Showing 51001 words to 54000 words out of 103547 words
Zuwa ya dawo anan gaba don haka cikin raunanniyar muryana ta soma magana.
“Yallabai ni ba sonka ne ba na yi ba, asali ma kai abun alfahari ne ga duk macen da ta same ka ballantana makaskanciya mai tsananin rauni. YallaBai zuciyata ce cike, da fargabar abin da zai iya zuwa ya dawo, wallahi ina tsoron tashin hankali ban son abin da zai sanya rayuwa ta damuwa ko ya yake.’
Cikin farin ciki Dr. ya ce, ‘Haba Saudat ai matukar ina “ciki Kin gama zubar da hawayenki a kan damuwa, sai
dai k0 hawayen soyayya wanda farin ciki ke sawa a ‘ zubar dasu saboda shauki irin na soyayya.’
Kuka da dariya suka kwacewa Saude Iokaci guda, ‘tasa tafin hannu ta rufe fuskarta, Dr. ya yi murmushi . tare da Juyawa ya yi wa motar key yasa mota hanya suka cigaba da tafiya
» tare da waninsu ya sake magana ba.
Horn din da ta ji yana wa maigadi shi ya tabbatar ~ mata sun iso Cinna hancin motar cikin gate din gidan ya yi daidai da bugawar zuciyar Sanue dif zuciyar ta ** tsaya da aiki a take.
Ina ga k0 Asma ce za ta fito, Saude ta ji muryar Dr na fada wanda ba ta ma fahimtar me yake fada ba saboda tsabar rudu da kaduwa da take ciki.
Saude ta runtse idanuwanta ganin Asma ta nufo motar tasu, Dr ya ji tamkar ya juya sai dai babu dama don kuwa tuni masu gadi sun riga sun rufe gate kuma k0 kafin su sake budewa ya tabbatar ta iso.
. Don haka ya yi dabarar bude motar ba tare da ya gyara fakin ba ya fito yasa key ya kulle motar ya nufe ta tun kafin ta Karaso yana fadar
“Saukar yaushe My dear.”
,, Turus ya ja ya tsaya saboda k0 kallon shi ba ta yiba ta wuce shi ta nufi wurin motar, gaban Dr ya yi wata masifaffiyar faduwa ba wai don yana tsoron Asma ba, a a saboda Saudat don ya lura ta yi matukar ’ 'firgita da ganin Asmar matuqa don haka Jikinsa a ‘ sanyaye yabi bayan ta
Tana qarasawa gaban motar ta ja ta tsaya ta miqawa Dr. hannu, ‘Bani key da motar." Ta fada cike da gadara.
Dr. ya ja ya tsaya a gabanta cikin nuna halin ko’in kula ya ce, ‘Ba zan bayar ba kina da ajiya a ciki ne?”
Cike da mamaki Asma ke kallonsa kafin ta iya bude baki ta ce, ‘ba zaka bayar ba ni ka ke fadawa haka Ahmad? Hmmm! Da kyau ba zan yi mamaki ba tunda ka dauki ‘yar iska kun flta kun gama yawan iskancinku kun dawo ai dole za ka sawa mota key tunda Allah ya toni asirinku. .
Amma ka sani daga rana irin ta yau ka gama marmarin fita da kowace. karuwa don sai na sa ka yi nadamar da baza ta taBa qarewa ba wallahi, dan ba irin Asma ake wa irin wannan tozarcin da wulakantar ' ba a cikin gidanta, mayaudari, munafuki kawai.’ Tana maganar tana kwance dankwalin kanta.
Ta hau daura damara a qugunta tamkar mai shirin shiga filin dambe ta durkusa ta kwashi duwarwatsun da aka baza a harabar gidan ta hau jefa su a gilas din motar tana fadar.
“Wallahi yau sai dai k0 ni ko ke a gidan nan ‘yar iska wallahi sai na yi ajalin ki, karuwar banza."
Dr. da ke tsaye ya yi saurin rike ta yana fadar, ‘Wai me ye haka Asma kina da hankali kuwa ki ke abu kamar ba. educated ba, wannan ai hauka ne ki ke da
RaShin hankali a gaban mutanen da suke a qarkashin ki wannan ai kanki kike jawa abin fadi a duniya.’
