Showing 42001 words to 45000 words out of 103547 words
ido waje tare da janyo
abincin da saurinta ta ci gaba da ci, ya yi dariya a ,
zuciyarsa sosai ya ce matsoraciya.
Tun kafin ta gama cin abincin likitan yazo ya duba ta sosai
tare da rubuta mata wasu magunguna, ya kira direba yasa
ya je ya siyo mata su, ya dinga lallashinta yana rokon ta a
kan ta rinka shan magungunan, sannan ya ba ta ta tafi
Cikin tsoro ta shiga sashin nasu don gani take Asma na nan
na jiranta. ' .
Tana shiga sashinta ta maida qofa ta rufe ta ajiye
magungunan ta haye kan gado ta janyo wayarta da .taketa
faman ruri tun dazu ta ci gaba da wayarta.
Washe gari da yamma tana zaune a bangaren Dr.
tana aiki, zuciyarta sai faman sake-saken neman mafita
take saboda wayar da su kai da Hamid jiya da
daddare
Dr. ya sauko daga samansa yana sanye. da qananan kaya
irin na hutawar turawa, ya tsaya daga gefen kujera yana
kallon Saude wadda ke durkushe tana 'goge goge
‘ . Jikinta ya ba ta tamkar ana kallonta, don haka ta yi
‘saurin waiwayawa, tsaye ta gan shi a gabanta ya harde
hannuwansa a kirji tamkarmai nazarin wani abu. Saude ta
yi saurin durkushewa tana masa sannu
da fltowa, bai amsa mata. ’ba‘ sai ma ya sake gyara
tsayuwarsa. “Me yasa baki san hutawa?”
Saude ta dan kalle shi kadan kafin ta ce ‘Ai aikina ne shi
yasa.’
Dr. yadan dauke kai kafin yace, ‘Ai kin kusa barinsa, saki
wannan aikin ma taho mu fita mu sha iska.”
Bai jira abin da za ta ce ba ya yi gaba abinsa,
Saude ta raka shi da idanuwanta. To me yake nufi da ita?
Ba dai korarta za su yi ba? Da sauri ta zabura ta bi
bayansa.
. Hadaddan wurinn shakatawa ne wanda aka kashewa
dubban nerori wurin Kawata shi, don an zuba abubuwan ban
sha’awa da debe kewa. Saude ta . koma jikin wani dodon
roba, tana kallon Dr. wanda ke wasa da dan biri, can ya
dago ya yafito ta da hannu alamar ta zo duk da tsoron da
ya cika mata zuciya haka ta dake ta tafi inda yake, ta tsaya
daga gefe tana kallon su, ba ta ankara ba ta ji ya fizgo
hannunta ya hada da na birin, yana wa birin magana cikin
harshen turanci.
Mutuwar tsaye ta yi don tana bala’in tsoron sa sosai, don
ma yana dan Karami, sai ta ga ya ’fadi' Kasa alarnar
gaisuwa. Dr. ya yi dariya yana kallonta ya ce “Ana gaishe
kifa?” Kallonsu kawai take bata ‘ iya yin magana ba, birin ya
mike yana ta faman zazzagaya ta yana tsalle-tsallen
murna. ' ,
Dr. ya janyo hannunta suka nufi wani.‘ qaton lilo
na roba mai matattakala ya dan kalle ta da murmushi a
fuskarsa ya ce “In hau za ki jujjuya ni’?’ ‘Duk da
haushin riKon da ya yi mata ya kama ta sai da ta yi dariya
saboda yanda ya yi maganar.
Ya ce, ‘Okoy, dariya ma na baki to bari in dora ki in jujjuya
ki.’ Tun kafin ta yi wani yunkuri ta ji ya sure ta ok ya dora
saman lilon.
