Showing 6001 words to 9000 words out of 103547 words

Chapter 3 - YAR TALLAH complete

Start ads

Unknown   

24 Aug 2025

392

Middle Ads

da gajiya dake cinta
Laure ta haskata da cocila au kukama kika tsayayi kenan ni inanan ina jiranki?
To malam zoka gani da idonka saude na zagina
Malam bala ya zaburo tamkar shayayye
Zagi kuma laure wani irin zagi ba dadin ji?ya hankade labulen dakin ke ba magana ake miki ba yar jakar ubannan shine kika zauna kinama mutane kuka
Idanda uwarkice ta dawo daga lahira ta sanyaki aikin ai bazakiyi kukanba ko?
Fitonan inji wanda kike zagi
Saude tahau rantse rantse abinka da yarinta kuma ta rikice sai fadi take wallahi baba karya take ban zageta ba na rantse da allah ban zageta ba
Malam yace shin zaki fito ko saina shigo dakin?
Rabiu yace kayi haquri don allah baba wallahi bata zageta ba
Malam yace au karya tayi mata kenan?
Ta zabura ta boye bayan rabiu tana kuka tana bashi haQuri amman bai sauraretaba yasa hannu ya fisgota daga bayan nasa ya jata a qasa kiyyyyyyyy
Har waje ya janyo igiyar guga ya shiga laftarta ta ko ina bugu bana hankali ba baya ko duban inda zai doka sai ihu take tana roqonsa
Rabiu ya duqar da kansa qasa baya ko iya motsi hawayene kawai masu zafi dake diga daga idanunsa
Saida yayi mata dukan bala,I ya farfasa mata jiki sannan kuma ya tabbar da ko motsi batayi sannan ya kyaleta harya wuce ya dawo ganin alamun kamar ta suma yasa ya janyo ruwa cikin guga ya sheqa mata ta sauke nannauyen numfashi yace sannan ki tashi maza ki dora tuwon siyarwan don lokacin sahur ya gabato
[1/8, 4:44 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/9, 9:55 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER 6*

