Showing 21001 words to 24000 words out of 103547 words

Chapter 8 - YAR TALLAH complete

Start ads

Unknown   

24 Aug 2025

400

Middle Ads

kafin ya ce, “Ki yi hakuri kar kice na fiya shishshigi da yawa;”
' Saude ta dauke kanta kafin ta ce, “Lafiya dai ko?
‘ “Lafiya kawai dai ina so inxo in Kara duba kine don ban sani ba ko wani abu ya same ki.”
Saude ta wuce shi tana fadar, “Ni babu abin da ya same ni.” Hamid ya yi tsaye yana kallon tafiyarta hatta kusa Bacewa ganinsa, ya ja wani taqaitaccen murmushi
murmushi mai sauti tabbas yau zuciyarsa ta samu abinda takeso,zaicigabada binta harya samu ya samo kanta. Ya juya ya shiga motarsa ya bi ta a baya harkofar gidansu ya rakota batasanai ba, sannan ya koma abin sa.
Saude nashiga gida, Laure ta bitada kallo kafin ta ce, ‘Wai kin je gidan nasu kuwa?”
Saude ta daga mata kai alamar eh laure ta yatsina fuska kafin tace “Amma abinda mamakine da akace min amaryarsa mugun kishine da ita aina dauka sai sun karya miki qafar baya.” Ta ja tsaki mts!
“Sai ki wuce kafin tallar yamma ta qarisa
Saude ta wuce dakinta simi-simi ba tare da ta sake tankawa ba. Tana shiga daki ta kwanta, wani irin abu ya tokare mata zuciya, ta lumshe idanuwanta fuskar mutumin nan ce ke mata gizo, har yanzu hancinta baidaina shakar kamshin turarensa ba mai sanyin kamshi.
Dama yace yanasonta tabbas da saitayi kukan dadi. Makaskanciya irin ta a ce irin wannan namijin yasota aidakamar wuya wai gurguwada auren nesa. K0 ‘Yar Baba da ta fita komai ba ta samu kamarsa ba, ballantana ita mafi kaskanciya mai tsananin rauni Taja wani gwauron numfashi tare da
saurin kawar da abin dake zuciyarta, don ta san k0 a mafarkinta hakan ba zai taba samuwa ba.
Washe gari Saude ta dawo daga tallar safen ta, sannan ta dauro alwala ta yi sallah; sannan ta fita’ tsakar gida ta zauna, Laure ta sauke alalar aka zazzage mata a bokiti ta dauka ta fice abin ta.
Hanyarta ta kullum yau ma ta ita ta bi idonta na saman hanya ta wuce ta qofar gidan Alhaji Bashir, Hamid da ke zaune saman teburin maigadi ya ga tahowartaya zabura ya mike, ya dubi Malam maigadi yana fadar.
“Ina zuwa Baba bari in dawo.” Bai jira abinda zai ce ba ya yi saurin bin ta dan kar ta Bace masa.
Saude ta tsinci muryarshi na fadar. “Assalamu Alaikum. ” Ta waigo tana kallon shi da mamaki a fuskarta ta
kasa bude baki balle ta iya furta wani abu, Hamid ya yi murmushi kafin ya ce, “Ruwan zuma ne ni ba madaci ba na kasance mai began ki tun a lokacin da na soma ganin ki ba wai sha katafi ba, mene na tunanin a kan hakan?”
Saude ta fara nutsuwa tana kallon kyakkyawar fuskarsa, wadda ta qawatu da dogon hanci da yalwatattun idanuwa wata nutsuwa 'ta dirar .mata muryarta a sanyaye ta ce, “ZaBina ba tsakanin zuma k0 madaci ba ne, kyakkyawan zabina shi ne yawaita ayyuka, masu kyau da gujewa munanan dabi’u na kasance mai zurfin tunani da. Kwakwalwa ba da zuciya‘ ba, me ye tunanin ka a kan hakan?”