Saude ta fasa wata uwar kara saboda razana, don ita gaba
daya ma lilon tsoron shi take yi, dariya ta bawa Dr. sosai na
kauyancin nata, don haka yana dariya yana jujjuyawa da
ita, mutuwar zaune ta yi ta . runtse idanuwanta tana
sauraren ikon Allah, shi kuwa dariya kawai yake mata, yana
zolayarta ganin ba shi .da niyar daina juya ta yasa ta bude
idanuwanta tana shirin kuka, ta hau rokonsa.
‘Don Allah don Annabi ka sauko da ni.’
Dr. ya tsaya da lilan ya matsa yana fadar, ‘To sauko tunda
ba kya so.’
Saude ta waro idanuwa don ta san ko da kudi aka bata
bazata iya saukowa ba, ya yi murmushi tare da mika mata
hannunsa ta rike sannan ya sauko da ita, yana mata dariya
yace matsoraciya duba ki ga aku na .kallon ki. ’
Saude ta yi saurin juyawa, caraf ya riKo hannunta ya ja ta
da saurinsa. Haushi ya kama ta yanda ya maida ita kamar
Karamar yarinya. Saman wasu kujerun roba ya zaunar da
ita shi ma ya zauna, suka
sa zagayayyan tebur din a tsakiya. Saude ta bi abin . da aka
dora' saman tebur din da kallo, wanda a kai ‘
‘ rafin din shi gwanin burgewa. Dr. ya miKa hannu ya dauko
ya mika mata ta tsaya tana kallon shi ya miqa mata tare da
fadar.
“Karba mana.’
Ta mika hannu ta karba,tana kokarin bude rafin leda din.
Dr. ya yi saurin tsaida ita yana fadar, ‘tsaya tsaya waya
fada miki idan aka bawa mutum gift budewa yake'a take
bakauyiya ai bari ake sai an tafl.’ Yana maganar cike da
zolaya. .
Saude ta zumBuro baki" jin ya kira ta da bakauyiya, dariya
ta kama shi ya ce, ‘A’a ‘yanmata ashe kin iya fushi irin
haka?”
Ta dauke kanta ba tare da tace Kala ba. Ya ce, ' ‘Wai fushin
ki keyi da gaske am so sorry, tuba nake -kaina bisa
wuyana.’
Dariya ta kubce mata yanda ya yi maganar a ladafce sai
kace ba YallaBai din da ta sani ba, ganin dariyarta yasa ya
mikc yana fadar
“Taso muje kin ji ana ta kiran sallah a_ masallaci.’ ‘
Saudeta tashi ta mika masa gift din da ya bata, ‘ya dan
zuba mata idanuwansa babu alamun wasa a fuskarsa ya ce
‘Da shi za ki tafi kyauta ce daga gare‘ ni.’ Yana gama fada
ya juya ya yi. gaba abinsa, ba tare da ya saurare abin da za
tace ba.
Tsabar mamaki da kaduwa su suka hana Saude furta
komai, har sai da ya kusa bacewa ganinta
saunan ta iya wage murya tana fadar, “Na gode kwarai.’
Hannu kawai ya daga mata ba tare da ya juyo ba
ya Bace abinsa, ita ma ta yi gaba cike da zullumin
abin da aka nannade haka. Tana .shiga dakinta ta fada kan
gadonta ta yi zaman dirshan ta shiga bude kyautar, ta ciro
wani
kyakkyawan kwali mai kyan gaske da zanen waya waya a
jikinsa. Saude ta bi hoton wayar da kallo kai da gani ka san
ta yi tsadar gaske, a zuciyarta ta furta ‘Allahumma
arzuquni" tasa hannunta ta bude kwalin.
Gabanta ya yi wata mummunar faduwa ta yi ‘ masifar firgita
ganin sabuwar wayar kwance cikin kwallin, ta ciro ta tana
jujjuyawa, touch screen mai shegen kyau, wadda ta san ko
da kudl aka hada ta ba za ta iya kunnata ba.
