Showing 9001 words to 12000 words out of 103547 words

Chapter 4 - YAR TALLAH complete

Start ads

Unknown   

24 Aug 2025

399

Middle Ads

faman kuka, “Ina ki ka je ‘yar iskar nan? Yawace-yawacen bin ' mazan ne naki ya fara k0 Allah ya baki sa,a, wadanda ma suka fiki basu ci riba ba ballantana ke ‘yar ‘ tatsutsuwa, daga ki hura mini wuta ki sa qafa ki fice har in gama wainar ta sandare sannan ki dawo
Malam yace, ‘Gaskiya Laure ki qarasa ido kan yarinyar nan don yanzu Malamin makarantarsu ‘Yar Baba ya rinka gaya mini irin abubuwan da yaran nan ke yi idan sun tafi wurin talla ki rinqa ja mata kunne
Wallahi kar taje ta dauko mana abun kunyar da ba zamu iya saukewa ba."
Laure: ta ja tsaki tana fadin, “Yo ‘yarinya Ma : ta sake ta kwaso abun kunyar ai sAi ta san inda ta nufa, don wallahi korarta za mu yi daga gidan sai dai ta nemi wasu iyayen."
Malam yace, “Gaya mata dai.” Yasa kai ya shige dakinsa.
Laure ta haure ta da qafa, “Tashi ki sauki tallar ki tafi muguwa kuma Batan sisi kikai min sai na ci ubanki cikin gidan nan kin dai san halina ba ni da kyau ba ni da dadl wallahi." ‘
Saude tana kuka ta duka ta dauki wainar ta fito tana sharar hawaye. A waje su kai karo da Rabi‘u yana ta bunzuma sauri yana ganinta ya nufo ta.
“Saude ina ki ka je ana ta neman ki ba inda ban jeba cikin unguwar har kin tada mini hankali.”
Saude tasa bayan hannunta tana goge hawayenta tace, “Ai Baba na bi zau kai ‘Yar Baba makarantar boko shi ne da muka dawo Inna Laure ta doke ni.”
Rabi’u yace, “To ke in ban da abin ki me ya: kaiki bin su Baban na dai san ba cewa ya yi ki raka shiba ko?
Taqara share hawaenta tana fadin “Eh, ai ni na bisu Yaya ina san makarantar in tafi can yanzu?
Rabi’u yace, “Haba Saude ya za ai ki tafi
kowa sanya shi ake baki ga ita ma Baba ya sanya taba?” ‘ Ta ce, “To, kai ma ka sanya ni yanzu.”
Ya dan yi shiru yana nazarin wasu al’amura, Saude ta riqo hannunshi tana girgiza shi, “Don Allah nima ka kai ni ka ji Yaya?”
Ya tsura mata ido yana kallonta zuciyar shi cike da al’amura masu yawa yasa hannu ya dafa kanta cike da tausayawa ya ce, “Ki yi haquri Saude insha Allahu za ki yi karatun boko, duk rintsi sai na ga kin yi ilimi dole zan cika burin mahaifiyarmu Saude kullum maganarta a kan karatunki ne insha Allahu zan cika mata wannan burin, dole zan nemi kudi k0 dan saboda kek0 dan saboda rayuwarki insha Allahu ba zan bari rayuwarki ta lalace ba, ki je tallar l
Ki dawo kin ji?”
Kai ta daga masa ya sake ta ta wuce sannan shima ya kama hanya ya yi gaba .
Al’ amarin ya damu Rabi’u matuqa a zuciya yana san Kanwar shi ta yi karatu k0 dan wata rana ta taimaki kanta da kanta, koda baya raye tunda Allah kadai ya san gawar fari. To wacce sana’a ma zai yi yanzu a duniya? Tunanin da ya fado masa kenan, in dai ba ya rinqa' sana’ar Baban Bola ba, sai dai ita wannan sana’ar dole sai kana da jari a hannu ka rinka tara naka kana siyan na wasu kana
hadawa. Ya ja numfashi sosai yana nazari, can abokinsa Halliru Maigini ya fado masa.
Tabbas shi ya kamata ya nema don yanzu ya tabbatar yana da qarfin da zai iya sana‘ar ginin, ya mike daga kwancen da yakw: ya fito ya yi gaba, yana jin Inna Laure na Kwala masa kira bai kula ta ba, don yanzu yanda yake jin zuciyarsa idan ta ci gaba da takurawa rayuwarsa gab yake da daukan mataki (Namiji kenan).
Cikin sa’a kuwa yana zuwa wurin abokinsa ya raka shi har “wajen mai gidansa ya amince ya karbe shi ya sanya shi cikin yaransa masu nazari da koyan aiki yace zai rinqa ba shi dari biyar duk safiya, amma ban da ranar da ba a fita aiki ba. Dadi da murna suka kama shi a ganinsa yanzu ya samu sana’ar da zai taimakawa rayuwar Kanwar tasa da ita, don haka har ya qagara gobe ta yi don ya fara . zuwa aikin shi ma ya ga yana rike naira dari biyar tashi ta kan shi. Mahaiflyarsa ta fado masa a rai, wayyo ina ma tana raye tabbas da ya zamo daya daga cikin ‘ya'ya masu kyautatawa iyayensu.
Kukan Saude ne ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula ya zabura da sauri ya yo waje, ya iske Inna Laure zaune ta dora qafafuwanta kan ta tana ta mintsini ta ko’ina ita kuma sai ihu take, tana roqonta.
Rabi’u ya jingina da bangon dakinsu yana kallon muguntar da take mata ‘yar Baba ta ruga ta dauko bakin wuta ta mikawa uwar tana fadin, “Karbi ki dake ta Laure.”
Rabi’u ya dauke idanuwansa ba zai iya kallon wannan muguntar ba. Sai da Laure ta tabbatar ta yi mata burdun-burdun da tabbuna sannan ta sake ta ta haure ta tana fadin
‘Tsinanniya ‘yar iska gobe ma idan halin ki ne ki sake Batar min da kudi.”
Saude ta kwaso da gudu ta fada jikin Rabi’u tana ihun kuka ya ja hannunta suka nufi dakinsu, ya zaunar da ita gaban shi yana lallashinta, yasa hannu yana goge mata hawayen, mur‘yarshi a sanyaye yake magana
“Kiyi haquri Saude kidaina kuka kinji insha Allahu komai ya kusa zuwa qarshe nan ba da jimawaba
komai zaizama tarihi,yanzu haka nasamu aiki gobe ma zan fara zuwa, share hawayenki nan ba da jimawa ba wadannan hawayen zasu daina zuba kinji?”
Ta daga masa yana gage mata hawayen ya ce, “To ki yi murmushi mana kobakiji dada bane?’
Dariya ta shiga qalqalawa tanayi kamar wata tababbiya shi kan shi har ta ba shi dariya ya dungure mata kai yana daria itama tace ala dole saita rama.