Hamid ya dan saurara kafin ya ce, “Ikon Allah ga .shi nima yanzu haka Dady jirana yake, amma ba damuwa, ki fada masa zuwana gobe insha Allahu
zan dawo.”
Saude ta amsa da to, sannan ya juya ya tafi ta raka shi da idanuwanta.
Ikon Allah mai tsaida wando ba zariya. Mamaki da al‘ajabi su suka dabaibaye zuciyar Saude, har yanzu bata fidda ranta da cewa mafarki take ba, za ta iya farkawa a kowane irin lokaci. Ba
Washe gari Saude ta dauki tallar wainar .ta. Bayan ta siyar karfe sha daya da ‘yan mintuna ta dawo, Laure ta hada' ta da sanwar alala duk da matsananciyar ranar da ake kwalawa haka ta zauna a tsakar gidan gaban murhun sai gumi ke tsiyaya a jikinta.
Tamkar daga sama yaro ya shigo ya yi sallama, Saude ta amsa tana kallon shi, ya ce, “Wai' ana sallama da Malam in ji wani mutum a waje.” Saude ta nuna masa dakin Laure da hannu tana fadar.
' “Shiga can ka fada masu.”
Yaron ya wuce ita kuma ta ci gaba da abin da take, yaron bai yi minti biyar da fita ba Malam Bala ya fito cikin shirin tafiya masallaci kasancewar yau
Juma‘ a bai fita kasuwa da wuri yasa kai ya fice Tsawon wasu mintina da suka haura goma zuwasha
biyu sannan‘ ya dawo gida yana faman Kwalawa
Laure kira‘ . “Laurel Laurel! Laure!!! Wai kina ina ne nake ta
faman kira kin yi shiru
Ta hankado labule ta fito tana fadar, “Wai ya akai ne, ka keta faman kwala min kira sai ka ce yaki?”
Malam Bala ya yi kwafa, “Amma dai ai kin san ruwa baya tsami banza, kin san dai daga jin kiran‘ nan kin san da walaki.” Laure ta ce ‘To mu gani a qasa
Ya ce, ‘Tabarma zaki ba ni dan gidan Alhaji' Bashir ne yazo wai wurin ‘yata yana son a bashi izinin turo iyayensa maganar aurenta.”
Inna Laure ta zaro qananan idanuwanta haqoran nan suka yo gaba sai ka ce kamfanin cokula ta ce “Kai don Allah yana ina? ’
Malam ya ce, “Yana waje
“A’a bari a kai masa tabarmar.” Ta juya daa ‘hanzarinta ta nufi daki ta janyo masa tabarma bayan qaure ta fito fana fadar.
“Ga shi Malam ka shimfida masa a soro gatanan zuwa.” Ya amsa ya juya da hanzarinsa har yana tuntube
Inna Laure ta nufi dakinta can kurya kan gado bonanza ta shiga inda ‘yar Baba ke kwance tana faman sheka baccinta Inna Laure ta shiga tashinta.’ ‘Yar Baba ta bude ido da kyar cikin magagin barci. ‘ ‘
Ki tashi da alla kin ji aikhairi yazo mana har ‘ cikin gida, da rana tsaka.”
IKilima ta ja wani’ tsaki ta juya daya barin ta ci gaba da baccinta, Inna Laure ta Kara bubbuga ta Ta zabura a fusace.
“Wai mene ne don Allah za ki dame ni kawai ina baccina
Inna Laure ta ce, “Ki tashi banza arziki ne ya zo mana da qafafuwansa dan gidan Alhaji Bashir yaron nan ya z0 wai neman auren ki tashi banza, banza ki shirya.”
‘Yar, Baba ta zabaura ta tashi zaune idanuwanta a warwaje tana fadar, “Kai Laure don Allah da gaske ki ke?”
Laure tace, ‘A’a ai sai ki tashi ki gani da idon ki yana soro shi da Babanki.”
IKilima ta buga wani uban tsalle ta dire daga kan gadon, saboda doki, ta kwasa da gudu zata fita Laure ta yi saurin riqo ta.
