Showing 90001 words to 93000 words out of 93383 words

Chapter 31 - DUKAN RUWA

Start ads

10 Aug 2025

573

Middle Ads

falon ba, har da Mami da Abba wanda bai je kasuwa ba saboda lamarin fasa auren Ummita sosai ya taɓa ransa, dama kuma ya san da zuwan ranar, amma babu yanda iya.

"Kai Mubarak, mene ne haka kake ihu a gida?"

Mubarak da idanunsa suka kaɗa gaba daya ba cikin nutsuwarsa yake ba, daga shi sai singilet da wando three quarter, fuskarsa ta yi jazur abinka da farin mutum. Waya kawai ya miƙawa Abba, Mami da su Humaira har su na rige rigen zuwa leƙa saman wayar. Rubutu ne a ka yi dogo, headline din rubutun mai jan hankali sai ko rubutun.

_*GASKIYA TA YI HALINTA..._*

_*Rahina Sani da Humaira Yusuf wadanda kwanakin baya ake tunanin sace su aka yi, a yanzu gaskiya ta yi halinta._* _*Yan matan sun bi samarinsu ne yawon sharholiya inda a karshe har ɗaya ta zubar da cikin da ta yi yayinda ɗayar kuwa Allah ya tona asirinta cikin ya ƙi zubewa tana nan yanzu haihuwa yau ko gobe. Bincikenmu ya tabbatar da cewa ba sace su aka yi ba, dama ƴan hannu ne suka bi abokan watsewarsu ganin asirinsu zai tonu ne ya yi sanadin da suka haɗa baki suka yi ƙaryar an sace su._* *_Tabbas inda ranka za ka sha kallo da mamaki._*

Sakin wayar Abba ya yi har yana taga-taga zai fadi, da taimakon su Mami dake kusa da shi ya samu ya zauna a kujera mafi kusa saboda rawar jiki. Humaira kuwa zuciyarta ke wani irin tafarfasa ranta idan ya yi dubu ya ɓaci, waye wannan ke kokarin ɓata musu suna a idon duniya? Mene ne ribarsa?

"Wannan wace irin rayuwa ce? Daga wannan sai wannan? Waye da wannan aikin? Kai Mubarak a ina ka samo mummunan labari haka?"

Duka wannan zantukan Abba ke yinsu lokaci guda cikin rawar murya mai nuni da zallar ɓacin rai. Mubarak da ya dauki wayarsa ya amsa.

"Abba ina zaune naga an turo group din da nake har da masu bibiyata ta inbox su na tambayar ko dagaske ne. Da na duba naga an yi forwarding sama da sau hamsin. Wannan ya sa na fahimci koda ace ba a jima da baza labarin ba, toh ya samu karɓuwa ainun."

"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! A duniya ba ka sanin cewa kana da maƙiya sai irin hakan ta kasance. Ina so maganar nan ta tsaya iya mu da wadanda suka sani a gidan, koda wasa kar a faɗawa yarinyarnan ko don yanayin da take ciki. Mu rufe duk wata ƙofa da za ta tsinci labarin. A karɓe wayarta, ku kuma ku kiyayi tayar da zancen a gabanta. Ni kuma in sha Allahu sai inda ƙarfina ya ƙare wajen ganin an bi maku hakkinku, koda ace abin da na mallaka zai ƙare sai na sanya an bincikomin me wannan aika-aikar an hukuntashi ya kuma faɗi dalilinsa na aikata wannan abu."

Kowa a wurin ya gamsu da batun Abban, Mami kuwa tunani kawai take yi na waye wannan da ya fi ta nuna ƙiyayya ga yaran? Fatanta kar ya kasance wacce take zargi. Ta sani tunda har Abba ya ci akwashin ɗaukar mataki akan al'amarin to fa babu fashi.

Da wannan aka kashe zancen amma fa ran kowa a ɓace, koda su Humaira suka koma ɗaki, sun tarar Ummita ta shiga bandaki wannan ya sanya da sauri ta ɗauke wayarta ta kashe ta jefa a sif, da Ummitan ta fito ma babu wani a cikinsu da ya nuna mata komai. Ita ɗin ma ba ta lura da yanayinsu ba balle ta mayar da hankali, damuwar rashin Sahabi ya rinjayi komai. Tana buƙatar ganin ta samu nutsuwa ko ya ya ne, tana tsoron ciwon da damuwa za ta haifar mata. Wannan dalilin ne ya sanya ta jin tsoron tambayarsu dalilin kiran da Mubarak din ya yi musu, sai ta zaɓi yin shiru gami da kwanciya ta hau jan carbi.

