Showing 42001 words to 45000 words out of 93383 words

Chapter 15 - DUKAN RUWA

Start ads

10 Aug 2025

586

Middle Ads

itama zamu yi magana da ita naji ko tana da tsayayye. Na san dai wani yaro da ta kwallafa rai a kansa amma shi bai san tana yi ba."

Abba ya ɗan yamutse fuska.

"Ai kinji irin shirmen yaran yanzu masu biyewa soyayya, ban da shiririta ke ba manema kika rasa ba, mutane nawa ne suka tare ni akan suna sonki amma ki nacewa wanda ba ya so? Allah ya kyauta, lallai ki ce mata nace ta nutsu ta fiddo miji a haɗa aurensu da ƴar uwarta. Kina ji dai iyayen shi Hamza sun ce nan da wata shida suke so a yi komai a ƙare."

"Shikenan, zan mata magana." Mami ta amsa a sanyaye, fatanta Allah yasa Futuha ta cire ran da ta kwallafa akan Ibb ta kama wani.

***
  Futuha na zaune tana danne-dannenta a waya kamar koyaushe, bidiyo mai zafi ta ɗora tana bin waƙa, ta ci ado a bidiyon har ta gaji, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya da dankwalinta na leshi, karanta comments kawai take tana jin dadi tana zabga murmushi, wasu kuwa zagi ne da addu'ar nema ma ta shiriya. Irin wannan sai dai ta ja tsaki ta wuce. Ta ci gaba da kallon bidiyoyin jama'a nan ta ci karo da wani bidiyo da ya ɗaga hankalinta wacce wata Sa'a Ƴar snow ta yi a kanta, zagi ne na cin mutunci da sharri, wai Baby Futuha ta tiktok karuwa ce kuma tana da hotunanta da shaidu akan hakan. Tashin hankalin har da hotonta daga ƙasa gefen bidiyon. Ba ta san sadda ta kwalla ƙara ba a ɗakin bar ya farkar da Humaira me baccin sha biyu. Su biyu ne dama kaɗai a ɗakin, ita Humaira ma ba ta san Futuhar ta shigo ba domin gaba daya sun fita makaranta, kenan ta dawo ita. Kuka sosai Futuha ke yi hannunta har yana kakkarwa. Humaira ta ji hankalinta ya tashi, duk kuwa da cewar ba sa shiri ta miƙe ta ƙarasa gareta.

  "Anti Futuha lafiya?"

Ba ta ko kalleta ba ta wuce da sauri ta yi hanyar fita. Humaira dai na kallon ikon Allah. Toh me ya yi zafi haka? Ta watsar da batunta gami da buga hamma.

Futuha kai tsaye falo ta nufa, babu kowa, cikinta ya ɗuri ruwa, yanzu wa za ta faɗawa wannan abu? Muddin Mami ta ji ranta zai ɓaci don dama ba da son ranta Futuhar ke ɗora bidiyo a Tiktok ba. Anna kuwa, ba lallai shawararta ya yi wani tasiri ba. Don haka kawai sai ta yi ɗakin samarin yayyunta. Kwankwasawa take iya karfinta, babu kowa sai Dawud dake baccin rana. Ya taso a firgice, har zai soma masifa amman ganin yanayinta sai ya fasa.

"Meyafaru?" Ya tambaya a ruɗe. Ta bude wayar da tuni ta shige lock, miƙamasa ta yi. Ya kalla tun farko har karshe, ya dafe kai yana mai runtse idanu.

"Kinga irinta ko! Kin ga abinda nake faɗamaki. Na faɗamaki matan nan na Tiktok muddin suka ga kina musu shiga hanci da kudundune zasu sanyoki a gaba. Ballantana ma ganin kin kama hanyar shahara. Sa'a ƴar snow! Yarinyar ba ta da mutunci ko kadan, matar da ke ikrari a fili ita karuwa ce kuma ba ta ga ranar da za ta rabu da karuwanci ba sannan ta shirya tone-tonen yan barikin tiktok."

Futuha ta jinjina kai har sannan tana sheshsheka, ta san da wannan, haka ɗin ne ma ya sanya ta shiga ruɗu da tashin hankali, waɗanda za su yarda da zancen sun fi waɗanda ba za su ɗauka ba yawa. Ko ba komai jita-jita ya fi saurin yaɗuwa koda kuwa akan ƙarya ne.