“Ke da Allah tsaya haka za ki je sai ka ce wadda ta tabu, ai sai ki ja ya ce ya fasa, maza ki shirya da Allah karya gaji da jira. ’
‘Yar Baba ta dan nutsu kafin ta ce, “Ba za ki gane bane Laure yaron ya hadu yanda ba ki tsammani kyakkyawa ne, kuma dan gayu, daga qasar waje fa ya dawo ya kammala digiri dinsa. Laure idan na aure shi wallahi na gama more miji, ai duk samarina
korarsu zanyi "Ta dan yi shiru kadan kafin ta ce
“To wai ma me zan sanya?” Laure ta ce, “Ki sa wannan shaddar taki sabuwar
Ginznar nan tana yi miki kyau sosai.”
‘Yar Baba ta kada kai alamar ta game, sannan ta juya ta bude akwatinta ta Ciro shaddar dinkin riga da siket ne ya sha aiki matuka, ta saka kayan wadanda suka dame ta matuka komai na jikinta ya flto. ‘
Ta zauna ta yi kwalliyarta sosai ta kawo dankwalinta ta 'kafa daurin‘nan mai suna ture-kaga tsiya, sannan ta saka dan kunne da sarka, ta mike ta janyo wani dan ficicin gyalenta mai kama da matacin koko saboda shara sharansa ta yafa, ta saka takalminta mai tudun dunduniya ta saka, ta dauko wata gingimemiyar jaka saikace waddazatabiki ta rataya a kafadarta, ta juyo tana kallon Laure tana wani murza idanuwa.
“Toya kika ganni?”‘
Laure ta ce, “Kin hadu qarshe ‘yata ai shi yasa nake qara son ki, dan kuwa kyan ki daban yake dana sauran mata shi yasa kullum sai an mana sallama.”
IKilima ta sheke da dariyar jin dadi na kwarzantawar da Lauren ta yi mata ' Malam ya hankado labule “Wai me take Jira ne har
yanzun kunsam jirafa bashi da dadi
Inna Laure ta ce, “Ai ga ta nan fitowa Malam, ya yi hakuri. ” Malam Bala ya saki labulen ya juya
‘Yar Baba ta dubi Laure ni“Na tafi Laure.”
“A’a mu je in taka miki.” Laure ta fada tana yake hakora.
A tare suka fito, Saude na durkushe a gaban murhu sai faman hawaye take saboda hayakin da ya turnuke ta, har ba ta iya ganin gabanta sai sharbar' mijina take.
Suna isowa inda take Laure ta dube ta, ‘To ‘yar iska munafuka wutar ce ba za ki hura ba k0 so ki ke alalan ta jike a cikin ruwa, annamimiya munafuka.’ Ta duma mata wani uban kulli wanda ya sa ta yunkurin amai ta zabura ta mike tana faman sosa inda ta 'maka mata dundun. .
Ta ce ‘Wallahi Inna itatuwan ne danyu sun ki su kama.”
Inna Laure ta haure ta da kafa, ‘Kan ubanki ke da danyun yanzu dan kina munafuka wadannan itacen' sune danyun,to idan ma kinbarta tayi danya dan kanki,danni yaddah kika fita da ita haka zaki saida ta ko ta kwabo ban ce ki dawo da ita gidan nan ba, wuta kuma kar ki hura ki yi shekaru dubu anan
Saude ta surce majina tare da goge ruwan hawayen da ke zuba daga idanuwanta, ta duke. ta ci gaba da hura wutar da baki, amma illahirin zuciyarta
LOL YA abin yake NE GUN WA HAMID YAZO IKILIMA KO SAUDE
MUCi GABA Dakasancewa DA ADmin Dboy DONJIN yadda WANNAN TAQADDAMA ZATACI gaba DA KASANCEWA
[1/19, 5:11 PM] I love my mum: 📚📚DAGA GROUP OF HYPE HAUSA NOVELS BOOK WHATSAPP 08064400100📚📚
[12:17PM, 02/02/2017] 🙆🏼‍♂@lh@ji🙆🏼‍♂: [1/19, 5:14 PM] I love my mum: *YAR TALLA*

