Showing 39001 words to 42000 words out of 103547 words

Chapter 14 - YAR TALLAH complete

Start ads

Unknown   

24 Aug 2025

406

Middle Ads

ce, “Please kar ki sake
yin kukan nan don Allah.”
Saude ta daga masa kai alamar to, ya ce, “Kin yi alkawari?’
Da kai kawai ta amsa masa, sannan ta . juya ta fice
A yanzu mamaki yake ba ta ba ta taba tunanin yana da
tausayi da jin Kai irin haka ba, ashe dama yana da
kyawawan halaye irin haka ya Boye su, Allah Sarki, ko da
yake ai rayuwarta abin tausayi ce ga duk wani mutum mai
imani. _ ' .
Ta zauna bakin gadonta ta janyo Wayarta miss ‘ call biyar
ta gani, ta san kuma duk aikin Hamid ne, ‘ Allah Sarki
soyayya. Ta ajiye wayar karkashin
Kanta ta kwanta. Hirar ta da shi jiya cikin dare ta dawo
mata tamkar yanzu ‘suka yin ta, ta yi wani ”murmushi tare
da yin wani juyi
. Da safe misalin Karfa takwas ta nufi Gangaren Dr Ahmad
da mamakinta yau kwance ta same shi cikin falon Kasa,
saman doguwar kujera da News paper a hannunsa yana
dubawa, yana sanye da wando three quater wanda ya wuce
gwiwarsa sai
bakar singileti a jikinsa. Saude ta durkusa tare da ‘ ”gaishe
shi.’
Ba tare da ya dago kansa daga karatun da yake ba ya amsa
mata gaisuwar. Saude ta mike ta soma aikinta kamar yanda
ta saba, sai da ta kammala tsaf sannan ta soma turare
falon da turaren wuta, kamar wadda aka cewa dago kanki,
karaf su kai ido hudu, ‘gaba daya idanuwansa da
hankalinsaya tattara su a ‘kanta.~
‘ ’Saude ta ji ta yi wata masifaffiyar tsarguwa, cikin
basarwa irin ta gogaggun maza ya‘ yi
mata alamar kira dakansa, jikin Saude ya Kara yin sanyi ita
dai ta fara tsorata da irin kallon da yake mata, ba yanda ta
iya haka ta ajiye bonar din ta nufl
: ' inda yake ta dan durkusa kusa kadan tare da fadar, _
“Ga ni‘ Yalla Bai.”. Idonsa na' kanta kamar mai san
karantar wani abu cikin idanuwanta ya ce“Ya kamata a
tsaya da aikin
nan haka a kawo mana abun karyawa k0 ke ba ki soma jin
yunwa ba ne?” Yadda ya yi maganar cikin "salon nuna
tausayinsa a kanta shi ya ba ta mamaki
Saudat ta sunkuyar da kanta qasa‘ tana kallon yatsun
hannunta, sannan ta amsa, da to muryarta a sanyaye, bai
tanka. mata ba har ta mike ta fice daga falon, ya koma ya
kwanta ya dora hannun shi guda a kan shi ya lumshe
idanuwansa komai yake tunani? Oho.
Saude ta karBo break din ta kawo da sallamarta ta ajiye
masa. tiren kayan abincin a gabansa tare da fadar, ‘Ga
abincin. ”
Dr. Ahmad ya yunkura ya tashi zaune ya sauko daga kan
kujerar ya zauna a gabanta tare da harde qafafuwa tamkar
wani karamin yaro ya ce, “Zubo mana. ’ Saude ta yi saurin
kallonsa tana san tambayarsa shi da wa amma kwarjinsa
ya hana,
don haka ta sunkuyar da kanta. Ta dauko ' plate biyu za ta
zuba Dr. ya sa hannu ya janye dayan yana fadar, ‘Plate
guda za ki zuba mana.” Ba ta musa ba ta dauki saving
spoon ta , debo soyayyar agada (Plaintain) tare da alalar
nama da kwai sai soyayyar da nama cikin dankali ta zuba
su kowane gefe da gefe a tsakiyat plate dim sai ta zuba
wata hadaddiyar miya kadan sannan ta tura plate din a
gabansa ta rufe kulolin, sannan ta dauki
kofi guda biyu ta zuba kunun madara da gero tasa ‘cokula
ta miqa masa.