"Ya zan yi Dawud? Na shiga ruɗani, me zan ce jama'a su yarda sharri ne aka yimin?"

Dawud ya yi shiru, shima dai kansa ya yi masifar ƙullewa. Ya rasa me zai ce, daga  kuma irin yanda ake zuba ruwan comment na zagi da ma  masu rubuta ai za ta aikata lamarin ya samu karɓuwa kenan.

Kafin su ce komai sai ga wayar Aina'u ya shigo, Dawud ya ɗaga.

"Ke Futuha! Kinga wani  ɗan iskan bidiyo da Snow ta yi a kanki? Wallahi na shiga rudani, mene gaskiyar abin da ta ce game da ke?"

Hankalinta ya kara tashi.

"Aina'u ke ce mafi kusa da ni a ƙawayena, yanzu kin yarda da abin da aka ce a kaina? Idan kika yarda waye ba zai ƙi yarda ba? Wallahi Allah karya take yimin, ni Futuha ban taɓa zina ba a rayuwata. Ke kanki kin sani."

"To ai kuwa wallahi kinji na rantse sai kin yi dagaske za ki wanke kanki a idanun duniya musamman ƴan Tiktok, yanzu na faɗamaki a whatsapp na ci karo da bidiyon an turo group dinmu na makaranta."

Zaro ido Futuha ta yi, ji take komai tamkar a mafarki, ta kasa amsawa. Ga Aina'u a layi tana faman hello hello, ga kuma sunan Babban Yaya (Wato Mubarak) yana yawo a saman screen din, shaidar kiransa ya shigo. Dawud zai katse na Aina'u ya ɗaga  cikin sauri Futuha ta warce wayar ta kasheta gaba ɗaya. Cikinta ya murɗa ba ta tsaya ba shi amsa ba ta ruga ɗakinsu. Ta tsallake Mami wacce fitowarta kenan daga bangaren Anna su na tattaunawa akan auren Tasleem da wadanda ya dace su gayyata cikin yan uwansu na Agadez. Mami ta bi ta da kallon mamaki da tunanin ko lafiya, wayarta ta yi ƙara, ganin Mubarak yasa ta ɗaga.

"Mami, kina sane da abin da yarinyar can ta aikata ko?"

Cikin rashin fahimta da tsananin ruɗewa ta ce.

"Wa kake nufi? Meyafaru wai?"

Nan ya ba ta labarin ire-iren raye-raye da Futuha ke ɗorawa a Tiktok, ya kuma cewa Mamin ta duba whatsapp zai aikomata da wani bidiyo ta gani. Hannayen Mami har rawa suke yi, ta hau online bayan ta kunna data, saƙonni suka shiga faɗowa har na Hajiya Lubna wacce itama bidiyo ta aikomata. Sam hankalinta ya yi gaba akan saƙon Mubarak, ta buɗe ta soma kallon irin ruwan rashin mutuncin da wata wai Sa'a ƴar Snow ta saukewa Futuha, ga hoton Futuhar nan daga ƙasa. Mami tuni hawaye sun wanke fuskarta, ban da innalillahi ba abinda take furtawa, ya yi daidai da shigowar Dawud falon, ganin yanayin Mamin sai ya tabbatar abin da yake gudu ya afku, wato dai Mubarak ya sanar da Mamin komai. Ya kuma san halinsa, maganar ba iyakar Mami za ta tsaya ba, sai ya dangana da Abbansu.

Ganin tsayuwa na neman gagarar Mamin sai ta zauna a hannun kujera mafi kusa da inda take tsaye. Dawud ya karasa da sauri.

"Mami, yi a hankali."

Ta girgiza kai, ina batun hankali anan bayan ɗiyarta ta jawomusu abin kunya abin kuma magana. Kamar kuma wacce aka tsikara ta mike da sauri ta nufi hanyar dakin su Futuha sam hankalinta ba ya tare da ita. Ganin haka Dawud ya mara mata baya, fadi yake "Mami wallahi sharrin ƴan Tiktok ta hadu da shi, ke kin sani diyarki ba za ta aikata maki abin kunya ba. Don Allah Mami ki saurare ni, nasan wace wannan Sa'ar, ba ta da mutunci na ƙarshe."

