Showing 66001 words to 69000 words out of 93383 words
motar da ba ta aiki ba, ya kwantarwa da Abban hankali ya nunamasa kar ya damu su Humaira za su kuɓuta a hannun ko ma su waye.
Mami ta dubi Abban a rikice bayan ya gama wayarsa.
"Abban yara sun kiraka ne naji kana sanar da D.P.O?"
Bai kalle ta ba ya ja akwatin jiki na tsuma ya ce.
"Eh Maryama mun yi waya da su. Bari naje kar lokacin ya ƙure mintuna kawai suka ba ni."
Mami ta sha gabansa.
"Meyasa za ka yi ganganci da rayuwar yarana? Mene dalilin sanar da D.P.O? Ba ka tsoron su cutarmin da su?"
Sai ta fashe da kuka jikinta babu inda ba ya rawa.
Abba bai da lokacin rarrashinta sai kawai ya ce.
"Kiyi hakuri, babu abin da zai faru da su lafiya kalau zan maidomaki su in sha Allahu. Ku sanya ni addu'a har na dawo dai."
Yana kaiwa nan ya fice riƙe da muƙullin motar Jannat da Mamin ta aro masa tun jiya an kuma zuba mai dama jiran su kira kawai ake. Tasleem dake laɓe ta yi baya da sauri zuwa dakin Anna jikinta har tsuma yake.
Abba yana hanya ma sai ga kiran Fadeel, Abban ya kwantar masa da hankali ya ce sun yi waya yanzun yana hanyar fita amsar su. Ya tambayi Abban inda suka ce, kamar ba zai faɗi ba sai dai ya faɗamasa. Fadeel ya ce zai biyo bayansa. Dakyar Abban ya hana shi gudun samun matsala.
***
Bakwai da mintuna uku Abba ya iso dab da kogin da suka yi masa umarni. Yana tsayuwa ya ji wayarsa na ringing. Jiki na rawa ya fiddo ya ɗaga.
"Mun ganka, ka fito da jakar ka ajiye gefen wannan kogin, mu kuma za mu turomaka yaranka. Ba ruwanka da kalle-kalle, ka saukar da kanka ƙasa har ka ajiye ka bar wurin."
"Toh."
Yana faɗin haka a gaggauce ya ja jakar ya fita. Bisa bin umarnin nasu kansa yana ƙasa amma fa ta ƴan maza kawai yake sai dai zuciyarsa na ta harbawa da ƙarfi. Sunayen Allah ya shiga ambato da fatan samun matsaya.
Wizzy kuwa da suke can gefe ƙasan wata ƙatuwar bishiya, su na ganin fitar Abban ya sanya Badboy da Babba cicciɓar su Humaira da suka ba su kwayoyi suke ba a cikin hayyacinsu ba suka nufi motar Abban da nufin sanya su ciki. Kiran da Wizzy ya samj ne game da batun zuwan ƴan sanda wurin ya sanya shi fitowa gami da dakawa su Badboy tsawa.
"Ku dawo da su mu bar nan! Shegen ya kira ƴan sanda!"
Jin haka sai kuwa aka soma harbi, dayake Allah ba azzalumin bayinSa ba, sai kawai suka yashe su a wurin sakamakon harbin da aka yiwa Badboy a kafaɗa ya saki ƙara, da gudu suka koma cikin motar kiii suka tayar suka soma yunkurin barin wajen.
Abba da sai kawai maganganu ya ji da ƙarar harbi bai san sadda ya juya ba a ruɗe hantar cikinsa na kaɗawa don ya gama saddaƙarwa su Ummita aka harba. Sai dai ganinsu a yashe a tsakar filin ya sa shi sakin jakar kuɗin ya nufe su da gudun da a shekarunsa bai san ma zai iya ba. Su Wizzy tuni sun bar nan su na cizon yatsar wannan babbar asarar da suka yi. Yayinda D.P.O da mutanensa suka ƙaraso cikin jin zafin kubcewar da suka yi musu.
"Yallaɓai ba kuka ya kamata ka yi, kamata ya yi mu miƙa su asibiti."
