Showing 63001 words to 66000 words out of 103547 words
faskara, don haka na yanke shawarar~ ’ zuwa wurinki da qoqon barana don Allah Mariya ki taimaka ki soni koda da kwayar zarra ne” Ni a lokacin sai na rinka jinSa tamkar ; : mafarki don tunda nake babu saurayin da ya taba tara ta da irin wannan maganar sai shi,
don haka ban wani dauki abin da muhimmanci ba na dubeshi kafin in ce
“Ka yi haquri, kamar yadda Yaya Sani ya fada maka ni ba aure zan yi ba, karatu zan yi, na gode, sai anjima”.
Ina ji yana ta faman kirana, ama ban tsaya ba don ni a tsorona kada wani dan gidanmu ya wuce ya gan ni.
Abu kamar wasa Karamar magana ta zama babba, don kuwa duk inda za ni sai na ga Bala, k0 makarantar boko' 'ko ta allo, k0 kasuwa za ni ke kamar ana fada masa ga ni nan zan fita, kuma in dai siyayya zan yi ko ta nawa ce shi zai biya kudin, duk wulakancin da zan masa ba ya ji, ya zame min kamar wani kaska na rasa yadda zan yi da shi, tun ina wulakanta shi, har ta kai ga na gaji na sa masa ido, daga baya ma sai ya koma ba ni tausayi saboda yadda ya ke shan wulaqanci amma bai taBa bata ransa ba, idan aka aike ni kasuwa. Siyayya kuwa k0 ta kai ta nawa shi zai zaro :
Kudi ya biya ya yi tafiyarsa ya bar ni in rasa yadda zan yi da kudin a hannuna haka na dinga Boye su a cikin buhun kayana don tsoron kar
‘ wani ya gani in shiga uku, wasa-wasa na tara 'kudi masu tarin yawa. ~ ‘ Ahaka ahaka Saudat har saida Bala ya sarke min Zuciya na manta da duk wulakancin ‘ da nake masa ta kai ta kawo ma in ban ganshi ba, ko bacci ba na iya yi a dantsakanin mu fa ‘ soyayya mai qarfi ta shiga tsakaninmu, amma babu wanda ya sani a gidanmu. ‘ Idan Bala yana son mu hadu sai ya ' rubuta ‘yar takarda ya soke a kyauren gidanmu da ma na sani kullum sai na duba kyauren don in ga k0 ya soke sakonsa, idan ya sanya in dauko in ruga in Boye in karanta, bai dai wuce. sakon mu hadu Wuri kaza, karfe kaza, kuma duk abin da nake in dai ya ce yana jira wuri kaza sai nace k0 ban da lafiya ne kuwa. ' A haka watarana . Bala ya soke . takardarsa da yamma na dawo daga kai nika na“ , gani na duba, yana son mu hadu bayan gidanmu bayan sallar magaruba, dadi ya kama. ni don da ma mun kwana biyu ba mu hadu ba, don haka ina shiga gida na sauke wa Umma nikan a tsakar gida na suri bokiti na nufi bakin rijiya .zan jawo ruwa, .Ummana :dake zaune
saman kujera‘ yar‘ tsugunne ta dube ni yadda nake ta rawar jiki kafin tace “Wai saurin me ki ke haka ne Mariya? Me zakiyi da wannan ruwan? ’ , ' “Wanka” Na bata amSa a takaice ‘ Umma ta ce, “Wanka kuma bacin wanda kika yi da rana?” na amsa Ba tare da na kalle ta ba nace zan Kara ne Umma, Maman su Bilkice tace in shirya in raka ta dubiya, Kaninta bai da lafia” Umma ta ce “Dubiyar ce kuma Mariya har sai an yi mata wani ado sai ka ce wanda zashi gidan biki?” ‘ “Yo Umma a‘i kamar gidan bikin ne ldan kinfa san gidansu gidan‘ yan gayu ne”. INa maganar tare da kinkimar bokitin ruwana na nufi bayi ba tare da na tsaya na saurari abin da za ta ce ba, Umma taja numfashi ta ci gaba da abin da ta ke. “ Kafin a yi sallar magriba na gama, Shiryawa tsaf cikin sabon yadin bambalasta wanda aka yi min dan doguwar riga mai ' .hade da zani sun sha aikin surfani, yadin mai
kalar jinin kare, duk daba wata kwalliya aka" iya ba a lokacin amma na yi kyau sosai
Dan daman can ‘kyakkyawa ce, fara“ ce tas; ‘yar siririya kamarke Saudat,saidai ninafiki manyan idanuwa, ga gashina har baya baki sidik ya yi min saje a gewayen fuska, kina kallona kin ga kyakkyawar bafulatana ‘ , Na zaro gyalena na flto tsakar gida a
lokacin Ummana tana kicin tana tuqin tuwo na leka kicin din tare da fadar.