Inaa! Ba ta san ma yana yi ba, shigarta ɗakin ya yi daidai da fitowar Futuha daga banɗaki, har a lokacin sheshsheƙa kawai ta ke yi. Humaira tuni ta tashi tana zaune gefen gado ta yi shiru, ita dai ta san babu lafiya. Ba ta taɓa ganin Futuha na irin wannan kukan ba kamar na wacce aka yiwa mutuwa. Shigowar Mamin ya sa ta maida hankali gareta, ba ta yi wata-wata ba ta hau dukan Futuha tana kuka tana fadin.

"Shegiya marar tarbiyya! Wato ke ga yar iska ashe raye-rayen da na nunamaki bana so shi ne kika cigaba da yi har ya jawomaki kalmar karuwa?!"

Mami bugu take ita kuwa Futuha tana ihun kuka. Humaira da Dawud hakuri kawai suke ba Mami, su kansu hankalinsu ba a nutse ba. Babu kamar ita Humairar da ba ta san hawa da sauka ba. Mami don kanta ta ture Futuha ta juya, har za ta fice ta dawo ta nuna ta da yatsa.

"Na ba ki mintuna uku ki gaggauta goge account dinki kaf na social media da kike raye-rayen banza, wallahi kika bar ko guda daya ban yafemaki ba. Shashasha kawai!"

Tana kai wa nan ta fice daga dakin har tana bangazar Dawud. Jikin Humaira a sanyaye ta kalli Dawud, kamar jira yake kuwa ya watsa mata banzan kallo.

"Algunguma, ficemin daga daki za mu yi magana da yar uwata."

Kamar ta ce mishi ai Abba ya hana su shigowa dakin sai dai ta hadiye ta fice sum-sum zuwa falon da babu kowa ta zauna jugum. Yau ba ta je gidan Anti Laila ba sakamakon rasuwar da aka yiwa Anti Lailar a can dangin mijinta. Tana nan zaune ta ji muryar Abba a bangarensa yana tashi har zuwa cikin falon, faɗa yake kamar zai ari baki. Mamaki ya kama ta, Abban bai fita kasuwa ba ko kuwa dawowa ya yi? Yanzun tare suke tafiya da su Yassar har Dawud wanda shi yau din bai jw ba sanadin ciwon kai da ya addabe shi Abban ya ce ya zauna, ya ce musu sam ba ya son zaman banza.

Humaira ta mike tsaye kirjinta na bugawa da sauri. Ta dai tsinkayi Abban na cewa "Cire ta zan yi daga makarantar! Itama ta fiddo miji na aura mata ko kuma na aurar da ita ga koma wane ne don wallahi ni dai Isuhu ba za ta yi sanadin zubewar mutuncina ba a garinnan!'

Gaba daya jikin Humaira ya hau rawa, ko ba a faɗa ba ta sani akan Futuha ake tashin hankalin nan. To me ta aikata mai muni har haka da maganar ta yi zafi? Tana nan tsaye Yassar ya shigo falon bai ko kalle ta ba ya yi hanyar dakinsu, shi ma Dawud na ciki. Ba ta motsa ba kuma sai ga yan makaranta sun dawo. Hankalinta ya dan kwanta ganin Raihana da Ummita. Ta karasa da sauri.

"Ku gidannan fa ba lafiya. Kin sani ne?"

Ta jefawa Raihana tambaya ganin yanda hawaye suka wanke fuskarta. Jikinta ya kara yin la'asar. Raihanar ce ta ba ta labarin abin da aka yiwa Futuhar, dafe kai Humaira ta yi gami da ambaton sunan Allah.

"Tirƙashi!" Abin da kawai ta ce a baki kenan. Dama tun sadda Futuha ta soma yayin ɗora bidiyo Tiktok ta so ace ta mata magana amma ta sani ba za ta ji komai ba. Watakila ma ta kira ta da mai hassada kamar yanda ta kira Tasleem sadda ta yi yunƙurin hana ta ɗorawa. To na kusa ma an mishi wannan ikrarin ina kuma ga ita da suke mata kallon bare a cikinsu?

