Showing 75001 words to 78000 words out of 93383 words
a yanda take juya mijinta a gida hakan yasa ta yanke shawarar tuntuɓarta. Tun sadda ta yi aure ba ta ƙara nemanta ba saboda a ganinta ajinta ya fi nata, sai a yanzun da buƙatarta ta taso.
Kasancewae Aneesa ta iya barikanci, ko kusa ba ta nunamata komai ba suka gaisa hannu bibbiyu. Sai kuma Futuha ta warware mata damuwarta. Dariya Aneesa ta yi kafin ta amsa.
"Ai wannan ba matsala ba ce yar uwa, amma ki yi yanda yace. Ke banda abinki mene ciki don kin zubar da cikin wanda ya nuna ba ya son haɗa zuri'ar da ke? Kuma wallahi kika yarda kika haihu da shi to ina mai tabbatar maki nan da nan za ki lalace ki zama wata daban. Ki daurewa ranki ki zubar da cikin idan ya so ki kawo kudi mu san hanyar da zamu bi ki mallake shi, yanda ko tsinke bai isa ya tsallake ba matukar ba ki yi mishi izini ba."
Cikin sanyin jiki da kuma ɗan nutsuwar da Futuha ta samu ta ce.
"Toh Aneesa. Ni dama tsoron mutuwa nake, kada na sha na mutu naji ance masu zubar da ciki mutuwa suke yi."
"Mutuwa ai sai lokaci ya yi, nidai ina ba ki shawarar ki zubar kuma ki je ki yi planning abinki hankali kwance. Matukar dai kina so mu cimma burinmu."
Ta sauke ajiyar zuciya ta jawo ledar magungunan sannan ta ba Aneesa amsa.
"Shikenan, yanzun nan zan sha. Nagode Aneesa, zuwa gobe duk yanda ake ciki zan kiraki mu ji abinda ya dace a yi."
"Shikenan, sai na ji ki."
Daga nan suka yi sallama. Ta ƙurawa magungunan idanu, a wata farar takarda suke, ta yi shiru can kuma kamar wacce aka tsikara ta mike ta dauko gorar ruwa ta bude, ta zazzaga magungunan a hannunta ta shanye su tas sai jiran sakamako.
***
Tana kwance tana juyi yayinda yan uwanta duka ke bacci abinsu. Ta mike zaune ta yi shiru, tashin zuciya take ji sai dai ta rasa yanda za ta yi ba ta kaunar ta yi amai motsin yunƙurin ya tashe su. Zuwa lokacin ta soma shan jinin jikinta, tsoro da firgici ya soma shigarta. Bai fi kwanaki uku watan da suke ciki ya mutu ba amma har yau babu labarin ganin al'adarta. Tsoro iyaka Ummita na cikinsa. Ta kasa jurewa tashin zuciyar da take ji sai ta bude dakin ta fita da sauri zuwa falon bandaki, nan fa ta shiga kelaye amai kamar hanjin cikinta za su zubo. Duk wani kayan kwalam da ta ci a ranar sai da ta dawo da shi. Ta kammala ta wanke fuska ta gyara wurin, ta kuma ɗauro alwala ta dawo falon ta zauna. Sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ga wani irin mugun sanyi da ya lulluɓe ta lokaci ɗaya. Ba ta son koda tuna kalmar da take tunanin shi ya zama damuwarta balle har ta furta.
'Idan ya tabbata haka din ne ya za ki yi da Sahabi?'
Zuciyarta ta watso mata tambayar, ta rike kai sai kawai ta fashe da kuka sosai. Ba ma Sahabin kawai ba, ta ina za ta soma karɓar wannan ƙaddara na rainon cikin da ta same shi ta hanyar fyaɗe? Fyaɗen ma daga ɗan ta'adda?
Tana wannan kukan mai tsuma zuciya ba tare da sanin irin ƙarfin buɗe muryar da ta ke yi ba har sai da ta ga hasken fitila a falon an kunna saboda akwai wuta. Mami ce, kafin Mamin ta ce wani abu sai ga Humaira a gigice ta fito itama. Kusan lokaci guda suka ƙaraso gareta.
"Mene ne ya faru Ummita?"
Humaira ta tambaya jikinta har yana rawa nan da nan itama ta soma hawaye ba tare da sanin ainahin dalilin kukan yar uwarta ba.
