Showing 60001 words to 63000 words out of 103547 words

Chapter 21 - YAR TALLAH complete

Start ads

Unknown   

24 Aug 2025

409

Middle Ads

ce “lnsha Allahu"
Doctor Mariya ta yi wani murmushi kafin ta ce “To na gode
kwarai“.
Ta dan ja numfashi ta ci gaba da cewa, “Da ma ba wata
magana ba ce kan maganar ‘yar uwarka ce Saudat a
katinta na ga ka
. rubuta sunan unguwarku wadda ke cikin Dandagoro haka
ne? ‘ Ya daga mata kai alamar eh
~ Ta girgiza kai, "To amma Hamid ka ce. Saude Kanwarka
ce, don Allah ka yi haquri ka
fada min gaskiya, ya ka ke da Saudat tsakaninka da Allah?”
Hamid ya dan zuba mata idanuwa yana mamakin tambayar
tata, kafin lokaci guda ya sauke numfashi; “Duk cikin
magarta babu wadda na fada miki ba daidai ba, Saudat
Kanwata ce wani abu ne likita?"
Dr. Mariya ta koma ta jingina da bayan kujerarta cikin
sanyin jiki ta girgiza masa kai alamar a’a kafin ta buda baki,
“Saudat ta samu tsagewar qashi a hannunta na dama
sannan a qafarta ma ta goce, sannan akwai buguwa a
qashin bayanta duk da dai buguwar
ba ta cossing din wata matsala ba, amma na yi . ‘
mamakin irin wannan manyan ciwuka haka a . jikin mace,
kuma qaramar yarinya ga shi ka ce ba hadari tayi ba, ba
komai ba”.
Hamid ya ce “Wallahi ba hadari ba ne, duka ne kawai".
Dr. Mariya ta ja wani tsaki-kafin ta ce “A gaskiya akwai
marasa tausayi a duniya, yanzu ko dabba ai ba a yi mata
irin wannan dukan ba”,
Ta qara jan wani siririn tsaki sannan ta ja dan siririn gilas
dinta ta sanya a idonta, tare
da janyo biro ta yi wasu rubuce-rubuce ta yage ta mika
masa, ya sa hannu ya karBa tare da miqewa ya yi mata
godiya ya fice. Dr. Mariya ta kwantar da kanta saman
makarin kujerar tana kallonsa har ya fice daga ofls din nata.
Hamid bai bar asibitin ba har garin Allah ya waye yana ta
faman zurga-zurga siyo wannan auno wannan, karbo
wancan har sai da aka kira assalatu sannan ya tafi
masallaci ya yi sallah, a lokacin an daura mata karin ruwa,
yana gama sallar ya dauki mota ya fice don hado mata‘
abin karyawa, sannan ya wuce gida, kai tsaye restaurant ya
nufa ya yo take away sannan ya fito ya siyi fruit da kayan
tea da duk abin da yasan za ta iya bukata sannan ya dawo
asibitin a lokacin kuma ya iske Doctor na ta nemanshi aka
ba shi wani list din abubuwan da zai siyo, kuma sai ya fita
asibitin, Hamid ya sauke numfashi don yasan yana zuwa
yanzu Dad dinsa ya gama Kuluwa don tun cikin daren jiya
ya keta faman kiran wayarsa yana fad‘a masa ga shi nan za
shi nan, daga qarshe ma sai ya
kashe wayar gabadaya tabbas ya san kuwa sunada dabi a
gidan yau.
Ya zura hannu cikin aljihunsa ya ciro wayoyin tare da kunna
su sannan ya yi gaba yana ta faman sauri kamar mai shirin
"tashi sama, ba shi ya samu ya yi saitin din komai ba sai
wurin daya saura na rana, shi ma kuma yana kokarin tafiya
Dr. Mariya ta tsayar da shi za ta rubuta masu sallama.
Hamid da ke zaune bakin gadon na Saudat ya ji wani farin
