ta yi.
"Na fito, ina Mami?"
"Tana sashinta." Daga nan ta nufi sashin Mamin, a falo ta iske ta tana waya tana dariya, ganinta yasa ta yi sallama da ɗaya ɓangaren ta ajiye waya. Cike da walwala ta ce.
"Ƴar Mami har an fito?"
Kunya ta kamata, ita kunyar Mamin take ji wallahi, ta karasa ta durkusanta gaida ta.
"To, wata sabuwar gaisuwa ce nan ban da wacce muka yi ɗazu?"
Mamin ta faɗi cikin wasa da dariya, Humaira dake sunne kai ta ɗan murmusa, ita ta manta ma sun gaisa ɗin. Mamin ta ƙara magana.
"Au, ashe gidan Laila za ki ko? Bari ma na ba ki saƙonta ki tafi da shi." Mamin daga haka ta miƙe ta nufi ɗaki, can ta fito ɗauke da leda wacce Humairar ba ta san ma ko mene ba ta karɓa. Ta ba ta kuɗin mota tana fadin.
"Abbanki ya riga ya fita na mance ban karɓar maki na motar ba, ki je kawai idan ya dawo sai na karɓa."
Ta gyaɗa kai ta sa hannu ta karɓa da godiya, ganin ta ƙi motsawa balle ta tashi ya sa Mamin tattaro nutsuwarta gareta.
"Lafiya Humaira? Akwai magana a bakinki ko?"
Gyaɗa kai ta ƙara yi a karo na biyu, cikin nutsuwa kuma ta soma magana.
"Mami dama akan abin da ya faru jiya ne, ina neman gafara."
Murmushi Mamin ta yi ta girgiza mata kai.
"Kar ki damu, ni nasan ba laifinki ba ne. Hakan ya sa na yi maki uzuri. Ki cire komai a ranki kedai ki tattara nutsuwarki ki cigaba da maida hankali ga darussanki. Laila na ta yabon kwazonki don haka ki ƙara dagewa, na maki alƙawarin Kabeer ba zai ƙara shiga sabgarki ba, kin ji ko?"
Sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya ta samun nutsuwa, ta amsa da toh daga nan suka yi sallama ta mike ta fita, Mamin ta bita da kallo tana murmushi.
***
Tuƙi ɗan sahun ke yi cike da nutsuwa, sosai tuƙin ke mata daɗi yayin da iskar dake kaɗawa a garin ke ƙara jefa ta cikin walwala. Damuwar da ta kwana da shi a ƙarƙashin ranta, tas ya wanke ya koma annashuwa. Don haka murmushi take yi ma ba tare da sanin tana yinsa ba. Ba zato ta ji ta yi wani irin hantsilawa sai ga ta a bayan ɗan sahun nan hannayenta rungume a kan wuyansa kai kace wacce aka goyo. Shi kuwa ɗan sahun kansa ya ƙumu da jikin gilashin da karfi har sai da gilashin ya tsage, saura kaɗan adaidaitar ta wuntsila amma Allah ya taƙaita faruwar hakan, sai ya koma baya da ƙarfi har tayoyin na bugun ƙasa da ƙarfi, wannan ya sa ta koma mazauninta, lokaci guda ta saki ƴar guntuwar ƙara sakamakon cikinta da ya bugu da ƙarfen jikin mazaunin direban yake mata zafi dalilin buguwar da ta ƙara yi dalilin komawa baya. Ta runtse idanu daidai sadda ta ji salatin jama'a a kansu. Gaba ɗaya ma ta kasa buɗe idanunta tana dafe da cikinta, ta yi shiru kawai don hayaniyar ma ba burge ta