Showing 63001 words to 66000 words out of 93383 words
Har yanzu dama yana tare da Humaira? Shi ne don munafunci Humaira ta ci amanar Mami ta ɓoye zancen?"
Murmushi Jannat ta yi.
"Ke ban da abinki ina Humairar take a yanzu? Kina tunanin shirin na wasa ne za ta dawo, ai daga can inda take sai wata duniyar kuma ba wannan da muke ciki ba. Duk fa wanda ya samu dama ya dama. Kuma da kike wannan maganar ba yanzu gashinan kin auri Hamza ba? Ba kya sonsa kika bari ciki ya shige ki?"
Tasleem ranta ya ɗan yi sanyi jin yadda Anti Jannat ke fadin kaddarar Humaira kai ka ce ita ta rubuta hakan. Batun cikinta ya ƙara jefata damuwa, dama ba da son ranta ta samu ba kuma Hamza ya rantse sai ya yi mugun saɓa mata idan ta zubar.
"Wallahi Anti idan har zan samu na auri Fadeel zan iya kashe ko nawa ne a yimin aiki a kan Hamza ya sake ni. Anti wai kin taɓa ganin Fadeel kuwa da irin yadda ya haɗu? Wallahi ba zan iya zuba idanu wata ta kwacemin shi ba."
Anna tsohuwar banza ta kwashe da dariya madadin ta yi kwaɓa akan wannan haramcin da ake aikatawa sai ma ta ce.
"Kina da Jannat Firdausi ai babu ke babu fargaba. Yadda aka yi wancan haka wannan ma zai kasance labari."
Suka yi dariya. Can kuma Jannat ta ɗan jinjina kai.
"Ko wane ne wanda ya aikata wannan kidnapping din ya yi matuƙar burgeni, da ace ina da damar ganinsa sai na mishi babbar kyauta. Sai hakan ya zo mana da nasara kuma akan gaɓa, Boka ya tabbatarmin da cewa Humaira a can za ta haɗu da ajalinta. Itama Ummita babu tunanin za ta rayu balle har su samu damar kuɓuta su dawo. Kawai dai zan so dawowar ita Ummita, yarinyar ta iya bauta."
Tasleem ta yi murmushi.
"Nima dai Ummita ba ta yimin komai ba, ba ni da wani ƙulli da ita kamar Humaira. Wallahi Anti na tsane ta na kuma tsani duk wani mai sonta."
"Har da ni kenan!"
Suka juya don ganin mai furucin a razane.
®️Rufaida Umar
*LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.*
*5407827015*
*FCMB*
*Farida Abdullahi*
09034973645
*TALLAH!* *TALLAH!!*
*Ina ma'abota ƙamshi, su yi ƙamshi suna birge kansu suna birge wanda ya shaƙa*
*Ku danna wa.me/2347010137848 ku ce ta yi saving lambar ku watarana zaku ga garabasan ƙamshin da ba za ku iya Bari ba*
Tasleem ce ta soma kauda kanta gami da jan guntun tsaki ciki-ciki ba tare da ta ce uffan ba.
Raihana wacce ta gama jin dukkan munanan maganganunsu ta tako tsakiyar dakin sosai ta cigaba da magana.
"Har da ni kenan! Wannan ba Ummita ko Humaira kaɗai ku ka tsana ba Anna, har mu jinin Abba. Na yi mamaki dama da Anti ba ki ɗau mataki akan abin da Humaira ta yi maki a kwanakin baya ba, ashe dama ke tarkon da kika ɗana babba ne? Ashe wannan damar kike jira? Kai duniya! Mutum ya ƙi mutum har ta kai yana mishi fatan mutuwa? Me suka tare maku? Ku ji tsoron ranar da haƙƙin su Humaira zai kama ku!"
"Me kika ji ance da za ki rufe mutane da faɗa tamkar kina magana da Muhsin ko Waleed?"
Jannat ta furta a ƙoƙarinta na shanye firgicin da ta ɗan shiga, toh koda ace ba su da hannu a satar Humaira da Ummita, ai wannan ɓarin zancen da suke yi zai iya jawomusu matsala tunda ana kan bincike ko yau ɗin da safe sai da D.P.O ya zo wurin Abba.
Raihana ta yi murmushin takaici.