Asma ta kwace daga riwon da ya yi mata tana haki ta ce ‘Kai da alla ni rufe min ba ki kai har wani mutunci ne ka 'sani bacin wanda ka zubarwa kanka a bainar jama’a, ai idan akwai wani sakarai marar hankali to bayan ka yake, mutumin da ya maida ‘yan aikin gidansa abokan cin garinsa, ai sai yanzu na fahimci abin da ke korar duk ‘yan aikin da na kawo maka, kuma wallahi ba zan taBa rufa maka asiri bu sai duniya ta san abin da ka aikata, kuma yarinyar nan yau sai na halaka ta.
Bai ankara ba ta rarumi wata qatuwar adda wadda ake aske fulawowi da ita, ta sauke madubin motar, wanda ya yi daidai ta fasa qara Saude wadda ke zaune a gaban motar.
Dr. ya yi saurin rike Asma yana fadar, ‘Wai ke wace inn mahaukaciya ce wallahi za ki jawa kan ki aikin dana sani, dan na rantse da Allah idan ki ka kashe yarinyar mutane wallahi sai na yi shari’a da ke
Da sauri ta kalle shi bakinta a sake cikin sarkewar murya take fadar, ‘Za kai shari’a da ni Ahmad akan karuwar? Lallai kam da na nuna maka kai Karamin dan bariki ne. To bari in kashe ta sai kai qarar tawa."
Dr. ya qara rike ta gam kafin ya ce “Asma ya kamata ki shiga hankalin kifa dan kin sani sarai ba zan lamunci wannan haukan naki ba, don ban ga abin da a kai ba, wanda zai sanya ki wannan jakancin ba idan mun fita da Saudat sai me ‘yar aikina ce ina da
Right din fita da ita mu yi siyayyar abin da ake buqata. dan me za ki nemi tarwatsa mini tunani haka kawai?"
Asma ta girgiza kai, ‘Lallai Ahmad ka cika dan akuya yanzu a kan karuwar ne ka ke kirana da jaka, lallai kam ana yi, kun tafi siyayya ne shi yasa ku ka . tafi ku biyu babu k0 da direba, kuma ta zauna a gaban
° mota. Kai gaskiya ne ai na ga hakan, amma sai dai abin daka manta k0 ranar da ka fara ganina a duniya da hakorana talatin ka gan ni cur, ballantana ka maida ni
. Karamar yarinya, wadda ba ta san abin da take ba.
Kuma wallahi tallahi na rantse maka da Allah sai na yi ajalin ‘yar iskar yarinyar nan jaka sakarya
daqikiya ballagaza wadda iyayenta suka sadaukar da ita saboda abun duniya, wallahi daga yau ta gama karuwanci da kowa.”
Dr. ya cc, ‘Hmmm! Asma kenan kina ba ni mamaki yanzu har iyayenta sun miki laifi dan sun Sadaukar da ‘yarsu ta zo ta yi miki abin da ki ka gaza Min a rayuwar auren ki ashe har sun miki laifi?"
ldanuwanta a warwaje ta soma fadin, ‘Ban gane ba? Dama na dauke ta aiki ne don ta maye gurbina?”
Cikin rashin damuwa ya ce “Yes k0 kin dauka ‘abinci shi ne kawai matsalata ni ba mutum bane? Dole
kwai wani abun da nake buqata bayan wannan, dole ‘
lna buqatar kulawa ta mace, sai dai bata gurbatacciyar hanya wadda take haramun ba, don sanin kanki ne ni Ba mazinaci ba ne shi ya‘sa na yanke hukuncin auran Saudat don na ji dadin maye gaba dayan gurbin '
naki wanda sabgogin yau da kallum suka saki ka "watsar.”
Cikin tsananin firgita da razana Asma ta kwace daga rikon da ya yi mata tana fadar, ‘Kutumar ubannan Kai karya ka ke wallahi tallahi karya ka ke Ahmad ba ka isa ba na rantse maka da Allah babu ‘yar matsiyatan da ta isa ta shigo cikin gidan nan batare da na nuna mata bakin rijiya ba wajen wasan makaho ba ne.’
