Showing 99001 words to 102000 words out of 103547 words

Chapter 34 - YAR TALLAH complete

Start ads

Unknown   

24 Aug 2025

411

Middle Ads

ya waro ido, “Muje ina Saudat? Ba ki san k0
Karfe nawa ba ne yanzu? Takwas saura fa".
Saudat ta marairaice masa, “Don Allah ka zo mu
je, wallahi ba zan iya runtsawa ba yau in ban
ganshi ba, k0 ka sa direba don Allah ya kai ni”.
Dr. ya dan yi kasaKe yana kallonta, yadda duk ta
firgice lokaci guda a take kuma sai ya ji
tausayinta ya kama shi, tabbas ta yi kewar yayan
nata, za ta iya ma shiga kowane irin hali. Ya
sauke kansa daga kallonta ya mike ya suri
wayoyinsa da ke kan teburin, ya ce, “Dauko
mayafinki kizo muje”.
Sai kuma tausayinsa ya kama ta, k0 awa 'daya
bai yi da dawowa daga wata tafiyar ba, sai dai ba
yadda za ta yi, tana son ganin yayan nata a
yanzu fiye da komai. Ta juya ta dauko mayafinta
kalar atamfar ta dauko wayarta da jakar takalman
kafarta ta tattara kudaden da Dr. ya ba ta wanda
ko dubu hamsin ba ta taBa a cikinsu ba ta zuba a
jakar, sannan ta fito. Yana nan tsaye inda ta bar
shi yana jiranta. Yana ganin ta flto ya yi gaba ta
biyo shi a baya, sabuwar motarsa ya shiga. ‘
Saudat ta dube shi, “Ba direba zai kai mu ba
Yallabai?”
Ya ce, “A’a mu je kawai na tuqa mu, zamu fi
sauri”, , ' Ba ta sake tankawa ba ta zagaya
kujerar da ke gcfen direba ta bude ta zauna, ta
samu ya kwantar mata da kujera, don haka ta
kwanta sosai, shi kuma ya yi wa motar key suka
fice daga gidan suka hau hanyar Katsina, inda
suke sauraren karatun alkur’ani mai girm wanda
Dr. ya kunna musu a motar, hakan yasa kowane
ya nutsu yana saurare sai ‘yar maganar da ba a
rasa ba. Ba karamin gudu ne Dr. Ahmad , yake
sharawa ba a kan titi, don Karfe goma da minti
talatin ta yi musu a cikin Katsina a gidan su
Saudat.
Tun kafin ya ida tsayawa Saudat ta Balle murfin
Kofar ta fito a guje, ta nufi cikin gidan tana
Kwalla wa Yaya Rabi’u kira. Tana shigowa ' falon
tana wurwurga idanu, can hango shi cikin
doguwar kujera yana shan fan-milk, Saudat ta
fasa wata uwar Kara ta kwatsa a guje ta fada
jikinsa ta
kankume shi tana ihun dariya. , * Shi kansa
dariyar yake yana ambaton sunanta ‘ tare da
Kokarin dago ta don ganin yadda ta koma amma
taKi sakinsa, su Nabil da Nabila ma ‘suka rufa
mata baya suka rungume ta suna murnar ganinta.
’ . Momy dai dariya kawai ta ke musu zuciyarta
dauke da matuqar farin ciki da shaukin ganin
sanyin idaniyar nata 'Dr ya yi sallama ya shigo
falon rike da jakar Saudat da wayarta ya durkusa
agaban Momy yana
gaishe ta cike da girmamawa, Saudat ta zame
daga jikin yayan nata tana kallonsa, kuka ta ke
sosai shi kansa sai da kwallar ta zubo masa cikin
karfin hali ya soma share mata hawayen yana
fadar, “Ya isa haka Saudat, ba kuka za mu yiba,
sai mu gode wa Allah”
“ Dr Ahmad ya mike har zuwa inda suke ya mika
wa Yaya Rabi u hannu yana fadar, “Your welcome
Yayanmu, mun yi farin cikin ganinka” .
