Showing 3001 words to 6000 words out of 93383 words
a cikin matasan ya furta yana dubanta, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla.
"Kai Yassar, bana son haka. Sannu da zuwa Humaira, maza Ummita kai ta ɗakinku ta yi wanka lokacin sallah ya gabato."
Da sauri na kalli matarnan, na sha mamaki ganin kamar ba ita ba, ta saki fuska sosai tana murmushi har haƙorin makkanta ana gani. Har Ummita ta faɗi saƙon Abba, Humaira ba ta iya tankawa ba hakanan ba ta iya ɗauke idanu daga kanta ba, itama jefi-jefi tana magana da Ummita tana kallonta ta kuma rasa dalili. Har Humaira ta bi bayan Ummita zuwa ɗaki ba ta daina waigenta ba, kuma itama Mami ta ƙi matsawa balle ta dauke ido a kanta.
Ita kam Humaira jikinta ya ba ta kamar akwai wani abu.
®️Rufaida Umar.
02
A hankali ta bi kowace kusurwa a ɗakin da ido, gado ne kananu har hudu kowanne a nashi wurin, a gefen kowane gado akwai sif na kaya kamar dai ɗakunan makarantun kwana, babban daki ne mai yalwa wanda har akwai gurbin da ire-iren gadon uku za su samu matsuguni. Daga can gefe jikin taga kuwa, ƙaton madubi ne a saman dirowar gaban cike da kayayyakin kyalkyali na adon fuska da mayuka. Dakin tsaf-tsaf babu ƙazanta, ɗakin ƴanmata kenan. Ummita ta ɗaga akwatin tana shirin ajiyewa saman ɗaya daga cikin gadajen nan, baki bude tana kallon Humaira da niyyar magana, aka daka mata wani uban tsawa daga baya.
Muka juyo, wannan dai budurwar ce ta ɗazu mai ƙibar ciki. Ta zo da sauri ta janye akwatin ta yi wurgi da shi gefe. Idanu cike da masifa ta soma magana.
"Wallahi kar ki kara gangancin ajiyemin jakar wannan korar yunwar a gadona, don gulma da kinibibi idan abin naki dagaske ne meyasa ba za ki ajiye a naki gadon ba. Aikin banza kawai, uwar shishshigi. Haka za ki ƙare."
Tana kai wa nan ta fice daga ɗakin tana mita, Ummita ta kalli Humaira gami da jifanta da murmushin yaƙe.
"Ki yi haƙuri."
Ta gyaɗa mata kai tana maida mata martanin murmushin sai dai can ƙasan ranta, tana maimaita kalmar da ta ambata "Korar Yunwa". Ta fahimci manufarta tsaf, ta kuma gane ko wace ce ba ta samu karɓuwa a wajenta ba. Koda dai, ba ma ita kaɗai ba, ta lura da irin kallon da Mami ta watsamata. Ko ya zamantakewarta a wannan sabuwar duniyar za ya kasance?
"Hey, tunanin me kike? Amm..nidai bari kawai na kiraki da Humaira, kinga babu damar ce maki Aisha kai tsaye saboda sunan Umman Abbanmu kika ci ko? Hakan ya yi?"
Humaira ta gyaɗa kai karo na biyu tana mai sakin fuska, ta lura Ummita akwai kirki. Bandaki ta nuna mata, ita kuwa ta yi godiya, har za ta shige ta dakatar da ita.
"Yauwa Humaira ga wannan zanin ki yi amfani da shi ki goge jiki."
Ta sa hannu ta karɓa, zani ne a wanke a goge. Ummita har ta kama hanyar fita sai kuma ta dawo ta shiga bandakin gami da ba ta umarnin ta bi bayanta. Su na shiga ta kunna mata famfo gami da faɗin amfanin kowannensu. Ta fiddo mata sabon sabulun wanka daga cikin wata ƴar kwaba dake a gefe jikin bangon, sai kuma ta tambayeta ko ta taho da soso, Humaira ta amsa da eh. Hatta da ƙofar banɗakin sai da Ummita ta nuna mata yadda za ta ƙulle kuma ta buɗe, daga haka suka fito, nan ma sai da ta ajiye mata dardumar sallah saitin gabas sannan ta fice ita kuma ta ciro sosonta a akwti ta koma banɗakin ta rufe.