Jin haka sai Abban ya ji kamar an masa tuni, ya ɗaga Humaira, macen ƴar sandar da ta biyo su ta ɗaga Ummita suka sanya su a mota sai asibiti. Jakar kuɗaɗen kuma yana cikin motar ƴan sandan suka mara musu baya. Fadeel da ya kasa haƙuri ya biyo bayan Abban, kafin ya kai ga ƙarasawa ya hango Abba a mota kawai sai ya yi reverse ya bi bayansu jikinsa babu inda ba ya kaɗawa. Yana son ya kira Abban don jin ko an same su amma yana tsoron jin akasin haka daga gareshi wannan ne ya hana shi kiran gaba ɗaya.
Murja ta jima tsaye jikin tagar falo tana hangen fitar Fadeel a gigice. Ranta idan ya yi dubu toh ya ɓaci. Hankalinta kuwa idan akwai abin da ya fi gaban tashi toh ta ya yi wannan dalilin ne ya sanya ta komawa cikin daki da sauri-sauri ta ɗauko gyalenta sai ko waya da jaka ta fice daga gidan a birkice har Anti Amarya wacce ta fito daga nata ɗakin tana tambayar ko lafiya kuma ina za ta je amma babu amsa.
***
Kasancewar tare suka isa asibitin da ƴan sanda wannan ya sa a gaggauce aka karɓi Humaira da Ummita zuwa emergency. Abba ya kasa zaune balle tsaye, ban da hawaye babu abin da ke fita daga idanunsa, ga jiri na kwasarsa yana ta ambaton sunan Allah kamar zai ciri baki. Daidai lokacin Fadeel ya shigo a birkice ya ƙarasa ga Abba.
"Abba sun fito? Su na ina? Me ya same su?"
Dukkan waɗannan tambayoyin ba a hayyaci yake yin su ba. Abban ma da ba a wani nutse yake ba sai ya kasa tanka mishi kawai sai ajiyar zuciya da kallo ga lebban na motsi amman ko harafi guda ya kasa fitarwa sai D.P.O ne ya karɓi zancen ya yiwa Fadeel bayani.
"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu babu abin da zai faru garesu. Likitan ya tabbatar mana ga dukkan alamu kwayoyi aka ɗura musu amman in sha Allah za su yi iyakar ƙoƙari a kansu."
Fadeel ya dafe kansa ya yi juyin, ya yi safar ya dawo ya kai marwar amma wannan kalmar ta ya kwantar da hankalinsa ya kasa samun matsaguni a zuciyarsa. Kwayoyi? Ya ma rasa inda zai jefa zancen a kwakwalwarsa ballanta ya samu ya yi aiki da shawarar D.P.O Salahuddeen.
***
A can gida kuwa, Tasleem tun sadda ta kai labarin tafiyar Abba fanso su Humaira, Jannat ta dauki waya hankali tashe ta kira Bokanta. Kaca-kaca suka yi sosai tana zaginsa akan ita fa ba su yi haka ba. Wannan ya sa Boka tun a wayar ya ci alwashin sai ta girbi wannan tozarcin da ta yi masa. Kasancewar idanunta sun rufe ruf sai kawai ta ja mugun tsaki ta katse kiran.
Awa bai fi ɗaya tsakani ba, sai ga wayar Abba zuwa ga Mami, a gaggauce ya sanar da ita kuɓutar su Ummita ya kara shaida mata cewar su na asibiti. Hankali a mugun tashe suka fice tare da Ƙasim da Raihana wacce lokaci guda wani mugun zazzaɓi ya rufe ta musamman jin cewar su na asibiti. Suka yi kiciɓus da Kawun Humaira da matarsa Hajjo wadanda isowarsu kenan garin. Ba su tsaya yi musu dogon bayani ba, Kawu ya bi su yayinda ya ce Hajjo ta tsaya ta jira dawowarsu a gida.
***
BAYAN AWANNI...