Rabi u ya ce “Ni ma haka, amma yanzu cikin
,daren nan ta taso ka? ”
Dr ya cc, “To ya na iya‘? Ai yayanmu yana da _
muhimmanci a rayuwarmu”.
Dadi ya kama Rabi’u ya yi na’am kuma da
zamowar Dr. Ahmad mijin ‘yar kanwar tasa.
Saudat ta mike ta nufi wurin mahaifiyarta tana
fadar, “Don Allah a ‘ina ku ka ganshi?”
Momy wadda bakinta yaqi rufuwa ta ce, “Saudat,
yanzu cikin daren nan ki ka taso mijinki,
tsakaninki da Allah kin kyauta? Ai da na ‘sani da
sai gobe na fada miki
Saudat ta ce “Kai don Allah Momy, shi fa ya ’ ce
mu taho”.
Ta yi maganar tare. da satar kallon Dr. wanda
aka yi sa’a shi ma ya kallo ta ta yi saurin dauke
kai, “Don Allah Momy ina ku ka ganshi?”
Momy ta ce, “Ta hanyar Inna mai danwake, tunda
ki ka fada min Rabi’u ya bada sako a baki nake
aikawa wurinta a kan a karBo min sakon mijinta
ke fadamana vata nan ta yi tafiya zuwa garinsu
har
‘ ,ta kai ga ,ina zuwa da kaina, amma ban yi
nasarar
' samunta ba, tsawon wata daya da sati biyu sai
yau na
tayar da direba na tura shi kasancewar mijinta ya
ba mu tabbacin yau ne za ta dawo. Cikin ikon
Allah kuma ya yi nasarar samunta ta dawo daga
garin nasu
a jiya, aka yi sa’ a kuma ta bawa direban saqon
cikin
waccan jakar”.
Momy ta yi musu nuni da wata ~leda mai
tambarin Aminci Super Market Katsina, ta ci gaba
da fadar, “Direba na kawo. min jakar na zazzage,
ba komai bane a ciki sai wasu lesussuka guda
biyu, atamfa super Holland guda, sai takalma da
jaka da kuma sabuwar waya a cikin kwalinta
tecno p.2 da'sabon layi a ciki. Jikina na rawa na
kunna wayar sai ga lamba Kwara guda a ciki, a
take na danna kira cikin sa’a kuma lambar ta
tafl. Bugu biyu ya dauka muryar har rawa ta ke
wurin sanar da shi k0 ni wace ce, shi kansa ya
shiga rudani kuma k0 minti talatin bai Bata ba ya
iso nan gidan”.
, Saudat ta cd“Wayyo Yayana, Allah sarki ashe ba
ka manta da ‘yar qanwarka ba? To yaya da baba
ya kore ka kai ina ka nufa?"
‘ _ Rabi’u ya dan yi‘ murmushi kafin ya ce“Ai
*duk halin da na shiga Saudat ban tunanin zan
manta dakeba sai dai in har ba na numfashi, don
a
lokacin da Baba ya kore ni na dauki hanya ina ta
tafiya amma ban san inda zaniba ina ta tafiya ga
*gajiya ga yunwa ga duhun marece ya fara. Ina
cikin tafiyar nanne na fara shigowa gari nayi karo
da wata leda kamar zanwuce saikuma
watazuciyar tabani shawarar induba ko Allah
zaisa wani sauran abinci ne a. ciki in samu abin
da zan ci.
