Showing 51001 words to 54000 words out of 93383 words
wannan saboda ɗiyarki ta yi nisan da ba ta jin kira. Ita mai miji, burinta ta nunawa duniya ta fi kaunar ɗa wani sama da nata yaran. Idan kin ji yanda yarannan ke ƙorafin nuna halin ko in kula da take yi musu sai ki rantse ba ita ce ta yi naƙudar su ba a bola ta tsinto su. Babu ma kamar su Yassar wadanda su ubansu bai sakarmusu sun ji dadin rayuwa irin na matasa sa'anninsu ba, su ba su sami wata kyakkyawar kulawa a wurin uwar ba. Ni na rasa irin wannan gidan da rayuwar cikinsa. Ba haka nake rayuwa a gidan nawa mijin ba, shi koyaushe burinsa ya wadata mu da abinda za mu huta ni da yaransa, amma tun da na rayu a gidannan har na yi aure, mijinta bana jin ya kashemin sama da dubu ɗari biyar a rayuwa."
Mami ta miƙe tsaye tana duban Jannat, zuwa yanzu ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci.
"Ya isheki hakanan! Ke tsabar rashin kunya har kya kalli kwayar idanuna ki faɗan magana? A gidan dai da kika raina nan kika rayu sannan ko Yusuf bai kashe maki sama da kuɗaɗen ƙaryar da kika buga lissafinsu ba, ai kin ci kin sha daga jikinsa. Ke yanzu idan da kina can wannan dajin kina rayuwa, har kin isa ki ga shi mijin da kike tutiya da shi ki aura? Ni na isheki! Nan da kike ganina kar nake, na fi ku sanin inda ke mini ciwo. Ba damuwarki ba ce kuma balle ki sani, idan har ba za ki dauke idanu daga lamuran gidana ba, ki tattara ki..."
"Maryama!" Tsawar da Annan ta bugamata ne yasa ta yin shiru tana fesar da huci mai zafi, ta kalli Anna sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. Jannat nan ta haukacewa Anna wai Mami ta yi musu gorin zama a gidan don haka su tattara su bar mata gidanta. Anna dai ta dinga lallaɓa Jannat, ta sani muddin ta bi cewarta ta bar gidan to fa komawa can wani ƙauyensu dake garin Agadez ya kamata, yanda ta fito ta ɗanɗani rayuwar daula koda ace bai kai yanda ta ke so ba, ta gwammace ta cigaba da rayuwa a nan. Ta sani babu ta yanda za'a yi shegiyar surukar zamani irin ta Jannat ta amince da zamanta a gidan ɗanta. Dakyar dai ta samu Jannat ta janye ƙudurinta, tsana da haushin Humaira ya ƙara ninkuwa a ƙasan ranta.
***
Humaira kuwa sai ta nemi murnar da take yi na Oda ta rasa, jiki a saluɓe ta yi mata dahuwar dafadukan macaroni mai busasshen kifi. Ƙamshinsa ya karaɗe kicin ɗin da falo. Koda ta kammala ta haɗa komai a ƙaton faranti ta kai mata babu godiya ba kallon arziki, itama ba ta sa a ka ba kawai ta jya da zummar tafiya.
"Ke zo nan!"
Muryar Anna ta ji, ta runtse idanu kirjinta na dukan tara-tara cike da tunanin da wanne kuma Annar ta zo yanzu ta juya ta koma ta durkusa ba tare da ta kalleta ba. Ta soma magana a kausashe.
"Ɗago ki kalleni nan, ni da kike gani dai na fi ƙarfinki. Mun ci dubu sai ceto, zuri'ar Mamman Ɗan Jika daidai nake da kowane bafillace mai taƙama da asiri. Har mu za a gayawa asiri? Tun wuri ina gargaɗinki ki fice a rayuwar ɗiyata, idan ma wani mugun ƙullin aka kawoki da shi don ki shiga tsakaninta da yaranta toh ahir ɗinku, ni dai na fi ƙarfinku balle kuma tsatsona. Ki kama kanki tun kafin na ɗau mummunan mataki a kanki. Ɗan girkin da kike taƙama kin iya ni mai iya juya lamarinki da shi ne, idan kuma kina da ja ki cigaba kar ki fasa. Asir dai ba za ki nunamana ba, mun saka Allah a gaba ne kawai shiyasa muka watsar. Amma muddin kika ce za ki cigaba da juya ɗiyata kamar waina da shiga tsakaninta da yaranta da ta haifa da cikinta ni nan zan nunamaki iyakarki."
