Showing 90001 words to 93000 words out of 103547 words

Chapter 31 - YAR TALLAH complete

Start ads

Unknown   

24 Aug 2025

419

Middle Ads

kansa
Tun tana turjewa har ta gaji ta saki jikinta, saida
ya tabbatar ta qoshi sannan ya kyale ta ya ja "
hannunta suka mike suka nufi falo inda suka baje
.inda yaketa Koqarin ya ga ta saki jiki da shi “
Karfe biyar na yamma taga ya yi shirin; fita
zucayarta ta yi mata wani iri ta zuba masa idanu
ba tare da ta iya tankawa ba Dr yana lura da
yadda yanayinta ya sauya lolkaci guda, amma sai
ya mika mata hannu, “Taso mu je Madam in
zazzagaya dake kiga Bangarenki ki kuma gaisa
da ' ma,ai katanki” ' Ba musu Saudat ta mika
masa hannun nata ya janyo ta suka fice daga
falon sai da suka ratsa 'faluka kusan hudu
sannan suka hau matattakalar .bene suka sauka
falon qasa; sannan suka koma falon da ya’ fi
kowane girma a cikin gidan, a cikinsa kuma ke
da Bangaren ma’aikatan har su'uku ‘yan mata
biyu dattijuwa guda, sai kicin wanda yakr ta
' ,waje, nan kuma akwai mutum biyu masu girki
kwararru mace da namiji. Sai da ya zagaya da ita
ta ko’ina na Gangarenta wanda tsarinsa ya yi
matukar burge Saudat komai na ciki ya yi mata,
musamman wuraren shakatawa da wurin
hutawarta. Suna gama zagayen gidan ya ja ta
waje har inda harabar motocinsa suke da sunan
rakiya, ai ' suna isa wurin motarsa ta tubure sai
ya tafi da ita ' Dr ya riko hannunta yana fadar,
“Tsaya kiji bafa dadewa zanyi ba, just minti
talatin na dawo su Momy kawai zan je in gaisar,
insha Allahu ba zan jimaba
Saudat ta kWantar da murya kafin tace “Allah ya
kiyaye” hanya Dr ya dan zuba idanu kafin ya ce
Kinmin izini da gaske har cikin zuciyarki na tafi
karfa sai na dawo in fuskanci fushinki” ‘ ' Saudat
ta dan yi dariya tana fadar, “Haba ni na isa? Ai
sai”
Bangazar da akai kai mata ce ta katse maganar
da take qokarin yi, ta yi taga-taga ta fada ‘_ kan
motar da ke gabanta, kanta ya bugi motar,
Saudat ta dafe goshi ta waigo tana ganin mai
,wannan aikin, ba ta yi mamakin ganin Asma ba
wadda ta sha gaban Dr; har jikinsu na gugar
juna.
Saudat ta ji wani irin abu ya dakar mata zuciya
tamkar saukar guduma, musamman yadda taga
ya kafe ta da fararen idanunsa ba ya k0 son
kiftawa, yana kallon yadda take magana cikin
kissa da gadara
“Zan yi magana da kai?”
Ya mantar da tasa muryar kasan tata, “To ga shi
kuma fita zan yi yanzu a yi haquri sai na ‘ dawo”.
, .
Ta watso masa wani fari mai kama da harara '
sannan ta juya a fusace ta nufi inda sabuwar ’
motarta ta ke mai baqin gilashi “ta fada
mazaunin dircba tare da dagawa escort
Dinta hannu ; ta ja abinta a guje ta fice
DR Ahmad ya yi wani dan gajeran murmushl tare
da kallon inda Saudat take wadda . tsabar takaici
yasa ta wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta,
Dr. ya yi saurin janyo ta jikinsa yana fadar, "Am
sorry tawan baki dai ji ciwo ba ko?”
r Saudat: ta watsa masa wani kallo mai cike da
tuhuma kafin tace “Au ban ji ciwo bama zakace
. bayan kana kallon abin da tayimin
, Ya ce, “To me zan ce mata Saudat? Ta yi
tayine don ta Bata min rai, ke kuma ta sa ki
Bata kwalliyarki to da na nuna mata ban damu
ba ai ga shi ta tafi k0, kuma ke don ina tsaye sai
ki ce ba za
ki iya rama wa kanki fada ba sai dole nina rama
miki Ai sai kuma na zama marar adalci a
tsakaninku k0 ba kya so na zama adali ne?”