Dr. Ahmad ya ce Ai ko sai dai kada a Kara; domin zuciyar Ahmad ta riga ta yi nisan da mai rai ba zai gane iya adadin gudunta ba, kuma ina mai tabbatar miki k0 da malaman da ke Barno da Nijar. malamanki ne ba ki isa ki hana wannan lamarin ba. Da fatan kin gane Asma ta hau ja da baya da baya tana fadar ‘Ni. .ni Ahmad wallahi qaryarka ta sha karya wallahi ba ka isa , ba Ta durkusa tana kokarin daukar addar daya yar a ‘ ‘qasa, wadda ya kwace daga hannunta.
‘ Dr ya kalle ta yana fadar, ‘Wallahi idan ki ka matsa kusa da motar can a bakin auren ki ’
Yaja wani dogon tsaki ya juya ya yi gaba ya bar ta ' ta fasa wani gunjin kuka ta durkushe a gun Dr ya fada motarsa sai dai ganin halin da Saude ,ke ciki ya daga masa hankali kuma ya ga madifar" dauriyarta don gilas din motar da ya fashe sai da ya yanki goshinta, jini ya zuba sosai duk ya bata mata fuska, hankalin sa ya tashi ya tayar da‘ motar ya fice
daga gidan ba tare daya sake kallon inda asma take
ba, ya nufi asibiti da ita. Suna zuwa kuwa aka karbe ta akai mata dresin
din ciwon aka rubuta mata magunguna, sannan suka baro asibitin. A cikinsu babu mai magana kowa da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Can Dr. ya dan waigo
ya kalli Saudat sannan ya maida kallonsa a kan titi cikin sanyayyar muryarsa ya ce.
“Don Allah don Annabi ki yi haquri Saudat kada dan wannan abun ya daga miki hankali k0 kadan, ni daina ce ina son ki kuma ni zan zauna da ke ba Asma ba. To insha Allahu na yi miki alqawarin farin ciki da jin dadin rayuwa a duk inda suke zan nemo miki su, fatana ki’ rayu cikin farin ciki da walwala, kar ma abin datayi dinnnan yadameki kinji?"
‘ Kai kawai ta daga masa alamar eh, amma qasan zuciyarta cike yake da tsabar rudani da tsoro. Dr. ya ~ tsaya ‘Gidan Abinci’ ya yi take away sannan ya dawo suka wuce. Kai tsaye daki ya kama a wani hadaddan hotel mai tsadar gaske kwana daya, ya ba ta makullin dakin mai lamba 12, sannan ya ajiye mata ledar take away din ya gwargwada mata komai a cikin dakin Wanda yake da qaton falo da bedroom sai bandaki da dan wurin hutawa.
Sannan ya dube ta a nutse, “Dafatan dai babu wata matsala?”
Saude da kc tsaye tana kallon shi ta sunkuyar dakai qasa muryarta a sanyaye ta ce, “Babu.”
Dr. ya ce ‘Okey zan wuce mu jeki rufe dakin ki tabbatar kin kulle sosai sai Zuwa da safe,,insha Allahu zan dawo sai mu wuce Katsinan a tare kin ji ko?” "
, Saude ta dago da idanuwanta wadanda suka ciko da kwalla ta daga masa kai, Dr. ya dan tsura mata idanuwa jikinsa a sanyaye ya ce ‘Saudat hawaye nake gani a idanuaki me ye kuma?”
Saude ta sadda idanuwanta tana wasa da yatsun hannunta ba tare da ta ce uffan ba Dr Ahmad ya Kara matsowa daf da ita cikin sanyayyar muryar shi ya kira sunanta
“Saudat me yasa ki ke san tayar min da hankali ne?
'Me yasa ba kya son ganin nutsuwa ta? Kinfi son ki
ganni a firgice ne, iye Saudat?” Kai kawai ta girgiza masa ba tare da ta kalle shi ba Ya ce, ‘To meye? Ba kya san in tafl ne in zauna tare
. da ke. " Da sauri ta daga masa kai don kuwa abin dake
zuciyarta kenan, don gani take tamkar idan ya tafi ba zata sake ganinsa ba.