Lol kuma sance dani donjin yaddah laure da rabiu zasu kaya

Naku har kullum
Dboy
[1/12, 5:44 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[1/15, 6:40 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

*CHAPTER 8*

Rama ya rike hannuwanta duka da ta yunkuro zata dokeshi sai ya tura hannun ta daki kanta, ya yi tayi mata dariya.
Sun shagala sosai kuma kana ganin suka san suna cikin nishadi ba su ankara ba sai dai suka jiyo muryar Laure na fadin
“Sannun ku ‘yan iska watsatstsu, taBarar ceta motsa kenan shi yasa aka shiga daka k0 jin kira ba ayi dakyau aikana qoqari gara kayi amankaka lashe abin ka, ka ga tuwanka manka kenan. Kuyi iskancin ku san ranku babu mai hana ku, ai dama barewa ba tayivgudu danta ya yi rarrafe ba gado kuki ai dama abun, kun tsotsa,ne ku yi sha’aninku kun ji.” Ta = saki labulan ta juya ta yi gaba. Rabi’u ya girgiza kai yana jin tamkar zuciyarsa
Zata fashe saboda bakin ciki, idan akwai abin da ke
daga masa hankali duniya ya dungunzuma masa lissafi to bai wuce a tuna masa abin da ya faru a * baya ba, wanda ke daga masa hankali ya dagula masa lissaii duk wata annashuwa ta shi take take Bacewa Ya jingina da bango yana kallon Saude ya jirkita ta kwanta jikinta a sanyayc. ‘ Washe gari tunda safe Rabi’u ya yi jidar ruwansa gamida duk wasu aikace-aikace da ya san zai yi qarfe takwas daidai na safe ya sa kai ya fice abinsa b tare da ya fadawa kowa inda za shi ba.
Saude ta dauki taller wainarta ta tafi sarfiyar yau jikinta jinshi take babu dadi ko kadan da kyar ta samu ta iya saida wainar a hanya ma amai sau biyu tanayi harta samu ta iso gida da kyar, ta mikawa Inna Laure kudin tana neman faduwa, saboda juwar da ke
barazanar kayar da ita. Inna Laure ta zuba mata idanuwa cike da jin haushi kafin ta ce.
“Wannan lambon kuma na mene ne kl ke faman yi? Duk na kar ki dauki taller alalan ce k0 me?”
Saude ta girgiza mata kai alamar a’a tana nishi. Inna Laure ta ja tsaki tana fadin “To sai ki wuce ki dauka ga alalan can ta Murtala shida ce da goma
Saude ta langwaBe kai cike da jin jiki ta ce, “Ki yi hakuri don Allah Inna wallahi ban da lafiya bazan iya ba.”
Inna Laure ta waro ido waje tana fadin, “Uban me ki ka ce? Ni ki ke fadawa ba ki da lafiya Saude? To Allah yasa mutuwa ki kekina dawowa wallahi sai kin dauki tallar nan, ‘yar iska na lure kwanan nan wani tashan balagar tsuntsaye ce ke cin ki, kuma wallahi zan tatsiye miki ita tas za ki tafi ki dauka ki bani wuri k0 kuwa?”
Saude ta wuce tamkar wadda ta yi ciwon shekara goma ta dauka ta fice, tana tafiya tana hutawa k0 ta sule ba ta kai ga siyarwa ba ta zauna saman dakalin qofar wani gida tana faman kakarin amai numfashinta na fita sama-sma tun tana sanin inda
Har ya kai ta flta hayyacinta ta fadi can gefe sime.
Wani mutum da ke tahowa ta Iayin cikin shirin masallaci kasancewar yau Juma’a ce ya yo kanta a gigice ya jijjiga ta amma ba ta k0 motsi, kafin ka ceme mutane sun taru a kanta ana ta tambayar wanda ya san ta, amma babu saboda kullum dai ana ganinta
