Showing 93001 words to 96000 words out of 103547 words

Chapter 32 - YAR TALLAH complete

Start ads

Unknown   

24 Aug 2025

413

Middle Ads

na samu wata? Tunda
matan ga su nan tamkar ledar pure water wanda
suka kai ki da ma wanda ba su kai kiba”‘ ‘Asma
ta dago da sauri tana kallonsa, ya “ daga gira.
“Yeah, duk abin da ki ke takama da shi su _ ma
sauran matan suna da shi, sannan don kuma a
rashin kunya za ki nemi rusa min kwanciyar , :
hankalin iyali don kawai kin ga ina kyale ki?
Wallahi I will surprise u matukar ki ka Kara shiga,
hurumin Saudat zan iya yi miki komai, Sannan da
kike kiranta da matsiyaciya, kodaddiya, ai Saudat
ta fiki komai a idanuna kuma don ina sonta na
aure ta kamar yadda kema nake
sonki na aure ki, kuma duk wani shirmenki da
haukanki ba zai sa na rabu da ita ba don ita ce
rayuwa ta, wallahi tun ranar da naga tausayina. a
cikin idanunta na soma jin soyayyarta a zuciyata,
kina tunanin'wannan soyayyar ta wasa ce?
Ki gafarce ni Asma, da gaske nake ina son
Saudat, wallahi I can anything please Asma ki
taya ni mu so ta in har da gaske kina sona“ Wani
inrin ihun kuka Asma ta saka saboda yadda ta
rinqa jin kalamansa na neman tarwatsa ' mata
zuciya, ta daga masa hannu cikin karaji tana
fadar, “Stop it... don’t repeat dis word to me
again please, ba sai ka bude baki ka fada ba zan
gane ka daina sona ba, ba sai ka fada ba Ahmad
zan fahinci ka gama dani ba, na yi condaim a
wurinka amma don Allah ka kyale ni haka da
wadannan zafafan kamalan naka masu qona min
zuciya da sassan jiki”.
Dr. Ahmad ya koma kan gadon tare da rungumo
ta yana fadar, “Please Asma, wallahi ban fada
miki wadannan maganganun don ranki ya Baci
ba, iya gaskiyata nake fada miki, kuma ki daina
fadar na daina sonki, wallahi har yau har gobe
sonki yana nan a zuciyata, kuma a shirye nake da
na ninka shi idan har ki ka gyara halayyarki, ki
tuna fa ke din mai ilimi ce amma ki rinka
abubuwan da mai hankali ba zai yarda da su ba,
haba Asma”.
Kukanda ta ke tare da sauke ajiyar zuciya shi ya
tabbatar masa kalamansa suna shigarta, ya dago
da kanta ya Dora a kan kiirjinsa yana share
mata hawaye, tare da gyara mata gashin kanta
cikin _ sassanyar muryarsa ya ci gaba da fadar,
“Am sorry
Asma, ki yarda da mi wallahi har yanzu ina sonki
idan har ki ka sauke gadara da girman kanki zaki
same ni a duk yadda ki ke so.
A yanzu Asma ta daina kukan sai dai sauke
numfashin da ta ke, Dr. Ahmad ya janye ta daga
jikinsa ya barta a kan gadon ya nufi bandaki ya
hada mata ruwan dumi da beltn robb sannan ya
fito ya kinkime ta ya nufi bandakin da ita Sai da
ya watsa mata ruwan ya wanke ta sol sannan ya
fito da~ ita da kansa ya Ciro mata kayan
baccinta ya bata ta saka, sannan ya kamo
hannunta ya kwantar da ita a. kan gadonta ya ja
lallausar bargonta ya. lulluba ta ya kashe wutar
dakin tare da furta mata sai da safe.