Da wannan tunanin na tsaya na dauki ledar,ina
dubawa amma damamakina sainagawani kwali
ina duba kwalin sai ga sabuwar waya a ciki, dadi
yakamani nasamu abindazan siyar inci abinci,
don haka da kwanrin gwiwata na ci gaba da
tafiya harna shiga cikin gari da tambaya aka
nunamin wurin saida wayoyi harna isa kasuwar
tsaitsaye wadda ke cikin garin Katsina donna
bada wayata a siya, sai dai abindaya dauremin
kai shine farkon tayi aka tayata naira dubu dari
da hamsin mamaki yasa na gaza cewa komai, shi
kuwa mutumin dauka ya yi k0 ba zan siyar masa
bane ya hau kora min jawabi. ‘
“Malam damaka siyarmin dawayarnan haka don
ba wata uwar ribace zanciba don dubu dari da
saba,in ake saida ita
Cikin sanyin jiki nace yabada kudin babu kuma
vata lokzaci ya qirgo kudi a aljihunsa ya _
mikamin nakirgasu naga sun cika sannan najuya
nasoma tafiya.Saidaifa inda gizo ke saqar bansan
gidanwa
zannufaba, gadai kudi ahannuna ammabanda
wurin zuwa don haka najana zauna asaman wani'
dakalin dake wajen kasuwar na kira mai abinci na
.siya na ci na qoshi, na sha ruwa na ci gaba da
kallon titi, wannan mota ta wuce, waccan ta wuce
a haka fa aka yi sallar magriba da isha, dare ya
soma duk ina a zaune a nan fa fargaba ta fara
shiga ta.
‘Banyi auneba naji andafani,harna dan firgita ashe
mutumin dana siyarwa waya ne. ya zauna a kusa
da ni yana tambaya ta, “Wai lafiyarka kuwa
Rabi’u?”
Jin ya kira sunana ya sa nayi saurin kallonsa, sai
a lokacin na shaida shi ashe Yasayyadi ne dan
dan oganmu wanda nake aikin Kasa a wurinsa.
To in takaice muku nan na sanar da shi halin da
nake ciki, na korata da mahaifina ya yi har tsintar
wayar da nayi. Ya yi matuqar tausaya min, a nan
yace in tashi mu tafi shi zai taimake ni.
Yasayyadi ya kai ni shagonsa da yake kwana
wanda ke like jikin gidansu ta waje nan na ci
gaba da zama, kwanana uku Yasayyadi ya ba ni
shawara da na fara sana’a, ni ma ya ga kamar
masu shi go da shinkafa a Kasar nan suna samu
k0 zan fara? Na amince, ya hada ni da wani
abokinsa muka fara safarar shinkafa daga qasar
Nijar zuwa Najeriya da ma ina da jari a hannu.
Allah Ubangiji kuma ya sa min albarka, sai ga ni
cikin fan kankanin lokaci na tara kudi masu kauri
a hannuna, a lokacin ne na sanar da Yasayyadi
ina son. shiga makarantar boko, shi ma ya yi
na’am da
shawarata, don shi a lokacin yana shekarar
Karshe ta kammala digiri. Shiyayi duk wanicuku-
cukun da akeyi na hada takardun firamare natafi
js3 kaitsaye cikin yan watanni nazana. JSCE
sannan na wuce SS one na maida hankali sosai a
karatuna, wanda bai hana ni neman kudina ba.
Abin ma kamar harda sa hannu don duk abin da
na taba cikin ikon Allah sai ya zama kudi, a haka
naci gaba da karatuna zan shiga aji biyar na
tsallake na wuce aji shida. Ina kammalawa na
zana jamb na yi sa’a kuwa na bugo point din da
ake so, wato 200 point don haka ban " samu
wani matsala ‘ba wurin samun admission a
Umaru Musa ‘Yar 'Aduaa university suka ba ni
Mass
Com na soma karatuna cikin nasara ina level 2 na
fara shigo da motoci daga waje zuwa Najeriya a
lokacin ba zan rasa jarin da ya wuce naira
miliyan ashirinba, don harnafara aje yara suma
sunaci a qarqashina nayi gida nayi mota na tashi
daga gidan su Yasayyadi na koma. gidana, a
lokacin shi ma ya yi aure ya samu aiki da
hukumar zabe ta qasa yana zaune da matarsa a
lokwas din kofar: Maruba.
A lokacin da na gama digirina aka turani garin
Lagos in yi sabis dina, na tattara na tafi watana
biyar aka bamu hutu naxo gida mahaifina ya
sakemin korar kare a karo na biyu nanna bada
sakon' kaya da wayagidan Inna mai danwake a
ajiya miki'
na juya na tafl ina kuka jin wai an tura ki aikatau,
kwanana biyu na koma Lagos.