‘ “Umma na tafi,sai na dawo” . ta amsa Itama a lokacin ma hayaki ya ishe ta,don k0
waigowa ba ta yi ba ta ce min, “A dawo lafiya,
kada ai dare”.
Na amsa mata da, “To Umma” .
. Na nufi hanyar fita, qanwa ta Zuwaira ta taso za ta biyo ni na haurar da ita ina. ji tana kuka nayi gaba abina, don a lokacin Wasu » masallatan har sun gama sallah.
: Ina fita nayi karo da Yaya Sani ya dawo daga kasuwa, ya watsa min harara, “Gidan uban wa zaki?”
‘ . . Na dabarbarce ina in ’ina, sannan na samu na fada masa, “Raki.. .ya zanayi, kuma ‘Ummama tasani"
,, "‘ Yayi tsaki ba tare daya sake kulaniba “ ya yi cikin gida abinsa.
[1/30, 9:54 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼♂@lh@ji🙆🏼♂: [9:59PM, 1/30/2017] A Dboy: *YAR TALLA*
BOOK 3
*CHAPTER 25*
Na saki qafa don kar ya fito ma ya ’hango ni na san halinsa sarai, bai da kirki don bacin yan kirkin na kansa na san da da bugu zai maida ni gida, na saki qafa na zagayo ta' bayan gidanmu tun daga nesa na hango Bala zaune saman wani dan kututturen ice yana jirana Na karaso da sallamata tare da' gaisha shi, ya mike tsaye yana amsa min da fara’a a ‘fuskarsa ya bani wurin da' yake na zauna shi kuma ya tsaya daga tsaye yana fadar. '
“Sannunki da zuwa mai kyau, da ma ’ .zuciyata ta ba ni kina hanya”. ' * “ Na yi murmushi kawai ba tare dana
tanka masa ba * Bala ya ‘ce, “A gaskiya Mariya abin da
yasa na ce kizi nan saboda mu tattauna wata magana ne, kin ga dai kun yi interview, result
kawai ku ke jira yanzu kin kammala firamare dinki ya kamata a zo a tsayar da maganar“ auremnu haka nan, ni dai na fara gajiya, , mahaifina har yamin maganar auren da kansa, : . tunda bakin gwargwado dai kin san inada sana,a kuma zan iya, rike ki da ita ke bama keba,
ko' mata. hudu zan iya riKeWa don haka ban ga amfanin zaman haka ba, k0 ya kika ce?" . Na dan yi jim ina dan nazari, ni kaina zan so auren fiye da zama haka duk da ban san me ye qunshe a cikin auren ba, amma ina
sonsa musamman da masoyina Bala. Na dago a hankali ba tare dana bari
mun yi ido hudu ba na soma magana.
“To amma ai ka san Yaya Sani ya fada maka karatu zan yi, kuma duka gidanmu so suke ma idan na gama sakandire in wuce makarantar asibiti"
Bala ya katse ni ta hanyar fadar, “Assha! Asshaii Haba Mariya da hankalinki' yanzu saiki barikinaji kinagani aturaki wani karatu to idan kin gama karatun sai wa ya aure ki? Kin san dai yadda masu karatun nan ke tsufa ba sa samun masu aurensu sai tsaffin, Alhazawa. Gaskiya kiyi tunani da kyau Mariya,don yadda ki keda kyan nan da siga , ‘ kyanki aure kawai, amma Wallahi idan aka tura ki karatu an kashe ki, kuma an wargaza " miki rayuwa”.