Ummita ta rungumeta tana kuka sosai.
"Ciki Humaira, Humaira zan haifi shege."
Da karfi kuma cikin daga murya Humaira ke girgizata kamar zararriya tana fadin.
"Wa ya fadamaki kina da ciki? Karya ne! Karya ne ba ki da ciki!!"
Mami ta dago Ummita.
"Wa ya fadamaki wannan mummunan labarin? Kin ga wasu alamomi ne?"
Mamin ta fadi nata hankalin itama a mugun tashe, nan da nan cikinta ya duri ruwa. Cikin sheshsheka Ummita ta ce.
"Ma..ma.mi, amai nake ta yi."
Ajiyar zuciya Mamin ta sauke.
"Haba Ummita, amai kuma sai aka ce maki yana nuni da cewa kina da ciki kenan? Amai ai alamun cutuka ne da dama, ba lallai sai ciki ba. Lokacin al'adarki ya yi ne?"
"Eh Mami, har ya wuce."
Gaban Mami ya buga da ƙarfi, Humaira sunan Allah ta shiga ambato sakamakon ji da ta yi tamkar an zare mata wani laka na jiki. A durkushe take amma kuma jiri ne ke kwasarta. Tana ji tamkar a mafarki ake wannan diramar ba a farke ba.
"Maryama, meke faruwa ne?"
Suka juya gaba daya, Abba ne sanye fa jallabiya a tsaye a ɗan rikice, ya tako ya ƙaraso ganin Ummita na kuka ya sanya shi ƙara jin rashin nutsuwa sosai.
"Ummita, meyafaru kike kuka?"
Mami ta yi saurin share hawayen da suka zubomata, ta miƙe tsaye.
"Babu komai, ba ta jin dadi ne. Humaira ku shiga ciki. Ki kwantar da hankalinki gobe idan Allah ya kaimu zamu yi test a gani."
Bayan wucewarsu Abba wanda ya daskare a tsaye cikin wani mugun faduwar gaba ya ce.
"Maryama, meye hakan kuma? Na kasa gano bakin zaren wannan tattaunawar da tsakar dare?! Me kike son ki ce?"
Gaba daya ma Abban ya diririce ko kadan ba ya cikin nutsuwarsa.
Mami ta dafe hannunsa.
"Babu komai Abban yara, muje zan maka bayani."
Zai ƙara magana ta hana shi ta hanyar roƙonsa akan su tafi dare ne kar a ji sai kuma ya hadiye maganar ba musu ya yi gaba zuwa ɗaki ta bishi a baya bayan ta kashe fitilun falon.
Ya ji zancen tamkar saukar aradu, nan da nan ya dafe kansa.
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Maryama wannan mummunan labarin da me ya yi kama? Tashi tashi muje asibiti yanzu a dubamin ita."
Mami cikin hawaye ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar dafe kafarsa gami da girgiza kai.
"Aa Abban yara, kar muyi haka. Yin hakan tamkar tonuwar asirinmu ne. Duniya sai ta san halin da muke ciki. Ka kwantar da hankali tunda ana siyar da Pt-strip na awon ciki, gobe da safe mu bayar a siyo a auna fitsarinta don mu ga halin da take ciki. Mu yi fatan alheri da fatan kar zatonmu ya tabbata.
Ajiyar zuciya mai karfi Abba ya saki.
"Innalillahi...Ya Ilahi! Wannan ranar dame zan kirata ni Isuhu? Inama tun farkon fari ban hana Hajiya Maijidda riƙon Ummita ba tun tana ƙarama, da watakila ba zan ga wannan ranar ba."
Wani irin zuciya ya tasowa Mami, ta ji tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu. Ranta ya yi mugun ɓaci, wato duk hakuri da dauriyar shanye damuwa da bakin cikin RIƘON BARE da ta yi, da wannan sakayyar Abban zai bi ta? Ta so ta furzar da abinda ke ranta sai kuma ta daure kamar koyaushe ta shanye rabi da kwatan ɓacin ranta ta ce.
"Wane irin rashin tawakkali ne haka Abban yara? Ka isa ka hana Allah ikonsa ne akan al'amarin Ummita? Ummita ko bangon duniya ta je idan hakan ya ƙadartu a kanta sai ya afku. Ban da haka ma, kenan kana kaicon rayuwar da ta yi a hannuna? Kana kaico da irin abin da ya fada mata? Ko a tunaninka a sanadina ne aka sace su har kaddarar fyaɗe ya faɗa kan Ummita?"
