Showing 87001 words to 90000 words out of 93383 words
ta san abin da ya danne wannan soyayyar ba.
Tasleem ta amsa sallamarsa ciki ciki yayinda Futuha ta saki fuska sosai aka gaisa sannan ya dubi Humaira da shanyayyun idanunsa bayan ya cire gilashin.
"Boddo, barka da yamma."
Ya fadi yana mai ɗan dunƙule hannu da ɗan ranƙwafar da kai kaɗan tamkar wani basarake. Nan fa gaba ɗaya idanun ya koma kansu ana ganin ikon Allah.
*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
Ba ta ce uffan ba sai idanuwanta da ta sauke a cikin nasa. Ya ji kallon har a ƙasan ransa.
"Sauri fa muke yi." Tasleem ta furta cikin ɗaure fuska, gaba ɗaya wani irin mugun kishi ke cin zuciyarta. Fadeel bai ko kalle ta ba ya dubi Futuha.
"My sis, ko za ki ban aron ƙanwartaki for just 5mins?"
Murmushin da bai kai zuci ba Futuha ta yi.
"Ba ka da damuwa. Humaira jeki."
Humaira da ke jin kamar ta shaƙo wuyan Fadeel amma sai ta kasa yi mishi musu ta bi bayansa sadda ya yi gaba zuwa inda ya ajiye motarsa. A jikin motar suka tsaya su na hangen su Futuha da ke hira sai ko Tasleem da ta zubamusu idanu tamkar makauniyar da ta samu ido.
"Ka kirani kuma sauri muke za mu tafi."
Ya ji babu dadi daga yanayin muryar da ta yi mishi magana, ya dai daure ya haɗiye kamar koyaushe.
"Humaira kina addu'a sosai kuwa? Kina nafilfiloli da sallar dare? Kina mayar da hankali wajen yawan karatun Alkur'ani?"
Ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ta sani tana sallolinta biyar akan lokaci, tana kuma addu'a daidai gwargwadon yinta, amma yawan karatun Alkur'ani da kuma sallolin dare da ma nafila ba za ta iya buɗe baki ta ce mishi aa a kansu ba, kawai sai ta ji hakan ya yi mata nauyi a saman harshenta.
Ya tsinci amsoshin tambayarsa daga shirunta, don haka ya cigaba da magana a nutse ba tare da ya dauke idanu daga saman fuskarta ba.
"Salollin farillah wajibi ne Humaira, amma su Nafiloli neman ƙarin lada ne da kusanci ga Ubangiji. Za su buɗemaki ƙofofin rahma wadanda ba ki taɓa zato ba. Hakanan shi kansa karatun Alkur'ani, yawan tilawarsa da yin azkar safe da yamma zai ba ki kariya daga shaiɗanu da ma jinnu. Babu wani ko wata ko kuma wani abun da zai cutar da ke. Ina roƙonki ki yawaita addu'a, ina kuma ba ki shawarar yawan hailala, istigfari da salatin Annabinmu s.a.w. Ki ɗauka tamkar wani ɗan uwa ne gareki na jini yake ba ki wannan shawarar. Kin yarda kin amince za ki amfani da ita?"
Ba ta taɓa jin wani irin sanyi da nutsuwa tattare da kasancewarta da Fadeel ba sai a yau kuma a yanzun da yake kwararo mata waɗannan shawarwarin. Sai gaba daya ya tuno mata da Kawunta da ma Dada, ta tuna da kalar rayuwarta a Nijar, koda wasa idan ta idar da sallah, Dada ba ta barinta ta bar saman darduma sai ta yi nafila ta kuma tsaya ta ga ba ta yi wasa da addu'a ba, hakanan tilawar Alkur'ani, duk juma'a Kawunsu na tattara su har yaransa su yi tilawa, kowacce ta biya inda ta iya. Shaiɗan kwarai ya yi tasiri a zuciyarta da har ya sanya ta yi watsi da dukkan wannan, ta zama daga ta idar da sallar asuba sai bacci ba kamar a farkon zuwanta Kano ba da ma rayuwarta a Nijar inda koda wasa ba ta isa ta koma shimfaɗarta ba har sai rana ta fito bisa koyarwar Dada. A farko tana yi daga baya duk ta watsar. Ummita duk ta fi wannan kokarin. Ita kuwa kasala ya mata yawa.