A yanzu haka yau satina guda da kammala sabis
dina inda na samu saqon tashin hankali, wai Allah
ya yi wa Yasayyadi rasuwa, mutuwar ta gigita ni
ba kadan'ba, don haka na dora wa kaina nauyin
kulawa da iyayensa kasancewar bai taBa haihuwa
ba, sai ga sakon kuma farin ciki ya same ni, wai
mahaifiyata .da qanwata sun bayyana, wallahi
farin cikin da na tsinci kaina bazai misaltu ba”.
Saudat ta cce “Allah sarki yayana ka sha wahala,
kuma ka samu duniya, shi ya sa na ga ka zama
wani dan lukuti”.
Duka suka sa dariya sannan Saudat ta ba shi
labari tun daga ranar da ya tafi har ya zuwa
aurenta.da Dr. Ahmad, Rabi’ u har kuka ya yi
saboda tausayinta, don haka ya ce Dr. ya yi
musu .alfarma gobe su je Dandagoro ya ga
mahaifinsa, kuma ya ga Hamid; Dr. ya amsa da
Allah ya kaimu sannan ya mike ya yi musu sai da
safe.
Momy ta ce “Au dana. 'zata a nan zaka kwana?"
Dr. ya dan yi murmushi tare da fadar, Momy na
riga na yi bukin a Katsina Hotel".
Momy ta ce, “Amma da ka daure ka kwana
Ahmad Abbanka ba ya qasar k0 Bangarensa ba
sai ku sauka ba?”
Ahmad ya ce, “Ayi haquri dai Momy? da safe zan
dawo” " Ta ce, “To Allah ya kai mu” Ya amsa da,
“Amin” Ya yi wa Rabi’u sallama ya fice. . Saudat
ta sabi takalma ta bi shi da‘ zummar suyi sallah;
yana tsaye bakin motarsa har ta Karaso ya bude
mata qofar motar yana fadar, “Muje Saudat,
wallahi na yi bala’in gajiya”. ‘ Saudat ta waro ido,
“Muje fa kace Yallabai? Haba don Allah, ni
gaskiya bazan iya binka ba”. ' Dr. ya zuba mata
ido a raunane yana fadar, “Kin yi min adalci ke
nan Saudat? Kin san dai a ‘ yanzu ina buKatarki
kusa dani, ki tuna fa tsawon lokacin da na dauka
ba mu tare”. ‘ Saudat ta langwabe kai a
shagwabe._ tana , fadar, “Allah YallaBai ni dai
kunya nake ji, kuma yau dai daya don Allah ka
barni in gaisa da dan uwana". . Dr. ya kada kai
tare da fadar, “Shi ke nan Saudat sai da safe”. Ya
juya ya fada motarsa ya ja ta a hankali ya fice,
zuciyar Saudat ta yi matuqar rauni sai dai ba
zata iya yin abin da yake son ba, tajuya ta nufi
cikin gidan ta ja ta zauna suka dasa hira da Yaya
Rabi’ u da " Momy wadda da ta gaji ta mike ta
shige dakinta ‘ Amma su kam yadda suka ga
rana haka suka‘
, ga dare, sai da aka kira sallar asuba sannan shi
ya tafi
~ , masallaci, ita kuma ta nufl Bangarenta in da
ta dauro'
alwala ta yi sallah, kana tahau kan gado ta
kwanta. Sai dai ta kasa runtsawa, tunanin halin
da ta jefa mijin nata a jiya ya tsaya mata a
zuciya, ta lura tamkar fushi ya yi da ita don haka
ta lalubo wayarta ta soma rubuta masa saqo
kamar haka.