Tana kaiwanan ta juyar da kai tana girgiza ƙafa na bala'i. Humaira ta dubi Anna dakyau, an zo gaɓar da ba za ta jure ba sai ta ba ta amsa ko yaya ne. Ƙazafin sihiri ba za ta jure shi ba don haka ta soma magana da wani irin ƙunar rai.
"Kiyi hakuri Anna, amma kalamanki laifi ne ko a wurin Ubangiji, kin yimin mummunan zato kin kuma yimin ƙazafi. Lallai Ubangiji zai yi mana hisabi a gobe ƙiyama. Na samu kyakkyawan tarbiyya a wurin Dada da Kawuna irin wanda nake da yaƙinin ko uwar da ta haife ni sai haka. Ban san boka ba balle mugun malamin da zan je ya yi min wani mugun aiki ba, asalima ban da a fina-finai da kuma labari ban taɓa karo da su ba. Wanda ya riƙi Allah, ai ba zai aikata abin da kuke yi ba. Kullum cikin zagi da aibata musulmi ɗan uwanku, ni Humaira babu wani mahaluƙi a duniyarnan da zan kai ya yimin aiki a kan wasu, kenan idan nayi hakan ma ban riƙi gaskiya ɗaya ba, ban yi imanin Allah zai iya amsamin addu'ata ba komai muninta komai kyawunta ba kenan. Ai Ubangiji ya wuce duk zatonku. Balle ma ban taɓa roƙo mai muni kan kowane ɗan uwana musulmi ba, kuma ba zan fara akan Mami ko yaranta ba. Tsakanina da Mami sai addu'a, ta yimin riƙon da ya sa nake jure dukkan wani abu da za ki yimin ke da jikokinki. Har abada kuma bisa darajar Mami ba zan taɓa daina ganin mutuncinki ba. Kiyi hakuri idan da abin da na faɗi mai zafi."
Tana kaiwa nan tuni ruwan hawaye sun wamke fuskarta, a bisa tilas ta kalli idanun babbar da ba ta riƙe girma da tsufanta ba ta gasamata maganganu. Ita ta fi Anna jin ciwon haka, sai dai haka take, ba ta iya hakuri idan aka kai ta bango musamman idan abin ya kasance ya haɗu da baƙin ƙazafi. Juyawarta ya yi daidai da saukar igiyar chaja a gadon bayanta, Jannat ce wacce a farko ta yi ɗif don gani tayi tamkar a mafarki wai wata ƙaramar yarinya na gasawa uwarta maganganu, sai da ta motsa da zummar barin ɗakin sannan ta zabura ta janyo igiyar chazarta. Nan fa ta hau jibgar Humaira amma kamar ba mutum ake duka ba, ta ƙi tafiya ta kuma ƙi ƙwatar kanta. Zuciyarta tafarfasa take yi. Kallon Jannat take kawai tsakar idanu yayinda idanunta suka kaɗa sosai sai ruwan hawaye. Ganin da ta yi Humairar babu ko gezau sai kawai ta hau wanke ta da mari tana zaginta. Ta yi biyu, za ta ƙara ta riƙe hannunta gam, ba ta san ya aka yi ba, ba ta kuma jin za ta iya tunanin mai kyau da marar kyau a lokacin, kawai ta ji yatsun hannunta sun sauka saman fuskar Jannat da mugun ƙarfi ji kake tas!!! Ya yi daidai da faɗowar su Futuha ɗakin waɗanda dawowarsu kenan daga shoprite cike da nishadi. Ganin abinda ya faru ne ya sa Tasleem sakin ihu mai ƙara da ya ja hankalin Abba da Mami dake a sashin Abban, suka nufo da sauri Abba ya ɗan tsaya daga ƙofa yayinda Mami ta kutsa kai ɗakin. Alokacin rufewar idanun Humaira har ya kainta shaƙi wuyan Jannat ta dangana ta da bango, babu sautin kuka sai ruwan hawaye, Jannat ta raina kanta, ta ji ashe ba ta da ƙarfi don ji tayi kamar ba iyaka Humairar ba ce ta shaƙe ta ba.