Wanka ta yi gaba ɗaya ta ɗauro alwalar Magriba, koda ta fito wannan budurwar ta ɗazu tana zaune gefen gadonta tana waya, suna haɗa ido ta bita da harara ba shiri Humaira ta kauda kai. Idanunta ya kai ga akwatin kayanta, ƙarasawa ta yi ta buɗe sai dai gaba ɗaya ba'a nutse take ba sakamakon idanun wannan budurwar a kanta suke duk kuwa da wayar da take amsawa. Turanci zallah take zubawa har wani shagwaɓa take yi tana dukan gadon, kalmar I Lobiyun da ta ce yasa Humaira ta fahimci koma dai wane ne toh masoyinta ne. Ba ta ko ƙara kallonta ba gudun ganin abin da zai sosa zuciya, ta fiddo doguwar rigarta ta yadi ta warware ta zura. A gurguje ta ciro hijabinta, ta linke kayan da na cire na ajiye daga saman akwatin. Ba ta jima da tada salla ba sauran ƴanmatan nan biyu suka shigo suka cika ɗakin da hayaniya, rabin hirar tasu da harshen turanci suke yi. Koda ta idar ba ta iya nutsuwar jan addu'a mai tsawo ba, ta yi istigfari da hailala da salati ta shafa. Zama ta cigaba da yi anan ba tare da ta miƙe ba gudun ma kar ta yi wani abin ya jazamata baƙar magana. Hankalinta yana ga Abbanta wanda take da tambayoyi birjik da za ta yi mishi a kwakwalwarta. Eh yana sonta yana ƙaunarta, amma meyasa bai ƙara waiwayarta ba, meyasa ba ta taɓa ganinsa ba? Meyasa kuma koda a waya bai kira domin su gaisa ba? Dukkan wannan rashin kulawar nasa da ba ta samu ba, ace yana kaunarta ya kuma damu da itq? Ita kam tana son sanin amsar da zai fito daga bakinsa.
"Ke Indo."
Ta ɗaga kai ta dube su kawa, suka kwashe da dariya.
"Kai Raihana ba ki da kirki wallahi, au ba ma za ki kirata Humairar ba sai Indo ko?"
Wacce aka kira da Raihana ta yamutse fuska.
"Aa, ina ce sunan Umma gareta, tunda kaka ce ai ko Indon ma da na ce ta gode min. Ku ni ba wannan ba, wallahi mu tashi mu yi magana fa tun kan a ƙaƙaba mana ita a ɗakinnan. Ni wallahi tsoro ma take ban. Mu faɗawa Granny ta yiwa Abba magana don Mami ba za ta goyi bayanmu ba."
Humaira ta kalle ta dakyau, doguwa ce kamar dai Abba, don ta fi Maminsu tsawo, Mamin ba ta da tsawo sai jiki kuma gajeriya ce. Fara ce tas itama kalar buzayen, gashinta da ya sha kalba ya sauka har gadon bayanta, riga doguwa ce ƴar kanti ta sa mai kama jiki.
"Kallon me kike yimin kamar wata mayya? Kar ki ji ance wai wani ke ƴar Abbanmu ce ki yi ƙoƙarin haɗa kanmu da ke, wallahi kar ki kuskura don bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne, atoh. Gwara ma Abban ya zo a yi meeting ɗin a bambance tsakanin aya da tsakuwa."
Duka wannan bayanin daga bakin Raihana su ke fitowa, Humaira ta sauke idanunta a hankali zuciyarta na zafi, dagasken dai ba ta samu karɓuwar kenan ba, zuciyarta na da ƙarfin jure abu idan har wanda ya fi ta a shekaru ne ya aikata gareta, amma ba ta jin za ta iya ɗaukar wannan rainin wayon.
"Futuha mene ne haka wai? Meyasa kullum burinku ku tozarta mutum?"
Maganar Ummita ya sanya Humaira ɗago kai, ashe wai akwatinta wacce aka kira Futuha ta nufa ta buɗe. Ita dai wacce ke faman waya tun ɗazun.