*CHAPTER 13*

a cunkushe take saboda duk abin da ake tana jin ‘Yar Baba ta tabe: baki ta wucc soron gidan, Saude ta tsaya da hura wutar tana kallonta idonta ya ciko da hawayce
Hamid yana zaune a barin tabarma yana karkada kafafuwansa ya yi irin zaman nan na masu cin tuwo, ‘Yar Baba ta jingina da bangon soro ta kafe shi da ido cikin ido tana wani murmurtsa idanu.
Hamid ya tsaya yana qare mata kallo cike da mamamki ya ce, “Ke kuma fa wace ce?”
‘Yar Baba ta‘yi wani qasaitaccen murmushi irin na gogaggun yan duniya kafin ta ce “Ai ni ce iKilima wadda aka fi kira da ‘Yar Baba, da alama baka gane ni ba ko?” Ta Kara jan wani munafukin murmushi tana fadar.
“Kowa ma idan nasa kayan nan haka yake fade: beganeni:ba ashe dama haka nake da kyau hummml Kayan suna mini kyau sosai.”
Wani takaici da haushi suka kama Hamid cikin takaici ya ce, “Ke da Allah saurara kin ji bana can shirme da sakarci kin, Saudat na ce a kira mini ita nake nema ba wai keba kin gane? ’
‘Yar Baba ta ji tamkar ya watsa mata ruwan zafi a zuciya cikin Bacin rai ta ce, “Ai ba ita Baba ya ce kana nema ba ni ya ce kana nema
Hamid ya dan sassauta murya, “Kin ga kiyi hakuri don Allah ki je ki kira mini ita ta sanda zuwana please ban san ku biyu bane a gidan."
‘Yar Baba ta waro ido tana kallon shi bakinta na fadar, “Kutumar... wallahi ba zan je ba har ma ta isa in kula ta ‘yar tallan gidan namu ba zan jeba wallahi, sai dai ka daskare a nan.’
Ta juya za ta tafi Hamid ya yi wani murmushin takaici ya zura hannu cikin aljihu ya ciro kudi‘ yan dan biyar biyar sababbi dal guda hudu ya miqa mata.
‘An shi ga wannan ladan kiran nata idan ba za ki kira ta don Allah ba. ”
‘Yar Baba ta sa hannu ta fizge kudin tana fadar, “Ai raba mugu da makami ibada ne” Ta juya ta yi cikin gida.
Laure ta tarye ta tana fadar, ‘Ya akai ne?"
‘Yat Baba ta fashe da kuka tana fadar, “Wai Laure wai ba ni yake so ba, wai SAUDE yakeso.’
Laure ta ja wata ashariya ‘Kan habbm.... Bake yake soba uwar wa yake so?”
‘ “Yar Baba ta nuna' mata kudin da ya 'ba ta, “Kin gama waiyabani inkiramasa ita
Laure tace daukomin mayafina naje na sameshi ‘Yar Baba ta kwasa da gudunta ta dauko mata mayafinta ta baza saman kafada ta nufi soron kamar an hankada ta.
Hamid yana zaune hmnunsa riqe da qatuwar
wayarsa yana wasa da ita, yana ganinta ya fadada fuskarsa da fara’a.
“Sannu da fitowa Umma barka da rana.’ Inna Laure ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa
sannan ta gyara tsayuwarta tana fadar, “Kai ne bakon Saude?”
Ya dan sunkuyar da kai qasa alamun kunya kafin
ya ce “Eh nine Umma.”
Laure ta kuma gyara mayafinta mai kama da an kwato shi daga bakin kura ta ce “To Saude dai da ka ke ganinta shegiya ce ‘yar gaba da Fatiha, ce yarnan da ka gani kuwa ni ce mahaifiyarta nina haife ta da cikina, kuma ka san an cewa shi dan gado sai ya zarta to Saude kuwa har tace ban iya ba, dan wurin gantali da yawon bariki gari gari babu inda Saude bata zaga' ba. Kai in taqaice maka har cikin shege sai da ta yi.’
Wani irin abu ya dakarwa Hamid zuciya mai zafin gaske ya samu da kyar Ya iya hadiye shi kafin ya iya fadar, “Amma Umma da mamaki a gaskiya ba zan Boye miki ba Saude ba ta yi wa rayuwarta adalci ba sululu kenan macijin sari ka noqe
Ki yi hakuri Umma insha Allahu ba zan guje mataba don wannan qaddarar ta fada nayi
miki aIqawarin auranta a hakan in ceto rayuwarta.”
Laure ta ce, “A’a ahir!.Dinka karka fara don ba zaka taba iya ceto Saude ba saboda kin Allah irinna yarinyarnan ya wuce tunanin ka” Laure ta sa kukan munafurci har da su fyace majina.
Hamid yana kallonta saidata gaji dankanta ta dan sassauta ta ci gaba da fadar, ‘Dan nan shu’umancin Saude yana ci min zuciya wai yarinyar hartasan tanemi mace ‘yar uwarta,bacin mazan datakebi yandakasan karyar mazahaka take.