ciki ya kama shi, ya dafa gadonda Saude ta ke zaune a kai,
wadda ta sha ledojin ruwa biyu, ta yi fayau kuma tana nan
kamar an kulle biredi, muryarsa a sanyaye _ ya ce, “To
yanzu idan aka sallame ki ina ki ke ’ ganin zan kai ki Saudat
kafin in nemo mana mafita?"
Saude ta lumshe idanuwanta wanda .damuwa ta ke cike fal
a cikinsu, Hamid ya sake kiran sunanta, “Ki yi hakuri Saudat
ki manta, insha Allahu lokaci ya yi da zaki dandani zaqin
rayuwa ke ma kin ji?"
' Saude ta bude idonta da kyar tana kallonsa, aka turo Kofar
dakin aka shigo daga ita har shi suka zuba wa mai
shigowar idanuwa, ba kowa ba ne sai mahaifin Hamid,
fuskarsa ba yabo ba fallasa ya shigo ‘
Dr. Mariya na bayansa da takardu riqe a hannunta. Yana
qarasowa tun kafin Hamid ya yi wata magana ya cire hannu
ya zabga masa wani mari wanda ya sa shi saurin dafe
kunci, Alhaji Bashir ya nuna shi da dan yatsa, ni za ka dauka
mutumin banza ka nuna ‘ wa duniya ban isa da kai ba?
Wato har wannan
‘ yarinyar ta fiye maka mu k0 Hamid?
Kai yanzu in bacin ma ba ka da zuciya har ka sake kallon
yarinyar nan wadda ubanta ya nuna bai sonka, bai Kaunar
tarayyarka da ita, amma shine kake like ka nace har ka ke
bibiyarta da aurenta? To wallahi ba za ka zubar min da
mutunci ba, cikiri satin nan zan daura ‘ maka aure da duk
wadda tayimin tunda nalura auren ka keso, wuce mu je
mutumin banza kawai, na san babu abin da ke dibarka
~ sai wannan kyan fuskar”
. Hamid ya zaro ido tare juyawa baya, muryarsa a sarKake
ya ce“Dad ka tafi zan zo don Allah 'ka dubi halin da yarinyar
nan ta ke~
. ciki, ba ta da kowa sai ni sai Allah idan na tafi ' na barta
zata iya shiga kowane irin hali, don “ Allah Dad ka yi haKuri
ka ba ni awa daya",
Alhaji Bashir ya zuba masa idanuwansa cike da mamaki,
kafin ya ce, “Ka san kuwa abin da ka ke fada Hamid? Wato
har wannan abin yafi ni ke nan k0? Yanzu kai har kana da ~
hujjojin kare kanka idan iyayenta suka samu labari, yanzu
har ka manta cin mutuncin da mahaifinta ya zoya yi mana
har gida ke nan? To wallahi tallahi ka Kara minti biyar a nan
ban yafe maka ba, mutumin banza kawai”.
Ya juya a fusace ya bar dakin, Dr. Mariya ta matso daf da
Hamid muryarta a sanyaye ta ce“Hamid ka yi .hakuri ka bi
mahaifinka kada fushin Allah ya tabbata a kanka”. '
Idon Hamid ya kawo Kwalla cikin sarqewar murya ya ce,
“Doctor ba ta da kowa baiwar Allah ce idan na tafi na barta
ban san halin da za ta samu rayuwarta ba, na tabbatar
tafiya in barta ita ce silar da rayuwarta‘ za ta salwanta".
Dr. Mariya ta sa hannu ta dafa kafadarsa tana fadar, “Ka je
Hamid nayi maka
alqawarin rike Saudat a hannuna' daga yau har zuwa
lokacin da za ku satelin da mahaifinka, na yi maka wannan
alkawarin".
_ Dadi ya kama Hamid ya soma zuba mata godiya, ya zaro
wasu sauran kudin da suka rage masa ya mika mata,
wadanda bai
san ko nawa ba ne. “Ga wannan don Allah ki fara rikewa a
hannunki kafin in dawo”. Dr. Mariya ta girgiza masa kai.