Dr. Ahmad ya zuba mata manyan idanuWansa da dan
murmushi a fuskarsa ya ce, “Sannu.’ Ba ta amsa ba saboda
yanda ta ji nauyin yanda ya mata sannun,
kamar ba yallaBan da ta sani ba. . Da kan shi ya matso da
plate din a gabanta shi
ma ya matso tare da miqa mata kofl guda na kunun Gaban
Saude ya yi wata mummunar faduwa ta yi
saurin matsawa tana girgiza masa kai alamar a’a. Dr. ya
hade fuska tare da fadar.
“Karbi mana meye haka?” Yanda ya yi maganar cikin tsawa
ya sa ta saurin mika hannu ta karBa.
Ya ce “To sa hannu mu ci maza.’ Ta yi saurin kallonsa
idonta 'ya ciko da kwalla ta gaza yin magana, Dr. Ahmad ya
girgiza kai cikin damuwa ya ce “Abincin ne ba zaki ci ba shi
ne za ki yi kuka?”
Ta yi saurin girgiza masa kai,alamar a’ a Ya kada kai cike
da damuwa ya mike ya koma kan kujera ya kwanta ya
lumshe idanuwansa ba tare daya yi magana ba. ~
Wani irin abu yayi wa Saude tSaye a zuciya, shin wai ita me
ya maida ta ne? Yanzu abincin ma da zai ci sai ya wahalar
da rayuwarta a kansa, abin da yake mata ya soma ba ta
tsoro. Ji take tamkar ta mike ta
bar masa falon, in ya ci ma k0 bai ci ba ruwansa. Bude
idanuwansa da' ya yi shi ya katse mata tunanin
take cikin sanyayyar muryarsa ya ce “Na takura ki k0? Ki yi
hakuri kina iya tafiya kawai. ’ ‘ Gaban Saude ya yi wata irin
masifar .faduwa cikin muryar kuka ta ce“Ka yi haquri dan
Allah ’ Ya dauke kansa kafinn ya ce “Aini banyi fushi ba.” ‘ .
. Damuwar da ta gani qarara a fuskarsa ne ta
Narkar da zuciyarta, ita kanta tana mamakin kannta -.
yanda hankalinta ke tashi idan suna tare bata san lokacin
da bakinta ya bude ba sai dai ta ji tana ‘ fadar
“Ka yi hakuri yanzu ai zan ci.”
A hankali ya dago yana kallonta, ta ta" sunkuyar da
idanuwanta kasa, wani takaitaccen murmushi ya yi tare da
saukowa daga kan kujerar ya: zauna gefenta. Da kan shi ya
dauko kofi din kunun ya mika mata, ta sa hannu ta karBa
cike da jin nauyi ta soma sha, dadin kunun ya ratsa mata
kwanya ashe haka yake da dandano a baki, tun tanajin
nauyi har ta dake ta ci sosai tana cire hannunta yana cire
nasa.‘ a
Ta dan zuba masa idanuwanta, ya daga mata gira, alamar
ya aka yi? Shiru tayi “ta kwashe kayan ta dawo ta gyara
wurin da sukaci abincin sannan ta qarasa inda yake zaune
yanacikin karant
jaridarsa, ta dan durkusa. _ “Zan tafi Yallabai ko akwai wani
abin da~ ka ke so?” '
Dr. Ahmad ya dago da kansa ya kalle ta a nutse~ kafin ya
ce, “Me yasa za.ki tafi nan ba falo ba ne? Me yasa ki ka
kasa sakin jiki?” Saude ta yi shiru ba tare da ta iya cewa
komai ba Dr. ya girgiza kai tare da fadar samu guri ki zauna
ina san mu yi magana.’ Ba musu ta samu gefen kujerar da
yake zaune ta zauna a saman kafet. Dr. Ya wurgar da
jaridar kan kujera tare da gyara zama ~sosai ya harde
yatsun hannunsa guri guda sannan ya kira sunanta.