Mummunan labarin da ya iske su Abba na keta alfarmar da aka yi ga Ummita ya sanya shi sumewa bai ko iya jin ƙarshen ba balle ya san ko har Humairar ma an taɓa. Nan aka kwashe shi shima don ba shi taimakon gaggawa. Raihana kuka kamar ranta zai fita yayinda Mami ke taya ta. Kawu da Fadeel kuwa tashin hankalin da suke ciki ba zai misaltu ba. A gabansu aka fiddo su bayan an yiwa Ummita ɗinki na mugun raunin da aka ji mata aka sauya musu ɗakunan zuwa na hutu, daki mai gado biyu. Fadeel ya ƙurawa Humaira idanu kamar kirjinsa zai fashe haka yake ji, nan take idanunsa suka kaɗa jawur. Gaba ɗaya ta lalace ta yi rama tamkar wata halittar ce ba ita ba sai ko hancinta da ya ƙara fitowa. Har aka shige da su bai iya kauda kansa ba. Shi ya yi ƙarfin halin biyan dukkan abin da aka kashe har da na kama ɗaki.
Cikin ƙanƙanin lokaci labarin kuftowar su Humaira ya cika gari, mutane da waɗanda suke dangi da ma yan uwa na gari suka dinga tururuwar zuwa yi wa su Abba barka, babu wanda aka bari shiga wajensu, hakanan labarin abin da ya afku gare su bai fita ba. Yan jarida kuwa suka dinga yaɗa rahoto, hakanan social media ta dauka. Futuha mutanen Dubai ta ƙara yin bidiyo mai nuni da damuwa da kuma farin ciki tana shaida wa jama'a cewa an ga ƙannenta. Nan aka hau taya ta murna sosai.
Mutanen Bichi da labari ya iske su su ma baa bar su a baya ba. Anti Maijidda ta yi kuka kamar ranta zai fita jin labarin keta haddin da aka yi ga Ummita, matsayinta na babbar yaya ga uwarta ya sa Abba sanar da ita a sirrance.
Sahabi kuwa baki har kunne, sun zo shi da abokansa yayinda mahaifinsa takanas ya zo ya taya Abba murna da addu'ar Allah ya kiyaye gaba.
Kwanakin su Humaira biyu suka dawo hayyacinsu. Ummita ce ta soma farfaɗowa, ranar Allah ya taƙaita Anti Maijidda na zaune tare da Baba Amina sun yi jugum su na dan hira jefi-jefi hannuwansu riƙe da casbaha. Wani gigitaccen ƙara Ummita ta saki da ya yi masifar tayar da hankulansu.
"Wayyo Allahna! Kar ka kashe ni! Ka rabu da ni! Na haɗa ka da Allah ka rabu da ni!! Wayyo Allahna!!!"
Cikin kuka da tashin hankali suka yi kanta su na riƙewa, aka bankaɗo ƙofar aka shigo, su Abba ne da ihun Ummita ya iske su. Raihana a guje ta nufi wurin Nurses dake tahowa, kafin ta kai ga magana suka ce sun ji. An tafi kiran likitan. Su na shiga sai ga Likita, aka fitar da kowa a ɗakin.
Gaba ɗaya matan kuka sosai babu kamar Raihana da take jin kamar ta shiɗe. A yadda take jin zuciyarta za ta iya fille kan wanda ya aikata wa yan uwarta wannan tozarcin.
Koda likitan ya ƙarasa gareta flask din ruwan zafin dake ajiye a gefenta kawai ta ɗauka ta jefa masa. Ba don Allah ya sa shi kaucewa ba da babu abin da zai hana a same shi.
Tana cikin wannan gigitar Humaira ta farka a matukar firgice, ta kira sunan Ummita da karfi sannan a guje ta diro ta zo ta rungumeta tana kallon jama'ar ɗakin kamar wasu sabbin halittun da ba ta taɓa gani ba.
"Su waye ku? Me za ku yi mana?! Ku fice ku bar nan! Wallahi ku ka yi ƙoƙarin zuwa kusa da mu zan ji maku ciwo."
Sai kuma ta juya a mugun firgice tana tattaɓa jikin Ummita dake kuka kamar ranta zai fita.
"Ummita! Yi shiru, Abba zai zo. Naji suna cewa yana hanya. Yi shiru, sai mun kashe su."
"Kin.."
Likitan ya ƙaraso zai soma magana Humaira ta juya da azama tana nunashi da yatsa. A sannan su Abba gaba daya sun shigo sun kasa daurewa.
"Kar ka taɓamin ƴar uwa! Zan kashe ka!!"
"Humaira, Ummita."
Humaira na ganin Abba ba ta ko damu da sauran jama'ar Abba ta karasa a guje ta rungume Abba tana kuka mai tsuma zuciya.