Na zubarwa Saude ciki yakai biyar a asibiti har sun haddace mu, sun gaji idan mukaje ma yanzu kararmu sukace zasuyi wai saboda zubdawa Saude cikin da muke yakai iyaka.”
Hamid ya ce“Duk wannan ba matsala ba ce Umma, wallahi ahakan insha Allahu indai saude mai shiryuwa ce sai na shiryar da ita.”
Inna Laure tace, “Kai malam,Saude bazata taba shiryuwa ba saboda ba ta tsoron Allah k0 kadan babu Allah a ranta.”
Hamid ya ce “Ai Umma Islamiyya zan sanya ta insha Allahu kekanki saikinyi mamakin yanda zata shiryu ta nutsu.”
Inna Laure tace“Dannan kenan bakasan Saude ba har yanzu, ai kwakwalwarta a dode take ba
ta daukar komai ba ka da abin da Saude ke iya dauka ballentana harta iya haddace shi.’
Ya ce, “Ai Umma babu abin da yafi qarfin addu’a, sai mu taya ta da addu’a insha Allahu za mu yi nasara amma ni ina son ta kuma wallahi aurenta zanyu
Inna Laure ta harzuka cikin haushi ta ce “Tokai baza,a auramaka itadinba ‘yatadaicetonayi mata miji koka tashi kabarnan yanzunnan wallahi k0 in maka ihu kwarto, dan iska kai ana gwada maka Annabi kana rintse ido.”
Hamid ya mike ya ajiye mata bandir din yan dari bibbiyu na dubu ashirin ya ce, “Zan tafi Umma ga wannan a sai sabulu zan dawo sati mai zuwa da fatan za ki sauko daga dokin qiyayyar da kika hau, na gode
Ya juya ya fice daga soron ya bar Laure tsaye dakam tamkar wadda aka kafe sai zazzare na mujiya take a kan kudin, wani abu na yi mata zarya a zuciya ta duke ta suri kudin ta yi cikin gida tana kwalawa Saude .kira Sande da take duke gaban murhu ta yunkura da niyartatashi, amma ina dukanda Laure ta soma
kai mata yasa ta duke babu shiri, Laure ta janyo
bakin wuta tana faman dukanta sai ka cc yaqi fidi
take. “Yau sai na kashe ki har lahira in ga ta
soyayya, ke nan har kin isa wani ya ce yana son ki a hakan. To idan ma farar fatar ce ta janyo shi yau
sai na lalata ta.” Tun Saude na ihu har ta soma Kokarin kwatar
kanta, ‘Yar Baba ta tare ta tana fadar, ‘Laure fuskar za ki toya ki lalata mata ita mu ga ta kyau da iyayi.”
Saude .ta sa wata irin kururuwa, ta kwace daga hannun ‘Yar Baba ta yi dakinta ta maida qofa ta rufe, tana jin Laure na fadar k0 ta bude ko ta cin nawa dakin wuta amma ba ta motsa ba.
Kuka take sosai kamar ranta zai flta, dan Laure duk ta tattaya mata jiki da bakin wuta abin ka ga jar fata duk jikinta ya yi jawur. Ai kuwa nan ta sulale Kasa ta zauna tana faman kukanta.
Tabbas ya zame mata wajibi ta cirewa zuciyana kwadayin wata rayuwa mai dadi, dan ta tabbatarwa kanta Inna Laure ba za ta taBa barinta
ba, tasa hannu tana sharar kwalla. Inna Laure ta sake bubbuga qofar tana fadar,
“Sai ki flto ki daukar mini talla ta in ba haka ba in karya kyauran in shigo.”
Yadda ta ke dukan kyauren da Karfinta ya tabbatarwa Saude za ta iya ma abin da ya fi hakan, ta ta miKe tana kallon kayan jikinta, tun leshin da ta saka ne ta je gidan Garba Gurgu ne a jikinta, har yanzu ga shi Laure duk ta qona shi. Ta dauki hijabinta ta sanya ta bude kofar ta fito, Laure ta kai mata wani duka tana fadar.
“’Yar iska munafuka!”
Ta watsa mata kayan hannunta, ‘Karbi maza ki canza kayan jikin ki duk wani abu da ki ka san na kwalliya ne a cikin dakin nan ki ki miqo mini shi yau sai na ga qaryar soyayya ai dai sai da kyan aka soyayyar ko to zan gani.”
Saude ta amsa ta koma dakin, wata kodaddiyar atamfa ce riga da zani ba dankwali, rigar sai a hada irinta mutum hudu su shiga ciki ga ta duk ta yage saboda tsufa. Sai zanin Jaka tsaye ya yi matukar shan jiki ya sha gamun baki har wuri hudu, ga shi babu dankwali 'sai wata abaya, hawaye suka ciko a idanuwan ta tausayin kanta ya kamata ta cire kayan jikinta ta sanya wadanda ta ba tan, sannan ta tattara komai na cikin dakin ta fito da shi.
Laure ta kwashe tana fadar “Munafukar banza, kuma wallahi ki sake in

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login