Saida yayi mata dukan bala,I ya farfasa mata jiki sannan
kuma ya tabbar da ko motsi batayi sannan ya kyaleta harya
wuce ya dawo ganin alamun kamar ta suma yasa ya janyo
ruwa cikin guga ya sheqa mata ta sauke nannauyen
numfashi yace sannan ki tashi maza ki dora tuwon
siyarwan don lokacin sahur ya gabato
Anan muka tsaya
Rabiu ya miqe ya rarrafa wajenta gamida jawota jikinsa
yana sharar hawaye baisan sanda wani irin kuka maiban
tausayi ya kubce masa ba saida yai mai isarsa sannan
Ya janyeta ya tafi hura wutan tuwon don daman ya iya
tuwon duk da ba sosai ba don tun yana yaronsa inna laure
ke sanyashi kafin saude tayi kwari amman abinda ba
aikinkaba har saude data girma daga baya taxo ta fishi
iyawa
Saidai yau haka ya zage bakin kokarinsa yayi tuwon da
miya laure ta murmula musu naira biyar biyar ta zuba
tuwon a baho miyar a bokiti gamida basu fitila
Rabiu ya dauki kwanon tuwon akai kana ya dauki na miyan
a hannu yace saude ta koma ta kwanta shi zaije ya siyar
har bakin tasha yaje dukda rashin kyan hanyar ya samu
wuri ya zauna inda yan garuwa direbobi da matasa ke zama
Acan yayi sahur dinsa daida akai sallar asuba sannan ya
dawo saidai bai saida duka ba
Laure tahau fada tsohon munafuki ai daman don mugunta
kaqi tafiya da sauden don kaje ka dawomin dashi
Inda kun tafi tare ganinta ai wanda baiyi niyyar siyabama
sai ya siya tunda yana ganin mace amman shine kai ka
kwasa ka tafi
Zan gani duk uban daya daure muku gindi a garinnan yau
zan ganshi don sahur din da za,ai na gobe da ita zakaje
Munafikin bazan da wofi wanda yayi gadon baqin hali insha
allahu qarshenku bazaiyi kyau ba
Yaddah uwarku ta mace a wulaqance kuma haka zaku bita
daya bayan daya
Rabiu ya ajiye mata bahon ya wuce zuciyarsa na faman
suya da tuquqi mai ciwo
Wasu irin hawaye suka dinga zarya a saman kumatunsa
Yana isa dakin tun kafin ya zauna ta zaburo ta nufo dakin
ta hankade labule saika fito munafukin allah kaxo ka jido
mana ruwa ka tashi wannan yar iskan taxo ta fara aikin
gida ita kuma aiba wani kuka ajeba da zaku kwanta kuyi
barci shikuma yai muku aikin gida maza ku taso
Rabiu ya goge hawayensa sannan ya tayar da ita zazzabine
fal a jikinta tausayinta ya kamashi ya kamata suka fito yana
nashi aikin yana nata har suka gama basu suka zaunaba
saida rana ta haske gari gaba daya
Sannan suka kwanta hakanma badon tasoba saidon babu
sauran ayyukan da zasuyi matanne amman da bata barsu
sun kwantan ba
Sun samu barci yakai na awa biyu kafin masifaffiyar ta
tashesu ta turasu markade daganan basu sake samun
zamaba har dare
Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin kunci da takura har
azumi yakai ashirin da tara kowa nasaran gobe sallah duk
inda ka gifta anata yankan kaji
Wasu natakai markaden abincin sallah inda su rabiu da
saude ke tsugunne kan dakalin dakinsu duk sun zubawa
inna laure ido wacce ke zaune a bakin murhu saman kujera
sai faman suyan naman shanu take
Iklima yar baba (sunan da take kiranta dashi kenan)sai
faman kaiwa da komowa take tana miqa faranti ana tsomo
mata
Suna tsugunne harta kammala suyar ta zuba cikin babban
langa ta juye man tayi daki tabar iklima zaune waje tana
yagar nama
Malam bala yai sallama niqi niqi da laidoji a hannunsa
Rabiu ya tarbeshi da sannu da zuwa ya miqa hannu zai
karbi kayan dake hannun nasa ya noqe yana fadin
A,a barshi kawai gyaramin tabirma kawai na zauna a bakin
dakina
Rabiu ya kwasa da hanzari ya gyara masa tabarman ya
zauna
Sannan shima ya koma wurinsa kamar daxun inna laure ta