tana wucewa babu wanda zai ce ga daga unguwar da take tahowa, tun kafin a tafi masallaci har aka dawo sallar Juma’a, amma ba a samu wanda ya san unguwar su Saude ba.
Yamma liqis Rabi’u ya dawo daga wurin aikinsa ya yi dumu-dumu da yashi da suminti kana ganinsa kaga mai aikin Kasa, ya yi sallama ya shiga gidan. Laure da ke zaune a bakin rijiya ta dago tna kallonsa ya giftata zai wuce ta zabura ta mike ta cimimiyo rigarsa tana fadin
"Daga gidan uban wa ka ke dan iska tun safe ina gararin neman ka rumfa-rumfa ban gan ka ba daga ina kake?”
“Daga wurin aiki.” Ya ba ta amsa kai tsaye
Laure ta maimaita, ‘Aiki. Aiki fa ka ce? Eh lallai Wuyanka ya yi kwari wato harka san ka kakkare
Ka tafi wurin aiki, tabbas lallai wata rana sai ka
Shaqeni shi kenan jeka jeka kawai." Ta fada tana . murmushi
Rabi’u ya wuce dakin su kai tsaye ya cire rigar ya kwanta saboda gajiyardaya kwaso ga shi abinda ba ka sababa. A take bacci barawo ya sace shi, kiran salla ne ya farkar dashi
Ya tashi a gigice saboda rashin ganin Saude ya fita tsakar gidan amma batanan abinda batataBa ba yanufi kofar dakin laure ya duka daga bakin qofar muryarshi da alamun rudani yace, “Inna ko $aude tadawo?”
Laure ta watsa masa wani kallo kafin tace,“Ban saniba tana indata dawo da baka gantaba Ko kudice dazan Goyata?”
Gaban Rabi’u ya yi mummunar fad'uwa hankalinsa yayi masifar tashi.To inatake?
“Shin ba zaka tafi kanemota baneba zakatsaya kallon jama’a ne?” Muryar mahaifinsu ta katse masa dogon tunanin dayake ciki
Ya yunkura ya mike jikinsa asanyaye yafice.'shin ta inama zai fara neman nata ne? Wayyo Allah Ya Ubangiji kada kajarabeni da abinda bazan iya daukabaYaAllah kasa duk inda Saude take tana hannu nagari.
Abinda yake fada kenan azuciyarsa,yayanka yayi hanyar rewa
Tasha dukda yanada yaqinin zuwa yanxu an rufe tashar amman babu yaddah zaiyi yanashan kwanar layin nasu ya
Ci karo da jama’a wani na rungume da Saude wai za,a kaita gidan mai unguwa.
Hankalin Rabi'u ya yi masifar tashi ya tsare su yanavfadin qanwarsa ce su kai masa ‘yan tambayoyin da za su yi masa sannan suka ba shi ita ya nufo gida hankali tashe tun a hanya yake ta faman rusar kuka don shi duk a tunaninsa mutuwa ta yl.
, Yana shiga gidan ke Laure ta zabauro masa wai ina kayan tallarta, ita ta sana’aarta take ma. Wani_abu ya zowa Rabi’u iya wuya yanda ko kadan mahaifinsu bai damu da halin da Sauden ke ciki ba. Ya shimfideta a tsakar gida jikinsa na rawa ya nufi rijiya ya janyo ruwa ya shiga Sheqa mata, cikin ikon Allah ta farfado m har tana magana, ko motsin kirki ba ta yi, saidai sambatun datake tyi iri irin wanda ya zare hankali
Rabi’u yana kuka ya nufi dakin mahaifin nasu ya durqusa gabansa yana fadin, “Don Allah Baba ka ba ni kudi in kai ta asibiti ta farfado, amma ba ta motsi kada ta mutu.’