***
Wasa-wasa sai ga zance ya yaɗu a duniya. Abinka da soshal midiya masu jran ƙiris sai ga labari salo-salo ana juyawa har da masu fitowa su na ƙara nasu gishirin su na ƙara yaɗawa. Abin mamaki da tsoron shi ne har asalin su Humaira da Ummita na kasancewarsu yaran riƙo a gidan da suke haka aka dinga yaɗawa ana faɗin watakila musguna musu ake yi ya yi sanadin shigarsu karuwanci yayinda a wani gefen wasu ke cewa mai yiwuwa son duniya ne ya kai su ga faɗawa halin da suka tsinci kansu. Har da kuma wadanda suka ce koda ace ba karuwancin suka fita da zummar yi ba, zai iya yiwuwa sun yi ne domin su samu maƙudan kuɗaɗe amm a ƙarshe abokan ta'addar nasu suka cutar da su ta hanyar yi musu fyaɗe. Labaru dai iri-iri akan bayin Allahn nan biyu Humaira da Ummita babu irin wanda bai yaɗu ba. Mafi rinjaye sun fi aminta da cewar da haɗin bakinsu aka sace su hakan ta kasance. Ƙalilan ne masu tsoron Allah wadanda ba su yarda da wannan labaran ƙanzon kurege da ake ta fafutukar yaɗawa ba.
  Tsintar wannan labari a wurin dangin Ummita da ma Humaira sam bai zo musu ta daɗi ba. Hankali tashe Anti Maijidda ta diro Kano, ko kaɗan ba su da labarin wai Ummita na da ciki, a hakan ma ba ta amince ba sai da ta zo don kanta ta ga Ummita da tulelan ciki, wannan baƙin ciki yasa har suma ta yi ta kuma tiƙe lallai sai dai Abba ya ba ta Ummita su tafi. Mami kuwa tashin hankalinta bai wuce na wayar da Wizzy ya ƙara yi mata bayan bayyanar labarun da ake ta yayatawa ba akan lallai Ummita na haihuwa ta ba shi ɗansa yana so zai kai wa gyatumarsa idan kuwa ta saɓa zai iya tona asirinta. Wannan dalilin ne yasa itama ta kafe akan Ummita ba za ta tafi ba.

Anti Maijidda ta fusata ainun ta dubi Mami da hawaye jage-jage saman fuskarta tana kai nunata da yatsa.

"Ke Maryam! Ni ba sakara ba ce ki dube ni dakyau! Idan idanun kowa ya rufe ba a ganin aibunki ni kuwa Maijidda ko ruwan teku za ki shiga ki wanke jikinki ki fito ba za ki taɓa sauyawa daga yanda nake kallonki ba. Don haka tun wuri ki fita idanuna na runtse, idan kuma ke kika yi naƙudar Ummita a yau sai ki hana ni tafiya da ita mu gani!"

Jin haka sai kawai Mami ta sa kuka sosai, Abba ransa ya ɓaci yayinda Ummita ta kwantar da kai a kafaɗar Humaira tana nata kukan.

"Hajiya Maijidda ina ganin ƙimarki kuma albarkacin Jamila da abin da ta haifa ya sa ban taɓa ɗaga idanu na faɗamaki maganganu ba. Ko ba komai kina ganina da wannan girman, amma fa ba zai yiwu ace koyaushe ki zauna kina kushe Maryama ba. Haba, duk ƙoƙarin da take yi akan Ummita bakya gani? Meyasa kike nema ki yanke zumuncin da ke tsakanina da ɗiyar ɗan uwana? Ke a ganinki idan ace yau Maryama na cutar da ita zan zuba idanu ne nayi shiru? Ni ga sakarai?"

Mami ta ɗan dube shi ta gefen idanu kawai, yayinda Maijidda ta ji zafin maganganunsa.