“A’a, kai dai kawai ka je, ga Katina mu .yi magana”. Hamid
ya karBa yana godiya, sannan ya zuba da gudu ya flce don
tsoron cikar lokacin. Yana fita Dr. Mariya ta wuce ta nufi
qofa, ta maida ta kulle sannan ta juyo ta dawo inda Saude
ta‘ ke, wadda tunda mahaifin Hamid ya shigo ta lumshe
idanuwanta tana maimaita innaIiIIahi saboda yadda ta kejin
zuciyarta na barazanar tarwatsewa. Dr. Mariya ta dawo
cikin dakin ta ja kujera ta 'zauna tana fadar, “Bude idonld ki
kalle ni nan Saudat".
Sosai Saudat ta bude idanuwanta wadanda suka yi jajawur
tana kallonta, kafin ta ce, “Saudat waye mahaifinki?"
Saude ta ji tamkar ta caka mata wuqa a kirji cikin
dusasshiyar muryarta ta Malam bala. . Dr. Mariya ta ce,
“Mahaifiyarki fa?” Saude ta dan yi shiru tamkar ba zatayi
magana ba, kafin ta bude baki cikin muryar kuka,tace “Ban
santa ba, banma taba ganinta ba tunda na tashi na ganni
da Yayana Rabi’u da matar mahaifina Inna Laure, tunda na
tashi ban san dadin uwa ba, ban san wani ' gata ba wanda
da ke samu wurin mahaifinsa ba saboda ni. . .” .
Saude ta saurara daga bayanin da ta ke saboda hawayen
da ta gani suna zubowa daga idanuwan matar, idanuwan
Saude suka yo warwaje muryarta a sarqaqe ta soma fadar,
“Lafiya dai Doctor, me ya faru?”
Dr. Mari'ya ta riko hannunta gam ta rike tana motsowa cikin
kuka ta ce; “Saudat nice mahaifiyarku, nina haife ku da
cikina tun... ” ‘
Kuka yaci qarfunta ta soma wani kuka
mai cin zuciya.
Saude kuwa dif ta tsaya da kukan nata tana kallon matar
muryarta na sarkewa ta ce “Kece mahaifiyarmu? Idan ke ce
' mahaifiyarmu me ya sa ki ka tafi ki ka barmu? Me ya sa ba
ki sake waiwayarmu ba ki ka manta da mu ki ka watsar da
rayuwarmu kika wofintar da mu, k‘i ka bari aka tarwatsa
mu, muka sha wahala muka rasa mataimaki a duniya, kowa
ya tsane mun . Dr. Mariya ta yi saurin rufe mata baki cikin
kuka tana fadar, “Ya isa! Ya isa haka Saudat wallahi ban bar
ku ba sai don hakan shi ne mafita, ban watsar da kuba sai
don ina jiye muku tsoron wahalar da za ku iya fuskanta idan
na ce zan tafi da ku alhalin ni ma ban san inda zan nufa ba,
ku yi hakuri Saudat ina .yayanki?” ‘ Saude ta runtse
idanuwanta wasu hawaye suka ziraro mata, cikin kuka ta ce
“Sun raba mu tun shekarun da suka wuce Baba ya kore shi
ban sake ganinsa ba, ban san halin
da yake ciki ba. Nan ta labarta mata labarin rayuwarsu
tun farko har izuwa yau.
‘ Dr. Mariya kuka ta ke sosai ta rungume Saudat a jikinta
suna jin dumin juna, soyayya tsakanin uwa da da ta rinka
shigarsu tsawon lokaci kafin. su saki juna, Dr. Mariya ta ce,
“Taso mu je gida Saudat ki huta in baki tarihin .mahaifinku
da irin taskun da na shiga a lokacin aurena da shi". -. . Ta
riqo Saudat ta taimaka mata ta miqe, ta dauki makullin
motarta suka fita har zuwa
harabar asibitin inda aka tanada don ajiye motoci.
[1/30, 4:30 PM] A A Dboy: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/30, 9:54 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