‘Tuba nake mai gidana, banji dadin abinda nayi
makab wallahi yanxu haka ina kewarka kamar
yadda kake kewata, ina bukatarka fiye da yadda
kake buqatata, saboda a duk Iokacin da nake
manne dakai sai injini na zama kamar wata
tauraruwa,a cikin taurari
Tana gama rubutawar ta yi murmushi tare da
tura masa saKon ta koma ta kwanta, sai dai k0
minti biyu ba a yi ba sai ga amsa ta shigo, ta yi
dariya don ta san da ma za a rina ta jawo wayar
ta soma
karantawa kamar haka.
‘A kodayaushe ki dinga tunawa ke daban ce a
cikin duniyata, erro lets go am sorry plz
Saudat ta maimaita karanta sakon ya fisau goma
kafin ta tura wayar a cikin jaka ta koma ta
kwanta, ba ta jima ba kuma bacci mai nauyi ya yi
awon gaba da ita, wanda ba ta tashi farkawa ba
sai
sha daya. na safe. Tana mikewa bandaki ta nufa
ta watsa ruwa ta fito, ta sake shiryawa cikin
atamfarta ta
sannan ta flto Sai dai da mamakinta ta samu
Momy da Rabi’ u da Dr a falo suna hira, da alama
sun
dade suna hirar ; Ta durkusa ta gaishe su daya
bayan daya, sannan taja gefe ta zauna tana
fadar, “Da ma kun tashi Momy ba ki tayar dani
ba?” ' ‘ Momy ta ce “A’a na barki ne ki hantse
tashi ki karya maza ku wuce don ku daga can za
ku wuce”. Saudat ta yi saurin dagowa ta kalli Dr.
sai dai k0 inda ta ke bai kalla ba, hakan ya tilasta
mata mikewa ta nufi dinning ta zauna ta karya,
sannan ta dawo cikin falon Momy ta dauko mata
jakar da Rabi’un ya ba ta, ta qara mata da ‘yan
tarkacen tsaraba, sannan ta rako su. * , Saudat ji
take tamkar kada ta tafi, sai dai ba ta ~ da
yadda ta iya, haka ta shiga motar Dr. shi kuma
Rabi’u ya shiga tasa motar sabuwa dal mai suna
206 suka rankaya suka tafi Momy na musu fatan
alkhairi. ~ Sai dai lolkacin 'da suka iso gidan
Saudat mamaki ya kashe' ta, ganin yadda ya
canza ya dawo ginin bulo da bulo aka kawata shi
tamkar gidan wani dan karamin ma’aikacin
gwamnati, kanta bai ida daurewa ba sai da suka
shiga cikin gidan wanda aka canzawa tsari duka
falukan gidan aka hade su cikin guda, aka kaWata
su da sabbin kayan alatu na rayuwa, duk kan
Saudat ya kwance shi kansa Rabi’un
bin gidan yake da kallo, ‘Yarbaba wadda ke zaune
a““ gidan ita ta yi musu iso cikin falon tana ta
faman rawar jiki, sannan ta nufl wata kofa don ta
kira musu Malam Bala.
Saudat ta cika da mamakin ganin ‘Yarbaban a
gidan, lokacin da Malam Bala ya flto ya yi ido
hudu da Rabi’u sai ga shi ya. xube ya fadi kuka
yake wiwi kamar karamin yaro, yana roKon
gafararsu kan Saudat bai ida kwancewa ba sai
data ga ‘Yarbaba ta turo Inna Laure a keken tura
guragu, Saudat ta rude . ta shiga tambayar abin
da ya faru tunda ga Inna Lauren nan dai babu
alamar rashin lafiya a jikinta, . amma daga Inna
Lauren har ‘Yarbaba kuka ya hana
su magana sai Malarn Bala ne ke fada musu.
‘ “Lalurar hawan jini ceta kayar da Inna Laure tun
a lokacin da ya kulle ta a daki ranar da aka dauki
Saudat zuwa gidanta yana zuwa ya bude 'daki ya
ganta a sume hankali ya tashi aka kwashe ta aka
tafi asibiti nan fa aka sanar mana jininta ya yi
matukar hawa kuma qafafunta sun riqe don inba
wani iko daga Allah ba, ba za ta sake taka su ba.