Yinin ranar dai gidan ya kasance babu dadi, Abba ya yiwa Futuha kaca-kaca ya kuma rantse ya dakatar da karatunta har sai idan ta samu miji ta yi aure. Ya ba ta lokaci kankani akan ta fitar da daya cikin masoyanta a haɗa bikin da na yar uwarta. Idan kuwa ta ƙi shi da kansa zai nema mata abokin rayuwa.

Tasleem haka ita ma ta dawo daga asibiti ta iske wannan abin wanda tuni tana da labarin komai. Futuha ranar kamar an aikomata saƙon mutuwa haka ta wuni babu ci babu sha, Mami ta ce a kyale ta. Ganin ba ta da mafita ya sanya ta komawa ɓangaren Anna inda anan ne ta samu sassauci domin Anna goyamata baya ta yi, ta ce Mamin su yi mata uzurin kuruciya. Ta dai lallaɓa ta kwantar mata da hankali.

***
A sati biyun da Abba ya ɗibarwa Futuha don ta fiddo mijin aure, a wannan satin kafin su cika gaba daya ta rame ta zama mai wani irin sanyi, yan uwan Abba babu wanda ya goyi bayanta balle ya lallaɓa mata shi. Ganin haka Mami ta tashi takanas ta je ga aminiyarta Hajiya Lubna ko za ta amince Khalil ɗanta ya auri Futuha
su rufawa junansu asiri. Amma ina, Hajiya Lubna ta nunamata ita gogaggiyar yar boko ce ta biyo mata ta kissa ta nunamata ta amince, amma bayan kwana biyu ta kira ta tace Baban Khalil ya ce shi kam ya riga ya gama magana da abokinsa akan ƴarsa da yake son Khalil din ya aura. Ta kwantar da Mamin hankali akan Futuha fa kyakkyawa ce son kowa ƙin wanda ya rasa, ta kwantar da hankalinta komai zai tafi daidai.

Aikuwa cikin ikon Allah dai ga wani matashin ɗan chanji Alhaji Yakubu ya zo takanas ya samu Abba akan yana son aurenta. Mutumin ya jima yana ganin fuskar Futuha a Tiktok, kasancewarsa ɗan duniya, yana son mace mai irin wayewarta ya kuma jima yana bibiyarta akan ta amince ya aure ta, tana wulaƙatanshi. Tashi guda da ya ga abin da Sa'a ta yi mata ya ga dama ta samu da zai yi wuf da ita. Yana da mata ɗaya da yara uku, ya kuma tabbatarwa Abba koda Futuha ba ta son zama da matansa shi ɗin zai nema mata wani muhallin daban cikin waɗanda ya mallaka. Abba ya yaba da salon nutsuwa da ladabin da ya zo mishi da ita don haka ya ce ya je nan da kwanaki uku ya turo iyayensa. Wannan lamarin ya yiwa Yakubu daɗi sosai. Ya yi ta godiya.

Bayan tafiyarsa Abba ya yiwa Mami zancen, ta yi murna da hakan a fili musamman ganin yana da rufin asiri. Abba ya san shi don Alhaji Yakubu ba ɓoyayye ba ne, yaro ne abokin tafiyar manya. Yana da kuɗi sosai sannan akwai shi da kyauta. Ko kusa abin hannunsa bai rufe mishi idanu ba. Ya samu kyakkyawar shaida wajen jama'a da suka san shi a waje, a halayyarsa kuwa na baɗini wannan daga shi sai Mahaliccinsa sai kuwa wadanda ya buɗamusu suka sani.

Futuha fashewa ta yi da kuka sadda Abba ya yi mata zancen.

"Wallahi Abba bana sonsa, mutumin yana da son mata kuma..."

Wurgin da Abba ya kai mata da carbin dake gefensa ya sanya ta saurin yin gum da bakinta.