"Wayyo Allahna! Ku taimaka za ta kashemin yarinya!"
Jin wannan furucin na Anna ya sa Abba danno kai cikin ɗakin. Tsawa ya dakawa Humaira ba ta ko kalleshi ba. Ya kuwa ƙarasa ya ɗauketa da wani marin sannan ya fincike hannunta. Mami kuwa mutuwar tsaye ta yi, ita kadai ta san me take ji a zuciyarta, wannan shi ne lokacin da take gudu, ta juya da sauri ta bar ɗakin. Su Futuha kuwa suka yi kan Antinsu suka rirriƙe suna kuka yayinda Anna ma kukan take har da biyu saboda ganin Abban. Shi kuwa rufe Humaira ya yi da duka sai da ya ga har ba ta motsi kafin ya karasa ga Jannat yana ba ta hakuri, Jannat kamar jira take kawai sai ta fashe da kuka sosai da fadin.
"Wannan wane irin cin mutunci da zarafi ne? Da aurena da darajata da shekaru sa'ar ƙanwar ƙanwata ta shaƙi wuyana? Wannan rayuwar da me ya yi kama? Kiyi hakuri Humaira, watakila laifina ne da na zo gidannan. Na saba ganin girmamawa daga mahaifinki, hatta da marigayiya Anti Fati ba ta taɓa yimin koda kallon banza ba, amma yau ga ɗiyarta nan ta shaƙeni tana ƙoƙarin kai ni lahira. Aikuwa a yau zan bar maki gidanku."
Ta ƙara fashewa da kuka, Abba ya ji kamar ya ƙara rufe Humaira da duka, wannan banzan halin a ina ta ɗaukoshi? Tabbas ba halin mahaifiyarta ba ce.
"Nima yau zan bar gidanka Isuhu, tun zuwan yarinyarnan naga rashin kunya iri-iri da ban taɓa gani a wajen yan uwanta ba. Na yi kokarin janta a jiki da nunamata kauna, sai dai ban sani ba ko tana ji a ranta ni ban kai ta girmamani ba saboda ina zaune ina cin arzikin gidan mahaifinta ba, tunda abin ya kai ga haka in sha Allahu zan tattara na koma can Agadez, kiyi hakuri Humaira, wallahi ni ba muguwa ba ce. Tsakanina da duk abin da ya fito daga jikin Isuhu babu komai sai girmamawa."
Dakyar Abba yake magana saboda ɓacin rai ga nauyin Anna da ya dinga ji, wai yau diyar cikinsa ce ke ci wa tsohuwar mutunci ta hanyar dukan ɗiyarta a gabanta.
"Ki yi hakuri don Allah Anna, wannan gidana ne ba na Humaira ba. Mallakina ne, kamar yanda uwata mahaifiya da ace tana raye take da iko kai karfi a kaina da gidannan, haka nake ganinki don haka ina roƙonki kiyi hakuri ki janye ƙudurinki. In sha Allahu daga yau irin haka ko da wasa ba zai ƙara afkuwa ba. Ni zan ɗau mataki kwakkwara a kanta."
Ya ƙarashe yana duban Humaira da sai lokacin take sheshsheƙar kuka, itama shi take kallo, ta sunkuyar da kai.
"Don ubanki ba za ki buɗi baki ki ba su hakuri ba?!"
Ya faɗi a tsawace, hakan ya yiwa ran su Tasleem dadi, yau dai ga wacce suke ganin ta fi su a wurin Abba tana ɗanɗanar kudarta. Abin ya zo musu a daidai. Ita kuwa mikewa ta yi dakyar ta durkusa sosai, hakuri ta shiga ba su har Jannat din. Dakyar suka ce ya wuce saboda ganin idanun Abba.
"Muje." Ba musu ta mike jikinta duk ya yi tsami ta bi bayan Abban zuwa falonsa yanda ya buƙata.
***
Fadeel da murmushi ya ɗagawa yayartasu hannu alamar jinjina. Yayar Ibb, Anti Ruƙayya wacce ke aure a Kano, sun saba sosai da Fadeel din tun kafin ma ta yi aure. Ibb ya dube shi.