Malam Bala ya ce ‘Rabi’ u ta mutu mana, ai ranta ba a hannuna yake ba, ban da ikon sanyawa ta rayu haka kuma banda ikon hanata kaxo sai wani rawar jiki kake akan ciwon d bai taka kara ya karyba
Don nasan baxai wuce bugun iskaba da masassara
Ka je ka kira Malam Maidala yaxo ya yi mata rukiya ga naira hamsin ka siyo panado ka bata ta sha.‘ Ya wurga masa kudin.
“Tashi ka tafi.”
Rabi’u ya mike yana jujjuya kudin a hannunsa wani sabon kuka ya Kara kwace masa ya sa kai ya fita, kamar yanda ya ce haka ya je ya kira Malamin yazo ya dubeta shida kan'shi yace ba iskabane zafin zazza6i ne, don haka a kai ta asibiti. Ya dawo ya sanar da mahaifin nasu, a lokaicn har ya kwanta. _
Don haka a fusace ya tashi yana fadar, Wai menene zaka dame ni da zarya shin wai nina dora mata ciwon ne k0 k0 me?”
Rabi’ u yace, “Kayi hakuri Baba, Malam ya ce ciwonta na asibiti ne zazzaBi ne mai zafl.”
Yace ‘To shine har saika tadani ina baccina, tunda yafada maka zazzabine kaje katsinko ganyen dalbejiya kai mata surace mana, haba ban san matsawa wallahi.”
Rabi’u ya mike jiki a sanyaye hawaye na faman zarya a kuncinsa, tsanar mahaifin nasu ta qara mamaye masa zuciya gaba daya. A lokacin karfe sha daya na dare ne haka ya shiga dakin ya dauki Saude a kafada ya tafi chemist da ita.
A lokacin Bala mai allura‘ na' qoqarin rufe , chemist din nasa Rabi’u ya dube shi, ‘Don Allah
Malam Bala marar lafiya na kawo na ga kana kokarin tashi.’
Mal. Bala ya waigo yana kallonsa kafin ya ce, “Ashshal Waye ba shi da lafiyar?”
Ya ce ‘Wallahi Saude ce tun dazu zazzabi ya
kamata hadda su suma, yanzu haka k0 motsi bata ”yi
Bala mai chemist yace, “Ashsha! Ai kasan ni ban san sunansu na gaskiya ba, ‘Yar Baba k0 “Yar Tallar wacce cikinsu?”
Rabi’u ya' dan ja fasali kafin ya ce ‘Yar tallar dai’
Bala mai allura ya ce ‘Ikon Allah, saukota na ganta.’ Rabi’u ya sauko ta yana nuna masa har a lokacin sambatun ta kawai take.
Bala mai chemist ya ce “Ai wannan zafin zazzbine wallahi maleria, wato zazzaBin cizon sauro, gaskiya Rabi’u ku gaggauta kai ta asibiti don Wannan ciwon bana zama bane hadari ne babba dole ana buKatar likitoci. kamar biyu zuwa uku a kanta.’.
Hankalin Rabi’u ya Kara masifar tashi ga shi bai ajiye ba, bai ba wani ajiya ba, nairarsa dari biyar ta aikin yau, ita kadai yasan ya mallaka sai hamsin dinda Baba ya ba shi. Ya dubi Bala mai allura yana fadar.
“Don Allah Malam idan da akwai taimakon da zakamin ka taimaka min ai mata kafin zuwa safe na
ga abin da Allah zai yi, amma wallahi yanzu ban da halin tafiya asibiti ”
Bala mai allura ya ce‘Ai babu wani taimakon da zan iyayi yanzu anan nafada maka hatsarine a wurina na duba ta cikin wannan yanayi da take ciki.’
Rabi’u ya kifa kansa a ka Saude yasa wani irin kuka mai ban tausayi, ya zai yi da rayuwarsa tunda baidashi baidawada zai taimakamasa yana kallo rayuwar ‘yar uwarsa za ta salwanta, saboda kawai ba shi da shi... Kuka yake sosai.
Sosai kamar ransa zai fita