Ta karasa zancen da wani irin kausasshen murya, ganin ya kalleta da sauri da alama zancen bai mishi dadi ba kuma bai san fassarar da za ta ba shi kenan ba ya sanya ta fashewa da kuka mai tsuma zuciya.
"Dama na sani Yusuf, watarana sai ka ga gazawata akan yarannan duk kuwa da..."
"Haba Maryama, don Allah don Annabi s.a.w ki yi hakuri. Wallahi zafin bacin rai da damuwa da tashin hankali ne ya sanya ni wannan maganganun marasa kyawun ji. Ko daidai da kiftawar ido ban taɓa kawowa za ki cutar da wani a cikin yaran da kika haifa a cikinki ba ma balle a kai ga Ummita. Yarinyar da kika daukaka ta kika kuma riƙe ta hannu bibbiyu tamkar ke kika haife ta a cikinki. Wane irin butulu ne ni da zan yi maki haka? Ki yafemin domin Allah. Na tuba kiyi min uzurin halin rudani da tashin hankalin da na tsinci kaina ciki."
Mami ta mike ta ja guntun tsaki ya yi saurin tarar gabanta.
"Haba Maryama, da wanne kike so na ji ne? Da tashin hankalin nan na Ummita ko kuwa da ɓacin ranki? Faɗamin, me kike so nayi ki huce?"
Jin haka sai kuma ta yi shiru tana goge fuska.
"Kar ka ƙara irin wadannan kalaman naka na rashin tawakkali."
Ya yi murmushin karfin hali ya rungumeta.
"Idan har wannan ne ba zan kara ba. Na ma yi istigfari tun sadda kika ankarar da ni kurena. Mu ji da damuwa daya yanzu."
Ta gyada kai, bandaki ta shiga ta ɗora alwala ta sanya hijabi ta hau saman darduma. Sosai yake jin so da kaunarta a zuciyarsa. Shima sai ya fasa neman wuri ya kwanta kamar yanda ya so duk kuwa da irin sakensa a ibada lokuta da dama. Kusan wannan shi ne kadan daga inda ya kuskuro, rashin tsayawa kai da fata wurin ibada sosai sai idan ya fada matsala babba.
***
Washegari tashin hankalin da suka riski kansu ciki sai ya mantar da su wani batun zuwa kai Humaira asibiti.
Gidan ya zama tamkar gidan makoki. Suna zaune jigum suna jira Mami da Ummita su fita daga bandaki don sanin matsayar Ummita, akwai cikin ko babu. Abba ya kasa fita kasuwa si safa da marwa yake a falon balle kuma Raihana wacce tun jin abinda ke faruwa ta kasa motsawa ballantana ta wuce makaranta. Sai Humaira da ta dau carbi tana jin tamkar an yi mata mutuwa. Mubarak kuwa wanda shi ya fita ya siyo abin awon cikin, sai ya jingina jikin bangon falon ya yi shiru cikin bugun zuciya.
A wannan yanayin Mami ta fito a gigice kuma a guje, gaba daya suka yi kanta har suna rige-rige.
"Meke faruwa?" Faɗin Abba yana jin kamar ya kife tsabar jiri.
Mami ta fashe da kuka.
"Mun shiga uku! Shikenan Abban yara asirinmu zai tonu. Ciki ne da Ummita."
Abba ya ja baya da sauri ya zauna saman kujera mafi kusa da inda yake, yayinda Humaira ta yi mutuwar tsaye. Ita kuwa Raihana kwasa ta yi a guje zuwa bandakin don ganin halin da Ummitan ke ciki. Aikuwa ta iske ta a kife tamkar babu numfashi. Ta kuwa ƙwalla ihun kiran sunan Abba. Kusan da rige-rige suka shiga banɗakin. Mubarak ne ya yi ta maza ya cicciɓe ta bayan ya tabbatar da bugun zuciyarta ya fiddo ta falon ya shimfiɗe saman kujera sai dai duk wani kokari na watsa ruwa da ma sauransu anyi amma babu alamun Ummita ta san ana yi. Ana shirin fita asibiti Mami ta dakatar ta ce gwara a kira makwafciyarsu wata likita gudun fashewar zancen a duniya. Abba ya yi na'am, Mubarak ne ya fita da rawar jiki har gidan Dakta Inteesar an ci saa kuwa ta fito cikin shirin tafiya asibiti. Ganin Mubarak aboki ga babban ɗan ta Najeeb ya sanya ta dakatawa. Roƙon da ya hau yi mata ya sa ba ta iya yi mishi musu ba sai ta shiga motarta suka kama hanyar gidan don akwai ƴar tazara kaɗan ita daga bayansu take. Cikin ikon Allah ta ba Ummita taimakon gaggawa ta farfado sai kuma ta dube su.