Saudat ta zame jikinta cike da da haushi ta
Nufi hanyar bangarenta. *
Dr ya girgiza kai a zuciyarsa yana fadar, “Mata
ke nan”
‘daniel ya bude masa gidan baya na motarsa, ya
shiga sannan ya rufeshi kuma ya shiga gida
gaba mazaunin direba ya ja shi suka tafi
Waiwaye adon tafiya Inji Malam Bahaushe bari
mu waiwaya baya muji shin wane ne Dr
Ahmad Muktar? Profassor Mukhtar L Kabir
shahararren dan boko ne, kuma fan kasuwa da
sunansa ya kewaye
Najeriya, kuma muhimmi a cikin lamarin da yawa
na shidda a cikin masu kudin qasar nan. Bai taba
rike wani mukami na siyasa ba amma kuma yana
daga cikin masu fada a ji a harkar siyasa da
mulki don yana tare da manya-manyan ‘yan
siyasa tun daga na qasar nan har zuwa qasashcn
qetare. Ahmad shi dan dansa na farko, sai da
aka kwashe shekaru goma sannan aka yi masa
kanwa Farida
kuma daga su ba a sake haihuwa ba, tun tasowar
Ahmad mahaifinsa ya so ya yi karatun boko mai
zurfin gaske don haka yana kammala firamare ya
tura shi qasar America a can ya yi sakandire
dinsa ya hada doctoring degree dinsa a kan abin
da ya shafi harkar siyasa da mulki. Yana
kammalawa ya ce ya tsaya iya nan, duk da
mahaifinsa bai so ba a dole ya kyale shi
kasancewarsa na dan gaban goshi.
' Dr. Ahmad bai fara harkar siyasa ba sai da ' ya
hadu da Asma don ita ce ma ta cusa masa
ra’ayin yin siyasar amma shi ya yi karatunsa ne
ba don yana ra’ayin yin mulkin siyasar ba amma
saboda' ita shi ma ya tsunduma kan harkar
siyasar wanda a yanzu ta rage saura ‘yan
watanni su sauka kuma ya yi alkawarin yana
sauka ba zai sake komawa ba don bai ga abin da
yake nema ba da zai
dora wa kansa wahala ba, a matsayinsa na dan
majalissar dokoki ta tarayyar Abuja, amma fa inji
shi saboda a ganinsa mulki wahala ne, kuma
bala’I ’ ba kadan ba ga wanda ya kasa tsaida
gaskiya da amana Wannan kenan .
