Showing 30001 words to 33000 words out of 87059 words

Chapter 11 - AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA

Start ads

Ashar   

11 Aug 2025

414

Middle Ads

iska ya ɗauke shi suyi sama su ɓace.

---------------------------------------------
See you next chapter Insha Allahu🤞
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 11

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚

A BANGAREN KHADIJA

Rufo kofar dakin tayi sannan ta zauna bakin gadon. Kuka Salmah take cen ciki ba'a jin sauti. Idan ta fara irin haka ba wanda yake iya lallashin ta, har Khadija ba abinda take iya fada da zai sassauto ta. Idan wani abun ya faru tafi son a barta taci kukan ta, hakan ne zai sa ta samu sauki a zuciyar ta kuma idan ta gama kukan zata manta da damuwar ta. Amma ganin ta cikin damuwa nasa ita ma Khadija na shiga damuwa. Amma duk da haka tafi son ace Salmah tayi juyayin ta anan kusa da ita da ace basu san inda take ba. Domin tsawon kwanaki kenan suna neman ta lungu da sako na garin, hakan ba karamin tayar da hankalin Khadija yayi ba, amma jiya wajen karfe uku na asuba lokacin da taji ana konkwasa kofa, nan da nan ta gane Salmah ce.

Fadawa jikin Khadija Salmah tayi tana kuka, lokacin da ta bude mata kofa. Khadija tayi kokarin jin inda taje amma taki magana. Tun.. jiyan shuru tayi taki magana. Tayi kokarin ta fada mata irin neman ta da suka yi ita da Ammar, amma bata nemi ta saurare ta ba.

“Na hada miki breakfast ko zaki ci?” Cewar Khadija.

Gyada kai Salmah tayi, sannan tace mata tana son a barta ita kadai kuma sai an jima zata ci abincin.

Ok, Khadija ta amsa da shi kafin ta fita daga dakin.

Zaunawa tayi falo tana jiran Ammar domin tuni tayi masa waya Salmah ta bayyana. Kuma yace mata yana zuwa nan da wasu mintuna. Salmah ta fada mata kar ta yi wani abun, amma ba zata iya hakan ba. Ba zata iya lallashin ta ba amma wata kila ta dan sauko idan suka yi magana da Ammar.

Sai da ta sake jira kamar na rabin awa kafin Ammar yazo.

“Sorry, na makale ne a gosulo.” Cewar Ammar lokacin da ta bude masa kofa.

Gaisawa suka yi sannan tayi masa iso zuwa ciki.

Ammar daga kallon sa zaka gane duk ya fita hayyacin sa. Dan kamar wanda aka kwato a bakin kura.

“Ina take?” Ya tambayi Khadija.

“Gaskiya tana cikin damuwa sosai. Kuma nasan zata ji haushi kan kiran ka da nayi. Amma nasan tana da bukatar ka a halin yanzu.”

“Kar ki damu Khadija zan yi iya kokari na. Nagode da kira na da kika yi.”

“Tana ciki.” Khadija ta fada tana nuna masa dakin ta.

Ok yace sannan ya nufi dakin.

Komawa Khadija tayi ta zauna a falo, cike da fargabar abinda zai biyo baya. Tana sa ran komai ya daidaita tsakanin masoyan.

Shiga dakin Ammar yayi cikin sanda. Ya tarar da Khadija kwance ta ba kofa baya. Yayi tunanin ko bacci take, amma yaji kamar alamun shasheka.

“Khadija nace miki sai an jima zan ci abincin. Ki rabu da ni please.”

“Ni ne.” Ammar ya fada a sanyaye.

Koda taji muryar shi, ta juyo ta kalle shi sannan ta tashi zaune da sauri. Ammar yaji ba dadi ganin yanda fuskar ta ta sauya tsabar tasha kuka.

“Me kake yi anan? Ka bar nan ko kaga bacin raina yanzu.” Khadija ta fada cikin sigar barazana. Shi kuwa Ammar ko a jikin sa domin baida tunanin tafiya yanzu bayan shafe tsawon kwanaki yana neman ta.

“Calm down please Salmah, magana kawai nake son muyi a nutse.”

“Ni kuwa nutsuwar ce bana bukata okay? Ka shafa min lafiya kawai. Kai ne mutum na karshe da zan so gani a halin yanzu.” Salmah ta fada da dan daga murya.