fito daga daki tana fadin
A,a malam sannu da zuwa ya amsa yauwa laure sannu da
gida taja ta zauna kusa dashi
Mu muka samu kuma malam?
Ya watsa hakorannan kaman an watsa wake miya kamin
yace kayankune na amso muku daga wajen tela sannan na
qara biyawa ta kasuwa na qara hado muku sauran
kayayyaki wasu kudine nai sa,a wallahi akaimin biyan
bashinsu yanxunnan
Inna laure taja ledar tana fadin sannunka kuwa malam bari
mu gani
Ta janyo ledojin tana zazzagewa
Atamface soso yar yayi aka dinka mata ita da yarta kala
bibbiyu sai takalmi danko kowa guda guda sai tsakiya ta
wuya data hannu kowa da nashi sai gyale kowa da nashi
Dadi ya cika laure aiko saita rangada guda aiyiriri wallahi
tallahi malam ka biyamu allah ya qara budi kaji
Shi kuwa sai ji yake kansa na qara fashewa ji yake dada
akwai saura cikin aljihunsa daya qara zazzage mata
saboda yaddah ta kodashi
Laure ta yafito iklima dake zaune tanacin namanta
Iklima ta kwaso da sauri cikin doki ta zauna tsakiyarsu tana
daddaga kayan
Dadi ya cikata ta miqe tana gwargwadawa tana tsallen
murna
Saude dake zaune ta daga kai ta kalli yayanta idonta cike
da hawaye yaya ni ina nawa kayan?
Rabiu ya kalleta cike da tausayawa yace kiyi haquri kema
anjima zan siyo miki naki kinji?
Kai kawai ta daga masa hawayen da suka taru idonta suka
gangaro yasa hannu yana goge mata
Inna laure ta miqe ta tattara kayan ta shige dasu daki
shikuma malam ya dauki buta yai bandaki
Rabiu ya dubi saude murya qasa qasa yace bari inje in siyo
miki naki kinji?
Kai kawai ta daga masa ya miqe ya shiga dakin nasu ya
bude kayan qyaure ya ciro kudin da yake tarawa yan
hamsin hamsin din da alhaji bashir ya dinga bar musu ta
cikon koko da kosai
Tun farkon azumi har zuwa yau ya fito ya fice abinsa
Kai tsaye kasuwa ya wuce ya zaga sosai ya samo mata yan
kanti doguwar riga da wandonta naira dari bakwai sannan
ya siyo mata yar qaramar abayarnan mai hade da kyale
waddah akema laqabi da gemun shaidan lol ya siyo mata
wannan naira dari biyu da hamsin
Sannan yasai mata takalmin dari biyar
Daman kudin dubu dayane da dari hudu ya tara kuma ko
naira bai dawo da itaba don saima da aka biyoshi bashin
naira hamsin
Yayi sa,a daya dawo ba kowa a tsakar gidan don haka ya
wuce dakinsu kai tsaye
Saude na kwance tayi rigingine tana kallon sama daka
ganta zakasan tana cikin damuwa ya zauna gefenta yana
fadin tashi saude ga kayan na siyo miki
Ta tashi cikin doki ya zazzage mata kayan ta daddaga tana
gama gani ta fada jikinsa domin murna shima ya rungumeta
yanajin wani sanyin dadi na ratsa zuciyarsa
Ganin farin cikin qanwar tasa ya fiye masa komai a duniya
Washe gari itace ta kasance ranar qaramar sallah idan ka
duba jama,a sai hada hada ake kowa yana cikin murna da
farin ciki yara da manya
Kowa yana cikin sababbin kaya cikin tsabta da kamshi
Haka gidan malam bala shida matarsa da yarsa suna cikin
wadanda suka raya wannan rana sunsha kwalliya cikin
sabuwar sutura amman banda
Rabiu da saude
Don tunda garin allah ya waye suketa faman aiyukan gida
suna gama aiyukan kuma saude tahau kai abinci gidaje
yara sai tsokanarta suke qazama qazama yau abin ko
kadan bai dametaba sbd itama tasan yau zatayi tsabtar
kamar kowa itama zatayi kwalliyar da take ganin iklima nayi
ta shafa jan baki tayi kwalliya a fuska tana gama rabon
abincin ta zura guga a rijiya cikin rawar jiki don itama tayi
kwalliyarta tayi yawon sallah
Yan matan unguwar tasu sukai sallama da yawansu don
aqallah zasukai goma duk sunsha kwalliya ji take babu na