"Ya dace a yi mata gwaji sosai din tabbatar da abin da ke damunta."
Ta furta hakan ta yi shiru don jin me za su ce, a matsayinta na likita ta gama tabbatarwa Ummita na da juna biyu. Shiru ta yi musu don ta fi son ji daga bakinsu sun amince da gwajin. Tana sane da labarin abinda ya afku ga Ummita. Su kansu mutanen gida ba su da masaniyar cewa duk yadda suka so da ɓoye labarin fyaɗen Ummitan sai da ya fita ba. A duniyar yanzun ai mutum ake kiwo ba dabba ba, kana abu kana ganin tamkar duniya ba ta sani ba amma zirr ake kallonka.
Abba ya yi yaƙe.
"Babu damuwa Dakta, zamu kai ta asibiti."
Ta lura ba su son zancen ya fasu, ita kanta ta tausaya musu babu kamar Ummita wacce tunda ta farfado uffan ba ta ce ba, kukan ma ta ƙi yinsa sai sauke ajiyar zuciya akai-akai. Haka Dakta Inteesar ta yi musu sallama bayan ta rubuta magungunan da ya dace wanda take da tabbacin zai taimaki Ummita bisa yanayinta na mai juna biyu. Mubarak wanda ke tsaye ya ƙurawa Ummita idanu yana jin abu mai nauyi na taso mishi wanda ya fi kama da tsabar tausayinta da kuma kauna ta ƴan uwantaka. Kamar dai yanda yake tunani. Shi ne ya karɓi takardar magungunan ya fice.
***
Kwance yake idanunsa a lumshe, babu komai a ransa sai Humaira. Yana ji a jikinsa an soma zuwa gaɓar da yake da tsananin buƙatar kasancewarsu tare a inuwar aure. Shi din fa ba dutse ba ne, namiji ne kuma lafiyye da yake buƙatar aure. Soyayya mai ƙarfin da yake yiwa Humaira shi ne silar da ya danne wannan buƙatuwar ya ɗora shi kacokam a kanta yana jiran lokacin da mafarkinsa zai tabbata. Sai dai kuma yaushe ne?
Wannan damuwar ce ta hana shi fita ko'ina, hatta da mai gyara mishi dakuna bai san yana nan ba, shi dai Nura yana falo yana aiki kafin ya shiga ɗakin. Hatta shi bai dan cewa Fadeel na gidan ba sakamakon motarsa da ba ta nan tun daren jiya. Ɓaci ta yi a hanya ya bar ta can makanikinsa ya je ya ɗauka.
Daidai lokacin Murja ta faɗo ɗakin da ƙunshin kayan gugan Fadeel din a hannunta wanda ta karɓa a hannun Sadi mai gugansu, dama ta jima a yar barandar da zau sada ta da ɗakin Fadeel tana tunanin dabarar da za ta yi wa Lawal ta shiga. Sai ko ga Sadi ya zo wucewa nan da nan ta karɓa ta ce za ta karasa da shi.
Suka gaisa da Lawal a falo, ta nuna zai karɓa ya shigar da su ta ce masa ya bar shi za ta karasa ladanta. Bai ce komai ba, dama a farko gargadin da Fadeel din ya yi mishi ne ya sanya shi dakatar da ita, ya hana kowa ya shigo masa sashinsa idan ba ya nan matukar dai ba Fu'ad ko Alhaji da Ibb bane. Amma ganin kayan wankin ne kawai za ta ajiye ta fito ya sanya shi ba ta wuri shi kuma ya ci gaba da kakkaɓe kakkaben kujeru da kayan kallo.