"Kar ku yi tsammanin ban ji mugun ƙullin da ku ke yiwa bayin Allahn nan ba. Amma ku sani, Allah na tare da bayinSa a duk inda suke kuma cikin kowane hali. Na rantse muku, duk iya yinku, duk iya ƙoƙarinku, ba za ku iya kawo sanadin koda karta a fatarsu ba balle a kai ga rasa rayukansu ba face sai da iznin Allahn da ya halicce su. Ku yi dukkan kokarinku, akwai ranar ƙin dillaci."
Tana kaiwa nan ba ta ko ƙara kallonsu ba balle ta ji me zasu ce ta sa kai ta fice daga dakin a guje zuwa nasu ɗakin wanda suka mallaka da su Humaira a baya. Haka kawai sai ta buɗe sif din kayan Humairar da Ummita ta fiddo abin da ta san sun fi so cikin kayansu ta yi ta kuka. Lamarin da ya sanya Mami hana ta kwanan ɗakin sai dai nata ɗakin. Ba za ta iya misalta baƙin cikin da ta ke ciki ba sanadiyyar ɓatan ƴan uwannata. A gefe guda ga baƙin cikin kasancewar Jannat yar uwa ga Maminta ballantana a kai kan Tasleem da take ji kamar ta shaƙe ta. Sai ko Anna da har ba ta kaunar ganin fuskarta a kwanakin nan tun da ta nuna ba ta wani bakin ciki da ɓatan yan uwanta.
***
Abba ya yiwa su Fadeel tarba na mutunci da dattako, gaba ɗaya idan ka ga Abba sai ya mugun ba ka tausayi sakamakon yadda ya koɗe ga kuma rama.
"Ka yi hakuri Fadeel, in sha Allah ƙiris ya rage na kammala haɗa kuɗaɗen fansar su, lafiya kalau za su dawo hannunmu. Kai dai ka ci gaba da addu'a."
Fadeel ya ƙara yin ƙasa da kai, Abban da ya ke da burin ya wayi gari ya gan shi a gabansa da zummar neman auren Humaira, su yi hira da dariya tsakaninsu sai gashinan ganin da suka yiwa juna na farko ba mai daɗi ba ne ko kaɗan. Zuciyarsa ta yi rauni nan da nan kuma ya ji idanunsa sun kawo ruwa daƙyar ya iya daurewa ya amsa.
"Toh Abba, Allah ya kuɓutar da su."
Abban ya amsa da amin, yana son ya ce idan da yadda zai tallafa, a ba shi dama amma ba ya so Abban ya ga kamar ya mishi katsalandan wannan ne dalilin da ya sa shi jan bakinsa ya yi shiru. Sun ɗan jima anan har Abban ke faɗamusu cewa Kawun Humaira suna hanya daga Maine, Ƙasar Nijar. Suka yi musu fatan isowa lafiya a karshe dai Ibb ya soma yiwa Abban sallama kan zasu wuce ganin Fadeel kamar ma ba shi da niyyar motsawa.
Bayan fitarsu Abba ya yi tagumi cike da tunani, a yanzu duka-duka dai abin da ya haɗa bai fi miliyan shida ba, ya kuma sani muddin ba gidansa da suke ciki zai siyar ba bayan motocin da ya sa kasuwa ya siyar, to fa babu ta inda zai samu cikon miliyan goma na fansar yaransa. Yana wannan halin ne Mami ta yi sallama ya amsa gami da ba ta damar shigowa. Ta shigo sanye da hijabinta ta zauna gefensa fuskarta dauke da damuwa ta ce.
"Baƙi ka yi ne?"
Ya numfasa.
"Eh, yaron nan Fadeel ne ya zo da abokinsa, ba su jima da tafiya ba."
Ta ɗan yi jim sai kuma ta numfasa ta ce.
"Allah Sarki."
Daga haka ba ta ɗora komai ba, shiru ya biyo baya kafin Abba ya girgiza kai ya ce.
"Maryam, an zo gaɓar da dole sai na siyar da gidannan na cika kuɗin fansar yarannan. Idan ya so sai mu koma wanda bai fi shi ba, lokaci na ƙurewa sosai, kaina ya ƙulle gaba ɗaya, dole na tashi na nemi mai siya ko kaɗan a kuɗin ne aka ba ni zai isa na cika na kaiwa wadannan mutanen."