"Kinji? Please."
Ya kara nanatawa. Ta dube shi sai ta yi murmushin da rabon da ya gan shi saman fuskarta har ya mance. Ta gyada mishi kai.
"Naji, nagode sosai da tunatarwa kuma zan kiyaye in sha Allah."
Ai sai ya ji tamkar an jefa shi wata duniyar ta nishadi da farin ciki, sai kawai ya rasa me zai ce ban da leɓe da ya ɗan lasa yana maida mata martanin murmushin. Ƙarar hon da aka danna da ƙarfi ya sanya suka dubi wajen, har ga Allah shi Fadeel ya ma mance adadin mintocin da aka yi mishi alfarmarsa, balle kuma Humaira da ta lula tunanin sakancin da take yi da addu'a tun zuwanta garin. Tasleem ce da wannan aikin ranta a mugun ɓace.
"Nagode, kije suna jiranki. Sai mun yi waya ko?"
Ta ji tamkar ta ce eh, sai kuma ta fasa ta juya kawai ta kama tafiya, ya bita da kallo sai kuma ya buɗe motarsa ya shiga, ya sani Abba ba ya nan balle ya shiga su gaisa. Don haka ya yi ribas aka buɗe gate ya fice. Itama tana shiga gaban motar kusa da direba, direban ya ja suna ɗagawa juna hannu ita da Raihana.
Tasleem da Futuha a bayan motar zaune sai yare suke yi. Ita kuwa duk ta tsargu amma ta haɗiye ɓacin ranta.
Tasleem ke mitar dole ne ma Humaira ta rabu da Fadeel tunda har ita ba ta same shi ba to kowa ma ya rasa. Yayinda Futuha ta ce ta kwantar da hankalinta soyayyar babu inda za ta kai. Haka suka yi ta gulmar Humaira ba tare da ta tsinci ko harafi ba. Ba ta da haɗi da buzaye balle ta fahimci akan abin da suke tattaunawarsu.
Har aka sauke Tasleem, ba ta da walwala, ganin haka itama Humaira ta ja jikinta ko ki gaida gida ba ta ce mata ba.
A gidan Futuha, ɗakin dai da ta taɓa sauka wannan karon ma shi ne ya kasance masaukinta. Ta ajiye jakar kayanta ta faɗa ta ɗauro alwala ganin ana dab da kiran sallar magriba, sai a lokacin ta jawo waya ta kira yar uwarta Ummita. Suka ɗan taɓa hira don ta ƙara kwantar mata da hankali, cikin ikon Allah ma sai ta ga ko a muryarta babu wata damuwa. Koda ta ajiye ta kara tsunduma da tunanin Fadeel, wai me ya yi mata ne ma da har ta tsaneshi hakan? Oho, ta ba kanta amsa, sai kuma ta ja tsaki cikin jin zafin rai, to meye nata ma na tsayawa tunaninsa? Don haka sai ta miƙe ta shimfiɗa darduma jin an soma kiraye-kirayen sallah. Koda ta idar sai da ta yi nafila sannan ta yi salati da istigfari. A karshe ta yi addu'a sosai. Sai kuma ta tsinci zuciyarta da yin wani sanyi tamkar an yayemata wata damuwar. Sabuwar wayarta ƙirar Huawei da Abba ya damƙa musu bayan fitowarsu daga hannun ƴan ta'adda ta yi ƙara sauti mai dadi shaidar shigowar saƙo. Ta ɗauka ta duba.
*_Babu wata damuwa ko baƙin ciki da Allah ba zai iya magancewa ɗan adam ita ba. Ki miƙa dukkan lamuranki gareshi, ki kusanceshi, zai kusanceki. Allah yana son masu ambatonsa safe, rana da kuma dare. Ina miki fatan alheri koyaushe._*
Ta karanta fiye da sau uku, ya yi mata dadi sosai, ta kuma kasa barin murmushi. Fadeel ne, koda babu suna a lambar tana da haddarta saboda kira na yau da gobe da yake yi kuma duk da ita ne. Ta sauke ajiyar zuciya, kwankwasa ƙofar da Futuha ta yi da shigowarta da sallama ya sanya ta ajiye wayar ta dube ta. Murmushi Futuha ta yi mata.