A lokacin da ta shiga dakin, Fadeel ya zagaya bandaki, yana dab da fitowa ya ji motsin mutum a dakinnasa, bai kawo kowa ba sai Lawal. Ya san ba shi da masaniyar yana gida bai fita ba. Don haka ya fito daga shi sai singilet da dogon wandon sport.
Daidai lokacin da ta ajiye kayan a gefe ta yi wurgi da filo ta ɗaga katifar gaba ɗaya da zummar sanya layar. Kasancewar idanunta ya rufe ko kadan ba ta ga wayoyin Fadeel din dake gefe ba a ajiye. Tana zuci-zucin ta yi ta ƙare kafin shigowar Lawal ya isketa.
Fadeel ya bude kofar ya fito, hakan ba karamin razanata ya yi ba ta saki layun dake a hannunta suka zube a ƙasan darduma. Mamaki mai tsanani ya kama shi har ya bude baki ya kasa magana. Ya karasa sosai ya kara kallo, tabbas layu ne. Nan da nan ya tamke fuska tamkar bai taɓa wani abu wai shi dariya ba.
"Zamanki a gidannan ya ƙare. Wallahi kin ji na rantse maki ko yau Anti Amarya ce ta haifeki dole ki bar gidannan. Ni Fadeel na fi ƙarfinki, na kuma fi karfin duk wani da zai sanyaki aikata mugun abu don ki ci galaba a kaina."
Jin haka sai kawai ta hau tsuma da borin kunya.
"Ni..nifa ba.."
"Shut up!"
Tsawar da ya yi ya sanya Lawal faɗowa ɗakin. Nan da nan hankalinsa ya tashi, shima idanunsa suka sauka kan layar dake ajiye a tsakar dakin. Fadeel ya hau shi da faɗan don me ya bari ta shigo masa daki alhalin ya gargaɗeshi.
"Ka yi hakuri Yallaɓai, wallahi na yi nayi da ita ta bani kayan gugar na kawo ta nunan ita za ta kai. Shi ne.."
"Shi ne me?!"
Fadeel a zafafe ya tari numfashinsa jikinsa har ɓari yake yi ga tsikar jikinsa da ya tashi gaba daya. Abin da ya faru shekarun baya kawai ya fadomasa a rai, sadda ya kama Mamar Fu'ad tsamo tsamo a ɗakin Mahaifiyarsa tana barbaɗa magani. Daga ranar ya tsane ta, rashin wayo da wauta kuma ya sanya bai yi tunanin sharewa ba. Tun daga kuma sadda mahaifiyarsa ta taka wannan magani ba ta ƙara zaman lafiya ba da Alhajinsu, har dai a karshe Alhaji ya yi mata sakin wulakanci. Shi kuma ya sha baƙar wahala a hannun Mamar Fu'ad. Ya ji ya ƙara tsanar Murja ninkin ba ninkin. Kuma yanda ya rantse ba zai yi kaffara ba sai Murja ta bar masa gida ubansa idan ko Alhaji ya ƙi to fa shi zai bar gidan gaba ɗaya.
Murja cike da kunyar kamen da aka yi mata ga uwa uba Lawal dake tsaye ya ƙi fita yana kallon ikon Allah, ta durkusa ta kwashi layun ta fice tana dakawa Lawal wata uwar harara kamar idanunta zasu zazzago.
Fadeel ya dafe kai yana mai runtse idanu zuciyarsa na tafarfasa tamkar an kunna ruwan heater.
"Ka yi hakuri in sha Allahu zan kara kiyayewa."
Gyada masa kai kawai ya yi gami da yi mishi alama da hannu akan ya fita, Lawal ya juya ya fice mamakin wannan hali na Murja da bai taɓa zato ba. Lallai mutum ba abin yarda bane.
Shi kuwa Fadeel sai da ya samu nutsuwa sannan ya fada wanka, ba shi da niyyar fita daga gidan amman daga faruwar al'amarin ya ji gaba daya gidan ya fita a kansa. Kai tsaye wurin Ibb ya tafi, dama tun jiyan yake faman kiransa akan zancen bikinsa da ya taso yana ƙin zuwa yana ba shi uzurirrika saboda damuwar Humaira da batun auren Ibb ke taso masa da shi.
Murja kuwa tana zuwa ta