Saude ta riqe wayar tare da dafe kai, yau na shiga uku ni
Saude, wai me ke shirin faruwa da nine? Wasu irin hawaye
suka ziraro daga idanuwanta ta lura mutumin nan so yake
ya jaza mata bala’in da ba zata iya dauka ba, yanzu
tsautsayi yasa Hajiya ta samu labari ya kenan?
Motsin taflyar da ta ji ne ya sa ta zabura ta maida
wayar cikin kwalinta ta tura a qarkashin filonta, tana
faman‘muzurai. Aunty ce ta shigo da sallamarta suka
gaisa sannan ta ajiye mata wata leda Saude ta mika hannu
ta janyo ledar tana duddubawa.
Sabulan wanka ne dana wanki tare da kayan shafawa da
mayuka, ta ajiye‘ leadar gefe ta koma ta kwanta tana fatan
gari ya waye ta je ta maida
masa wayarsa, don ba zata yarda ba ya jaza mata tashin
hankali da bala’in da ba za ta iya dauka. Ba
Dole nema ta runtse ido ta fada masa‘ ya fita daga
rayuwarta ita dai ba kowan kowa bace hakan kuma ba yana
nufin ba ta san mutuncin kanta bane da wannan tunanin
bacci barawo ya sace ta.
Washe gari da safe Saude ta tafl Bangaren Dr. Ahmad babu
kowa a falon nasa don haka ta zage ta shiga aikace-
aikacenta qarfe goma daidai ya sauko daga samansa yana
sanye da jallabiya sabuwa ruwan toka mai hade da hularta
Suna hada ido da Saude ya yi saurin qarasa saukowa daga
matattakalar yana fadar, “Zo. nan Saudat." *
A hankali ta dago ta kalle shi tare da gaishe shi cikin
girmamawa kamar yanda ta saba. Ya amsa' a tsanake
sannan ya jefo mata tambayar da ta sanya ta saurin
dagowa tana kallonsa, ya qara‘gyara tsayuwarsa tare da
maimaita mata tambayar.
“Na ce laflya ba ki bude kyautar da nayi miki ba
Ko baki iya bane?” Ya karasa maganar cike da tuhuma. ;
Saude ta dukar da kanta tana kallon kafet din dakin cikin
nutsuwa ta soma magana.
“Kayi haquri Yallabai ba wai ban yaba ba ne kawai dai na
ga kyautar ba ta cancanta dani bane shine yasa nayi'
tunanin maido maka, amma ka yi hakuri
Dr. Yayi wani takaitaccen murmushi tare da zama saman
hannun kujera ya zauna yana kallonta a nutse kafin ya ce
‘Dama ita kyauta cancanta ce ke sawa ayita idan kuwa
cancanta ce to ke kuw kin ' wuce wadda a kai miki kinfi
qarfin hakan.
Kuma idanma ba ki sani ba ina so yau ki sani dangantakata
dake tamkar hannu da ido ne yanzu sannu a hankali zan
shafe hawayen da ke kwaranya daga idanuwanki insha
Allahu sai na wanzar da dariya a idanuwan dake ta zubar
hawaye, kin fahimta?”
Saude ta girgiza masa kai tana fadar, ‘A’a Yallabai yin
hakan yana nufin zaka tsamo ni daga rijiya ka jefa ni kogi
ne Yallabai ka yi tunani zan iya shiga matsala wajen Hajiya,
na tabbatar idan ta samu labarin kudirin da kake nufo ni da
shi zata dauki kowane irin mataki a kaina,
Dr Ahmad ya kada mata kai yana fadar, 'Ko
kusa Saudat babu wandu ya isu ya yi wu mutum ”abinda
Allah bai masa ba haushin me Asmu za ta ji
don kawai ina kokarin taimaka miki meye abin da zai
tunzura ta a ciki? Ni ban ganshi ba, kuma koma
akwai ba zai dame ni ba, zan yi Kokari har sai na sauke
alkawarin da na dauka.”