Murmushi Mami ta yi.
"Kamar ka san shawarar da na zo na ba ka kenan Abban yara, sai kuma naji dadi da ka kasance mai yarda da ƙaddara. Siyar da gidan zai fiye mana alheri matuƙar dai za su bar yaranmu su dawo garemu."
Abba ya jinjina kai.
"Hakane Maryam, dama na riga da na yi magana da lauyana, na kuma bada damar an sa gidannan a kasuwa, ina ta tunanin ta yadda zan sanar maki kada ki ji abin daga sama shi..."
"Haba Abban yara, wace irin magana kake yi ne? Mene ne ciki don ka sadaukar da abin da yake mallakinka don fansar yarana? Idan da ace yau nima na mallaki wata dukiya kana tunanin ba zan iya sadaukar da ita domin ceto ransu ba? Don Allah kada ka sa naji kamar kana bambanta Humaira da Ummita da yan uwansu."
Tun faruwar al'amarin na su Humaira, Abba bai yi koda murmushi ba sai a yanzun, ya kamo hannun Mami ya riƙe gam cikin nashi.
"Ina kaunarki Maryam, Allah ya yi maki albarka. Nagode da kika fahimce ni."
Itama murmushinta ta faɗaɗa gami da shafar gefen fuskarsa.
"Nima ina kaunarka. Yanzu ajiye godiyarnan, ka daure ka sa abu a cikinka sai a je a san ya za'a yi. Ina fatan dai ba ka faɗawa D.P.O yadda ku ka yi ba ko?"
Abba har ya buɗe baki zai magana sai ya tuna yadda suka yi da D.P.O da safe. Sun tattauna ya sanar da shi komai bai rufe ba akan batun kuɗaɗen fansa da aka nema.
*_Koda wasa Yallaɓai kar ka nunawa kowa ka faɗamin yadda ake ciki. Komai kusancinka da mutum, ka ɓoye wannan tattaunawarmu saboda mutane su na da ban tsoro, koda ace ka faɗawa wanda ka yarda da shi yadda muka yi, to fa zai iya sanar da wani maƙiyin. Kaf duniya tun da dai daga ni sai Alhaji Bashir (Daddy) muka san da hakan, to ya tsaya iyakar nan, koda ace sun ƙara kiranka a waya kar ka bari wani cikin iyalinka ko ma waje ya sani. Mu kuma zamu yi iyakar yin mu, mu yi kokari mu cafke su duk sadda ka tashi kai musu kuɗin._*
"Ya naji ka yi shiru?"
Mami ta nemi sani tana mai ƙuramasa idanu. Ya numfasa.
"Babu komai Maryam. Ina tsoron na furta masa su ji labari tunda sun gargaɗe ni. Bana fatan a samu matsalar da yarannan za su rasa rayukansu."
Ta jinjina kai.
"Ina ji a jikina za su dawo gida cikin aminci."
Daga haka ta jawo kayan abinci ta shiga zubamasa tana mai lallaɓa shi don ya ci. Dakyar ya tsakuri kaɗan ya miƙe ya yi shiri ya fita don ganin ya kammala kafin ya kai.
Cikin rashin nasara, aka rasa mai siyan gidan Abba, a karshe dai tayin da ya ƙi karɓa a farko na iyayen Fadeel hakanan ya karɓi cikon miliyan huɗu ya haɗa aka tashi kuɗin fansa, babu abin da ya rage sai jiran waya daga kidnappers don a ji lokaci da kuma wurin da za a miƙa kuɗin. Mami ba ta san ya aka yi da batun gida ba, Abba dai ya ce mata an samu an haɗa kudade. Daga nan bai ƙara ko harafin A ba.
***
Humaira da Ummita na rakuɓe a lungu guda na ɗakin sun yi shiru don zuwa lokacin kukan ma ya ƙi fita, aka banko ƙofar ɗakin aka shigo. Su ukun dai da suka zame musu tamkar baƙaƙen kumurci su ne suka shigo. Suka ƙura musu idanu tamkar za su lashe su, Wizzy kamar koyaushe sigari ne a hannunsa, ya fesar da hayaƙin ya dubi Babba da Badboy cikin murmushi ya ce.
"Ni zan fara, ku kuma sai ku biyo baya."