"Wai ni ban gane ba, toh idan odar ta sauka wa zai karɓa?"
Fadeel ya yi murmushi karo na biyu.
"Nan gidan Antinmu za'a kawo mana, ni kuma sai na zo na karɓi rabona."
Hajiya Ruƙayya ta yi dariya.
"Amma dai wannan ina zaton ita ce zaɓin ƙanin nawa ko?"
Ya kasa magana sai shafar sumar kai, Ibb ya taɓe baki.
"Ita ce dai yake yiwa son mutuwa ba ta san da zamansa ba."
Fadeel ya harareshi shi kam dauke kai ya yi ya cigaba da ba Ruƙayya labarin komai. Sosai ta ji ya ba ta tausayi.
"Allah Sarki, yanzu kai zaman jiranta za ka yi kuma?"
"Um." Shi ne kawai abin da yace yana hararar Ibb da ya kasa rufamasa asiri. Ibb shima ya rama sannan ya ce.
"Ai wai haka yake nufi, nidai ban san irin wannan abu ba, ace mutum ya kasa hakura da son wanda ba ka gabansa? Kinsan Allah, mutumin nan akwai mata da yawa da suke kawo mishi hari, na ce ya runtse ido ya zaɓa ya darje amma ina. Wai ya hakura da auren har sai Humaira ta yi koda ba shi ta aura ba sannan zai yi nashi."
Rukayya ta yi salati.
"Fadeel kana cikin hayyacinka kuwa? Wannan wane irin so ne?"
Nan da nan fuskarsa ta sauya.
"Nawa son da haka ya zo. A sanya ni a addu'a kawai Anti."
Ta ɗan yi jim tana kallonsa. Sai kuma ta numfasa.
"Shikenan, Allah ya zaɓa abinda ya fi alheri. Zan so naga wannan yarinyar da ta sace zuciyarka har haka."
Ba musu ya fiddo waya ya buɗe hotunan Humaira wanda hatta a saman screen dinsa ita ce ya miƙa mata. Ta kalla sosai ta ce.
"Babu ƙarya Humaira kam ta haɗu. Daga kuma yanayin fuskarta ka san za ta yi haƙuri."
Yabon da ta yi sai ya karawa Fadeel farin ciki, a duniya ya tsani wanda zai kushe abar sonsa. Ganin har Ruƙayya ta yaba sai hankalinsa ya kwanta. Sun jima suna hirar lamarin Humaira kafin a karshe su yi sallama bayan Fadeel ya ce mata zai dawo idan an kawo odar snacks ya karɓa.
***
Jannat ce tsaye tana kallon hanyar waje, har lokacin zafafan hawaye take fitarwa na baƙin cikin abinda Humaira ta aikata gareta. Fuskarta ya yi jazur, ta juyo ta kalli Anna wacce ta yi shiru tana kallonta, a duniya Anna ba ta son damuwar yaranta.
"Anna, na yi alƙawari sai na ga bayan Humaira da duk abin da take taƙama da shi. Ta yimin cin fuskar da ban taɓa tsammata ba, ni zan nunamata iyakarta koda kuwa zan yi yawo tsirara."
A firgice Anna ke duban ɗiyarta, ta san halin kayanta, muddin ta furta abu, komai nisan lokacin da za a ɗauka sai ta aiwatar. Wani lokacin ma, sai ta tabbatar da shafewar abin a kwakwalwarka kwatsam sai dai ka ga sakamako a aikace. Don haka ta sani ko mene Jannat za ta aikata ba ƙarami ba ne duba da yanda ta saki fuska lokaci guda har da dariya. A karshe ma hatta da abincin da Humairar ta kawo sai da ta ɗiba ta yi zaman ci tana santi. Ita dai Annar ba ta ce mata komai ba, ta fi kowa sanin baƙar zuciya irin na ɗiyarta.