‘ Ni dai na yi sukuti ina saurarensa, bayaninsa na shiga ta ta ko’ ina, ban ankara ba
sai dai na ji saukar kara a jikina, na zabura na zabga ihu. Yaya Sani ya cukwikwuyo gyale na
kamar wata Akuya ya shiga zabga tada karan a
hannunsa ina ihu har sai da ya karkarye a jikina. Bala ya‘ rud‘e ya shiga riqe shi yana magiya, Yaya Sani ya dago a fusace, “Sakar ni mutumin banza idan ka sake rike ni wallahi za ka, ga abin da zai faru, munafuki, maciyi amana, yanzu ashe har za ka iya taimaka wa wurin lalata tarbiyyar qanwata? To Allah ya isa amma ka sani babu ni babu kai har abada, kuma wallahi idan na Kara ganinka da ita hukuma ce za ta raba mu. Ke kuma mu je gidan zakici ubanki yau”.
Ya ja ni kamar wata Akuya yana duka tun saman hanya har muka iso gida.
Ya wurga ni gaban Umma, ta zabura ta rike ni da hanzarinta tana fadar, “Me ye haka : kai kuma ka keyi, ba ka da hankali ne?" . ’
Yaya Sani ya soma magana cikin tsananin Bacin rai, “Umma yarinyar nan Sai kinsa mata ido, lalacewa za ta yi wallahi, Umma yanzu wai har ta san ta shirya taje su hadu dasaurayi ta debi gyale ta same shi don tana‘ yar iskar yarinya?"
_ " Umma ta dauki sallallami cike da firgici tace “Ana ka gansu dan nan?” '
‘ ’“a bayan gida na gansu ita da Bala dan gidan Malam Nata’ala mai tumaki, tana zaune suna zace”
. “Yau na shiga uku ni Binta, yanzu abin ‘_fada ki ke son kija mana ne a gari Mariya? Ina ‘ganinki sumu-sumu ashe kin iya munafurci . to ?’ Tasa kafata haureni, “Matsakibani. wuri munafuka. Da kayi mata dukan mutuwa inji uban da ya aike ta wurinsa, kuma Babanku na dawowa kamar bisa kunnensa akayi, yan sai na ga ta iskanci” .
‘ Haka Umma ta sa Yaya Sani ya yi min jan bugu kamar zai kashe ni, tana kallo ta sa masa ido, sai dai saukina guda ba a fada wa Babe ba, don nasan idan shi ne wataqila sai ya nakasani,amma dukda haka na bugu. ga shi Umma ta. juya. ' min baya, ba ruwanta dani, bata kula ni, bata tankamin dan idan natanka matama bata‘
Amsawa, ta cire sanya ni aiki, hatta girki ta daina sani nayi ke na shiga tashin hankali, , fushin Umma ta ya qara jefani cikin damuwa
amma dukda haka banmantada Balaba a zuciyata har, kullum burina in fita . in ganshi, amma abin ya ci tura, an daina aikena,. ’makarantar allon ma ba a barina zuwa, ga shi makarantar bokon bahu‘ muna jiran sakamako
‘Kwatsam ranar asabar ina kwance a daki da yamma, Ummana ta dago labule, “Ke tashi ki shirya ki tafi makarantar allo”.
‘ Tana rufe bakinta ta saki labulen ta_ yi
gaba abinta.
Wani dadi ya kama ni, na buga wani uban tsalle ‘yau zan ga masoyina, na nufi Kuryar daki na dauko hijabina da alkur’ani mai ‘girma, na zura takalmina na yi gaba “‘Amma abin haushin ban ga Bala ba wurin daWowa ma har ta qofar gidansu na biyo, amma ban ganshi ba Haka na dawo gida raina a Bace, ina ‘ “ dawowa kuma na iske wani bakin labari, Yaya Sani ya sama min makarantar kwana. Hankalina ya yi maSifar tashi don kuwa yanzu na cire zuciyata da karatu, aura kawai nake so, na shige daki kamar maitakaba inaji anata lissafin abubuwan da za a siya min, ni dai jinsu
kawai nake,amma nasan saidai akai waniba dai Mariya ba.