biyunta
Saude ta amsa musu sallamar dasuketa rerawa
Yar baba nanan?suka tambaya saude tace tananan a daki
suka wuceta suka shige ita kuma taci gaba dajan ruwanta
tana shirin wankane suka fito suna labarin zuwa masallaci
daganan su wuce yawon barka da sallah
Saude tace dan allah larai nima ku tsaya nayi wanka mu
wuce tare
Larai ta watsa mata wani kallo tabdijam waye zaije yawo
dake yar tallah duk nanma wacece qawarki? Tayi shiru tana
kallonsu
Salame tace ai sunanki ta kira kinga kenan kece qawarta
Larai tayi saurin fadar allah ya sauwaqe saidai ko yar
gidansu takebi yar baba yar uwarta yar baba ta turo baki
allah ya sauwaqe niba yar uwata bace yar tallar gidanmuce
yarinyama tace zata bini ba sai inci uwartaba
Lantana tace to a ware kowa ya ware muga wanda zatabi
kowa ya ware ya daddaure fuska
Saude ta hadiye kukan dake neman kubce mata tace ai
nima yara yanxu zanyi wankana insa sababbin kayan da
yayana ya siyo min inyi kyau
Yar baba tace ke matsa can kyan gidan ubanwa zakiyi
kullum sai qazanta jibeta da wani hancinta can sai kace
kajeren wando duk sukasa daria harda tafawa sannan suka
fice
Saude ta dauki ruwanta ta nufi ban daki tana fadin aidai
allah ne ya bani
Tayi wankanta ba soso ba sabulu don dama ta saba ta fito
ta shiga dakinsu batada ko man shafawa ballentana kayan
kwalliya
Don haka kayan kawai ta dauka ta sanya ta saka sabon
takalminta
Da gyalenta tayita juyawa dukda ba kallon kanta takeba
amman ji take tamkar babu wanda ya kaita haduwa
Rabiu ya riqe labule dariya ta kwace masa yaddah yaga
tanata faman juye juye sai kace mai rawa tayi saurin
juyowa
Tace yauwa shigo yaya wai don allah nayi kyau?
Rabiu yai murmushi mai hade da daria kamin yace aike
daman kyakkyawace qanwata ba kayanne zasu fito da
kyankiba kyankine zai fito da kayan kisha kuruminki insha
allahu indai ina raye saina fito da boyayyen kyanki a idanun
duniya dauko kusar can kixo in kwance miki kanki duk shi
ya bata kwalliyar
Saude tayi saurin dauko masa ya zauna ya kwance mata
tas ya sharce mata yasa tsumma ya daure mata shi ya
lulluba mata gyalen ta miqe zata fita
Sai kuma ina?
Tadanyi jim kafin tace waje zani yace to bari inci abinci sai
in sameki kofar me gari zan daukeki muje kiyi kallon sallar
Dadi ya kamata harda tsalle. Ta fice
Inna laure na zaune saman kujera tanacin soyayyen nama
wanda ko qashi batabamasu saudenba ballentana susa ran
tsoka
Cikin rudu da kidima laure ta dauki sallallami laila ha
illallahu muhammadur rasulillahi
Mezan gani yau ni laure saude zonan dan qashin ubanki
Ta zaburo ta shaqurota ta maqure uban waye ya baki
kayannan?
Yar iska kudina kike sata a gidannan ban saniba,,,
Ta dauketa da mari da qarfinta kokuwa maza kika farabi
iye?
Saude ta fara ihu tana kakari sbd shaqar da tayi mata
Laure ta hankadar da ita har kanta ya bugu da bango ta
shiga kwalama
Rabiu kira wanda tundata soma dukan nata yakejin kamar
ya hadiyi zuciya ya mutu sbd baqin ciki ya fito daga dakin
ya nufota yana fadin gani
Laure ta daukeshi da wani mahaukacin mari wanda ya
sashi dafe kunci ta nunashi da dan yatsa cikin bala,I bakinta
har kumfa yakeyi
Gidan ubanwa aka samu wannan kayan sata kukemin a
gidannan ban saniba?
Aiko sai laure tasa ihu yau na shiga uku na lalace abinda
nakeji a waje yau ya shigo cikin gidana ashe da yan fashi
nake zaune ban saniba
Lol
Su laure manya
[1/9, 9:55 AM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/12, 5:44 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