Ba ta da yadda za ta yi tana jinsa harya fice duk
yadda ta so danne zuciyarta sai data fashe da.
kuka, don ta sani a yanzu Ahmad ya yi mata
nisa, ta riga ta yi sake har dan hakin da ta raina
yazo ya tsone mata ido, duk yadda zuciyarta ta‘
kai ga. chashewa a kan al’amarin fa namiji a
yanzu ba ‘abin da tafi bukata sama da shi k0 don
ta lura yana neman subuce mata? ne
’ ’ Yau din nan ta kasance mata rana mai muni
saboda kunnuwanta sun jiye mata mummunan
albishir din rasawanda tafi so fiye da kamai a
rayuwarta, kuma yau ne rana ta farko data
fahimci.
rashin kyautatawarta a zamantakewarta da
mijinta kuma a yau ne ta gane kuskurenta bayan
ta
rasa shi, kuka ta ke sosai tare da nadama marar
amfani. . .
Asma mace ce mai zafin kai da izgili da raina
mutane, ba ta da son jama’a k0 kadan shi ya sa
ma k0 abokai ba ta da su, sai dai tana da
raguwar zuciya, ba ta da juriya ko kadan nan da
nan damuwa ke wujijjiga ta saboda ba ta saba da
ita ba, don haka a yanzu tunaninta guda,
hanyoyin da za ta bi don ganin ta karkato da
hankalin mijinta a kanta sun koma irin zamansu
na farkon aurensu.
Bangaren Saudat kuwa tunda ya fita ta tsinci
kanta da wani irin matsanancin kishi da damuwa
ta gagara runtsawa, sai faman juyi ta ke tana
duba agogo, amma har sha biyu saura bai shigo
ba, zuciyarta ta ba ta yana wurin Asma, to me
suke har yanzu da bai dawo ba? Wannan tunanin
ne ya sa ta ' soma ‘yar kwalla, sai karfe daya
saura kwata na dare ta ji ya turo Kofa, hakan
yasa ta saurin jan bargo ta lulluBa tamkar mai
bacci, tana jinsa ya hayo kan gadon ya ja ta
jikinsa ya kwanta tare da lulluBe su da bargo ya
soma shafar kanta yana kiran sunanta, amma ta
Ki motsawa tana jinsa har ya gaji ya yi shiru, a
haka bacci ya yi awon gaba dasu
‘ Da asuba ma suna kammala sallah Saudat ta
mike za ta fice taji muryarsa na fadar, “Ina kuma
zakije?”
Saudat ta dan waiwayo kadan kafin tace'
‘Bangarena” . .
Ya dan harare ta,“ “Okay nan din da yake
gutsirarki ake k0? To dawo ba inda za ki". ~
Kamar kada ta dawo din hakata daureta ' koma
kan gadon tana kokarin hawa ta kwanta ta ji ya
tisgota ta fada kirjinsa, har tana buge fuska. Ya
dago kanta yana fadar, “Wai fushin me ki ke da
ni? Saudat laifin me nayi tun jiya ‘da na fita na
dawo na lura kinata kumbura shiyasama nayita
magana ki ka share ni, ki ka nuna bacci kike, oya
fada ‘ min menene? '
Saudat ta kasa tankawa saboda irin riqon da yayi
mata, dakuma rashin takamaimain amsarda zata
bashi don tasan babu abin da ke damunta,
wandayawucc kishi, dakunya kumatadubeshi ta
'fada masa hakan, saidai damamakinta tajiyana
fadar, “Kishi ne ko Saudat? To sha kumruminki
Ahmad naku ne kubiyu, kuma soyayyarki daban
ce acikin zuciyarsa. Ki sani ni Ahmad ban buqatar
kowa tunda na same ki, ban bukatar abinci in dai.