Ba su ji dadin wannan hukuncin ba amma babu yadda suka iya, hakanan suka lashi lebbansu suka ja gefe. Shi kuwa kai tsaye ya ƙarasa ya finciko Ummita wacce ta ƙanƙame jiki guri guda ga jikinta dake masifar rawa.
"Ina za ku kai ta? Ku yiwa girman Allah ku yi hakuri."
Humaira ke zancen cikin ruɗu da tashin hankali. Suka kwashe da dariya.
"Haba Baby, kema ai zan zo kanki. Duk inda zan kai ƴar uwarki kema za ki je. Kuɗin fansarku aka kawo, za a tafi da ku gida."
Humaira sam zancen bai shige ta ba balle Ummita da ba ta san lokacin da ta shiga kuka sosai ba, su na jan ta tana tirjewa, Humaira na zabga uban ihu suka dauke ta da mari suka fidda kyalle suka rufemata baki da idanu. Wizzy haka ya ja Ummita har sai da ya dangana ta da wani ɗakin.
Humaira da suka fita suka rufe kamar ta yi hauka haka ta dinga bugun ƙofar tana gurnani tamkar wacce ake zarewa rai. Babban fatanta bai wuce su ceto Ummita da ko ihunta ba a ji ba sakamakon rufemata baki da aka yi da kyalle.
Ummita na ji tana gani Wizzy ya keta alfarmarta. Tsananin azaba ya sanya ta sumewa ba tare da sanin inda kanta yake ba. Shi kuwa ya fito yana sharɓar gumi, ya dubi su Badboy cikin annashuwa ya ce.
"Ku bari shegiyar ta farfaɗo sai ku ƙara farr mata, suman dadi ta yi."
Suka kwashe da muguwar dariya. Yana kai wa nan ya shige wurin Humaira.
Tana ji an bude ƙofar ta yi saurin karasawa gami da shaƙe wuyan rigar Wizzy tana um um saboda bakinta da ke ƙulle ta ma kasa magana. Ya yi dariya gami da tura ƙofar da ƙafarsa ta baya ya damƙe hannunta.
"Haba my love? Kokawarnan da kike wani sanyamin ƙarfi ai sai ki jigatar da kanki tun ma ba a je ko'ina ba."
Daga nan ya soma kiciniyar raba ta da kayanta yana taɓa wasu ɓangare na jikinta, nan da nan ta ji kanta ya soma wani irin sarawa, wani irin baƙin ciki da ba ta za ta iya kimantawa ba ya tsaya mata cak a ƙahon zuci. A sadda Wizzy ya yi nasarar keta rigar dake jikinta, a lokacin ne gaba ɗaya tsikokin jikinta suka mimmiƙe. Idanunta suka ƙara turuwa suka yi ja, ba ta san lokacin da ta shaƙo wuyansa ba har ya shiga kakarin mutuwa. Duk iya ƙarfin da ya sa da zummar ƙwatar kansa ya kasa, ga shi ba damar ihu saboda koda ya yi abokan aikinnasa za su yi zaton na lafiya ne. Haka suka ƙarasa har jikin ƙofar da ba ta rufe gaba ɗaya ba.
Anan ne Badboy da ke zaune saitin ƙofar ya hangi hannun Wizzy na lilo, da wani irin gudu-gudu ya tunkari ƙofar, shima Babba ya mara mishi baya. Daƙyar suka tura ƙofar ta buɗe. Abin da suka gani ya yi mugun rikita su, Humaira dai ta zame musu tamkar wata ƙaƙƙarfar damisa, daƙyar da suɗin goshi suka ƙwace Wizzy a hannunta, Babba ya fice da shi daga dakin yayinda Badboy ya tunkareta da niyyar kifamata mari sai dai yanayin da ya ga ta taso ta yi kansa ne ya sa shi ficewa babu shiri. Nan ta kife zaune tana rirriƙe kanta dake azabar sarawa tana huci ga uban gumi kuma ga baki a ƙulle. Kukan nan da ta saba yi ta shiga rerawa mai mugun tsuma zuciya, ta fi rabin awa a haka har ba ta san an shigo da Ummita an watsa ta a kusa da ita ba.