Da daddare na kasa haquri ji nake kamar zuciyata za ta tarwatse, da kyar na samu bacci ya dauke ni. Abin haushi kuma ba mu daina haduwa da Bala ba, sai dai abu kamar wasa na ga an fara yi min siye-siye katan din indomie, kwalayen madam, gwangwanayen ldii, comtlex, busasshen dambu da na fura da garin
‘ rogo, tuwon ruwa da sauran dai abincin ‘Ni dai kallonsu kawai nake ban san abin da ake ciki ba, sai da na ji rade-rade cikin satin nan za a kai ni makaranta, ai k0 kamar na taka rawar hauka don ranar da kaina na shirya da daddare najé har gidan su Bala na aika yaro ya kira min shi, na yi sa’a kuwa yana nan. Ya fito da zumudinsa yana fadar, “Da ‘ ma yanzu nake shirin na fito duk ma yadda za a yi mu hadu da ké mu hadu". , . Na gyara tsayuwata ina kallonsa, murya ' ta a raunane na soma magana,‘ “Ka san ina
cikin matsala Yaya Sani makaranta zai kai ni bodin wallahi ’ '
Ya tsaya da sauri yana kallona hankalinsa a tashe kafin ya ce kuma Mariya, ke kuma sai ki ka ce yaya?"
Na ce, “Ni dai wallahi ban so, amma ban kai ga fada wa kowa ba”.
Bala ya dan ja numfashi kafin ya ce “Ai wannan wauta ce Mariya, inda kina son kasancewarmu a tare sai ki cire kunya da tsoro ki'flto fili ki fada abin da ke zuciyarki, na san dai babu mai izawa a sa ki wannan karatun sai Yaya Sani duk shi ne ke da abin, kuma shi ke iza Umma, amma nasan ai Baba ba zaiqi goya miki baya ba”.
Na dan yi jim ina saurarensa, ina juya maganganunsa a zuciyata, can ba hango Yaya Sani da wasu abokansa sun nufo inda muke. _ Tun kafin na ida tunanin abin yi na ga Lawwali abokin Yaya Sani ya kwaso da gudu da ya kafa ya kwashe Bala ya fadi qasa.
Ai ban san iokacin da na kwasa da gudu ba, Yaya Sani ya kwaso ya biyo ni muka yi gida, ina shiga soro na yi karo da Baba yana ' shirin fitowa, ya rirrike ni yana fadar, “Ku tsaya, kyale ta kar ka sake ka buge ta, ai shi kangararren yaro duka ba ya shiryar da shi sai
dai addu’a, inda kun sanar da ni wannan labarin tun wuri da ba a kai haka ba, kyale ta kawai. Wuce ki shiga ciki”.
Ya sake ni na shige gida.
Kai tsaye na wuce zan shiga dakin Ummata ta tsaida ni, “Tsaya kar ki sake ki shigar min daki, ki zauna nan don ban hada shirgina da karyar maza zauna nan”.
Sunan da Umma ta kira ni da shi yafi komai tarwatsa min zuciya, na ja na tsaya jikin bango ina mazurai.
Yaya Sani ya shigo yana kallona, kallo mai cike da tsana, ya ja tsaki.
‘ “Kin dai ji haushi, sakarya jakkar yarinya wadda ba ta san abin da ta ke ba. Wallahi ji nake na tsane ki, kuma idan har ba ki sauya hali ba, ba za mu taBa shiryawa ba, kin kuma daura aure da wahala wallahi”.
Umma ta ja tsaki kafin ta ce, “Hmmn! In dai maza ne ai gata nan ga su nan, wallahi in dai a karatun maza ne yarinya za su biya miki iya yadda kanki zai iya dauka, kar ka so ka tona zuciya ta kaji yadda ta ke zogi da har ban son in waiwayo in kalli yarinyar nan, duk duk ki rasa ma yaron da zai hure miki kunne sai
Bala? Da ma can ni yaron bai kwanta min ba, na tsane shi ban sonshi wallahi".