*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA. KAR KI MANTA BAYAN NAN AKWAI CAN, ALLAH YA SA MU DACE AMEEN.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Gidan Alhaji Yusuf wanda aka fi sani da Maiagogo sun wayi gari ranar alhamis da shirye-shiryen bikin yaransa biyu, Futuhatul-Khair Yusuf da kuma Tasleem Yusuf wanda kwanaki uku kawai ya rage a fara. An samu sauye-sauye da dama, na farin cikin ya fi kowanne yawa ga Humaira da duk ma wanda ke tare da ita. A wannan watannin ta samu alheri mai yawa daga sana'arta. Babbar customer dinta ita ce Hajiya Rukayya wacce ta hanyarta kaɗai ma ta samu oda na biki da party har ya zamana tana gwada na abinci bayan snacks sai dai gaba ɗaya sau biyu ta gwada abincin taro ba laifi kuma masu shi sun yaba hakanan Hajiya Rukayya ta ji dadi da ba ta ba su kunya ba. Duk abin nan ba su taɓa ganin juna da ita ba sai dai waya. Mami ta sa an buga leda da stickers mai tambarin DEELSHA'S DELICACIES. Suna na musamman da Raihana da Ummita suka ba Humaira a sadda Mamin ta ce ta yi tunanin sunan da za'a sanya a ledar. Sunan ya yiwa Humaira daɗi ko kadan kuma ba ta tambayesu ma'anarsa ba. Mamin ma ta ji dadin sunan, ganin kalmar turancin ya sa ta tambayar wacce ta sa, nan Humaira ta sanar da ita su Ummita ne. Daga haka ba ta kara cewa komai a kai ba.
A yau da ya rage kwanaki uku bikin yan matan Mamin, gidan nasu ya soma karɓar baƙi ƴan uwan Mami daga Agadez sai ko ƙawayen Futuha waɗanda suka zo daga nesa kasancewarta mai jama'a fiye da Tasleem. Yan uwan Abba kuwa ba wanda ya zo gidan da zummar kwana. Mubarak shima ya zo gari, sai kuwa Anti Jannat. Ya kasance a wannan lokacin gidan ba ya rabo da jama'a, Mami ta sa Ladidi kawo mataimaka a aiki har su uku saboda yanayin cikar gidan da zummar bayan biki za ta sallame su.
Anko har kala biyar aka fitar, na ƙawaye daban wanda zasu sanya ranar kamu da na daurin aure da yini sai ko na ranar dinnerparty. Na manya su ma kala biyu, na fita kamu sai na ranar daurin aure.
Humaira, Raihana da Ummita daban aka fitar musu da na sisters wanda zasu saka na yini sai kuma na dinnerparty da Mami ta yiwa su Futuha jan ido ta karɓar musu katinsu ta riƙe a wajenta don a farko sun nuna su ko kusa ba su kaunar su halarci dinner din.
Amare sun sha gyara ba na wasa ba daga mai gyaran jiki na musamman da Mami ta samar musu suke sintirin zuwa. Hajiya Lubna ita da kanta ta ɗauki nauyin gyara su, gyara irin na mata. Ta kashe kuɗaɗe masu kauri kuwa wanda hakan ya burge aminiyarta kwarai ta yaba. Ba ma ita ɗaya ba, ƙawayen Mami da dama manyan mata masu kudi sun ba da gudunmuwa mai yawa na kudi, kanta ya fasu sosai ta kuna ga fa'idar mu'amala da masu hannu da shuni.
Su Raihana sun karɓi dinkunansu a hannu, sun yo ƙunshi da kitso abinsu sun fito fes.
A na washegari kamu ne su na zaune suna hira a daki tare da wasu yan uwan su Raihana sa'anninsu da suka zo daga Nijar, Tasleem ta shigo. Fatarta har wani ɗaukar ido yake, ba ta da ƙiba irin na Futuha ita nata jikin daidai misali ne, duban Humaira ta yi fuska ba fara'a.
"Ke Humaira, ke da Ummita ku zo na aike ku."
Humaira ta ji ciwon ke din da tayi kiranta da shi, ita kuwa Ummita ko a jikinta ta miƙe tana murmushi. Hakanan halittarta yake, tana da yawan murmushi, abinda zai sanya hawayenta zuba kuwa, toh fa ba ƙaramin abu ba ne kamar dai akan Humaira ko kuwa wani abun daban. Kamar ba za ta miƙe ba sai kuma ta yi tunanin ba komai ta yi tunda dai aure ma za su yi su bar gidan sai ziyara don haka ta taushi zuciyarta