Fara matsowa a hankali inda take yayi.

“Ammar kar ka karaso inda nake.” Ta fada tana mai jefo masa pillow shi kuwa ya cabe kafin ya kai ga jikin sa.

“Na gane cikin bacin rai kike. Ki yarda da ni nima cikin tashin hankali nake. Bana bacci cikin dare, saboda rashin sanin halin da kike ciki. Ya kamata ki yarda da ni, ban fadawa mahaifiya ta komai ba game da ke. Na rantse miki da Allah.”

“Amma ai kai kadai kasan hakan. Ba zaka ce min taji bane haka kawai by chance dan ba yarda zan yi ba. Ka fada kawai kai ka fada mata, kuma kaci amana ta.”

“Ban san me zan yi ba dan ki yarda da ni. Please, kar ki bar wannan zancen ya ruguje mana soyayyar mu da muka gina.”

“Tuni komai ya ruguje, kana tunanin mahaifiyar ka zata yarda ka aure ni? Ko ba ka ji irin cin mutuncin da tayi min ba?”

“Ba mahaifiya ta bace zata aure ki, ni ne zan aure ki kuma ni zan zauna da ke. Idan muka yi niya zamu iya auren mu ko babu amincewar ta. Kasancewa da ke ni shi kadai ne buri na.”

“Ba zai yiwu ba hakan, ba zan so ka bijirewa mahaifiyar ka ba saboda ni. Kawai mu hakura mu manta da juna.” Ta fada tana goge hawayen fuskar ta.

“Mu manta da rayuwar da muka yi? Ko kin san me kike fada? Mu manta da duk wata soyayya da goben da muka tsarawa kan mu. Nasan kin fada ne saboda kina cikin damuwa.. amma ki bari zamu yi magana daga baya... Zan yi...”

Katse shi tayi.

“I'm sorry, amma ba na fada bane saboda ina cikin damuwa. Sai da nayi dogon tunani. Nasha wahala sosai a rayuwa ta, ba zan iya juriyar tunkarar mahaifiyar ka ba. Ta tsane ni kuma babu abinda zai canza hakan. Ina son ka da iya dukan zuciya ta da ruhi na, amma nafi son kaina a kan son da nake maka. Ba zan iya jure wannan tashin hankalin ba. Nasan zan shiga damuwar rashin ka, na kwanaki, watanni ko ma shekaru amma nasan dole wata rana zan manta da kai.”

Tsoro ne ya kama Ammar a halin yanzu, tsoron rasa Salmah. Sun sha yin fada har suce sun daina soyayya amma basu yin sati basu shirya ba, saidai basu taba yin irin wannan ba da gasken gaske.

“Please, ki daina..fadar.. haka. Kin min alkawarin jure duk wani abu da zai zo ya shiga tsakanin soyayyar mu.”

“Eh, amma ba zai yiwu ba wannan karon. Wata kila Allah bai yi ba ni matar ka ce. Kayi rayuwar ka.. nima naje nayi tawa rayuwar.”

Wani bacin rai ne ya saukarwa Ammar da yasa ya naushi bango da iya karfin sa. Take jini ya fara zuba daga hannun sa, amma shi ko a jikin sa.

“Ta yaya kika iya kallon kwayar idanuna ki ce inje inyi rayuwa ta? Kece rayuwa ta Salmah, dagaske kina tunanin zan iya wata rayuwa mai dadi babu ke? Ke ma nasan ba zaki kasance cikin farin ciki ba babu ni. Mun riga mun zama daya ko kin manta?”

Kuka Salmah take kasa-kasa, shi kuwa Ammar na kokarin ganin yayi controlling fushin sa.

“Ba zan iya ba Ammar, i'm so sorry.”

Matsawa yayi kusa da ita, ya rungume ta sosai a jikin sa... Sosai ta yanda numfashi yaso ya gagare ta. Kokarin ture shi take amma shi kuma ya kara kankame ta. Ihu ta fara har saida Khadija ta shigo da gudu cikin dakin ta raba su. Tsoro ya kamata ganin jini jikin bango da kuma hannun Ammar. Da sauri ta kalli Salmah ganin ko bugun ta yayi. Ita kuwa Salmah komawa tayi gefe ta cigaba da rera kuka.