K0 da Saudat ta koma sashinta kai tsaye
bédroom dinta ta nufa ta fada kan gadonta ta
kwanta zuciyarta cike da haushin abin da
Daktanta ya yi mata, da taimakon sanyayyen
sanyin air conditioner wani nannauyan bacci ya
yi awon gaba da ita. *
Ba ita ta farka ba sai qarfe bakwai da rabi da
yan mintina ta yi saurin saukowa daga kan gadon
zuciyarta na mamakin yadda har ta bari ta yi
baccin yamma ga shi har magruba ta kubce
mata. Cikin gaggawa ta dauro alwala ta fito ta yi
sallar magriba da isha tare da shafa’I da wuturi
sannan ta tsaya gaban madubi daga tsaye ta yi
‘yar kwaliyarta marar nauyi, sannan ta nufi gaban
wardrobe ta ciro kayanta ta saka English west
riga da siket. ~
Fara: shirt silk sai dogon siket dinta baki irin mai
fadin nan yana da adon fararen fulawowi ta
warware gashinta ta daureshi da farin ribbon
'Kwara guda sannan ta makala wa kunnenta‘ yar:
‘ Karamar barima ta gwal ta yi kyau sosai, ta
koma. tamkar irin yan matan turawan ta zira
silifas na fata, sannan ta fito falonta ta tsaya
gaban talabijin din da ke girke gaban bango tana
canza channels
.”Dr. Ahmad ya shigo da sallama Saudat ta amsa
ba tare da ta juya
* ta kalli inda; yakeba ya shigo cikin falon ya dire
katuWar lrdar dake hannunsa mai dauke da'
tambarin Alshukur shoppin mall ya fada kan
kujerada alamun gajiya a tace da shi ya mika wa
Saudat hannu, ‘Come on my baby, wallahi I am
"‘ very tired zo in ji duminki kusa da ni ko na
wartsake" . Saudat ta waigo ta dan kalle shi
kamar ta share shi sai dai girman da yake da shi
a cikin idanununta baza su barta ba, don haka ta
nufi inda yake ta zauna kujerar da ke nesa da
tasa tare da fadar, “Sannu da zuwa”
Dr ya tsare ta da narkakkun idanunsa wanda
ya tilastta wa Saudat kallon kafet ya koma ya
jingina bayansa da makarin kujerar tare da fadar
.“Zo ki duba ledojin nan ki ga abin da ke ciki”.
. Saudat ta mike ta :nufi gefensa ta durkusa kan
kafet tare da janyo ledar daya ta shigo da ita, ta
bude kwalaye ne har guda biyu, manya sai dai
daya yafi daya girma ta dan dago tana kallonsa
yace
“Bude mana Bare kwalayen” .tayi Saudat ta
gyara zama sannan ta soma bue qaramin kwalin
sai ga razananniyar ‘ waya
iphone6plux kwance a cikin kwalin ta ajiye a
gefe
ta bude babban kwalin sai ga wata Yar qaramar
abu mai kamar komfuta ta daago tana kallonsa
da niyyar ta . yi magana ya katse ta ta hanyar
saukowa dagakan '
’ kujerar ya zauna gefenta ya karbi yar abar ya
Kunna yace“Wannan da kike gani sunanta ipad
kamar camputer yake zaki iya shiga yanar gizo
da komai _ Ta ciki nasa an zuba miki abubuwa
da yawa a ciki Wanda zai bude miki Kwakwalwa,
kuma zai rage 'dinga debe Niki kewa idan har
bana nan tunda ldan kinga ni din ba mazauni
bane cikin watan man da wuya inyi kwana hudu
a gida, saboda abubuwan da ke kaina ;NASA
milki kudi a ciki nayi miki saitin komai a . yanzu
zan fara koya miki yadda ake amfani da ita,. : Sai
kuma wayar da nayi miki alqawari gata ' nan
akwai akwai sabon sim a ciki na hada Saka miki
kudi a ciki, akwai lambar Momyn Shukura a ciki
idan za id kira su”. ' Ya zura hannu cikin aljihu
sai ga key din mota ya miqa mata, “Wannan
kuma makullin‘ . ‘mota ne saboda ko watarana za
ki ji sha awar' ” yin tuki da kanki, saboda zuwa
makarantar dana
sai miki form din shiga makarantar social .
development Abuja, karatune zakiyi nayan
watanni zaki zama basic illetrate wata hudu
zakiyi ki gama ki amshi certificate dinki sannan
ki tafi ki karanci
social welfare wata Tara , sai ki Kara karBar
certificate wanda shi zai ba ki damar ki tafi
jami’a ki hada difloma in kina da bukata ma har
digin‘ dinki sai ki hada da fatan za ki maida
hankali don ke maki zama wani abu watarana”.