"Abba za su kashe mu! Abba ka cece mu! Ka ɗauke mu mu bar nan!"
Irin riƙon da ta yiwa Abban ba na wasa ba ne har maɓallan wuyar rigarsa sai da suka fita.
Cikin hawaye ya ce.
"Mamana babu abinda za su yi maku, likitoci ne. Kun kuɓuta daga hannun azzalumai. Ki kalla dakyau, ga Maminki ga yar uwarki Raihana. Kin gane Kawunki?"
Ta tsaya cak kamar wata sokuwa tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Ummita kuwa da nos ta lallaɓa ta yi mata allura tuni bacci ya kwasheta. Kawai sai ta soma ruwan wasu sabbin hawayen ta ma kasa cewa uffan. Zuciyarta ta gasƙata eh sun kuɓuta daga hannun azzaluman, amma kuma ta ji tana tantama tana gani ko mafarki ne. Wannan ya sa Raihana tahowa da sauri ta rungumeta ta kara sautin kukanta.
A hankali ta ɗaga hannunta ta ɗaga fuskar Raihana ta na kallo kamar wata baƙuwar halitta ce gabanta, sai kuma da rawar murya ta ce.
"Raihana ce?"
Raihana saboda ƙarfin kukan ma ta kasa magana sai kawai ta ɗagamata kai. Humaira ta rungumeta sosai suna kukan tare.
"Amm, don Allah a ragu a ɗakinnan. Alhaji ina son magana da kai."
Fadin Likita, ganin haka duk aka fice banda Raihana wacce Humaira ta riƙe hannunta gam tamkar ita kaɗai ta gani.
***
Likita ya dubi Abba cikin nutsuwa ya soma magana.
"Lamarin ita Ummita na buƙatar rarrashi da ja a jiki. Kaso casa'in na ire-irenta da hakan ke afkuwa a kansu sukan samu matsala ta rudani, firgici da kuma rashin yarda ga kowa. Wasu kuma yakan taɓa musu kwakwalwa. Zamu yi mata gwajin kwakwalwa don a tabbatar da komai na ta lafiya kalau yake."
Abba ya share fuskarsa.
"Toh Likita, nidai babban burina lafiyarsu. Allah ya sa komai lafiya."
"Ameen." Ya amsa cikin tausayawa yana mai lallaɓar Abba.
***
Cikin iko na Ubangiji an yiwa Ummita gwajin kwakwalwa kuma an tabbatar da komai lafiya. Wannan ya kwantar da hankulansu. Humaira dai ba ta dogon magana tun farkawarta, kowa ta gani sai dai ta ambaci sunansa, idan an rungumeta an sa kuka itama ta soma. Da daddare ba bacci sai razana, ga Ummita haka. Wannan yasa aka raba musu ɗaki. Fadeel na zuwa, kuma abin mamaki Humaira na ganinsa ta kira sunansa, abin sosai ya ji dadinsa ya kuma tsaya a ransa.
Sai da suka kwashe sati biyu a asibiti kafin su tattara su dawo gida. Babu laifi sosai zuwa lokacin sun samu nutsuwa ba kamar farko ba. Sai dai daga Ummitan har Humaira duk sadda tunanin cin zarafin da aka yi musu da kuma keta haddin da aka yiwa Ummitan sai su yi ta kuka. Har zuwa lokacin babu wanda ya san da mummunan labarin sai ko Anti Maijidda da Mami wadanda Abban ya faɗawa.
Anti Maijidda nan fa ta dage akan lallai sai a ba ta Ummita su tafi Bichi, Abba ya ƙi amincewa. A dole ta haƙura ta tafi tana ƙunar rai da jin tsanar Mami har cikin ƙoƙon ranta.
Jannat ko a fuska sai ka rantse nan jimamin duniya take yi akan lamarin don ba ta nuna komai wanda zai sa wanda bai sani ba ya fahimci takun saƙarta da su. Hakanan Anna wacce ta daurewa zuciyarta ta taka har ɗakinsu ta duba lafiyarsu bayan ta je asibitin a baya har sau uku. Wannan ya wanke ta daga zargin mutane da rashin nuna kauna ga su Humaira a baya.