Mijinki yaxo Saudat a lokacin muna asibiti, shi ya
yi ta dawainiya ya ba da kudi aka wuce da ita
asibitin Aminu Kano da ke cikin jihar Kano ya ba
da .makudan kudade, kuma shi ya yi mana
wannan gyaran, amma a asibitin can ma sun ce
iya bincikensu
ba su ga abin da ya rike Kafafuwanta ba, don
haka suka sallame mu, k0 kwana hudu ba mu yi
ba da dawowa gida sai ga ‘Yarbaba cikin wani
mummunan
‘ hali, wai mijinta ya kwashe kayan dakinta ya
siyar, ta yi magana shine ya yi mata dukan tsiya
duk ya raunatata, ya yi mata tsirara ya turota
waje ya ce ya sake ta Saki uku, sai dai makota
ne suka ara mata tufafin da ta iso gida dashi.
Yau satinta guda da dawowa shi yasa ku ka
ganta ta yi kyan gani, amma kwanakin baya idan
ku ka ganta sai kun zubar mata
» da hawaye, ni nasan haqqinku Saudat ba' zai
barmu ba matukar ba ku yafe mana ba, don Allah
Rabi’u ka yafe mana ba don mu ba ba don
halinmu ba”. ‘
Rabi’u ya ce“Ai ni ban' rike ku da komai ba baba,
wallahi na yafe har cikin zuciyata”.
Inna Laure ba ta da ta cewa, sai kuka sai ma
‘Yarbaba ce ta yi Karfin halin bude baki ta nemi
gafararsu. Sun dade a gidan kafinsu yi musu
sallama. za su tafi, Dr. ya yi musu kyautar
makudan kudade, haka shi ma Rabi’u naira dubu
hamsin ya bawa mahaifinsa da zummar idan ya
dawo zai’ ga abin da ya kamata ya yi musu,
Saudat kuwa dumtsowa kawai ta yi ba tare da ta
san k0 nawa ba ne ta bawa mahaifin nata, ta ba
wa Inna Laure sannan ta miKa wa ‘Yarbaba ‘yan
sauran da suka rage.
Ai k0 sun sha godiya da sa albarka, haka suka
bar gidan kowa zuciyarsa cike da alhini, da ma
haka rayuwa ta Kunsa, idan kai ne yau gobe ba
kai bane, idan ba ciwo akwai ajali idan ba ajali
akwai tsufa haka rayuwa take tAfiya a kwana a
tashi mai maida yaro tsoho.
Dr ya dauki matarsa suka koma gidansu suka Ci
gaba da rayuwarsu cikin nagartacciyar soyayya
da kaunar juna, Saudat tana bawa mijinta irin
kulawar data kamata dukda karatunda takezuwa
baihanata ba shi duk wata kulawar da ta san zai
iya bukata dagagare ta ba. A yanzu karatunta ya
yi zurti, don kuwa har ta kammala Basic Illetrate
ta karbi certificate ta kuma ci gaba da karatunta
na wata tara Wanda za ta karanci Social welfare,
don haka ta dage “*dakaratun ta donma canjin
jikindata'samu narashin kwarin jiki wanda likita
ya tabbatar da ta samu shigar cikin wata uku,
wannan albishir din ba qaramin faranta zuciyar
Dr. yayi ba, an inda labarin cikin Saudat har a
cikin ‘yan uwansa, ‘ saboda tsabar rawar qafarsa
a kan haihuwa.
Cikin Saudat yana da wata takwas ta kammala
karatunta na wata tara a lokacin an soma siyar
da
form din jarabawar waec external da kuma jamb
din
ta cike abinta ba su zana jarabawar ba Saudat ta
haihu' wata tara daidai ta sunkuto qaton danta
mai kama da ubansa sak tamkar ya yi kaki ya
tofar
' ‘ Ai k0 a wannan lokacin Saudat ta ga gata da
soyayya don Dr, da iyayensa sun saki bakin
aljihuna sun mata bajinta, kuma sun gwada mata
ita din ta zama tasu ta zama wani Bangare na
jikinsu wanda

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login