Ai kuwa kamar an mintsile ta haka ta miƙe tsaye a zafafe, ta ƙarasa daidai sadda Futuha ta ɗaga akwatin da niyyar doka shi da ƙas, da wani irin zafin nama ta ture ta, daga ita har akwatin suka faɗi, akwatin ya faɗa saman gado, ita kuwa ta yi rashe-rashe a ƙasan gadon bayan ƙugunta ya bugi katakon. Ai kuwa ta kurma ihu, Raihana da ɗaya budurwar da Ummita ta ambata da Tasleem suka yo kai Humaira gadan-gadan, Ummita ta tare su. Ita kuwa Humaira ko a jikinta ta nufi akwatin ta shiga harhaɗa kayan da suka zube tana maidawa lokaci ɗaya hawayen da ta fi zaton na ɓacin rai ne, su na kwaranya. Ya yi daidai da faɗowar Maminsu ɗakin wanda hakan bai wuce sanadiyyar ihun Futuha da ya mamaye ilahirin ɗakin ba. Jin muryarta da ta yi sai da gabanta ya faɗi, ta rasa dalilin da yasa take jin haka a kanta. Ta shiga ambaton sunan Allah a ƙasan ranta.
"Lafiya? Me nake gani haka kamar waɗanda aka ƙwato daga bakin kura? Ke Ummita sake ta, kyale su na ga gudun ruwansu. Au, don ku nuna mata rashin tarbiyyarku ba komai ba ne ba ko? Har kun soma yada halin?"
Tana maganar ne fuskarta a murtuke tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, ita dai Humaira sam ba ta tofa ba sai ci gaba da tsince kayanta da tayi tana harhaɗawa tana mayarwa ciki. Ba ta san ma'anar juya harshe zuwa wani can daban da ba ta sani ba, ta dai ji Mamin a cikin yare ta yi musu magana wanda ba ta fahimci koda harafi guda a ciki ba, sai gani kawai ta yi duka sun fice daga ɗakin idan ka cire Ummita da ta durkusa tana taya ta haɗi da ƙara ba ta haƙuri. Tana niyyar amsawa Ummita ta ji an shafa kanta, ta runtse idanu ba tare da ta ɗago kai ba don tasan Mami ce.
"Ki yi hakuri kin ji Humaira, su Tasleem su na da irin wannan halayyar na son yiwa baƙo shaƙiyanci. Kinga yau ki ka zo kuma kafin su karɓe ki za'a ɗan kwana biyu, a hankali idan sun gane ke ɗin ɗaya ce a cikinsu komai zai wuce kin ji ko? Ki ɗauke ni madadin Uwa, don mahaifiyarki mun yi zaman mutunci da nutunta juna da ita. Kema kuma nasan muddin dai kyawawan ɗabi'unta kika kwaso, ba za mu samu kowace iriyar matsala ba. Ina fatan haka?"
Jin bayanan Mamin sai ta tsinci zuciyarta da yin sanyi, ta ji lokaci guda kaso saba'in na fargabarta akan Mami ya ragu, wannan furuci nata na madadin Uwa, ba ta jin za ta iya kwatanta daɗin da ya sanya ta. Kai ta gyaɗa alamar toh, Mamin ta maida dubanta ga Ummita.
"Sai ku hanzarta ku fito ta ci abinci daga nan zuwa bayan sallar isha'i, Abbanku na neman mu duka."
"Toh Mami." Faɗin Ummita cike da girmamawa. Daga haka ta fice ta bar mu. Ummita ta kalli Humaira da murmushi saman fuskarta.
"Sai fa kin yi hakuri sosai Humaira, da gaskiyar Mami, dama ya lafiyar giwa balle an jefe ta da kashi. Su Tasleem ba su da kirki, har gwara su Yassar a kansu, don su ba su kunyar ido, za su yi maka abin da suka so. Ki yi hakuri don Allah. Nima haka nake fama da su, don ma dai babu yadda suka iya da ni ne, Mamin na taka musu burki sosai a kaina."
Jin haka ta ji ta sosamata inda yake mata ƙaiƙaiyi. Aikuwa ta kasa shiru sai da ta furzar.
"Yauwa nikam Ummita, amma ba Mami ce ta haifeki ba ko?"
Ummita ta yi dariya.
"Kin gan ni ƴar baƙa ko?"
Sai kuma ta gyaɗa kai ta ɗan sauya fuska alamar damuwa.