"Alhaji Yusuf, na ji Maryam ba ta cutar da Ummita, amma yau idan har ni na isa da Ummita matsayin yaya ga mahaifiyarta ina neman alfarma a wurinka ka bar ni na tafi da ita Bichi. Ka ga dai yadda abubuwa suka rincaɓe, sunanmu gaba daya ya gama ɓaci, ba naku ba, ba kuma ga namu ba ƴan uwan mahaifiyarta. Don haka ina  roƙon arziki ka bar ni na wuce da ita."

Ummita ko kusa ba ta gane ɓacin sunan da Antinta ke magana a kai ba, sai ta yi tunanin ko don cikin dake jikinta ne kuma ga shi nan an soma sani a gari. Abba kuwa, ya yi shiru yana nazarin maganganunta, da alama sun yi tasiri a zuciyarsa. Ganin haka da sauri Mami ta dube shi.

"Yau kenan kana ƙoƙari ka nuna ba ni na haifi Ummita ba? Kokari ka ke yi ka sallamawa Maijidda Ummita ta wuce da ita ko? Kana son nunamin ba ni na haifeta ba, ashe Raihana idan ace ita hakan ya faru a kanta ba zamu yi hakurin duk abin da zai je ya zo ba mu bar ta karkashin kulawarmu ba? Lallai ka sani Yusuf, a yau idan ka amince da dauke Ummita daga hannuna toh ka sani cewa ta tafi kenan har abada ba za ta dawo wurina ba. Na kuma gode da nunamin iyakata da ku ka yi."

Tana kai wanan ta juya ta soma tafiya cikin zubar hawaye, wannan ya tashi hankalin Abba da ma su Ummitan.  Abban na kiran sunanta ta yi banza da shi, ita dai Anti Maijidda na tsaye riƙe da hannuwa a kirji tana kallon irin salon makirci na Mami mai ban mamaki. Ummita cikin sauri ta miƙe ta riƙo hannun Mami tana kuka  kamar ranta zai fita lokaci guda tana girgiza kai amma kalma ɗaya ta kasa fita daga bakinta. Mami ta dube ta cikin hawayen sai kuma ta shafi gefen fuskarta ta yi murmushin yaudara. Cikin karyar da murya ta ce.

"Kar ki damu Ummita. Da nan din da can duk ɗaya ne."

Sai a sannan Ummitan ta magantu.

"Aa Mami, kiyi hakuri. Wallahi babu inda zan je, ke din tamkar uwa kike a gareni. Idan har a duniya za iya barin mahaifiyata toh kuwa zan iya rabuwa da ke. Kin rungumeni a sadda na buɗi idanuna babu iyaye, kin maida ni tamkar ɗiyar cikinki, kin kaunace ni ta kowace fuska. Ni kuwa me zai sa na zama mai butulci a gareki? Kiyi hakuri da kalaman Anti Maijidda, ta yi su ne saboda tsantsar tausayi da kuma ganin kamar zan fi samun kwanciyar hankali a can, amma na tabbata ita kanta ta sani kina nunamin kaunar da ba don kar nayi wauta ba, zan ce ta fi na Raihana da su Anti Tasleem."

Anti Maijidda ta kasa cewa komai tayi gum sai kallo, Abba kuwa sai kalaman Ummita suka kashe mishi jiki, shakka babu gaskiya ta fadi kuma ba zai so a yiwa Mami butulcin nan ba. Ya dai so a farko ya amince da batun Anti Maijidda idan har sauya wurin zai dawo da walwala da farin cikin Ummita. Humaira sosai ta ji dadin kalaman da Ummita ta yi ga Mami, ta tabbata hakan ne kawai zai sanyaya zuciyar Mamin, sai kawai ta ji Anti Maijidda ta sire a ranta. Ita a duniya yanzu ba ta da maƙiyi irin mutumin da zai kushe Mami da ƙoƙarinta a kansu, abin da dai ta fahimta shi ne, ba a iyawa DAN ADAM, wannan sai mahaliccinsa. Ba ta san mene ne ribarta na aibata Mami ba.

Murmushi Mami ta yi tana dubanta kafin ta dubi Anti Maijidda da ta yi mutuwar tsaye. Sai a lokacin Anti Maijidda zuciya ta tunzurota ta soma magana tana duban Ummita.

"Yau kin watsamin ƙasa a ido ko Ummita? Ni kika nuna bani da wani matsayi ko ƙarfin iko a wajenki? Wa.."