‘ “Saudat, kiyi hakuri da takura ki da nake ki daure ki ba ni
labarin ki ina san in ji labarin ki na damu da in san wace ce
ke kuma me ye dalilin kawo ki aikatau maimakon a inganta
rayuwarki da ilimi k0 dan ke ma ki amfanar da wasu a
gaba?”
Saude ta yi shiru tana tunanin dan abin data sani a cikin
rayuwarta, idonta ya ciko da kwalla-ta dago tana kallon shi
da sarqaqkiyar muryarta ta ce
“YallaBai babu komai a cikin rayuwaba sai duhu, . babu abu
guda na haske a cikinta, idan ma na samu
to ya suBuce mini. ban san komai a cikin rayuwata
ba sai wahala da. Qaskanci, haka rayuwar tawa ke tafiya...
‘ Kukan da take riqewa ya soma kwace mata, ta sa
hannu tana goge hawayen kafin ta ci gaba ‘ “Ni dai nasan
ance an haifeni ne a gafin Katsina, kuma na bude idona a
cikinta, don haka na
ci gaba da rayuwa a yanda tazo mini a ciki, "tunda nayi
wayo na ganni a: gabana Yayana Rabi’u sai mahaifina
Malam Bala, sai kishiyar mahaifiyata Inna Laure da yarta
iKilima wadda ake ce mata ‘Yar Baba.’ » A nan ta Iabarta
masa gaba dayan labarin rayuwarta har ya zuwa yanzu.
Tana gamawa ta kifa kanta a saman cinyarta tana kuka.
Tausayinta ya qara kama Dr Ahmad wanda yake jin tamkar
ya". zubar mata da hawaye, ya tausayawa halin da ta ’
tsinci rayuwarta tun tana yar karamarta har girma ta
mallaki hankalinta, amma Inna Laure ba za ta bar ta haka
ba wannan wace irin macece? ‘ ; Ya kira sunan ta cike da
damuwa ya ce.“Ki yi hakuri Saudat insha Allahu sai kin
yi,alfahari da rayuwarki ni zan maye miki gurbin Yaya
Rabi’u da kuma Hamid in dai ina numfashi. Saudat sai kin yi
‘ dariya da farin ciki kamar kowace mace, ki kwantar”da
hankalin ki ki daina kuka haka kinji?” ‘ _ Kai kawai ta daga
masa alamar eh ya zaro ~ hankicif cikin aljihunsa ya mika
mata ta karBa ta’ share hawayenta sannan ta mika masa ya
karba kafin yace, “Yanzu ki tafi kije Ki kwanta daga masa
alamar eh? Ya ce to shi kenan,‘kidab bani lokaci zan danyi
tunani a kan matsalarki kafin. in “ samar miki mafita da
fatan‘dai ba zaki yi fushi da;
Duk abinda rayuwa ta sake baki ba zaki karba da hannu
biyu
Saude ta daga masa kai alamar eh yace to allah ya kaimu
Jin yayi shiru yasa ta miqe ta nufi hanyar fita har takai
bakin korar taji ya kira sunanta ta waigo tana kallonsa yace
ki kawomin coffe yau da daddare kai kawai ta daga masa ta
juya ta fice abinta koda ta koma bangarenta ruwa kawai ta
watsa ta koma ta kwanta a binta wani barci ya dauketa ba
ita ta farkaba saida wayarta ta dameta da qara tasa hannu
ta dauka cikin magagin barci jin muryar hamid yasata
saurin watstsakewa daga baccin suka shiga hira sunfi awa
biyu a haka sannan sukai sallama da niyyar zai qara kira
zuwa anjima misalin qarfe goma daidai saude ta fito daga
bangarenta ta fita kai tsaye kichin ta nufa ta dauko flasks