***
*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Sai da su Humaira suka samu sati hudu cif kafin su ɗan maido da jikinsu, da kuma walwala kaɗan. Sukan zauna cikin jama'a, a taɓa hira da su idan ka cire Ummita da har lokacin ta tuno aika-aikar da aka yi mata sai kawai ta fashe da kuka wanda hakan ke tayarwa Humaira hankali itama ta sa nata kukan sai su haɗu su yi ta yi. Kawun Humaira ya so su koma can Nijar da ita amma nan ma Abba ya nuna sam bai amince ba dole haka ya tattara matarsa suka koma gida.
Su na zaune a ɗaki, Ummita riƙe da Alƙur'ani tana karantawa zuciyarta na yin sanyi yayinda Humaira ke kwance saman katifa ta yi shiru gami da zubamata idanu kusan ma hankalinta ba a kanta yake ba, ta lula wata duniya ta daban na tunani. Raihana ta shigo ta iske su haka, dawowarta kenan daga makarantar boko wanda har lokacin Ummita ta ƙi amincewa ta koma ganin haka babu wanda ya takura mata shi ma mai makarantarsu da ya zo har gida ya jajanta ya ce a kyale ta zuwa wani lokacin.
"Wash! Wallahi na gaji! Ke kuma kina da baƙo a falon Abba."
Ta faɗi da murmushi tana duban Humaira duk a ƙokarinta na son ta ga komai ya dawo daidai a mu'amalarsu. Humaira ta ɗan dube ta gami da ɗan haɗe gira kaɗan.
"Wa kenan?"
"Fadeel."
Ta yi shiru, ita ba ta ce uffan ba balle ta yi wani yunƙurin kawai sai ta maida kai ta kwanta ta yi shiru. A karan kanta ba za ta ce ga abin da take ji game da Fadeel din ba, lamarin dai ba yabo balle kuma fallasa. Ummita na ji ba ta iya cewa komai ba, Raihanar ma ba ta sake magana ba sai ta miƙe ta rage kayan jikinta ta shiga wanka, ba ta son duk abin da zai takurawa rayuwar ƴan uwannata da ta ƙara sanin girman ƙauna da shaƙuwar da ke tsakaninta da su bayan sun yi mata nisan da ta zaci har abada ba za ta ƙara sanya su cikin kwayar idanunta ba.
Ummita tana kai wa ƙarshen surar da take karantawa ta juya ta dubi Humaira.
"Ki je ku gaisa mana."
Humaira ta yi mamakin jin wannan furucin naga bakin Ummita, tun bayan dawowarsu ba ta wani magana kwakkwara, ko hirar Raihana ke jansu da shi, sai dai ta basar ta yi shiru. Wannan murmushin da ba ya barin fuskar Ummita, babu shi babu labarinsa tun dawowarsu. Ita ɗinma ƙarfin hali take yi don faranta ran Mami da su Raihana ga kuma Ƙasim waɗanda gaba ɗaya suke nuna musu kulawa da ƙoƙarin ganin sun saki jikinsu.
"Kin ji?"
Maganar Ummitan ya ƙara katse mata tunani. Tana so ta ja musu amma a yanzun duk duniya babu abin da ta ke so irin ta ga ƴar uwarta ta dawo tamkar yadda ta ke rayuwa a baya. Abu na biyu kuma ta sani ba ta jin za ta iya ɗaukar waya ta kira shi da zummar godiya bisa hidimar da ya yi akan fitowarsu, don ko cikon da suka bayar na kuɓutar da su a hannun ƴan fansa ƙin karɓa suka yi da Abban ya maida musu, ta sani wannan ita ce damar ta amma hakanan ba ta son Fadeel din ya cigaba da shigemata shiyasa.
Abban har gidansu ya je ya ƙara godiya sosai shi da Mami wacce a sannan ne ta ga gidan da ya kere na Aminiyarta Hajiya Lubna.
Ganin Ummitan ta zubamata idanu ya sanya ta miƙewa.
"Toh, na ji Ummita."
Ta faɗi kamar ta fashe da kuka sai ta miƙe ta ɗora hijabi akan doguwar rigar atamfar da ke jikinta.
Suka ci karo da Mami a falon wannan ya sanya ta tsayawa.
Gidan yanzu duk an watse sai su kadai, Jannat ta tattara ta koma bayan dogon kiran da mijin ya dinga danno mata har abin ya