Tsabar jin dadi da murna Saudat har ta rasa . ta
yadda zata iya furtawa wani Abu idonta ya ciko
da kwalla idan akwai abin da take q auna a
rayuwarta bai wuce karatu b a, ashe kuwa
Ubangiji zai cika mata burinta, tamkar za ta yi
kuka ta fara zayyano masa godiya. Ya daga mata
hannu, “Ya ishe ni haka Saudat, ban miki don ki
gode min ba, Ubangiji za ki gode ma wa don Shi
ne Ya kwato miki, kuma idan kina sha‘awar shiga
islamiyya to ita ma ki shirya ranar asabar mai
zuwa in kai ki Da’awa akwai sashin matan aure
sai ki rinka zuwa ranar asabar da lahadi da safe
kawai, taso mu je in gwada miki motarki".
Ya riko hannunta ya mikar da ita ba tare da ya
sake bari ta fadi abin da ta ke son fada ba suka
nufi harabar waje
Ganin shirgegiyar motar da Saudat ta yi sabuwa
dal ba karamin daga mata hankali ya yi ba, don
ba irin motocin da ta saba gani bane a kan titi,
ta qara wa motar kallomai suna Expedition baka
mai bakin gilashi wadda ta mamaye wurin
tsayuwar motoci uku ta” maida kallonta kan Dr.
tana fadar Ni yanzu ya za a yi ' in iya jan wannan
matar Yallabai? Tayi girma sai ai ta mamaye titi
gaba daya ' Dr, ya tuntsure da dariya yana fadar,
“Bakauya sai kawai Expedition ta mamaye titi,
saboda tsabar shirmenki? Muje ciki daga gobe
zan
.fara koya miki tukin k0 don na ci dariya"
Saudat ta bata fuska ba tare da ta yi magana ba,
ya ja ta suka nufl sashinta yana Kara zolayarta,
wurin koya mata ipad din ma sai da ya ci dariya
saboda qauyancinta don Saudat dai ko a waya ba
komai ta iya ba, to bare ta fahinci ipad cikin
sauki ' ta ida qulewa ne ta yi zuciya ta yi ciki
abinta, yana kiranta ta Ki kula shi don haka shi
ma ya tattara ya ‘ biyo ta da tarkacenta .
Washegari tunda safe Dr. ya bar gidan saboda
meeting din da ke gare shi, don haka Saudat ta
sha baccinta sai wurin azahar sannan ta shirya
ta fito donta ‘karya kai tsaye dinning saidata
wuce falo uku sannan ta isa don nan ne inda Dr
ya sanar da ita ' kuku zai rinka shirya abinci, ta
zauna ta karya , sannan ta koma falonta ta dauki
ipad ta soma latse
’ latse, sai da ta gaji ta rufe ta dauki waya ta
danna lambar Mammy wadda suka kWashe fiye
da mintina talatin '” sannan ta kashe ta kira
Shukura, itama sun dade
suna hira kafin su yi sailama, tana mamakin k0
“katin nawa ne maigidan ya loda mata? ,Har
bayan sallar isha Dr bai shigo gidan ba, harta
fara tunanin k0 lafiya, hakan yasa ta sa‘ waya ta
kira' shi, a daidai lokacin da yake shigowa gidan
ya ce , “Shigowata kcenan Madam, na gaji sosai
ki sameni a Bangarena don Allah”. Ba ta Bata
lokaciba ta Kara gyara kwaliyarta ta fita daga
Bangarenta ta nufi nasa Sangaren wanda ya sa
bangarensu tsakiya, wato Bangaren Asma da
nata. Tana shiga ta same shi baje a falo ya yi
daidai yana kallon allon talabiji. ’ ' -Tun kafinta
zauna ya ce, “Don Allah jeki hada min ruwan
wanka a bandaki”. Ba musu ta hau sama ta shiga
bedroom din nasa sannan ta shiga bandaki ta
soma hada masa‘ ruwan, tana gamawa ta juyo ta
fito suka hade yana tsaye gefen bed dinsa ya c
ire kayan’dake jikinta, daga shi sai dan Karamin
gajeren wando.‘ kallo daya Saudat ta yi masa ta
raBa shi za ta wuceya sa hannu ya fizgo ta,
yana fadar, “Gidan wa za kine yarinya? Ai ke za
ki min wankan nan” _' Ganin da gaske yake yasa
Saudat ta ’ .sOma qoqarin kwacewa, amma sai
da ya sureta ya ‘shiga bandakin da ita, tana ta
shure-shure ya ' tsumbular da ita cikin qaton
bahon wankan da ta cika masa shi da ruwa, duk
iya borenta sai da ya .