"Yauwa Humaira idan kin huta ki fito ki ɗebi abinci a kicin. Daga gobe za ki soma gwadawa Hafsatu yanda kike tsara abinci da komai, yau kinga sai ki huta ko? Ni zan shiga ciki ba lallai kuma mu haɗu ba sai da safe."
Ita dai ta amsa da toh kawai, bayan fitar Futuhar ta girgiza kai. Mamakin wannan rayuwa ta yaran Mami take, tabbas albasa ba ta yi halin ruwa ba, da ace sun biyo Mami hatta da girkin ba su da matsalarsa. Ta rasa menene ribar ɗiya mace idan ta zauna har ta yi aure ba ta iya girki ba. Banda shiriritar Futuha, ta gwammace a koyawa Hafsatu girki ta cigaba da yi mata bauta ita kuwa ta zauna ta miƙe ƙafa. A ƙarshe dai ta watsar da tunane-tunanen da ta tabbatar ba za su yi mata wani amfani ba ta cigaba da ambaton sunayen Allah har aka kira sallar isha'i ta gabatar ta kuma haɗa da nafila ta yi addu'a anan ma sannan ta ninke dardumar ta fita, abincin sam bai yi mata ba. Shinkafa ce dafaduka ta dai ji kaji wadanda daga ka kai saman hancinka sai ƙarni ya bugeka, da sauri ta mayar ta ajiye. Sanin da ta yi idan ta zauna sai ta kwana da yunwa ne ya sanya ta daukar indomie kanana biyu ta dafa ta ci ta sha ruwa.
Saita alarm ta yi ya tashe ta karfe uku, dakyar ta tashi saboda ba ta saba ba ga bacci dake neman fin ƙarfinta, sai da har uku da rabi ta buga sannan ta iya miƙewa firgigit tana ambaton sunan Allah. Hakan ya ba ta wani ƙarfi ta kuwa ɗauro alwala ta dawo ta yi nafiloli ta karanta alƙur'ani bacci na ɗaukarta, dakyar ta daure ta yi sallar asuba sannan ta kwanta anan bacci mai karfi ya kwashe ta.
Sai wuraren takwas na safe ta tashi ta yi wanka ta shirya tsaf ta dora hijabinta ta nufi kicin. Ta sani mutanen gidan ba sa tashi da wuri, maigidan kansa sai ya kai goma bai fita ba. A kicin ta tarar da Hafsatu na zaman jiranta har ta yi gyara ta wanke kwanuka. Suka gaisa fuska a sake, nan suka shiga haɗa kayan kari, kasancewarta babbar mace kuma mai basira tana hankalta kwarai da yanda Humaira ke sarrafa girkinta. Suyar dankali da agada suka yi sai ko sauce da ta haɗa, sai ruwan shayi da ya ji citta da kanumfari. Sai ko farfesun nama da ta yi da ya ji kayan lambu. Kicin din ban da ƙamshi ba abinda ke tashi, komai ta yi daidai gwargwado yanda ta tabbatar ba za'a yi almubazzarancinsa ba. Hafsatu ta fita da shi zuwa dinningtable na Futuha, ita kuwa Humaira bayan ta zuba wa Hafsatu ta ɗebi nata ta yi ɗaki don ba za ta iya jurar har sai su Futuha sun tashi ta karya ba saboda yunwar da ya addabe ta, a ranar kuma ta tashi da wani irin karfin jiki da walwala. Ta ƙara gasƙata cewar Fadeel, babu abin da ibada ba ta ɗaukewa na daga damuwa da ma ƙuncin zuciya. Hamdala kawai ta ke yi bisa yanayin da ta tsinci kanta a ciki.
***
A ɓangaren Fadeel kuwa, sosai suke shirin bikin Ibb da Dakta Salma wanda bai fi sati ya rage a yi ba. Abokansu duk wanda ya ji zancen auren Ibb sai ya tambaya ko an yi na Fadeel? Amsar dai bai wuce nan kusa shima zai yi ba. Kamar koyaushe a kwanakin nan, yau ma su na tare bayan ya raka Ibb wurin Dakta Salma jin tsarin events din da za ta gudanar, Ibb sai faman mita yake yi mishi akan kawai ya kai kudi a sanya aurensu lokaci guda shi kuwa murmushi kawai ya ke yi. Girgiza kai Ibb ya yi.