inajin muryarki, bani da bukatar ruwa matukar ~
akwai miyau abakinki banbukatar iska indai
'akwai numfashi acikin kirjinki bananeman komai
tundana sameki,karki kara damuwa balle har
shaidan ya cusa miki wasu al’amura kisa. a
zuciyarki kedin matata ce wadda nakc so’in
Asma matata ce wadda nake so, dukkaninku an
halicce ku ne da hakarkarina kuma kowaccenku
tana bukatar farin cikinta daga gare ni, idan na
wulakanta dayarku saboda 'daya ki sani Allah ba
zai bar niba please Saudat ina so in yi adalci a
tsakaninku”. Saudat ta lumshe idanunta tare da
kwantar da kanta a kan kirjinsa tabbas abin da ta
gani cikin idanunsa ya tabbatar mata da
haqiqanin gaskiyar da yake fada, ya kara matse
ta a jikinsa ta ji tamkar za ta rabu gida biyu ta
bude baki da hanzarinta, .tana fadar, “Wayyo
Yallabai, za ka karya ni”. maimakon ya sassauta
mata rikon sai ‘ma ”ya qara matse ta a qirjinsa
ta yadda .Saudat ke jin bugun zuciyarsa da sauri
da sauri cikin wata irin , rikitacciyar murya ya
soma fadar, “Yi haquri don Allah Saudat, wallahi ji
nake tamkar in maida ke cikin jikina don Allah
Saudat duk abin da ki ka zama a rayuwa kada ki
Juya wa zuciyata baya”. Wani irin abu ya rinqa
sukarwa Saudat ‘a Zuciya, tausayinsa ya kashe
mata dukkanin gaBobin jiki, duk da ta fahimci ya
saki layi amma hakan bai hana ta rungumar mijin
nata ba, wanda ta kejin *tamkar a yau ne ta
soma sonshi. a Cikin sati guda Saudat ta yi
matukar shaquwa" da Dr. ta saki jikinta da shi ya
koyar da ita darussa masu yawa, takuma bude
kwakwalwarta
ta dauka ba ta zubar da su a kwandon Shara ba,
duk abin da ta lura'ya fiso atareda ita shi ta ke
masa, har ma ta kara da kalar' nata salon don
qarin ~ armashi. ‘
Yau ta tashi da son shiga kicin duk da kuwa yau
din ne miji zai bar hannunta ya koma gurin Asma,
tunda kwanakinta sun Kare, so ta ke ta yi girki da
kanta, duk da ba wasu abubuwan kirki ne ta iya
ba a bangaren girki, to amma gani ta ke gwamma
nata girkin sau dubu a da wanda kuku ya yi musu
daren jiya, wanda ya sa ta amai babu ' gaira
babu dalili, shi kansa Dr. bai iya cinsa ba da ya
kira kukun don jin abin da ya girka musu, sai
cewa ya yi tuwon alabo ne da miyar manja,sai
drinks din kayan itatuwa da madarar ‘ruwa, da
danyan kwai, girkin sai kana Kasashen qetare.
Abin da ya qara tayar wa Saudat da zuciya kenan
take ta sa ya shigo kicin ya nuna mata yadda ake
amfani da kayan na’ urorin kicin din nata har Dr
na musu dariya.
Don haka yau tunda sanyin safiya ta gama
shirinta cikin wata doguwar rigar shadda ash
colour wadda aka yi wa aiki tun daga sama har
qasa bata daura kallabin rigar ba sai dai ta daura
qan qaramin mayafl a kanta wanda ya tsaya iya
kafadarta, ta
zura takalminta flat shoe ash colour sannan ta
fice; ta nufa kicin din ta bar Dr nata sharar
baccinsa.
Sai dai ba girin-girin ba ta yi mai, ga shi dai babu
abin da babu ta bangaren kayan .abinci tun daga
na gida Najeriya har zuwa na kasashen qetarc sai
dai ba ta san yadda za ta sarrafa suba.