Ya yi murmushi wanda ya bayyanar da haqoransa kana ya ce “Ki sha kurumin ki My dear insha Allahu babu abindazai faru kedai kiyanida addua kawai kinji?” . ‘
A hankali ta daga masa kai ya ce ‘Yauwa ko ke fa, ‘ kikwanta ki hutakinji, kiyibarci mai dadi saida safe. ”Ya ja mata hanci yana dariya sannan ya fice.
Saude t maida qofar ta rufe ta koma ta jingina da ; kyauren idanuwanta a lumshe zuciyarta na bijiro mata ’ d wata irin matsananciyar soyayyar Dr. Ahmad wanda take jin a yanzu tamkar ta bishi ta zauna a tare da shi, farin cikinta da fargabarta ba zasu musaltu ba. Farin cikinta dai shi ne ta samu namiji daya tamkar da goma ajin duk wata isasshiyar mace. Fargabarta kuwa itace. Shin kuwa zai iya auren ta don ita ta san ya riga yafi qarfinta ta kowace fuska, to idan ma ya ' aureta ta ya za ta yi da matarsa Asma, don yau ta ga. bala,in da: take fada mata.
A hankali ta ja Kafafuwanta ta nufi bedroom din; kai tsaye bandaki ta nufa ta dauro alwala ta fito ta yi sallar isha,i sannan ta tashi ta haye saman“ madaidaicin gadon da ya sha shimflda ta alfarma ta zauna ta jawo take away din da ya ajiye mata ta bude ta ci abin da za ta iya ci saunan ta kwanta, ba dan tana jin barci ba sai dan ta samarwa gangar jikinta hutu
Tunda {a kwanta ba ita ta farka ba sai Karfe shida saura ‘yan mintina, ita kanta ta yi mamakin tsawon lokacin data dauka tana barcin, don haka ta mike ta nufi bandaki ta dauro alwala ta fito ta yi sallah, sannan ta zauna tana lazimi tsawon lokaci sai da ta gaji don kan ta ta mike ta koma ta kwanta zuciyarta ta lula duniyar tunanin gida da irin abin da za ta iya fuskanta a can din. Rayuwarta ta baya a gidan ta dawo mata tare da tunanin masoyinta Hamid, har yau har gobe tana jin son shi a zuciyarta,“saboda shi ne mutum na farko da ta
Tara so a rayuwarta kuma shi ne mutum na farko da ya fara burin taimaka mata
Kwankwasa kofar da ake ne ya sa ta saurin tashi ta taje ta bude qofar, Dr. ya shigo yana sanyé da shigar wani sabon yadi milk colour, mai laushin gaske an yi masa aikin hannu a jikin rigar Yana .sanye da hula sai takalminsa na fata
'idonsa na sanye da siririn farin gilas, gaba daya kamshin turarensa ya mamaye falon.
Saude ta durkusa tana gaishe shi cike" da girmamawa, Dr. ya amsa yana fadar, ‘Daga yin knock sai ki bade kofa ba tare da kin tambayi k0 waye ba baki san nan batel bane? Komai na iya faruwa fa.”
Muryarta a sanyayé ta ce, ‘Ai na san kai ne
Dr. ya ce ya a kai ki ka sani? Ta dan yi jim kafin tace ai ka ce min zaka zo da safe. Ya dan yi wani murmushi kafin ya ce ashe ba ki da mantuwa kinsan in bayan dana manta ban nuna miki yanda za ki yi
kisa a kawo miki break ba da ba zan zo nan ba sai wurin sha biyu da wani abu
Ya ja ya zauna tare da tura mata katuwar jakar da ke hannunsa ya ce duba ki ga kayan nan idan sun miki saikisa yanzu sai mu tafi.’ Saude ta zauna saman * kafet tare da janyo ledar gabanta ta shiga bubbudewa a ~ sanyaye ’
Dogon wando ne baki irin mai kama qafafuwan nan an masa adon pink color sai rigarsa
» Shima ma pink mai adon baki, rigar mai yankakke wanda ake kira da v neck
Rigar mai dongon harnu ce,,,sai wata duguwar riga har qasa itama pink cclour ita ma mai dogon hannu, tana da yankakken gaba sai siririn mayafinta.