“Ya kamata ka tafi Ammar, na dauka kazo gyara matsalar ne ba wai ka kara rura mata wuta ba.” Cewar Khadija.

“Zan dawo, kuma ba zan rabu da ke ba. Zan dawo, kuma ina so ki sa a ranki cewa ke matata ce kuma ba wanda ya isa ya raba mu. Kiyi duk abinda kike so, amma soyayya ta gare ki mai karfi ce da zan iya jure duk wata guguwa da zata shigo tsakanin mu.” Ammar ya fada kafin ya fice daga gidan.

(.....)

A BANGAREN KAMAL

“Ka cewa dan uwan ka, ya dena nema na. Lafiya lau nake.”

Murza ido yayi ya sake karanta sakon, nan ya gane ba kowa bace face Salmah. Janye bargon da ya rufa da shi yayi cike da kasala, ya sauko daga kan gadon. Kallon agogo yayi yaga karfe hudu ne na asuba, wannan ne karon farko da ya samu irin wannan baccin. A da idan ya kwanta wajen karfe sha daya, sai karfe uku yake farkawa. Amma yanzu bai bacci sai wajen karfe biyu ko uku.

Kokarin kiran number ta yayi amma bata shiga. Wata kil ta kashe wayan ta ne. A ransa yace, bai dace ma ya kira ta yanzu ba, domin yanzu haka tana bacci ne. Amma zai jira zuwa karfe bakwai ya gani.

Amfani yayi da wannan damar, ya shiga ban daki. Tunani fal a ran shi. Ba zai iya cigaba da hakan ba. Gashi dai ba bacci yake yi ba da dare, kuma hakan zai iya zamar masa wata matsala. Tun abinda ya faru da Zahara, ya kasa dena tunanin ta. Ya tambayi wani malami aminin mahaifin shi. Ya fada masa da al-qura'ani mai girma babu abinda ba za'a iya warkarwa ba. Kuma yayi masa alkawarin zai gama shi da wani da zai taimaka mishi. Yanzu abinda ya rage shine ya shawo kan Zahara. Yayi kuskure da bai amshi number ta ba, amma tinda yasan gidan su zai iya zuwa gobe. Amma bai sani ba ko wannan ita ce mafita, dan bai sani ba ko tayi maganar da iyayen ta. Ba zai iya zuwa gidan su ba haka kai tsaye. Doguwar riga ya saka, ya sauko kasa ya nufi kitchen dan ya hadawa kanshi coffee.

Yana kishingide bisa kujera a falo, bacci ya sake dauke shi. Ba shi ya farka ba, sai da konkwasa kofa da ake yi ya tayar da shi. Tv a kunne, kuma ko coffee din da ya hada bai sha ba, bacci ya dauke shi. Gashi ko sallar asuba bai yi ba har karbe dayan rana tayi. An dade rabon da ya samu bacci haka.

Ba'a daina konkwasa kofar ba, sai ma karuwa da yayi... Ya tabbatar Ammar ne. Shi da yace zai zo tun takwas. Mikewa Kamal yayi yaje ya bude masa.

“Nayi ta addu'ar kar ace ka fita ne.” Cewar Ammar lokacin da ya bude masa kofa. “Wai bacci kake ne? Yaushe ka fara bacci wannan lokacin?” Shigowa yayi ya nufi falo ba tare da ya jira jin amsar dan uwan nashi ba.

“Salmah tayi mun texte jiya.” Kamal ya fada yana zaunawa a dayan kujerar.

Dauko wayan sa yayi da niyyar ya nuna masa, amma yace ai yaga Salmah.

“Ka ga wa? Salmah? Ta yaya?”

“Khadija ce ta kira ni. Dan naje na ganta.”

“Amma ai kace min kaje gidan su Khadija bata nan. Karya tayi maka kenan?”

“Ban sani ba bro, abinda kawai na sani so take ta rabu da ni yanzu.”

Sai yanzu Kamal ya fahimci dalilin da yasa dan uwan shi ke cikin wannan yanayin.

“Bacin rai ne kawai, ka dan bata lokaci.”

“Tace min sai da tayi dogon tunani. Ina tsoron na rasa ta bro. Ji nake kamar zan yi hauka.”