Can dubara ta fado mata ta yanke shawarar ta
girka musu alala da kunun gyada don a nan din
ta san ita gwana ce don kuwa sune sana’ar Inna
Laure, don 'haka ta nufi store ta debo wakenta ta
zuba a turmin ta sa ruwa ta surfa sannan ta nufi
wurin famfo ta wanke shi ta fitar da dusar ta
bude freezer ta debo kayan miya wadanda suka
daskarar da Kankara ta gyara su ta zuba a cikin
wakenta, ta ' sa a blander ta markade suka yi
laushi sosai sannan ta juye a roba mai fadi ta
kawo spices ‘kala-kala ta zuba ta yanka
alayyahu da albasa masu yawa, ta zuba ta sa
manja da mangyada ta motsa sosai sannan ta
daddaura a fararen ledoji ta zuba ruwa. a
tukunYa ta zuba alelenta a ciki ,ta dora a kan
gascooker sannan ta koma ta debo kullun
gyadarta ta dama kunun gyada sannan ta koma
tana gyara kicin din nata.
Dr, wanda ya farka ya laluba ya ga ba ta nan .
ya mike ya nufi bandaki ya watso ruwa ya fito ya
’shirya cikin qananan kaya bulue din jeans sai
milk din T shirt ya gyara sumar kansa, sannan ya
zura silifas dinsa na fatardamisa ya fice kai tsaye
kicin din ya nufa, ya ja ya tsaya ya tokare
bayansa da
qofar kicin din tare" da zuba hannuwansa cikin
aljihu yana kallonta. " Saudat ta juyo tana
kallonsa lokacin da ta
gama jera abincin a kan tebur din bakinta dauke
da murmusln ta ce “Bismillah mana, ya za ka ci
irin girkina, don Allah ka shigo”
Ya tabe baki yana kallonta tare da make kafada
alamar ba zai shigo din ba.
Saudat ta nufe shi ta riqo hannayensa tana
fadar, “Don Allah ka shigo ka gani ka taBa cin
alala?” Bai tanka ba hakan kuma bai hana ta
jansa ba har bakin‘ dinning table ta ja masa
kujera ya ‘ zauna sannan ta budr kula ta ciro
masa alala kwara biyu ta sa masa a faranti, ta
tura masa tare da cokali mai yatsu ta zuba masa
kunun gyada wanda ya ji madara ta mika masa
tare da cokalin shan tea, ta , langwaBar da kai
tana fadar, ‘Don Allah kaci kaji na iya?” Murmushi
ya yi kafim ya cokana cokalin ya . soma ci bai
tanka ba sai da ya cinye duka biyun tana zaune
tana kallonsa zuciyarta cike da jin dadi, > ita ma
ta zuba nata ta soma ci.
Yana cinyewa ta dube shi na Karo maka, ya
waro ido, “Haba Madam tausaya min bani dai
kunun insha”.
Ta miKa masa ya sa cokali ya soma sha a
nan fa ta ga santi ya dube ta, “Amma wannan ‘
kunun da madara ake yinsa k0?”
Saudat ta girgiza masa kai alarnar a’a, ya jinjina
kai, “Amma Allah wannan ana iya bude kamfani a
rinka yin na roba a rinqa siyarwa, ba qaramin
ciniki za a yi ba don ‘ni ban taBa shan irinsa ba
fa”. '
Saudat ta tuntsure da daniya, ta ciro mayafin
kanta ta nufe shi tana fadar, “Kai yallaBai bari in
yi maka waigi kada ka fadi”.
Ya tuntsire da dariya tare 'da riKo ta yana
Kokarin kwace kallabin suna dariya, nan fa
kokawa ta kaure basu suka baro kicin din ba sai
sha biyu saura, ya tsaya a falo tare da fadar,
“Jeki dauko key din motarki mu je in miki
rijistireshon din makaranta daga nan mu je
islamiya in sai miki form sai mu wuce Hikima
Driving School a nan za su koya miki
tuKi tare da shaidar yin tuqi idan ba mu yi
yammaci ba sai mu wuce mu gaida Momy”.