I will be back in no time

Via Dboy👍🏻
[1/15, 6:40 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/17, 7:43 AM] A A Dboy: *YAR TALLA*

*CHAPTER 9*

We miss 1page cours d page is damage I cnt c writting
clearly
Rabiu ya shiga mazaunin direba ya ja suka tafi. Kai tsaye
Federal Medical Center suka nufa a lokacin har shabiyu na
dare,ne da ‘yan mintuna.
Suna zuwa kuwa abin kada ma'aikacin wurin
cikin gaggawa aka wuce da ita Emagcncy Room da ita,
Malam Bala mai allura ya tsaya sai da ya kammala masa
duk wasu ‘yan shige da ficen daziayi masa sannan yayi
masa sallama ya tafl office don dama aikin dare yake.
Rabi’u ya dinga zabga masa godiya kamar zai kwanta
masa, abin har ya soma bashi kunya. ‘ A asibitin suka
kwana washe garida safe likitan daya dubata yaace yakoma
ya tawo da ‘yar uwarta mace ta kula da ita, hankalin Rabi’u
ya tashi ya ce, “Ai bata da ‘yar uwa.’ Likitan ya ceto gaskiya
ba zaiyiwu zamanka wurin jinyaba dole saika samu mace
yar uwarta koma wacece wadda zatayi jinyarta
A dole Rabi’u ya mike ya tafi zuciyarsa na faman suya, ya
nufi gida a qafa a lokacin karfe takwas 'na safe Yana isa
gidan ya samu Babansu a gidan ya duqa ya gaisheshi
yawaigo cikin Bacci yana kallonsa kafin ya ce
Rabi’u ka cika dan kanka yanzu gidan uwar wa ka kwana?” .
ya sassauta murya kafinn ya ce “Na kai
Saude Chemist ne daga nan mai Chemist din ya ce
yana taba ta yace wai dole sai an kai ta asibiti shine ya
daukemu yakaimu asibin acan:aka kwantarda ita,yanzu
haka ita tana can asibitin tama samu sauqi sosai, don har
tana iya gane wanda ke kanta‘. Yanxu likitanne ya ce in'zo
in taho da ‘yar uwarta mace, wadda za ta yi jinyarta.”
Kafin Malam yace wani inna laure ta hankado labule ta fito
tana fadar. “Ai k0 sai ka nemi ‘yar iskarda zata zauna
zaman jinyar badai laure ba donni hangar asibitinma banabi
ballantana in wuce ta gefensa, miyau wannan ban iya
hadiya cikin asibiti, don haka ma kar ku sake ku sani a
lissafi
Malam ya ja ihsali kafin ya ce ‘Ni duk ba ma wannan ba
Laure, shin kudin da za a biya a asibi'n ubanwa ya ajiye
zaibada nidai banidasu kuma ban ajiye ba, nan na ce kar ka
kai ta asibitin nan ammadayake kaibadan arzikibane shine
saida kakaita don kanunamini iyakata. Totundakai
dankankane basai kayi yaddakasoba,‘nidai kaga tafiya ta
kwandala ban maganinta.’ Yana gama fada ya juya ya fice
Laure ma ta hankada labule ta shige dakinta ta bar shi nan.
Rabi’u ya mike jikinsa amace ya rasa inda zai saka
Kansa haka yayita gararamba a gari data qarshe da yaga
vashi da mafita
Dole ya juya ya

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login