"Rufemin baki nace! Ke har kina da fuskar da za'a gani a aureki da ita, ban da ma shi so ba ruwansa, mutum mai mutunci da ƙima irin Yakubu mai zai yi da ƴar rawa? Macen da ba ta killace jikinta ba ta sake shi ko'ina yana yawo ana kallonta? Toh bari ki ji, muddin ni dai mahaifinki ina raye, ba ki da miji sai Yakubu. Na kuma ba shi damar turo magabatansa nan da kwanaki uku, karatu idan ya amince maki ki cigaba wannan shi ya ga zai iya, nidai ubanki ba da yawuna ba saboda ni yanzu tsoro kike ba ni, nema kike ki fi karfinmu. Wannan wayewar ta banza kuma da kika ɗaukarwa kanki, ki je can ki ƙarata da ita, Allah ya shiryeki idan ke mai ganewa ce. Tashi ki fice ki ban wuri, saura ki je ki kai ƙarata tun da ban isa da ke ba."


Yana nufin kai ƙara wurin surukarsa Anna kamar yanda ta yi a farko da ya yi batun auren har sai da Annar ta tako sashinsa da zummar lallaɓashi ya janye. Cike kuma da ba ta girma ya ce ta yi hakuri amma ba zai zuba idanu tarbiyyar yaransa su lalace ba. Ganin ba ta taɓa neman alfarma a wurinsa bai yi ba sai wannan ne ya sanya ta kama mutuncinta ta yi shiru da baki.

***
Su Humaira na ɗaki sai ganinta suka yi ta shigo tana aikin da ta saba kullum, wato aikin kuka. Humaira kukan yanzu kam ko a jikinta, ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, ta lura hatta Tasleem itama abin ya bar sosa ranta, kowa ya fice a harkarta ya gaji da rarrashi. Tasleem dai waya take amsawa da Hamza, ganin ihun kukan Futuha ya cika dakin kawai sai ta ja guntun tsaki ta fice. Su din ma hirarsu ta tsaya, kowa ya shiga danna waya, su kansu Abba ya ja musu kunne sosai ya kuma rantse duk wacce a cikinsu ta yi irin gangancin Futuha ba zai duba komai ba zai aurar da su. Wannan ya sa bakinsu ya mutu murus.

Humaira ta bude saƙon da ya faɗo wayarta a lokacin. Ta sani, shi kadai ne zai yi mata saƙo don haka ta buɗe.

_"Ko kinsan mai hakuri ba ya taɓa karo da rashin nasara a rayuwarsa? Ki sani ni ɗin masoyi ne a gareki, ba kuma hakan zai sauya komai ba. Ma'ana, koda ace zamu shekara kina wahalar da zuciyata, Humaira ki sani, Fadeel bai fara sonki domin ya daina ba. Muddin rai ba zan fasa neman soyayyarki ba."_

Ta karanta kusan sau uku, ta rasa dalilin da yasa ba zai taɓa turo kata saƙo ta karanta sau ɗaya ba, kuma ko kadan ba ta iya goge saƙonninsa. Abin da yake ba ta mamaki shi ne, ta ga yana hawa whatapp amma ko sau daya bai taɓa yunkurin yi mata magana ta can ba. Kira ma da ya ga ba ta ɗagawa ya bari. Sai dai akwai lambar da take zargin ko shi ke kiranta da shi. Za a kira ta ɗaga amma ba za a ce komai ba sai dai ta yi ta sallama tana sababin anƙi magana ƙarshe kuma ta ji ɗif an katse kiran. Wannan abu na ba ta mamaki, tana kuma zargin Fadeel ne. Ta yi shiru tana so ta hasaso dalilin wannan ƙiyayya da ta ke yiwa Fadeel amma duk iyakar tunaninta ta kasa, karshe ta ja guntun tsaki. Ta bar shi akan kawai ita ba ta kaunar soyayya, ba ta kaunar kowace mu'amala da za ta haɗata da namiji. Da wannan ta watsar da tunaninta.

***
BAYAN SATI UKU...

Garin aka tashi da shirye-shiryen shiga wata mai alfarma wato Ramadan, wanda ake kyautata zaton ganin wata a ranar ko washegari hakan yasa Mami suka yi dogon list na cefane ita da Humaira. Mamin ta dube ta bayan sun kammala tana murmushi.

"Wannan azumin a daɗinmu, girkinki zamu ci. Kin ga kina yi idan kin shirya komai sai ki yi hoto, Raihana ta buɗemaki account a instagram kina ɗorawa da sunan tallah, idan Allah ya taimaka zuwa sallah sai mu samu odar girkin sallah ko su samosa da sauransu. Da kaɗan-kaɗan kuma ki ji an soma neman

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login