"Anti please. Ki duba yanayin da take ciki mana ki rabu da zancen nan haka. Ina haɗa ki da Allah ki bar komai har ta rabu da abin da ke jikinta lafiya idan har dagaske farin cikin kike nema mata."

Mubarak ke wannan tun soma zancen ya shigo yana kuma sauraronsu. Ransa ya ɓaci ba kaɗan ba da yanda Anti Maijidda ke kushe masa uwa kuma mahaifiya amma ya fi jin zafin yadda take neman haifarwa da Ummita wai sabon ɓacin ran na daban. Jinjina kai Anti Maijidda ta yi, ta hadiye ɓacin ran nata kamar yanda ya nema. Dagaske ta fi kaunar samun lafiyar Ummita a yanzun da kuma kwanciyar hankalinta wannan yasa ta taka zuwa ga Ummita ta janyota ta rungume. Yadda Ummitan ke kuka hakanan itama take yi.

"Kiyi hakuri ya isa hakanan, shikenan magana ta wuce. Kiyi zamanki anan zamu dinga waya kin ji?"

Ummita ta gyada mata kai, daga haka kuma aka kashe zancen. Abba da Mubarak suka fita don haɗuwa da D.P.O don tsaurara bincike akan wanda ya yi wannan aika-aikar da ma neman alfarma gurin D.P.O akan ya fito gidajen yaɗa labarai ya faɗi abin da ya sani kan satar su Ummitan zuwa yanda aka kaya sadda aka je kwato su.

Mami kuwa ta ƙara jifan Anti Maijidda da murmushin cin nasara sannan ta juya ta bar falon zuciyarta fari ƙal yayinda ta bar Anti Maijidda da ɗumbin takaici da cizon yatsa. Ta sani addu'a babu abin da ba ya magani, za kuma ta dage da kai kukanta ga Allah, watarana halin Mami zai bayyana ƙarara a idon duniya.

***
Anti Amarya ta dubi Alhaji bayan gama nuna masa jita-jitar da ake yaɗawa akan su Humaira ta ce.

"Yanzu Alhaji wannan magana ko ƙarya ne a yanda sunan gidannan ya ɓaci fisabilillahi sai ka aminta da auren Fadeel da Humaira?"

Nan da nan Alhaji ya ɗaure fuska ya ajiye wayar.

"Me kike son ki cemin? Sai na tauyewa ɗana farin cikinsa akan ƙaryar da maƙaryata suke yamuɗiɗi da shi?"

Ta tari numfashinsa.

"Saboda farin cikin ɗanka mu kuma za ka zubar da namu ƙimar gidan a idon duniya? Ka san wannan ɓacin sunan kuwa ba iyaka Nijeriya ya zagaye ba? Allah kaɗai ya san inda lamarin ya tsaya. Alhaji ya kamata ka buɗe idanunka sarai ka dubi lamarin da idanun basira, ni ban taɓa ƙin Humaira ba saboda ban ga abin ƙi tattare da ita ba kamar yanda babu wani aibu da ta taɓa yi gareni ba. Amma ana magana ne na haɗa zuri'a, idan ya kasance sai bayan mai afkuwa ya afku maganar duniya ta tabbata gaskiya sai ka sa hannu a kumatu ka ce za ka yi tagumi da nadama?"

Shiru Alhaji ya yi, maganganun Anti Amarya suka shiga tasiri a zuciyarsa. Dagaske yanzu idan har zancen duniya ya tabbata shikenan ya haɗa iri da ɓata gari?

Anti Amarya ganin ya yi shiru sai ta yi ɗan murmushin mugunta, ko babu komai dai alamu sun nuna kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta yanda Fadeel bai auri Murja ba ya yi sanadin barinta gidan, toh shima har abada sai ta raba shi da Humaira. Sai ta ga iya gudun ruwansa.

"Shikenan Antin yara, zan dai duba zancen. Mu yi addu'a mu kuma jira mu ga ta inda gaskiya za ta yi halinta."

Ta sauke ajiyar zuciya ganin ta yi nasara.

"Hakane, Allah ya bayyana gaskiyar."

Ya amsa da amin.