“Tana cikin bacin rai ne yanzu, amma ka bata lokaci. Kuna son junan ku ba zai yiwu ku rabu ta sauki ba.”

“Zan tura su kawu gidan su, zan sa a daura auren mu ba da dadewa ba. Dan hakan ne zai sa Mom ta shafa mana lafiya.”

“Kar ka aikata hakan. Idan kana tunanin ta hakan ne idan ka auri Salmah Mom zata rabu da kai to kayi kuskure.”

“Toh me zan yi kenan?”

“Ka kwantar da hankalin ka, kayi tunani. Yanzu dai kayi kokarin daidaita tsakanin ka da Salmah. Sauran daga baya mun yi magana.”

“Ba zata yarda ba domin tasan Mom ba zata iya karban ta a matsayin suruka ba. Ya kamata na fara ta kan mom kafin naje kan Salmah.”

“Ya kamata ka tashi tsaye. Domin rayuwar ka ce, ba zaka bari kullum sai abinda mom tace ba game da rayuwar ka. Kuma kaima ka dena yi mata daukan kan nan da kake yi.”

“Kai ka fini sani, kullum tafi son ta nuna cewa ita ke kan daidai.”

“Shi yasa nake ce maka, ka lallaba ta, ka tabbatar ka shawo kanta.”

“Shikenan zan jaraba. Gashi kwana biyu na dena zuwa kamfani. Kuma har yau ban yi magana da Zahara ba. Nasan zata ji haushi na.” Cewar Ammar.

Kamal ba zai so ya fadawa Ammar abinda ke faruwa da Zahara ba. Kuma ita ma ya gargade ta da kar ta fada mishi. Zasu iya samun matsala ba tare da Ammar ya fahimci dalili ba.

“Yauwa kayi maganar Zahara, ko zaka ban number ta?” Cewar Kamal.

Kallon sa Ammar yayi na wasu yan mintuna.

“Ya aka yi ne?” Kamal ya tambaye shi.

“Shekarun ta 21 fa kawai.”

“Ban gane ba, me kake nufi?”

“Tambayar ka kawai nake, me yasa kake son number ta?”

“Kana magana kamar ni wani zaki ne da ke shirin abkawa barewa.”

“Kowanne namji zai iya komawa zaki, ko ba dade ko ba jima.”

“Ka sanni Ammar, ba zan taba iya cutar da ko waye ne. Believe me ba abinda kake tunani bane. Zamu yi wata magana mai mihimmanci ne da ita.”

“Yaushe kuka yi shakuwar da har zaka fada mata wani abu mai mihimmancin da ba ka so naji?” Ammar ya tambaye shi da mamaki.

“Ka ji da auren ka da Salmah. Nima naji da harkokin gaba na.”

“Ok, zan baka number ta amma idan wani abu ya faru da ita, ka ciji yatsa. Ba wai dan ina kanin ka ba, kayi tunanin ba zan iya maka komai ba.”

“Dena wannan cika bakin Ammar.”

“Khadija tasan kana son Zahara kuwa?”

“Kai Ammar, me kuma zan yi da wannan yarinyar? Kuma me sunan Khadija yake yi anan?”

“Da gaske baka sani ba, koko kana yin kamar baka sani ba ne?”

“Ban san me ba?”

“A'a.. cigaba dai da kwaikwayon makafi.”

“Toh a bar maganar tinda ba zaka fada min ba.”

“Da alamu Khadija sonka take. Kuma har Salmah tayi min maganar. Na dauka ta fada maka.”

“Ita ta fadawa Salmah tana sona? Ni babu abinda ta fada min ! Abokai ne mu kawai... Babu wani shirme tsakanin mu... Ko kuma a bangare na.”

“Toh gara dai da kace a bangaren ka. Ita ba abota take ji ba idan ta ganka. Maybe idan ka nuna mata alamu zata fada maka tana sonka.”

“Abikiya ce kawai, ban taba kawo wani abu makamancin haka ba a raina. Domin babu hakan a zuciya ta.”

“Bana bukatar sanar da kai tsufa kake kara yi. Ya kamata ace kati aure.”

“Ji malam wai matsalar ka kazo ka fada min ko tawa? Idan ma ina da bukatar yin auren yanzu da ka min zancen Khadija naji na dena.”

“Great, ba ni kadai ba za'a dinga yiwa ihun gwabro.”