din coffe da qananun kofinan da yakesha dasu ta nufi
bangarensa dasu saidai tun kafin ta qarisa ta hango
bangaren nasa dun dum babu alamar hasken wuta tsoro ya
kamata gashi bata taho da wayartaba ballentana ta haska
kuma babu damar ta koma
Wayyo allah taji tamkar ta fashe da kuka
Taja ta tsaya cak tana tunanin abinyi tun kafin ta
Qarasa nazarin taji wani haske mai Karfi ya taso da saukar
ruwan sama mai Karfi ai bata san lokacin data kwasa da
gudu ba ta yi Bangaren nasa, ba ga shi duk ta jike Tamkar
daga sama ta ji ta yi tuntuBe da wani abu ta fasa wata
uwar qara ta saki kayan ta kwasa a guje, karaf sukai kicibis
ta da mutum, ta sake kwala wani qara mai qarfi cikin
dabara ya rungume ta sosai a jikinsa yasa hannu ya kunna
wutar falon. Amma har a lokacin ‘ ihu take tana, zullon
kwacewa, hannu yasa ya
tallabo qeyarta ya juyo da fuskarta saitin tasa su kai
ido hudu. Sai Alokacin ta tsaya da ihun ta saki wata _
. ' nannauyar ajiyar zuciya cikin muryar kuka ta ce ‘Wallahi
ka tsorata ni na zata, na zata... ’sai kuma tayi
Shiru Yanda take maganar a shagWaBe ya barge shi har bai
san lakacin da ya saki wani murmushi ba yasa dan
yatsunsa ya lakace mata hanci yan fadar, . “You ar so
beautiful Ya lumshe idanuwansa tare da mata wani
murmushi,wadda ta tsaya iya makoshinsa kawai
' Sai a lokacin Saude ta lura da irin rikon da ya yi mata ta yi
saurin zame jikinta da na shi a kunya ce saboda yanda
ruwan. ya jika kayanta duk suka mammanne a jikinta
tamkar ba ta sa komai ba ta juya da gudunta ta bar falon
tana ji yana kiranta amma ba ta tsaya ba, haka ta koma
sashin nata cikin ruwan. '
Tana shiga ta hada kanta da bangon falon tana jin tamkar
qasa ta tsage ta shige ciki, saboda kunya da nauyi. Ai k0
ba za ta sake yarda su hadu ,ba duk rintsi kai dole ma in
bar gidan. nan, wannan abun " kunya har ina, musamman
idan‘ matar gidan ta samu labari ai ita ta san ta kade har
ganyen ta. Kunya ta isheta tarinqa jin tamkar tarusheda
kuka.
Ta samu ta yi ta maza ta cire kayan ta dauko tsohon
zaninta ta yi daurin Kirji da shi ta haye kan ‘ gadonta ta ja
bargo ta kwanta. Amma sai me? Da ta rufe ido sai ta ga
tamkar ga Dr. Ahmad nan zai rungume ta, ta zabura ta
tashi zaune tana muzurai, ga qamshin turarensa da ya
mamaye ta, ta yi wani gajeran murmushi tare da komawa
ta ‘kwanta: ta runtse idanuwanta a haka bacci mai nauyi ya
dauke ta. Washe gari tunda ta farka take zaune tana san
zuwa wurin aikin nata, amma kunya ta hana ta, ji ‘ take ba
za ta iya sake hada ido da shi ba, don haka ta
gidan.
Ita kanta ba ta san ta dan lokaci ba sai da ta soma jin
cikinta na kukan yunwa, ta daga kanta ta kalli agogo. Sha
daya da mintina, tana shirin tashi zaune ta ji an turo Kofa
an shigo. Ta yi saurin tashi tana fadar, “Sannu Aunty.".