"Ba Mami ce ta haife ni ba kuma ba Abba ne mahaifina ba. Mahaifina ƙanin Abba ne, mahaifiyata kuwa ƴar asalin garin Bichi ce, gaba ɗaya sun rasu ne a sanadiyyar gobara. Ni kaɗai ce rai da aka fitar a gidanmu ko kwarzane tun ina da shekaru biyar a duniya, amma daga su har ƙannena jarirai ƴan biyu duka sun rasu. Tun daga wannan lokacin ne, na soma rayuwa a hannun Kakarmu sai daga baya ne Abba ya maido ni gidansa ya damƙa amanata ga Mami. Matar da ta riƙe ni har zuwa yau ba tare da ta nuna bambanci tsakanina da nata yaran ba, kusan ince a zamanin dai samun irin Mami abu ne mai wahala. Ga kirki da son mutane, ke ba don dai kar nayi hauka ba zan iya ce maki Mami ta fi nunamin ƙauna da so fiye da nata yaran domin hatta da ragamar kula da ɗakinta da na Anna ni ta damƙawa. Ke daidai da shawara wani lokacin da ni take yi. Sai ta ture shawarar nata yaran ta ɗauki nawa."
Jinjina kai Humaira ta yi, eh lallai kam Mami ta yi abin a yaba mata, a zamanin nan kafin a samu mai fifita ɗan wani akan nashi abu ne mai matuƙar wahala.
"Wace ce Anna?"
Humaira ta watsa mata tambayar. Ta miƙe ta shiga rufe akwatin a lokaci guda tana ba ta amsa.
"Anna kakar su Tasleem, wacce ta haifi Mami. Ai anan gidan take rayuwa, a baya ma har da ƙanwar Mami da ba ta yi aure ba muka zauna. Amma yanzu Allah ya taimaka tayi aure tana zaune a can Misra da mijinta, ke kam ai Allah ya taimake ki ba za ki rayu inuwa ɗaya da ita ba. Don ta fi su Tasleem zafi da tsangwama, ke ta dai tsani duk wanda ba jininsu ba. Hatta da dangin Abba ba ta kaunar gani a gidannan, sai kuma Allah ya sa su ɗin ma ba su fiye zuwa ba."
Humaira ta buɗe baki za ta yi magana kenan sai ga wani ƙaramin yaro cikin yara ƙananu uku da ta gani ɗazun ya shigo a guje. Masha Allah yaron kyakkyawa duk kuwa da cewar bai ɗau hasken Mamin sosai ba, ya fi yin kalar Abba, amma kuma hakan ma sai ya ƙara mishi wani kyan na daban.
"Adda Ummi ku zo inji Mami."
Ya kai ƙarshe yana nuna su duka biyum da yatsa, alamun dai mu biyun ake nema. Sai ma ya ba Humaira dariya. Suka miƙe a tare zuwa falon. Ko ɗaya ba abokan faɗan nata a ciki, bada ɗayansu ba sa nan sai Mami da yaran, sai kuwa ɗaya a cikin matasan nan na ɗazu kwance saman doguwar kujera ya toshe kunnuwa da earpiece.
Suka ƙarasa ga Mamin, ta zauna a gefe a ƙasa. Duk yadda Mamin ta so ta hau kujerar ta ƙi, haka dole ta rabu da ita. Ummita ta kawomata abincin amma gaba ɗaya ta kasa sakewa balle ta ci, ƙarshe dole dai ɗakin suka yi da abincin bisa umarnin Mami. Nan din ma dai kaɗan ta ci ta ce ta ƙoshi. Hankalinta kuma ya koma ga Kawu da Abba, ba ta gaji da ganin Abba ba, ba ta kuma gaji da jin muryarsa ba. So take ta samu damar da za su yi doguwar hira da shi, tasan dai ba yau ba domin dare ya yi.
Suna nan da Ummita tana ƙara ba ta labari akan zuri'arsu har lokacin sallar isha'i ya yi, koda suka idar kai tsaye falon Abba suka nufa sakamakon kiran da ya yi musu. Nan suka tarar shima Kawu har ya ci abinci ya yi wanka, hirarsu kawai suke yi da Abba wanda shima ya sha doguwar jallabiya ruwan madara. Har Humaira ta zauna kallonta yake da murmushi saman fuskarsa kafin ya maida duba ga Kawu ya girgiza kai.