BOOK 3

*CHAPTER 24*

Taso mu je gida Saudat ki huta in ba ki tarihin mahaifinkuda irin taskun da na shiga a lokacin aurena da shi".
Ta riqo Saudat ta taimaka mata ta mike, ta dauki makullin motarta suka fito har zuwa
harabar asibitin inda aka tanada don ajiye motoci.
Ta bude wa Saude gidan baya ta shiga ta maida ta rufo sannan ita kuma ta zagaya ta shiga mazaunin direba ta yi wa sabuwar motar key qirar Jeep mai taya a baya suka hau hanya kai tsaye Goruba road suka nufa a road ta tsaya qofar gate din wani madaidaicin gida mai kyan gaske da wadatar furanni masu tsayi ta yi' oda kusan sau biyar sannan aka bude gate din gidan ta cinna hancin motar a ciki maigadi yana daga mata hannu ta yi cikin gidan kai tsaye harabar wurin ajiye motoci ta nufa ta raba motar tata kusa da wata Matris sabuwa dal ta kashemotar ta fito sannan ta bude wa Sande ita ma ta fito ta riko hannunta ta ratayo a wuyanta saboda taji dadin taka qafar sannan suka shiga falon inda qofa ta ke a gefe suka nufi falon kai tsaye
Bai da girma sosai, madaidaici ne wanda ya cinye saitin knjeru guda da show glass tare da kayan kallo da santa table a tsakiya. Suna shiga falon qananan yaran da ke zaune suna wasa suka yo kansu suna, “Oyoyo ga Momy”.
Saude ta bi yaran da kallo, ‘yan qanana \ masu Dr. Mariya ta yi wa Saude masauki saman kujera sannan ta bi ta kan yaran ta rungume su a jikinta tana amsa sanu da zuwan nasu, ta nuna masu Saude, “Bakuga Antynku bane? Kuje ku gaishe ta”.
Yaran gnda biyu mace da namiji suka durkusa gaban Saude suna fadar, “Ina kwana Aunty”. ‘
Saude cikin karayar zuciya ta amsa da lafiya lau tana kallonsu, macer ce ‘yar babbar wadda ba za ta wuce shekaru shidda ba, sai namijin wanda bai wuce uku ba, Dr. Mariya ta ce, “Kannanki ne, Nabil da Nabila suna karatu ne a nan Saude su duka da maigidana Alhaji Ashiru yana aiki a central bank yanzu kizo muje ga dakin baqi can ki wanka kici abinci ki huta, sannan inzo muyi magana". ,
Saudat ta amsa da, “To”. Sannan ta mike suka nufi dakin.
. Karamin daki ne mai dauke da gado da kujeru Kwara uku sai kayan kallo. Falon ya yi kyau sosai saboda yadda aka qawata shi da kayan dakwareshin masu kyau, akwai toilet da dan wurin hutawa a cikin falon.
Dr. Mariya ta juya ta fito ta bar Saude taqarewa falon kallo ganin abin ta ke take tamkar a mafarki wai ita ce yau da mahaifiyarta, ikon Allah ko’ina Yaya Rabi’u ta san da zai samu labari ba qaramin murna da farin ciki zai yi ba.
Dr. Mariya ta sake shigowa rungume da sabuwar jallabiya a hannunta ta ajiyewa Saudat tana fadar, “Ki je ki watso ruwan ga jallabiya nan ki saka nasan za ta yi miki a Saudiyya na siyo ta”.
Saude ta amsa da,‘ “To na gode”.
Dr. Mariya ta yimurmushi kafin tace, “Me ye abin godiya kuma Saudat? Don Allah ki saki ranki ki rinqa kallona a matsayin mahaifiyarki kin ji?”
Murmushi kawai Saude ta yi tare da
‘sauke idanuwanta qasa Dr. Mariya ta juya ta fita sannan ita ma Saude ta yunkura da kyar ta
mike tana tsangala kafar da kyar ta shiga bandaki ta watso ruwa ta dauro alwala ta fito
ta murza mai a jikinta sannan ta kawo jallabiyar baka ta saka ta nade kallabin rigar a kanta sannan ta yi sallarta ta daga hannuwanta ta soma tana godiya ga Allah da Ya muna mata wannan ranar, Dr. Mariya ta shigo ta kawo
mata abinci ta juya ta fita, Saude ta shafa addu ar ta mike ta nufi inda kulolin abincin suke ta bubbude, tuwon shinkafa ne da miyar alayyahu ta ji naman kasuwa sai gasasshen kifi da kayan lambu wanda ya ji curry da kayan kamshi, sannan kunun aya cikin jug wanda ya ji kwakwa da dabino da madarar gari.
Saude ta zauna kasa tana tsatstsakurar abincin ba wani da yawa ta ci ba ta ajiye ta sha kunun aya sosai, sannan ta dauki magungunan da ta ga an ajiye mata ta sha, ta mike ta‘nufi kan gadon ta kwanta.
Wani bacci mai nauyi ya dauke ta ba ita ta farka ba sai gab da maguriba ta mike ta nufi bandaki ta dauro alwala ta fito ta yi sallah,‘ tana nan zaune Dr. Mariya ‘ ta shigo da sallamarta, tana sanye da wasu riga da siket na