~ Ta ajiye kayan ta janyo wani qaton kwali ta bude” takalmi ne a ciki baki da ‘yar qaramar pose irin wadda ake makalawa a hannu, ‘yar qarama, sannan ta Ciro wata ‘yar jaka, saitin kayan shafawa ne a ciki hade da sabulu da turare kayan sun bala’in
Burge ta har cikin ranta, shi kan shi ya fahimci hakan ‘
a idanuwanta, don haka muryar shi a sanyaye ya ce. “Sun yi kyau k0?” Murmushi kawai ta yi ba tare da ta tanka ha, ya
*mike tareda fadar kije ki shirya dame zakikarya ?
Me za,a kawo miki?”
Saude ta sunkuyar da kanta tare da fadar, ‘Komai aka kawo min."
Cikin zolaya ya ce, ‘Ba dai komai ba k0 zaki ci shinkafa da miyar kwadi?”
Da sauri ta kalle shi ido waje, ya yi wani siririn murmushi kafin ya ce ‘Ye’s nan ba abin da ba sa dafawa har miyar dodon kodi.’ Saude ta Bata fuska
tamkar zatayi amai tace ‘Nidai a,a ‘ Ya yi wata dariya irin wadda ba ta taba sanin ya iya ta ba da alama yanda ta yi maganar cikin shagwaba ya. yi masifar barge sa tare da daukar _ hankalinsa, ya matso daf da ita yana kallonta da
ya ce, ‘Dan qara‘ maimaitawa mu ji please. ’
Kunya ta kama ta ta juya da sauri ta yi ciki ta bar shi nan tsaye harde da hannu a qirji yana kallonta
har ta bacewa ganinsa, ya yi wani murmushi tare da
‘lumshc idanuwansa ’
Saude na shiga bedroom din ta fada saman gadon dakin ta rungume filo cike da murna haka kawai ta ji wani irin farin, ciki ya baibaye ta, ta lumshe idanuwanta tana mai son tuno wani abu can
‘ kamar wadda aka tsikara ta zabura ta mike da gudugudunta ta fada bandaki ta watso ruwa a gurguje ta
‘dauro alwala ta fito ta yi nafila raka’a biyu tare da roKon Ubangiji ya kare ta daga sharrin Inna Laure, don tanaji ajikinta wannan karon idan akahanata auren Dr. mutuwa kaWai za ta yi.
Tana gama addu’ o ’inta ta mike ta janyo ‘yar jakar kayan shafawar ta fito da su ta mutsa mai lotion a jikinta, sannan ta shafa hoda ta sa abun
‘ gyaran gira ta gyara girarta, har ta soma sai da ta sa
. maskara ta gyara ta, sannan tasa brown eye a girarta ta bi bakinta da sassaiikan jan baki pink colour; sai ka rantse da Allah kalar lebanta ne haka.
Saude ta mike ta janyo kayan ta saka dogon §
' wandon: wanda ya kama ta tsam-tsam sannan ta
”’ kawo rigar ta sanya, wadda ta bi illahirin jikinta ta ta
lafe, Saunan ta kawo dogUwar rigar ta dora ta
* Warwaré gashin kanta ta Kara daure shi sosai, ta yi masa tamkar gamma a baya, ya zama tuntu sannan ta » ‘ kawo gyalen rigar ta yi kamar rawani da shi.
Ta Ciro takalmin mai tsini ta saka, ta dauko pose din ta saka sarkar da mahaifiyar Dr. ta ba ta a ciki saboda rigar ba a hada ta da sarka sai dai ta bar dan
kunnen a kunnenta tare da abin hannu da zobe
Ta dauki turaren ta faffesa ko’ina na jikinta,
saunan ta tsaya gaban madubi tana qararewa kanta kalla, Barakallahu! Masha Allahu ni dai abin da zan ‘ iya cewa kenan don a gaskiya na san Saude ta hadu qarshe, ita kanta ba ta san tana da wannan kyan haka ba Masha Allah.
Ta fito daga dakin cikin nutsuwarta, Dr Ahmad dake zaune saman kujera yasa kayan abincin a gabansa bai san lokacin da. ya mike ba yana kallonta, hatta qaraso