Idon Saude ya ciko da hawaye cikin muryar kuka ta ce, ‘Na
san ba zai dame ka ba YallaBai amma ni zai dame ni, wata
qila ma ya zamo silar barina duniyar gaba daya. ’
Dr. Ahmad ya ce, ‘Hakan ma ba za ta kasancewa ba Saudat
ki daina ma fada.’
Saude ta ce, ‘Idan ya kasance fa?”
Shiru ya yi yana kallonta Saude ta yunkura ta mike
hawayen da suka ciko daga idanuwanta suka samu damar
zubowa cikin kuka ta ce, ‘Zan bar gidan nan dole zan bar
shi, dan ina tsoron abin da zuciyata ke hangowa ina jiyewa
kaina, dan idan ma wani abu ya same ni babu wanda Zai yi
kukan rashina, babu ba ni da shi.... Kuka ya ci Karfinta
sosai.
Dr. Ahmad ya yunkura ya zagayo ta gabanta yana kallonta
cikin sanyayyar muryar shi ya soma magana.
‘Duk inda ki ka nufa a fadin duniyarnan sai na nemo ki, babu
inda za ki shiga ki layance min. Ina tare da ke Saudat har:
sai na ga kin yi dariya sai na ga rayuwarki ta inganta kin
samu farin ciki mai dorewa
na yi wa kaina wannan alkawarin kuma zan cika shi ko da
hakan yana nufin rasa komai na a rayuwata.’
Saude ta yi saurin juyawa tana kallonsa ya daga’ mata kai
yana fadar, "Tabbas kisa ido kiyi
kalio.’ ‘Ya juya a sukwane ya fICe daga falon ya bar ta
nan tana kallon qofar da ya fita. Wani irin kuka ya zo mata,
tsoronta daya a duniyar nan matarsa Asma; don ta san ba
lallai bane ta yi musu kyakkyawar .zargi ba, tana tsoron ta
yi musu mummunan zargin da zai‘sa ta yanke mata hukunci
daidai da zarginta. Saude ta Kara rushewa da kuka don har
ta hango irin bala” in da za ta iya fuskanta Haka ta karasa
aikinta tas ta bro Bangaren nasa, yinin yau haka ta yi sa a
kwance. Da daddare kuma Hamid ya kira ta ya Kara caza
mata Kwakwalwa. “Wai Saudat me ke damun ki ne shin k0
kin mance da yau saura sati uku auren ki? Na lura hankalin
ki kwance yake tun yaushe nake fama da ke kina gocewa.
Saudat idan harkin soma san Garba ne ki fad'a mini in fidda
raina kawai, amma don me za ‘ki ta yi min yawo da hankali
ki ce yau ki ce goba, idan kin san ba zaki iya fitowa daga
gidan ba ki 'fad'a mini ni in zo da kaina in dauke‘ki.’ 'Saudat
ta ja numfashi ba ta taba tunanin ya iya bude wuta haka ba,
ta ma rasa ta indaza ta fara, don . haka ta kwantar da
murya ta ba shi hakuri tare da yin .
masa alkawarin duk rintsi gobe za ta gudu ta bare ‘ Abujar.
» ,
Abun duniya duk ya ishi Saude tunaninta daya yanzu
hanyar da za ta bi ta bar. gidan ga YallaBai yana nema ya
taso ta gaba tsoronta daya ma yanzu kar ya ruguza mata
al’amuran ta, wannan tunanin ne ya hana Saude barci da
wuri sai kusan biyu da wani abu na dare ta kwanta, don sai
da ta harhada kayanta tsab na barin garin. .
Sallar Asuba ma da kyar ta iya yin ta saboda baccin da yaci
qarfinta. A kan sallayar ma wani sabon baccin ya sake
dauke ta. Ba ita ta farka ba sai qarfe sha daya da mintina.
Ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin da ta dauka tana
bacci, don haka ta mike da hanzarinta za ta shiga bandaki
ta ji kukan wayarta, don haka ta dawo ta dauka. '
Tun kafin ta qarasa sallamar ya katse ta ta hanyar fadar,
‘To yaya kin taho k0 kuwa yanzun ma ba ki samu damar
ba? .
Saude ta sauke numfashi tare da fadar, ‘Nina fada maka
Yaya Hamid insha Allahu yau zan bar gidan nan duk rintsi,
saboda ni kaina nafi ka kaguwa dana bar gidan nan don
Allah ka kwantar da hankalin ka insha Allahu babu abin da
zai faru.’
Ya ce, ‘Hmm! Saudat kenan na lura ba ki san irin son da
nake miki ba shi yasa har kike fadar kar in damu wallahi
yanzu kasancewa ta da ke ne kawai zai ba ni farin ciki a
rayuwata, don Allah Saudat kada ki ci gaba da nisanta kan
ki dani please; ’
Tausayinsa ya kama ta ita kanta ta soma jin irin yanda
yakeji yanzu don haka cikin sanyin murya
ta ce, “Kayi hakuri Yaya Hamid ni kaina. ina jin
yanda kake ji a yanzu, kuma nan da wasu ‘yan
awanni zan maka kyakkyawan albishir.”
. Hamid ya ce Allah yasa ki gaggauta kin ji?”
’lnsha Allahu.” Ta ce cikin sanyin murya, sannan ta. kashe
wayar ta mike da nufin maida ta wurinta, zuciyarta ta yi.
wata mummunar bugawa.
A tsaye yake jikin qofar ya harde hannuwansa a kirji ya tura
mata idanuwansa da ke sanye cikin farin gilas gaba daya ya
tattara duk wata nutsuwarsa a kan Saudat ta ji.tamkar ta
kurma ihu saboda tsaba: tsor da kaduwa duk ta
dabarbarce,.
, Dr. Ahmad ya take a hankali har zuwa gabanta ya mika:
mata hannu, “Ba ni wayar.”
Ba musu ta miqa‘ masa wayar hannunta na rawa. Ya ce,
‘miqo min har da waccan da na baki.’ Jikinta na faman bari
ta juya ta dauko masa, ya karba kawai ya juya ya fiCe
abinsa ba tare da ya ce da ita komai ba
Saude ta fada saman gadon jagwab kamar an zuba kayan
wanki har wata zufa ke tsatstsafo mata, ta daura hannu a
kai .Wayyo Allah na! Ya Ubangiji gani gare“ ka
, Asma. ta fado kamar an an jefo ta, ' ' Saude ta Zabura ta
miqe a tsorace tana kallonta,
Ta tsaya tana watsa mata wani malalacin kallo. Saude ta
durqushe a gun, tsantsar firgici ta bayyana a fuskarta
bakinta sai kyarma yake wurin fadin
‘In...ina... ina wuni
Asma ta tabe baki tare da jan wani dogon tsaki, ta shiga
zagaye dakin tamkar mai neman wani abu ta kai ta kawo ta
kai ta kawo, ta dinga binciken ta sai data gaji sannanta
juyatafice batare datace uffan ‘ba.
Saude ta yi suman tsaye, me keson faruwa ne da ita ne? Ta
yi masifar firgita, ita dai ta san ta shiga . tsaka mai ‘wuya,
don da za a auna ta a lokacin babu abin da zai hana a
tabbatar da hawan jininta, kukan ma ya gagare ta sai
muzurai kawai take yi.
' Wasa-wasa lokaci ya soma tafiya tana nan zaune, ” tabbas
idan ta yi wasa lokaci zai qure mata, don gangar jikinta ce
kawai zaune a gun amma zuciyarta na wurin Dr. Ahmad.