“Mtsww. Kai dallah bani number Zaharan kafin ka manta.”

Kallon tuhuma Ammar yake yi masa.

“Ni dai jiki na bai bani ba...” Cewar Ammar.

----------------------------
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 12

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚

Kwanaki hudu kenan Zahara ta kasa tashi daga bisa gado. Domin duk jikin ta a mace yake, babu karfi ko kadan. Bata cin abinci ko taci ma ba mai yawa ba. Koda Mama ta tursasa ta taci, mintuna talatin sun yi yawa ta amaye shi. Yanayin da ya tsorata duk dangin ta kenan. Karon farko da Mama da Abba suka samu matsala sosai, kamar Abba zai kai ga jikin Mama. Dalilin yana ganin Mama ce silar shiga halin da Zahara take ciki. Ganin Zahara kwance ba tare da ta iya yin wani abu ba, na kara harzuka Abba. Ita kuwa Mama bata nuna wani tashin hankali, kamar koda yaushe, amma duk da haka Zahara tasan boyewa kawai take. A bangaren Zahara ma tana iya kokarin ta ganin ta tashi ta samu sauki amma ta kasa. Tayi neman tayi neman cikin kwanyar ta ganin ta tuna abinda ya faru a makabarta amma, kawai abinda ta sani ta fita hayyacin ta ne yayin da Malam Shehu ya zuba mata wasu ruwa, kuma ta dawo hayyacin ta a cikin dakin ta bisa gado, da wata laya daure a hannun ta. A lokacin da ta farka ba taso tayi tambayar abinda ya same ta ba, amma bayan wasu kwanaki ta tambayi Mama. Saidai Mama bata yi mata wani karin bayani ba. Dan haka duk a cikin rudu take, gashi babu alamun ta samu sauki.

Kwanaki biyar bayan zuwan su makabarta, Zahara ta fara samun sauki. Lokacin da Mama tazo kawo mata break fast din ta, bata tarar da ita kwance bisa gadon ta kamar kullum ba. A dan kankanin lokaci, taji gabanta ya fadi ta dauka wani abun ne ya sake faruwa, amma ganin Zahara ta fito daga ban daki, tana tafiya lafiya lau kamar komai bai faru ba, yasa Mama ta sauke doguwar ajiyar zuciya tare da jin kamar tayi tsalle dan murna. Ajiye plate din abincin tayi, ta nufi wajen Zahara tana yi mata ya jiki.

“Ya jikin naki? Da kanki kika iya yin wanka? Me ya faru? Na kasa fahimta, jiya fa ko hannu baki iya motsawa.” Cewar Mama cike da farin ciki da mamaki.

Zahara ma farin ciki take ganin Mama ma haka. Saidai ita kanta mamakin warkewar ta take farat daya.

“Bansan me ya faru ba Mama, amma lafiya lau nake jin kaina. Ina jin har zan iya tashi na kewaya gidan nan da gudu.” Zahara ta fada tana murmushi.

Nufar inda wardrobe dinta take tayi, ta dauko wata doguwar riga da zata saka. Mama da har yanzu cikin mamaki take, a zuciyar ta tana tunanin ko layar hannun Zahara ce silar warkewar ta. Daman ta yiwa Zahara kashedin kar ta yarda ta kunce layar daga hannun ta. Ganin yanda Mama ke yi mata kashedi, ya isheta gane cewa layar tana da muhimmanci. Dan haka tayi alkawarin ba zata taba cire ta ba.

“Ki ci abincin ki 'yata. Zan je in kira Abban ki dan sanar da shi. Shi ma hankalin sa a tashe yake dalilin halin da kika shiga.”

“Toh, zan sauko na taya ki aiki idan na gama.”

“A'a.. a'a kar ki ma fara, ya kamata ki kara hutawa.”

“Ki yarda da ni Mama, na warke babu abinda ke damuna. Ba zan iya jure zama a dakin nan ba, ko na minti daya.” Zahara tana fada tana mai nunawa Mama a fuskarta irin yanda ta tsani kwanakin da tayi a ciki a kwance.

“Toh shikenan zaki iya saukowa, amma ba zaki taba komai ba.” Cewar Mama da sigar gargadi.

“Shikenan Mama.”

Murmushi Mama tayi mata

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login