Abin da Humaira ta aikata ne ya sanya Wizzy dakatar da su daga ketawa Ummita haddi, ya ce su kyale su kafin su kashe su labari ya sauya tunda gobe za su cafki kuɗadensu. Da wannan suka rufe su gam suka bar gidan su Babba da Badboy na ɗacin ran ganin samu da kuma rashi lokaci guda. Ganin haka Wizzy ya yi musu alƙawarin zai ba su sabuwar yarinyarsa da ya yi a wurin mashayarsu kowannensu ya more da ita, sun ɗan ji dadin hakan tunda ko ba komai ita bariki ke yayi a lokacin. Kowa kuma mararinta yake.
Ummita da har lokacin ba ta da kuzari, kusan ma yanzun suman zaune ta yi. Ga uban azaba da ta ke ji a ƙasanta, gaba ɗaya hawayenta ya kafe ta ma kasa koda kukan, tun shigo da ita abu ɗaya ne a bakinta take furtawa sanadiyyar ƙyallen da aka ciremata, Innalillahi kawai take ambato daga farko har ƙarshe, wannan daren babu wanda ya runtsa sai Humaira da bayan gama koke-koken wani bacci marar dalili ya ɗauketa kamar yadda ta saba.
***
A firgice Raihana ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi wai an soka wuƙa a wuyan Ummita, Humaira kuma tana kwance cikin jini. Wani ƙara ta saki mai firgitarwa ta zabura ta miƙe daga gadon Mami ta nufi hanyar fita daga ɗakin. A hanyar ƙofa ta ci karo da Mami kasncewae asuba ta kawo kai, Abba ya fita masallaci. Cikin tsananin ruɗani Mami ta riƙe ta.
"Meyafaru Raihana?"
Ta ruƙunƙume Mamin sai kawai ta fashe da kuka mai tsanani. Mami ba ta ce mata komai ba ta shiga shafar kanta. Don kanta Raihanar ta sassauta kukan sannan ta ɗago kai ta ce.
"Mami nayi mafarki marar daɗi akan su Humaira. Har yanzu ba su kira Abba a waya ba? Mami a kai kuɗaɗennan a dawomin da ƴan uwana yanzu kafin lokaci ya ƙure. Kar su kashemin su."
Mami ta riƙe hannuwanta.
"Kar ki damu da mafarkin da ba lallai ya kasance gaskiya ba. Ki yi addu'a da fatan alheri. Ina mai tabbatar maki babu abin da zai faru da su, lafiya kalau za su dawo gidannan ki gan su."
Raihana ta ɗauki maganganun Mami kawai don ta kwantar mata da hankali ta faɗi, amma ina da ta ke da tabbacin ganin ƴan uwannata cikin kwanciyar hankali? Haka dai ta dinga lallaɓa ta ƙarshe ta samu nutsuwa ta fice ta ɗora alwala ta tayar da sallah amma har sannan kirjinta na dukan tara tara. Wannan dalilin ne ya sanya ta tsaya ta yi addu'a sosai har ta jawo Alƙur'ani ta karanta ta roƙarwa yan uwanta tsari daga sharrin dukkan masu sharri.
***
Ƙarfe shida na safe daidai sai ga kiran Wizzy ya shigo wayar Abba. Abba ya ɗaga jiki na rawa. Nan yake tambayar ko kuɗaden sun samu, ya amsa da eh. Daga nan ya yi mishi kwatancen inda za su haɗu, ya ƙara da faɗin.
"Ina ƙara gargaɗinka, kar ka sake ka yi kuskuren zuwa da jami'an tsaro idan ba haka ba a gabanka zan yanka wuyan ƴaƴanka."
Abba ya hau girgiza kai tamkar Wizzy na gabansa.
"Aa aa, ni kadai zan zo. Ba zan saɓa alƙawarinku ba."
Daga nan kit aka kashe wayar, ya ɗaga kai ya dubi lokaci, yanzun shida da mintuna, an kuma ce mishi bakwai daidai ya isa wannan dalilin ne ya sanya shi miƙewa ba shiri ya janyo jakar kuɗaɗen. Tunanin ya kira D.P.O ya sanar masa yake amma kuma yana jin tsoron kar su cutar da su Humaira sai dai ya ɗan yi shahada ya dannawa D.P.O kira, suna cikin magana Mami ta iso, Abba bai ko lura da ita ba don hankalinsa ya yi gaba. D.P.O ya ce za su fito su ma cikin kayan gida da kuma