.ya rabata jikinsa hakan ya tilasta . ta“ kyale shi
ya yi mata wankan, ya yi nasa saman ya ; fito da
tawul guda sukai Fitowarsu ta yi daidai da ihun
da Asma ta
kurma cikin tsananin firgici . “Me zan gani
Ahmad? Me ye wannan?” .
‘ . Ta Shiga jadA baya tana nuna shi cikin
tsananin firgici har ta fice daga falon
‘_ Saudat ta yi matukar razana da firgicin ganin
yadda Asmar ta same su saida yasata ‘zubar da
hawayen kunya da takaici don ta lura ma ‘ shi
gogan love, a jikinsa sai ma Kokarin shirya tada ,
yake ba tare da ya bi ta kan hawayen da ta keba,
ba _ yadda ta iya ta kyale shi har sai da ya zura
mata _ sabuwar rigar bacci wadda ya feshe da
sassanyan
turaren romaine. _ Yana zura mata rigar Saudat
ta fada kan gadon tana kukanta Kasa-kasa bai
kula ta ba sai da ya saka kayan baccinsa riga da
wando farare masu ,. Laushi da Kamshi sannan
ya hayo kan gadon ya tankwashe qafafuwansa
tare da fadar, “Tashi zaune ‘ mu yi magana”
Ganin da ya yi vata da niyyar motsawa yasa shi
janyo ta jikinsa ‘ yana fadin meye abin kuka
Don dan ta Shigo ta ganki tare da mijinki Meye a
ciki? kukin manta ni din mijinkine kuma ba
, haramun muka aikatawaba? Haba Saudat ya
kamata
ki fara girma haka nan ai ke abin alfahari ne a
wurin kishiyarki ta zo ta same ki da mijinki a
haka k0 kamai kin kunsa mata wani abu a
zuciya, kuma dole daga yanzu za ta fahinci keda
ita matsayinku iri guda ne a wurina, amma shi
warin, kukan me ye ma’anarsa?”
Shiru ta yi sai dai ta sa bayan hannunta ta goge
KWallar hakan ya sa shi ya gyara mata filon da
ke gefensu ya kwantar da ita yana fadar “Ki
wanta yanzu zan je in dawo, just a minute”.
Bai saurari abin da za ta ce ba ya sauka daga
kan gadon ya kashe wutar dakin ya kunna bedsid
lamp ya fice kai tsaye Bangaren Asma ya nufa
wanda rabonsa da shigarsa zai iya cewa ya
kwash
fiye da shekara kamar yadda ita ma bats
shigowa nasa bagaren saida wani Kwakkwaran
dalili
A hankali ya taka qafarsa cikin bedroom din nata
wanda sanyayyen Kamshin touch neke tashi babu
haske a dakin sai lamp bed lamp duk da bai iya
hango taba. akan gadon ba, amma yanajin
shesshekar kukanta '
Sai da ya kunna: makyallin wutar dakin haskce
ya gauraye ko' ina sannan ya nufi wurin gadon
ya ja bed chair ya zauna yana kallonta tamkar ba
Asma‘ da ya sani ba, ‘yar gayu mai tsananin
kwalliya tamkar aljana amma duk ta firgita kanta
gashin kan babu gyara duk da tsananin tsawonsa
da laushinsa, amma ya turmushe babu alamar
kwalliya a fuskarta, ‘yar doguwar riga ce baqa
mai dogon hannu ta saka, babu k0 kallabi Asmar
da ko ciwo bai hana ta yin kwalliya.