Dadi ya cika'Saudat ta makale shi tana murna,
sannan ta yi falonta da gudu ta dauko key din ta
fito, yana nan tsaye inda ta barshi ta dafo
kafadarsa kamar irin abokinnan nata, duk da
kasancewar ya fita tsawo amma‘ ita ma din
doguwa ce, haka suka fice tana ta zuba masa
shagwabanta, shi kuwa sai Kara narke mata yake
ita kuma tana
Kara sangarcewa, shi da kansa ya ja su a motar:
kasancewar mai bakin gilas ce Sai da suka fara
zuwa wani studio aka yi mata passport sannan
suka wuce
social. development ya yi mata rajista da komai
da
kornai, suka wuce islamiyya nan ma ya siya form,
a
take ya yi mata komai, suka wuce Hikima ba su
suka kammala da komai ba sai shidda saura na
maraice, sannan Dr. ya nufi gidansu da ita.
Sun yi sa’a kuwa Faridat ta zo don haka 'Saudat
ta samu tattali da kulawar da ta dace daga
Momy din har Farida zuwa Daddy kowa sai
riritata yakce, ana wasa da dariya a nan nema
taji’ Dr. zai yi tafiya jibi zuwa qasar Singpore ya
yi sati biyu ya dawo majalissar Abuja, ya kwana
guda sannan 'ya wuce America ya yi sati guda ya
biyo ta Mexico city
ya yi sati guda sannan ya wuto gida.
Zuciyar Saudat ta yi mata ba dadi don a yanzu ta
riga ta saba da mijinta ba ta qaunar abin da zai
sa ya yi nisa da ita tun a lokacin ta soma jin ta
fara missing dinsa basu baro gidan ba sai bayan
sallar isha.
Suna. dawowa kuwa ya wuce sashinsa, kai tsaye
Saudat bandaki ta nufa ta watsa ruwa ta fito ta
saka kayan baccinta riga da wando baqaqe masu
. Iaushi ta daure gashin kanta da ribbon kwara
guda
sannan ta zira takalnan baccinta masu laushi ta
fito falo ta fada kan kujera ta ja ipad dinta ta
soma
latse latse don a yanzu ta soma Kwarewa, duk a
warin'ta shigowar mijinta ta ke saurare
Shi kuwa tunda ya isa sashinsa ya watso ruwa
ya saka riigar baccinsa mai budadden gaba, ya
fito falonsa ya zaunakan kujerar falon ya ja
Karamin tebur na gilashi ya! dora computer dinsa
ya soma turn sakonni, a haka Asma ta shigo
falon ta same shi ya dago ya dube ta ta cikin
siririn farin gilashin da ke idanunsa, sanye ta ke
da kayan bacci skinny dress kalar suminti sun
mata matukar kyau tamkar saukar Kasar Saudiya
don da ma can Asma kyakkyawa ce ajin farko
Ta zauna saman kujerar dake gefensa cikin jan
aji ta soma fadar, “Sannu da aiki dear”.
Ya amsa da, “Yauwa, kina lafiya?”
Ta dan tabe baki kafin ta ce, “Lafiya na shigo
dazu ka fita” , Da kai kawai ya amsa mata ya ci
gaba da abin
da yake tsawon wasu ‘yan mintina falon ya dauki
shiru, Asma ta mike ta koma kan kujerar da yake
zaune, ta kutsa ita ma ta zauna ta raba jikinta a
kan bayansa ta kwanta tana fadar, “So nake na
kwanta da wuri saboda yau muna da wani
meeting na gaggawa, qarfe biyu na dare”.