*CHAPTER 7*

Laure ta dauke shi da wani mahaukacin mari wanda ya sa shi dafe kunci, ta nuna shi da dan yatsa cikin bala,i
“Gidan uban wa aka samu wannan kayan sata: kuke min a gidan nan k0 kuma me?" Rabi‘u ya girgiza kai cike da kunar zuciya ya girgiza kai alamar a’a, ta hayayyako masa. “To gidan uban wa ta samu wadannan kayan?” Rabi‘u ya hadiye wani abu da ya tsaya masa a. zuciya kafin ya fada mata. yanda a kai ya samu kudin tun kafin ya karasa rufe baki ta sake dauke shi da wani gigitaccen mari cikin zafin zuciya take fadar. “Ni za ka dauka ‘yar iska ni zaka nunawa iyakata, Karya kake Rabi’u baka isa ba wallahi tallahi kaci karya ka kwana da yunwa baka isa kaja daniba,yandanaga bayan uwar data haifeku kuma bazaku gagareniba, don haka ka taka a sannu wallahi idan kai wasa sai na rufe babinka a duniyar nan k0 sunanka babu wanda zai sake ambata a garin nan.
. janyo Saude ta shiga cire mata kayan tana fadin. “Ban yi niyar ta sanya sababbin kaya ba, kuma kai baka isa ka sata sanya suba.”
Ta cire kayan gaba daya ta hankadar da ita gefe ta wuce daki tana. faman huci.
Rabi‘u ya runtse idanuwansa yana jin zuciyarsa kamar za ta fashe saboda baqin ciki da takaici
kukan Saude ya dame shi a zuciya ya tallabo ta a jikinsa ya wuce daki da ita, ya dauki kayanta masu datti ya saka mata ya ja ta a jikinsa ya rungume yana lallashinta.
“Ki yi hakuri ki daina kukan nan haka kinji ’ insha Allahu zan siyo miki wasu ki yi shiru kinji
' ban san yawan kuka
Da qyar ya samu ya lallashe ta ta yi shiru, har wani barci mai nauyi ya dauke ta sai ajiyar zuciya take saki akai akai, tausayinta ya dirar wa Rabi’u. Tabbas bacin ita da ta rage masa yana ga da ya gudu ya bar garin, to idan ya gudu bai san halin da gudar qanwar tasa zata shiga ba, a dole ya zauna, dole zai yi hakuri ya ci gaba da fuskantar rayuwar dake tunkarar su.
' Ya runtse idanuwansa wasu irin hawaye masu zafi suka shiga zubo masa a idanuwa suna sauka saman kan Saude wacce baccinta ya yi nisa sosai. yasa hannu yana goge hawayen da suka Bata. masa fuska.
Haka rayuwa ta ci gaba da taflya babu abin da da ya cansa sai ma abin da ya qaru, kullum da wahalar dake kunno kai. A tallar Saude kuwa sai ma abin da yayi gaba.
Wata rana da safe Sande ta dawo daga markade
Ta zauna bakin murhu' tana hadawa Laure wuta, Malam Bala ya fito riqe da hannun ‘Yar Baba tana
sanye da sababbin kayan makmantar boko, koran wando da farar riga da koran kallabi da farar abaya, ta sha takalminta sandal da farar safa, ta goya jakar: goyan ta.
Saude ta tsaya da hura wutar tana kallon su cike da sha’awa yanda ‘Yar Baba ta yi kyau cikin sababbin kayan, har bata san lokacin da ta mike ta soma bin su ba don kar ma su Bacewa ganin ta.
Tinqis-tinqis ta ringa bin su har suka iso makarantar ba ta tsaya aka ba ta labari ba hae: cikin oflshin Head Master ta bi su ta yi tsaye tana kallon su.
Malam Bala suka gaisa da Head Master sannan ya gabatar masa da ita matsayin sabuwar daliba, shugaban makaranta: ya riqo hannun ‘Yar Baba yana fadin
“Ai tuni wannan ta wuce shiga aji daya dan ta kai shekara goma zuwa sha daya, sai dai a kai ta aji uku idan ma ta maida hankali sosai maimakon ta shiga aji'shida sai ta wuce fom one kawai.”
Malam Bala ya shiga yi masa godiya, Head Master ya dubi Saude da ke tsaye tana zaro ido ya ce “Ke kuma fa lafiya, k0 tare ku ke” ‘
Malam Bala ya yi saurin juyawa yana kallon inda Saude take tsaye
Yasa sallallami ya mike yana fadin, “Yanzu biyo mu ki ka yi ‘yar jakar uba.” Ya fizgo ta yana rankwashi yana zagi.
Head Master ya yi saurin miqewa ya riko shi yana fadin, ‘Don Allah ka yi haKuri Malam ka kyaleta yarinta ce kawai.” _
Malam ya cw, “Haba, haba yanzu wace yarinta ce wurin wannan iskanci ne dai kawai.”
Head Master ya ce “A’a kar ka ce haka kila abin ne ya bata sha’awa hala ita ba ta makarantar neko?
Malam Bala ya cc, “Ba a sa ta ba ita talla take.”
Head Master ya ce, “Kai abin nan yana ci mana tuwo a kwarya wai yanzu yarinya kamar wannan a kashe ta a kashe rayuwarta da talla, kullum muna fadakar da iyayen yara a kan su kula da hakkin. ‘ya’yansu a kan su don kiwo ne a gare su Allah ya ba su amma ba sa ji.
Wallahi mafi yawanci ‘yanmata wurin talla nw suke lalacewa, don a wurin talla ne yarinya za ta saurari maganganun da ba su kamata ba. A wurin talla ne yarinya za ta ji batsar da tunda take a duniya bata taba jin taba. A wurin talla ne yarinya ke sanin abin da ke faruwa tsakanin namiji da mace, ba tare da shekarunta sun kai ta sani ba.
Malam idan na soma karanto maka illolin talla sai mu kwana anan ba mu idar ba, sai kun je inda matatarar maza suke ka iske mace ta kawo talla kaji
ikon Allah, daga nan sai ka fara ganin namiji ya ci abu ya ce ba zai biya ba yarinya na ta bin sa yaqi ya bayar, ka ga ta riko rigar shi sai ya ba ta ya kwace, ka ga yana gudu tana bin shi daga haka sai ka ga kokawa ta tashi, wata rana sai ka same su suna wasan banza da zabgegen saurayi da gandareriyar budurwa mts!” Mts! Ya ja tsaki cike da takaici yana fadin.
“Abin dai sai gyaran Allah.”
Jikin Malam ya yi sanyi ya yi wa Head Master sallama ya tisa Saude a gaba suka tafi yana jin wani abu na yi masa yawo a zuciya.
Yana yin sallama a gidan Laure ta yo kan su tana ' fadin, “Ina ka kamo wannan watsatstsiyar yarinyar? Tun dazu nake nemanta na karade gaba dayan gidan nan ba ta nan tun dazu na gama waina hatta sandare ina nemanta."
Ta fizgo Saude da ke gabanta tana

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login