" Ya gyara murya kafin ya ce, “Tashi zaune mu yi
magana”.
Ba musu ta tashi din, don ta fahinci shigowarsa
dakin, ta tashi a zaune tana kallonsa ba tare da
ta daina ku;kan nata ba.
Dr. Ahmad ya miqa hannu saman bedside drower
dinta yadauko tissue ya mika mata, “Karbi
wannan ki goge hawayenki”.
‘Ba musu ta karBa tana gogewar shi kuma bai
jira ba ya dora da fadar, “Me ya yi zafi haka
Asma?”
Tamkar ba za ta tanka masa ba, sai dai ma
zuciya ta zarce duk yadda ta ke tunani, don ta
azabtu ta kuma sha wahala a kan share ta da Dr.
Ahmad ya yi tare da nuna mata da ita da
rashinta duk daya ne a wurinsa kafin zuwan
Saudat din harya zuwa yanzu. duk abin da ta ke
yi juriya ce da karfin hali da nuna jarunta, amma
ita ta sani Ahmad wani Bangare ne na rayuwarta
ya koyar da ita darussan qaunarsa masu wuyar
goguwa a
shekarun baya da suka wuee tabbas idan ta rasa
shi za ta iya shiga kowane irin hali. Cikin muryar
kuka
ta soma fadar,’ “Ahmad, dama ashe xaka iya ba
sa wata mace a matsayi irin nawa a zuciyarka
har ka iya' hada jiki da ita? Ahmad ina alkawari
da amanar da “~ ke tsakaninmu? Ina soyayyar da
ka ce kana min? ' da ma wannan ita ce kaunar
da ka ke labarta min?
: Ahmad za ka iya tuna rabonka da ka shigo nan
inda-nake? Daidai da ranar da aka kawo maka
amaryarka Ahmad ya kamata a ce ka shi go ka
duba halin da nake a ciki amma k0 a waya ba ka
nemceni ba k0 in mutu k0 inyi rai ba damuwarka
ba ce, yanzu bar wannan kodaddiyar‘ yar
matsiyatan ta fi ni daraja a cikin idanunka Ahmad
yaUshe ka daina sona?’ Sai da ya Bata wasu ‘yan
mintuna yana kallonta tare da mamakin wai yau
shene ya ga weakness dinta (kasawarta) yau
Asma ce ta sauke duk wani girman kanta da
dagawarta tare da jin kai da jinkanta ”wai yau ita
ce ke jero wadannan zantukan ta ajiye gayun , ta
yi tuBus lallai‘ yan maza sun yi taushi.
_ Ya dauke idanunsa a kanta ya ja aji kamar ba
zai yi magana ba, ya basar, “To kedin da ki ke
sona Asma me son ya amfanar don a matsayina
na mijinki ba ni da wata daraja a wurinki, ba ki da
lokacina baki da lokacin kulawa da ni da
tarairayata a matsayina na mijinki, sai dai ki tura
‘yan aiki su
bani kulawar‘ da nake bukata daga gare ki
‘saboda
Yar Tallah will be airing this week tonight only
ANYTHING BY 11 TO 12
[3:21PM, 08/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: YAR. TALLA
CHAPTER34
kawai kin raina ni,’ kina ganin daidai kike dani
don kawai na baki ~‘yancin yin duk abin da ki ke
so, ki rinka yi min gadara da isa? Don kawai kin
ga ni din mai tsantsani ne, ban damu da harkar
wasu mata ba, k0 k0 don kin fahinci ina sonki ne
kuma kina da kyau shi ya sa kike min abin da ki
ka ga da ma ni ban sani ba? Ba ki san daraja
taba, balle darajar aurenaba shin ni dutse ne da
zan kasa watsar dake

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login