"Fadeel na sanka, kana da ƙoƙari sosai gun ɓoye damuwa, ba ka fiye son ɗorawa mutane nauyin damuwarka ba, amma ba yanda ka iya, mun taso tare kuma kai ɗin aminina ne dan uwana na maka sanin da wani mafi kusa da kai ɗin bai yi ba. Yanzu a ture zancen wasa, please and please ka yi abin da muke da tabbacin yiwuwarsa, idan yin a yi, idan barin a bari."
Tuƙi yake yi amma sai da ya ɗan juyo ya dube shi.
"Ban fahimceka ba. Me za a bari?"
Ibb ya kauda fuska yana ɗan shan ƙamshi.
"Auren mana, ko dole ne sai ita? Lamarinta ya fara kai ni bango, ita ba ƴar kowa ba a ƙasarnan sai ji da kai da taƙama. Matan da suka fi ta sun nuna su na yi da kai sun kuma nuna sun ji sun gani kowane yanayi ma a tafi da su amma ka nace mata, ka maƙale sai ita. Haba Fadeel, yaushe duk wannan zai wuce? Har yanzu kana da hope din cewa za ta amince da aurenka da bakinta?"
Fadeel bai ce komai ba, amma zuciyarsa zafi take. A duniya bai taɓa yin so ba sai akan Humaira, kuma da son ya tashi kama shi, sai ya yi mishi wani irin kamun dabaibayi wanda ko ya ƙi ko ya so, hakanan zai rayu da shi. Bai dai san abin da gaba za ta haifar ba.
"Ban iya ƙiyayya ba, kamar yanda ban iya soyayya ba ka san da haka ko? Meyasa ka ke tunanin akwai ranar da zan iya haƙura da Humaira alhalin ba ta yimin laifin da zan ƙi ta ba har yau? Ko ka yi zaton ta taɓa wulaƙantani ko zagina? Toh Humaira ba ni ta wulaƙanta ba, soyayyar da na furta ina yi mata ta wulaƙanta, amma na yi mata uzurin kasancewarta daga jinsin Dan Adam wanda muka riga muka san ajizancinsa. Ka yi hakuri, na sani kana jin babu dadi yadda ake maka ƙorafi akan aurena har da masu nemana da sharri. Please ina son ka toshe kunnuwanka daga garesu. Duk radda ni Fadeel na furta maka cewa na bar Humaira, toh ka sani ina nufin rabuwa ta har abada, amma yanzu bana jin ko ɓurɓushin hakan a zuciyata. Ba na jin kuma wannan mafarki naka mai tabbatuwa ne saboda ba ta yimin kamun wasa ba. Ka bi wannan ɗan uwannaka da addu'a Ya Sheikh, komai zai zamo tarihi fa in sha Allahu."
Harara Ibb ya wurga masa jin ya ambace shi da sunan zolaya, Fadeel kuwa murmushi ya yi mishi yana ƙara yi mishi kirari da Angon Salma. Nan kuma ya saki fuska aka bar maganar gaba ɗaya.
***
Cikin hukuncin Allah, a kwana a tashi har tsawon lokacin da su Abba suka ƙara roƙar alfarma a yi bikin Ummita da Sahabi ya kusa cika, a sannan Humaira ta tattara ta bar gidan Futuha adalilin mijin Futuhar da ko kallo suke sai ya dinga kiran Humaira wai ta fito su yi kar ta ƙumshe a ɗaka. Ko kuma ya yi ta santin girki yana fadin ai kaf gidan su Futuha ta fi su iya girki, Futuha tun tana yaƙe har ta zo ta kasa jure ɓacin ranta ganin tashi guda ya siyo wani rantsetsen leshi dan dubu arba'in ya kawo wa Humaira matsayin ladan girki da take yi musu. Anan ne gaba daya ta sauya fuskarta ta ce Humaira ta tattara ta koma gida, ta sa direba ya kai ta bayan ta karɓe leshin. Ba tare da sanin cewa ita Humaira hakan ya fiye mata komai dadi ba don dama ta gaji da zaman gidan, dadinta daya bai wuce na ibadar da take yawan yi yanzu ba sosai, kuma abin mamaki koda Fadeel ya kira ta ta rage jin wannan tsanar da ɓacin ran sai dai ba yabo ba fallasa.