Ta amsa da “Yauwa Saudat laflyadai ki kek0?” Saude ta ce
“To da sauqi dai kaina neke dan ”ciwo.” ‘ .
Ta ce, ‘Ayya, Allah Sarki kije Hajiya na neman ki tana falo.”
Gaban Saude ya yi wata mummunar faduwa, ta ce, ‘Lafiya
dai k0 Aunty? Allah yasa ba wani laifl na yi ba.
‘ Aunty ta ce “To laflya, YallaBai ne ya aiko kiranki.’ _
Hankalin Saude ya Kara tashi alamun tsoro ya . bayyana
karara a fuskarta, ta mike jiki amace tana fadar, “Ga ni nan
zuwa.”
Cikin sanyin jiki ta canza kayan jikinta sannan ta fito
zuciyarta na faman bugun dardari. harta qarasa .falon ta
hango’Asma, tsaye riqe da Kugu, tana sanye da wasu
riga‘da siket sari tare da 'mayafinsu tamkar wata
.Ba’indiya, takalmin nan mai shegen tsini a qafarta.
A danyi nesa da ita Saude ta tsaye ta durkusa tare ‘ da
fadar, ‘Ina kwana Haj iya.” .
Asma ta watso mata wani razanannan kallo kafin ta ce
‘Shut up ke nan har marar kunya ce wace ce ke? Uban
waye uban ki a garin nan da har za kiqi zuwa aiki saboda jin
dadi har Dr. ya aiko kiran ki, me ki ke ji da shi a cikin gidan
nan? Me ki ka taka'?
, Banza sakarya jaka‘ yar qauye.
Yau k0 rashin lafiya ki ke dole za ki sanar in ba daibakisan
inda kankiyake ba, tunda an ajiye miki wayar tarho da za ki
iya kira da ita ki sanar, amma ke isasshiya kin yi shiru abin
ki wato idan ana so a neme kito ki -sani wannan shi ne
laifinki na biyu cikin manyan laifukan da ki ka aikata a gidan
nan duk ran daki kikai na uku,kisani aranar”zakikarbi
takardar sallamar ki kinji na fada miki” Tana gama fada ta
juya ta haye sama a zafafe
Jikin Saude ya yi sanyi matuqa, ta lallaba ta mike ta fice
zuciyarta a cunkushe da baKin cikin yanda aka wulaqanta
ta ba tare da an saurari uzurinta ba.
Rayuwa kenan ,
Haka ta sa kai ta shiga falon tare da sallamar’ta, tsaye yake
tsakiyar falon ya goya hannayensa a baya yana jin
sallamarta ya yi saurin waigowa ya nufo ta da hanzarinsa
Lafiya Saudat me ya same ki? Ba dai ruwan jiya
, neya saki zazzaBi ba?”
Saude ta girgiza kai alamar a’ a, sannan ta durkusa tana
gaishe shi, bai iya amsawa ba ‘ ya sake jefo mata wata
tambayar
‘Ban yarda ba Saudat idan lafiyarki qalau me yasa yau ba ki
zoba?"
Saudat ta Kara dukar da kanta qasa tare da fadar, ‘kaina ne
yake ciwo kadan shi ya sanya.’
Dr. ya ce ni dai na sani, :nasan baki da da lfy Saudat bari in
kira likita ya duba ki, kin ci abinci ' ‘ kuwa? .
Da sauri ta ce ai na warke.
Dr ya. girgiza mata kai a’a Saudat ban san wasa da lafiya,
taso ki ci abincin kafin yaz0.
Ganin yana shirin riko hannunta yasa tayi saurin tashi da
kanta ta bi shi ya nuna mata tsakiyar kafet ta' zauna sannan
ya nufi dining ya dauko kayan abincin ya kawo mata, yau da
kan shi ya zuzzuba mata ya tura mata a gabanta tare da
fadar. ,
‘Don Allah ki daure ki ci.”