"Allahu Mai Halitta." Kawun shima murmusawar ya yi, ita kam sai ta yi kasa da kai. Zamansu ba jimawa sai ga Mami ta shigo ta lulluɓe jikinta da ƙaton mayafi. Sai da ta zauna ne ta dubi Kawu.
"Umar, kwana da yawa. Idan babu Fatima a gidan shikenan kuma sai zumunci ya yanke? Dama kun raba ni da ɗiyata, toh dama ƙarshen alewa ƙasa, ka ga yau dai ungulu ta komo gidanta na tsamiya."
Kawu ya yi ƴar dariya.
"Hajiya Maryam kenan, idan dai kin yarda kin amince da komai lokaci ne, ba za ki ga laifinmu ba. Sai dai kamar yadda kika ce, na yi kuskure kuma na ji kunya da ban tashi zuwa ba sai bayan babu Adda Fatima, Allah ya gafartamusu. Ina kuma neman afuwa."
Gaba daya suka amsa da amin. Abba ya yi gyaran murya ya dubi Mami.
"Ina yaran nan suka shiga ne wai?"
"Su na can wurin Anna, na rasa me suke yi alhalin na sanar da su. Bar..."
Ba ta ƙarasa ba sai ga su sun faɗo ɗakin kamar daga sama, babu ɗaya cikinsu da ya yi tunanin yin sallama. Yaron ɗazu ne da ya je kiranmu ya shigo a guje ya rungume kafaɗun Abba, wani da ya fi shi tasawa yana biye da shi a gujen. Sai kuwa su Tasleem da samarin nan uku.
"Kai Muhsin, me ya yi maka ne?"
Wanda aka kira Muhsin ya turo baki ya nunawa Abba bindigar ruwa da aka raba gida biyu.
"Ba shi ne ya karyamin bindiga ba. Allah kuwa sai ya biya ni."
Abba ya ja hannun karamin mai suna Waleed ya maido shi gabansa.
"Haba Autan Mami, ya haka? Ba shi hakuri toh."
Da dariya irin na yarinta ya furta kalmar sorry. Abba ya maida idanunsa ga su Tasleem waɗanda suka yi ɗare-ɗare saman kujera ba su ko gaisar da Kawu ba. Fuska ya ɗan ɗaure.
"Ba ku iya gaisuwa ba ne?"
Jin furucin Abban ya sa suja gaida Kawu ciki-ciki, ba tare da jin komai ba ya amsa har da nema musu albarkar Allah. Babu wanda ya amsa da amin a cikinsu. Mami ta kalle su ta yi musu alamar su sauko ƙasa su zauna, ba a son ransu ba dole suka zaune a ƙasan kafet kamar dai yadda Humaira da Ummita suka yi. Sai dai Abba ya buɗe taron nasu da addu'a sannan ya gabatar da Humaira a wajensa. Ya kuma gargaɗe su da kar su kuskura ya ji wani zance na daban koda nuna bambanci ne. A karshe ya sa kowannensu ya gabatarwa da Humaira sunansa. Su tara ne cif, Mubarak ne babban ɗan Abban, shi kuwa yana ƙasar Ghana yana karatu, sai Dawud, Yassar, Ƙasim, Futuha, Tasleem, Raihana, Muhsin da autansu Usman da ya ci sunan baban Mami suke kiransa Waleed.
"Humaira toh, yanzu dai ba wanda ba ki sani a ƴan uwanki ba ko? Sai babban yayanku shi kam sai ranar da ya samu hutu idan ya dawo sai ku gaisa. Ko kuma ma ina iya haɗa ku a waya wataran."
Jin abinda ya fadi ya sa ta murmushi, ta gyaɗa kai tare da furta toh. Daga haka Abba ya sallame su baki ɗaya suka tashi.
A wannan daren dai ba ta samu damar hira da Abbanta ba, ta koma ɗakin da ba ta kauna dalilin yadda suka kaya da masu ɗakin. Mami ta sa aka yi mata shimfiɗar katifa a ƙasa kafin nata gadon da sif ya iso, acewarta. Hakanan ta kwanta, mutanen ba su ƙara tanka mata ba musamman ma Futuha da ta sha ƙasa har lokacin ƙugunta na ciwo. Sun dai sha jinin jikinsu, sun kuma fahimci Humairar ba kanwar lasa