Qokon ta daya Allah yasa ya yanke mata hukuncin da za ta
iya dauka. Wasa-wasa ta lurawankin hula zai iyakaita
dare,don hakata yanke shawarar tashi ta je ta ba shi hakuri,
ba yanda ta iya haka ta lalalBa ta mike: jikinta amace ta
nufi Gangaren nasa.
Sallamar da take shirin yi ta makale a
makogoranta, tsaye yake goye da hannayensa a baya
wadanda ke rike da wayoyin da ya karba wajenta, duk da
bayansa take saboda ya bada
baya, amma hakan bai hana ta fahaimci yana cikin yanayi
marar dadi ba, tsoronta ya qaru matuka tana fargabar ya yi
mata mummunan zargi.
Jin shigowarta yasa Dr. juyawa a hankali yana kallonta da
jajayen idanuwansa ba tare da ya ce mata kala ba. Saude
ta durkusa a gabansa muryarta a sanyayc ta ce ‘Don Allah
ka yi hakuri Yalla6ai wallahi ba...
Dr. ya yi saurin daga mata hannu alamar ta dakata, ya yi
taku daya zuwa uku ya matso gabanta cikin razananniyar
muryarsa wadda ke fita a hankali ya fara magana.
“In yi hakuri laifin me ki ka yi min? Kina tunanin raina ya
baci ne don na kama ki kina kula maza?” Ya girgiza kai.
“K0 daya Saudat ko a jikina, ko da kuwa duk mazan duniyar
nan samarinn ki neba zai rage ni da ‘ komai ba, illah dai
kawai na tausayawa rayuwarki da ke qoKarin rugujewa, ke
yarinya ce Saudat ba za ki gane waye da namiji ba sai ran
da ya buga miki irin nasa tambarin, ranar ne zaki fahimci
irin wautar da ki kai a baya.
Ni ba zan takura ki ba in ce dole sai yanda nake so za ki yi
rayuwa ba, a baya wauta na yi da rashin bincike wanda
yasa na dauka zuciyarki shararriya ce
babu wani datti a cikinta, ashe ban sani ba tuni kin shigar
da soyayyar da take nema ta makantar da ke ta
kai ki ta baro ki.’ Ya dan yi shiru yana kallonta yana girgiza
kai, sannan ya mika mata wayarta.
“Ungo ga wayarki.”
Hankalin Saude ya qara masifar tashi ba ta san lokacin da
idonta ya kawo kwalla ba, sai dai ta ji zubar
su saman kuncinta. Dr. ya waro ido cike da mamaki
kafin ya ce ‘Kukan me za ki kuma Saudat ai na dauka
firgicin ki‘na raba ki da masoyin ki ne da na yi kuma sai na
ce na bar ki da shi, to me ye kuma abin kuka?”
Saudat ta sa hannu tana share hawayenta, wanda sukaqi
tsayawa ta soma magana cikin kuka. “Ka yi hakuri wallahi
ba da wani namiji nake magana ba Hamid ne.”
Nan ta kwashe labari ta ba shi tun daga sakon da ya aiko
Dillaliya da shi har zuwa wayar da suka yi. ~ Dr. ya ja
numfashi kafin ya ce ‘Saude kenan, a dan labarin da ki ka
ba ni na fahimci kina son Hamid shin haka ne?”
Saude ta ji tamkar ya dora mata Dala da Gwauron Dutse
aka, ta rasa abin da za tace masa ma.
Dr. ya sake cewa, ‘Da ke nake magana fa Saudat kin mini
shiru
Da kyar ta iya dagowa ta kalle shi, ya yi mata masifar
kwarjinin da ba za ta iya kallon idanuwan shi ta fadi abin da
ke zuciyarta ba. Murya: shi a sanyaye ya sake maimaita
mata tambayar a karo na uku, ba ta
san yanda a kai ba sai dai ta samu kanta tana mai girgiza
masa kai, alamar a’a.
Shin meye dalilin saude na cewa batason hamid mu tara
donjin yaddah