Kai kawai ta daga masa, sannan ya wuce ya dauki wayarsa
ya kira likitansa. Yana cikin wayar ne Asma ta sawo kai
falon tana wani taku sai ka ce wadda take filin. gasar iya
taflya, Dr. ya zuba mata idanuwansa cike da tuhuma. ‘
Karaf idonta ya sauka kan Saude wadda tuni hanjin cikinta
ya shiga juyawa saboda tsananin
firgita da tashin hankali, Asma ta ja ta tsaya tana ,fadar.
“Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce kecin abinci a faod
flask dinka, kam babban ....... ’
Kai jama,a akwai rikici fa sai kunjini agaba donjin yaddah
zataci gaba da kayawa naku har kullum admin Dboy🤔
[1/25, 10:39 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/27, 10:11 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER 19*

“Me nake gani haka Dr? ‘Yar aikin ce ke cin abinci a food
flask dinka, kam babban ....... ’
Ya watsa mata wani kallo lokacin da ya kashe wayar ya ce
“To k0 rai ya yi baki ne? Ai dai anawa take ci ba a baki ba
k0? Ya yi mata tambayar cike da ‘ isa da gadara. _
“ Asma ta qara shaqa kafin ta ce ‘Hmm! Dr. kenan amma
dai .ka san wannan ba qaramin kaskanci bane da zubdawa
kai girma ka yi bak0? A. Zo a iske yar aikin ka na cin abinci
a kwanan ka,
‘yar aikin ma ‘yar Kauye, jaka dakikiya, wadda talauci ya yi
masu daurin .....
Dr. yayi saurin daga mata hannu ‘ya isa haka Asma, kin
sanni sarai ban san cin fuska don Allah tunda ban aika miki
da katin gayyata ba ki bar nan, banasan ciwon kai.’
' Takaici ya kashe Asma, ta matsa daf da shi tare da
sassauta mur'ya ta ce ‘Yanzu Dr saboda ‘yar aikin ka ka ke
cimin fuska haka?” ‘ Ya ce ‘Amma kin sani Sarai ba a gaya
mini yanda zan yi ko?’ Haushi ya kama ta ta juya a zafafe ta
bar masa falon, ya taBe baki ya juya wurin Saude wadda “
lomar abinci ta yi wa tsaye a maqogaro tun dazu ta gaza
hadiyewa, saboda tsabar firgici da tsoratar da ta
Dr. ya zauna bakin kujerar dake fuskantar ta yana fadar.
“Ki nutsu ki ci abincin ki sosai ga likita nan zuwa.’
Hawayen da suka taru a kwarin idanuwan ta suka gangaro
cikin kuka ta ce, ‘Wayyo Allah na ka ja mini Allah kadai ya
san abin da za ta yi mini yau na
banu na lalace! ’
Dr. yace ‘Kuka kuma Saudat? Yanzu nan har an yi abin
kuka? Lallai ashe kina da kukan jini nan gaba. ’
Saude ta Kara rushewa da kuka, ‘Wallahi gida zan tafi”
Dariya ta kama Dr. ya ce, ‘Ashe matsoraciya ceke lallai
Saudat na tabbata da Asma ta ji haushin ki da k0 sama da
qasa za ta hade anan ba za ta kyale ki ba, ta riga ta san
halina ne sarai don haka ba ta damu da ke ba ta kaina za ta
dauki matakin don haka ki ma kwantar da hankalin ki ki ci
abincin ki ’
Saude ta ture abincin tare da fadar, ‘Na qoshi.’
“Me? Ai wannan ne baki isa ba k0 ki dauka ki cinyc shi ko
yanzun nan in kira ta ince kin cetazo ta kwashe kwanukan
kin gama.’
Saudc ta yi saurin waro

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login