Yaya Sani yace, “Al shi ke nan yau sai ya gane kurensa, don Lawwali a yau sai ya nakasa shi”.
Yana fadar nakasa na ji tamkar ya soka min mashi a Kahon zuciya, ai ban san lokacin
da na fasa wani ihu ba na durqushe a gurin na hau birgima. Ran Yaya Sani ya yi masifar Baci ya yo kaina da itacensa ya fara dukana.
Wallahi Saudat ban san lokacin da bakina ya bude na hau surfa masa zagi ba, kira nake,’ “Allah ya isa wallahi ban yafe ba, ai da ma na san ba ka qaunata, kuma karatun ban yi, tattara kayana zan yi wallahi in bi shi”.
Mamaki da takaici su suka hadu suka sa Yaya Sani ya tsaya da dukana yana kallona inda Umma ta hau sallallami harda kukanta tana fadar, “Yanzu Mariya saboda wannan dan iskan ki ke bude baki kina zagin dan uwanki haka? Yau na shiga uku ni Binta, Mariya idan ba ki kwashe kayanki kin bi yaron an ba kin raina Allah da ya halicce ki, ki tafi kibi shi, ni dai in har ina raye baki isa ki auri yaron nan
Idan kikaga kin aureshi saidai in bana numfashi,mutuka yarinya” ., ’
' Saudat abu wasa-wasa har dare ya tsala sosai sannan mahaifina ya dawo,naji yana fadin wa Umma wai wurin mahaifin Bala ya je ya samu bayanan.
, Umma ta ce, “To idan ka same shi me zaka ce masa Malam.”
Ya ce, ,“Babu ruwanki, na riga na gama yanke hukunci, kibar ni kawai”.
Umma ta ce “To barka Malam”.
Haushi ya kama ni ban ji hukuncin da Baba ya yanke ba, amma na kwana da shirin ,gari na wayewa zan tattara kayana in bar gidan, a wautata a amma da hauka irin ta zuciyar data kamu daso.
Kiran sallar farko Saudat a kan kunena akayishi ba wani bacci na yi ba,gyangyadi ne kawai, na lallaBa na tashi na d'auko biro da takarda na rubuta wa Bala wasika zan tafi garin “ Kano ta dabo tumbin giwa yaro k0 da me ka zo an fika zan sauka tasha in zauna in jira shi na gama rubutun na’ lunke takarda na lallaBa na shiga. dakin Umma» can _ cikin; quryarta don a lokacin ita tana dakin Baba, na
dauko buhun kayana na Ciro kudin da Bala ke ba ni na Kirga naira dubu biyar ce wadda a lokacin ta kai darajar dubu hamsin a yanzu. Dadi ya kashe ni na dauki hijabina na saka na rage kayan cikin buhuna don in iya dauka, sannan na kinkima na fito, babu wanda ya gan ni har zauren gidan, dana sararaf na
.zare na budr na fice abina. Garin tsit sai mutane jefi-jefi, sauqin abin ma hasken asuba ya fara na kwasa da qafa har bakin titi, na tsaida mashin ledis na hau na tafi tasha da ni na yi sa’a kuwa na samu mota ta kusa cika, sai dai abin takaici, ina qokarin shiga motar na ji ana kwallo min kira, na waigo in ga mai kiran nawa, Kawu Ummaru ne shaf na manta da yana zuwa tasha saida Kuli-kuli.
Na ji tamkar in zunduma da gudu ya Karaso yana fadar, “Ina. zuwa_ da wannan kinkimeman buhun haka na ga kina qoqarin shiga motar Kano?”
‘ Kin san marar gaskiya k0 cikin ruwa sai . ya yi gumi yake ga shi dama ni can ba ma'abociyar
Karya bace ban ma iya ta ba, nayi tsuru-tsuru ina muzurai.
Sai naga ya kamo hannuna yana fadar, “Wuce