wata atamfa super wax mai kyan gaske
Ta raBa saman gadon ta zauna tana jiran Saude ta kammala Saude ta shafa addu’ar ta waiwayo tana gaishe da Doctor.
Cikin fara’a ta amsa tare da fadar,
“Sannunki da qoqari, ai na dauka kina nan kina bacci, kin san marar lafiya bai san motsa jikinsa saukinki ma ba ki da Kan-jiki”.
‘ Saude ta dan yi murmushi tana kallon inda a ka yi mata dressing din ciwonta".
Dr. Mariya ta ce, “Da ma ina so mu yi° magana ne shi ya sa na bari ki huha ki dan samu natsuwa Saudat zan ba ki tarihina gabadaya ta yadda zaki cire qullatata a zuciyarki, da farko 'dai ni . ‘yar asalin Dandagoro ce mahaifina da mahaifiyata a can suka haifeni ni da yayana, kuma a ciki muka girma sana’ar mahaifinmu ita ce Kira, ana ce masa Lawai maqeri mahaifiyata kuma sunanta Badiyya, ita kuma tana sana’ar kitso da saka, asalin mahaifiyata bafulatana ce kuma gabadaya ita muka biyo.
Tunda na tashi ina qarama ta na iya saKa " harna fara girma mahaifina ya sani a makarantar boko a lokacin ina. da wana Yaya Sani sai ni sai turamu Yayana ya yi
karamin bokonsa‘ daganan ya tafi Sakandiri har zuwa Polytechnic inda ya yi N C. E dinsa, amma bai samu aiki ba a lokacin duk da unguwarmu yaya Sani ne kawai wayayye
, don shi me ya fara wucewa. gaba da sakandire.
Ina firamare aji bakwai, lokacin har aji . bakwai ake yi, watarana na hadu da mahaifinki Bala, a lokacin ina da shekaru sha uku, shi kuma a ‘ lokacin yana, saurayi don” bai wuce shekaru asirin ba, na hadu da Bala yazo Yaya . Sani' ya yi masa wani lissafin kudi ya buga masa da calculator. Suna zaune saman dakalin. Qofar gida suna magana, ni kuma na dawo daga makarantar allo da yamma na gifta su na gaishe su zan wuce Yaya Sani ya kira ni na dawo na durkusa a gabansu’, “Ga ni” , Ya ce, “Je ki kawo mana ruwan alwala”, ‘ ‘ na amsa da, “To” sannan na tafi cikin gidan na ajiye allona na samu Umma a zaune akan tabarmar kaba tana yi wa wata mata kitso ’ ' na gaishe da matar sannan na wuce bakin randa na zuba‘ musu ruwan a butoci na fito na
kai musu, na dawo gida na ci gaba da ‘sanwar tuwon da Umma‘ ta. dora,‘ban san wainar da
aka toya ba a waje tsakanin Yaya Sani da Bala ba kwatsam washegari Umma ta aike ni kai kudin daShi nan bayan gidanmu, na shiga gidan kafin in fito yaro ya shigo wai ana kiran ‘ Mariya. Gabana ya fadi, don nadai san ko sauraren Samari ban fara ba,kamar' kar na fita matar gidan tacemin,“kije kiga ko waye ki ka sani k0 yayanki ne?”
Jin hakan da ta fada ya sa na samu kwarin gwiwar fita, a rakube na same shi jikin bango ya harde hannuwansa a Kirji yana ta faman mazurai. Ganin Bala mamaki ya kama ni, ni dai na san ba haduwa muké ba, duk da. kuwa yana dan unguWannu don bama ruwana da shiga shirgin maza.
” Na dan tsaya nesa da shi na gaisheshi, ya washe baki yana amsawa kamar wanda aka , yi wa wata kyauta, nace, “Ga ni”
Kallona ya yi sosai kafin ya ce, "Nasan zakiyi mamakin kiran danayi miki ko?” ”
Ni dai kaina na kasa, Jira kawai naké in ji yace, ga inda zai aike ni Shikuma batare da ya tsaya sauraran amsata ba ya ci gaba da cewa ‘ .
“Ba komai bane ya 'sa na kira k8ba , ,Mariya wallahi Sai don na bude miki abin da ke cikin zuciya saboda na ga barinsa a qirjina bai ,da wani amfani Ni dai Mariya ina dawainiya da sonki a zuciyata ba wai yanzu ba ‘wallahi tunda dadewa amma Allah bai Sa na taBa fada ‘wa kowa ba sai jiya na sanar da‘yayanki Sani, amma sai ya nuna mini gaskiya in yi haquri don kuwa ke karatu za ki har gaba da sakandiri za ki wuce, don burinsu sai kin zama likita, ba yadda ban yi da shi ba amna ya Ki daga qarshe ma har dan saBani muka samu da shi a kanki. Na haqura na tafi gida, amma wallahi Mariya ban iya samun bacci ba a daren jiya, , idan na rufe idanuna hotonki nake gani yana yi min gizo, duk yadda naso in rarrashi zuciyata abin ya

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login