‘ Bai tanka mata ba sai dai sakonnin da ta aika
masa a gab0bin jikinsa sun yi matukar tasiri
wurin saukar masa da kasala
, A dole ya rufe computer din ya mikar da ita ya
shureta ya nufi dakin baccinsa ya kwantar da ita,
ya
mike da niyyar yace yayi wa Saudat sai da safe,
Asma ta qankame shi tare da saka masa kuka
tana fadar, “Haba Ahmad, don Allah boron ya isa
haka, karka koma kana daukar alhakina, kana
kallo fa da ajina da qimata da 'martaba ta na-
karya su na z0 inda ka ke, amma ka Ki ka yafe
min kuskurena haba Ahmad ka yafe min haka
nan, don Allah wallahi ba
zan iya jutre wannan horon ba”
Duk yadda ya kai ga mazantaka a wannan karon
lamarin yafi karfinsa ganin kasawarsa ya sa ta
Kara qaimi wurin cakume shi tare da Kara kunna
shi da salon kissarta. ‘
Saudat kuwa da ta gaji da danne-dannenta ta ji
bacci ya some kwasarta ta duba agogo, Karfe sha
daya da ‘yan mintina ta lalubo wayarta ta soma;
danna masa kira tayi ringin harta tsinkebai dauka
ba,tasake danna masa wani kiran harsaidatakusa
tsinkewa sannan ta ji ya dauka cikin wata
dakusasshiyar murya yake fadar, “Saudat bakiyi
bacci ba har yanzu? Ki kwanta kinji dare ya...”
Din-din taji an datse kiran.
, Ta bi wayar dake hannunta da kallo tsawon
lokaci zuciyarta na barazanar tarwatsewa a haka
ta kwashe tsawon wasu mintuna kafin ta haurar
da [pad
din da wayar ta. nufi dakin baccinta ta fada kan
gado, kishi babu dadi, sai dai haKuri ya zama
dole tunda
Allah ‘ya. halicce mu Shi Ya halitta auren mace
sama da daya. ‘ .
K0 da Saudat ta farka da safe bata fito k0 bakin
aofar falonta ba, tana kudundune cikin bargo bata
sauko ba, haka Ahmad ya turo kofar falon ya
shigo.
Da sallamarsa yana sanye da wata tsadaddiyar‘
shadda gezna fara mai laushin gaske ta sha aikin
hannu, kansa na sanye da hula zanna baka kalar
aikin shaddar sai siririn farin gilashi a idanunsa,
ya daura bakar agogonsa ta fata wadda ta
kwanta ‘ lallausar farar fatar hannunsa wadda
bakin gashi ya yi wa kawanya. ‘
Ya yi matuqar kyau musamman yadda fuskarsa
ke cike da annuri ya zauna bakin gadon da take
kwance tare da yayc bargon da ta lulluba ganin
kayan barcine a jikinta ya sa shi saurin duban
ago gon dake girke saman bed side drower, qarfe
sha biyu da rabi ya waigo yana kallonta lokacin
da take gayar da shi, bai amsa ba sai dai ya jefe
ta da tambaya, “Lafiyarki Saudat, baki da laflya
ne?” .
Ta girgiza masa kai ba tare da ta bari sun hada
ido ba, tace, “Lafiya ta Iau.
' Ya girgiza kai, “Yarinta na damunki Saudat,
yanzu don kina jin haushina shine ba zaki tashi ki
wanka ki gyara jikinki ba?”
Ya dan ja wani siririn tsaki, “To tashi tunda. *gani
nazo kije kiyi wanka kigyara jikinki
Saudat ta dauke kai cike da kunya. ta ce “Ni fa
ba. yanzu zan yi ba” .
Yace “Tokuma wannanne kobaki isaba". Ya sa
hannu ya janyo ta tana turjewa, ya
kyaleta yana fadar, “Kwanta keki ka sani qazama
ke zakita tsami bawaniba donni kuwayanzu
Katsina na nufa inyi wa su Momy sallama don so
nake inyi isha agarinnan kuma zankai kararki
wurin Momy infada mata baki wanka bare
kwaliiya... ”
Tun kafin ya rufe baki ta zabura ta tashi za ta
dafo shi ya yi saurin mikewa yana fadar, “A’a
qazama kar ki sake ki taBa ni ki bata min
kwalliya, na yi wankana”
‘ Saudat ta bi shi tana kokarin ya tsaya ta ba shi
sako wurin Momy, amma bai kula taba, ya fice
yana faman tsokanarta.
" A dole ta dawo tunda kayan bacci ne a jikinta
ga shi

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login