Tashin hankalin daake gudu dai shi ne ya afku, Abba ya zaunar da Sahabi da wani Kawunsa a dakin baƙi ya sanar da su abin da ke faruwa. Sahabi da yake jin wai wai a gari bai yarda ba ji ya yi har wani jiri na neman kwashe shi daga zaune. Kawunsa kuwa ya jinjina lamarin, ya kuma yi addu'ar Allah ya sauki Ummitan lafiya a karshe ya ce idan ta haihu ta yi aure ban da Sahabi don tuni dama sun yi mishi mata ganin ana ta yawo da hankalinsu akan Ummita. Sahabi ya kasa cewa uffan, idanunsa sun kaɗa. Tsakani da Allah yake son Ummita, ya kuma so aurenta, amma bisa gargadi iyayensa ga Kawu, matukar idan sun je ta tabbata ciki ne a jikin Ummita toh lallai su faɗi hakan. Sun kuma yi barazanar saɓawa Sahabi muddin ya musa zancen. Da wannan aka ƙulle mishi baki ya kasa cewa komai. Sai ma da zai tafi ne ya roƙi arziƙin ganin Ummita, nan Abba ya ba shi hakuri gami da nunamasa ba za ta iya jure ganinsa ba. Ya yi hakuri dai ya bi umarnin iyayensa. Daga wannan Sahabi ya ja jikinsa suka bar gidan bayan Abba ya damƙa musu dukkan wani abu da suka kawo da sunan aure.
Ummita na ɗaki ban da kuka babu abin da take yi, Humaira wannan karon ta ma kasa rarrashinta, ga ciki ya fito ras ana gani kasancewar bai fi watanni biyu ya yi mata saura ta haihu ba. Ta shiga watanni bakwai cif. Ita kanta Humairar hawayen take yi tana gogewa. Ta dai tabbata shikenan Sahabi ya rabu da Ummita duk kuwa da irin dogon wayar da suke yi da soyayyar da suke nunawa juna.
"Kaddararki ce Ummita, kiyi hakuri mu rungumeta da hannu bibbiyu. Watarana komai zai zama tarihi."
Ta girgiza kai.
"Humaira na sani ƙaddarata ce, amma wallahi Humaira na tsani cikin jikina da abin da ke cikin. Ba zan taɓa sonsa ba. Humaira duk sadda cikina ya yi motsi ji nake kamar na ɗauki wuƙa na caka a cikin abin da ke cikin ya mutu gaba daya koda ace nima nawa ajalin kenan. Allah ya isa, Humaira ba zan taɓa yafewa azzaluman nan ba. Har gobe mummunan fuskokinsu na nan a kwakwalwata, wallahi yau idan Allah zai nunamin su, sai na raba su da numfashinsu."
Hawaye sosai itama Humaira take yi, balle kuma Raihana wacce shigowarta kenan dakin sanye da Uniform ta dawo daga makaranta ta tsinci labarin fasa auren Sahabi da Ummita kwata kwata a bakin Mami, kuka sosai take yi sanin irin kaunar da suke yiwa juna. Ta karaso ta rungume kafadar Ummita tana kuka tamkar ranta zai fita ta ma kasa magana. Sai Humaira ke aikin rarrashinsu cikin ƙarfin hali duk da itama hawayen ne ke zubomata.
"Humaira! Raihana!! Kuna ina?!"
Jin muryar Mubarak yana kiran sunansu murya a sama ya sanya su duban juna kafin su fito zuwa falon gaba daya ban da Ummita da ko motsi ta kasa. Kirjinta ne kawai ke dukan tara-tara, zai wahala ta yi mafarki bai afku ba, tana tsoron kuma yanzun ace mafarkin nata ne ya tabbata. Sai ta hau ambaton Innalillahi a ƙasan ranta.
Ba Mubarak ne kaɗai a