Ɓangaren Fadeel kuwa har tsawon kwanaki uku da al'amarin ya fasu yake cikin wani irin tashin hankali da baƙin ciki. Soyayyar da yake yiwa Humaira ta yi ƙarfin da ko daidai da ƙiftawar idanu ba ya zarginta da fasiƙanci balle kuma ya aminta da jita-jitar da ake yaɗawa. Wannan ya sanya a ɓangarensa shima ya sanya aka soma bincike akan al'amarin don a gano bakin zarensa. Ga bikin babban amininsa nan da kwanaki uku amma hakanan damuwar yanayinnan ya gusar da murnar bikin a zuciyarsa. Ta yaya mutanen da aka ceto su cikin wani hali na maye da kuma muguwar rama da baƙi ace yawon duniya suka shiga? Har abada ba zai yarda da wannan ba. Da taimakon wani abokinsu na makaranta wanda yake babban ma'aikacin sirri na SS, bincikensu ya dinga zurfi. Ibb dai ya zuba idanu kawai yana ƙara mamakin wannan irin zazzafar kaunar ta Fadeel akan Humaira. Har shakka yake yi kada bayan aure ya zame mata mijin tace saboda shi kam abin ma ya shallake tunaninsa.

***
Tasleem tsaye tana safa da marwa a ƙuryar ɗakinta daga ita sai vest wacce ta ɗage mata saboda girman da cikinta ya yi sai ko ƙaramin short, waya ne a kunnenta, burinta kawai Antinta ta ɗaga domin ta ƙagu ta ji labari. Har sai da ta kusan katsewa sannan Jannat ta ɗaga muryarta a sake. Ko gaisawa ba su yi ba ta gangara inda yake ci mata tuwo a ƙwarya.

"Anti, ina ta neman wayarki a kashe na ƙagu naji daga bakinki. Kin ji labarin da ke yawo a media akan su Humaira ko? Anti hala aikinki ne?"

Wata dariya Jannat ta yi daga ɓangarenta tun ma kafin ta ce komai Tasleem ta samu amsar tambayarta, sai kuma ta magantu.

"Ni ce nan my daughter, ai ban fanshi marin da munafukar ƙanwarki ta yimin ba. Idan sunansu ya ɓaci a idanun duniya wa kike tunanin zai aminta da auren ɗaya a cikinsu? Ko a zatonki wancan sakaran Fadeel ɗin zai ƙara kallonta? Tasleem ki kwantar da hankalinki, yanzu na san na gama ɗaukar fansa akan Humaira don uwarta. Ita kuwa Ummita kinga cikin dake jikinta ya taimaka wurin da jama'a za su yi saurin aminta. Ke tun sadda al'amarin ya faru nake bibiyar kalaman jama'a ina dariya. Huumm muje zuwa."

Tasleem ta yi murmushi sosai.

"Na ji dadin rabuwar Fadeel da Humaira, na sani ko ya nace akan sonta zai wahala iyayen da suka san mutuncin kansu su yarda ɗansu ya aure ta. Amma Anti naji fa wai Abba zai sa ayi binciken wanda ya fara yaɗawa don a gano gaskiyar magana. Bakya tunanin idan aka kama shi asiri ba zai tonu ba?"

Tsaki Jannat ta ja.

"Nawa aka yi irin haka Tasleem, kin taɓa ganin waɗanda aka yi nasarar cafkewa?"

"A'a."

"Toh ki sa ranki a inuwa tawan, babu abin da za su iya. Yanzu ai na kira Abbannaku na jajanta masa har da kukan shegantaka, shi kuwa sai faman godiya da ban hakuri yake."

Suka yi dariya Tasleem har tana riƙe cikinta da ya ɗan motsa saboda dariya.

"Ina yinki sosai Antina."

"Nima haka yar uwa. Maminki ce dai ta matsamin da tambayoyi tun ranar farko shiyasa nake ta kashe waya, wai ita ga mai wayo, bugar cikina take yi don ta gane ko ni ce na sanya a yi amma na nunamata ban san komai ba sai ma da ta faɗamin. Kema ina jan kunnenki koda wasa kar ki kuskura kiyi maganar da kowa."

Tasleem ta amsa cikin jin dadi da walwala.

"Kar ki samu damuwa Anti. Ba ki da matsala da ni."

Daga haka suka yi sallama zuƙatansu cike fal da annashuwar ƙuntatawa bayin Allah.

***
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login