Showing 75001 words to 78000 words out of 87059 words
Afnan ya ɗauko ta. Afnan tace masa kar ya ƙara wahalar da kansa, tafi son komai ta yi da kanta saidai Ammar ba zai iya hana kanshi hakan ba. Yana ma so ya ɗauki wani da zai dinga aikin kai ta da ɗauko ta, har ma kula da ita.
Ƙarfe takwas da arba'in da biyar na dare Ammar ya iso gidan Kamal. Knocking Ammar yayi na wasu ƴan daƙiƙu kafin Kamal yazo ya buɗe masa. Ammar koda ya ga ɗan uwan nasa ya fahimci ba lafiya ba, ya ji tsoron ko rashin lafiya ɗan uwan nasa yake yi ba tare da ya sani ba.
“Lafiya kuwa? Ya naga duk ka koɗe?” Ammar ke tambayar Kamal yana rufe ƙofa bayan ya shigo.
“Yauwa Ammar gara da kazo."
“Idan haka ne me yasa baka kira ni ba?" Ammar ya tambaye shi.
“A'a bana son takura ka ne. Kai ma kana da naka matsalolin a halin yanzu."
“Ai da ka kira ni." Cewar Ammar.
Falo suka shiga tare da zaunawa bisa kujera. Ammar bin ko'ina yayi da kallo ya ga yanda falon yayi. Littafai ne ko'ina. Bai san dalili ba.
“Duk me ya kawo wannan littafan nan, kuma me yasa naga duk littafai ne game da aljanu? Ban fahimta ba." Cewar Ammar bayan ya ga sunayen da ke jikin littafan.
“Akwai wani abu dake faruwa a rayuwata kuma na tabbatar Amriya tana da hannu a ciki."
“Wacece kuma Amriya? Ko zaka iya min bayani?" Ammar ya tambaye shi.
“Ya kamata in ga Zahara, ina son inyi magana da ita."
“Wace alaƙa Zahara take da da wannan? Abinda na lura da shi, ba kun rabu ba? Ai sai da na faɗa maka nace idan kasan ba aurenta zaka yi ba, kar ka fara soyayya da ita. Bayan ka gama wasa da hankalin baiwar Allah yarinyar nan, daga ƙarshe ka koma ga best friend ɗinka alhali sai da ka rantse min ba son Khadija kake ba." Ammar ya faɗa rai a ɗan ɓace.
Kamal ajiye littafin da ke hannunsa yayi a hankali sannan ya dubi ɗan uwansa.
“Ka saurari me zan faɗa maka, ina son Zahara, ba ƙaramin so ba. Ka yarda da ni har zuwa yau na kasa fahimtar me yasa naji ta fita a raina. Lokacin da na ganta ɗazun, kamar duk wata soyayyar da nake mata da ta goge, ta dawo. Na fahimci duk wannan yana daga cikin siddabarun Amriya. Ta shigo rayuwarmu, kuma a halin yanzu tana wasa da hankalina har ma da na Khadija. Bani da tabbaci amma ina tunanin tana nan kuma idan haka ne Zahara, Khadija, ni wata ƙila har da kai muna cikin haɗari."
“Bansan me ka sha ba amma ko ma meye yanada ƙarfi sosai da zai sa ka ƙirƙiro wannan labarin marar ma'ana. Ina tunanin ya kamata na kai ka asibiti domin ka fara cin kai Kamal." Ammar ya faɗa yana taɓa gishin ɗan uwansa da yayi zafi gau.
Ammar ƙarawa yayi da cewa
“Ka gani, zazzaɓi ma gare ka. Na fahimci dalilin da yasa kake faɗar duk wannan shirmen. Kwanta, bari na kira doctor..”
“Daina ɗauka ta mahaukaci, dagaske nake ! Wannan aljanar ta shiga jikin Zahara... Shi yasa ta dinga yin wasu abubuwa bizarre a baya. Ya kamata ka san hakan domin kai ma hakan ya shafe ka."
A hankali Ammar ya fara tuna wasu abubuwa bizarre da Zahara ta dinga yi a baya. Kuma bata daina sauyawa ba. Zaharar yau daban, ta gobe daban. Amma hakan ba shi ke nuna akwai shafar aljanu a ciki ba.
“Ka yi tunani, zaka ga abinda na faɗa yana da ma'ana. Ni shaida ne akan duk wannan, kuma yau ɗinnan naga irin sauyin ga Khadija. Ta canza lokaci guda ! Ya kamata mu kora ta daga nan kafin ta cutar da mu da kuma baby."
“Wane baby?" Ammar ya tambaye shi har yau kansa a ɗaure.
“Khadija tana ɗauke da cikina, bansan ta yaya ko tun yaushe Amriya take cikin jikinta ba amma ya kamata na tseratar da su."
Ammar iya ƙoƙarinsa yake ganin ya iya lodar duk zancen nan da ɗan uwansa ya yi masa amma sun yi girman da ƙaramar ƙwaƙwalwarsa ba zata ɗauka ba. Yana so ya gaskata Kamal amma ya kasa.
Ɗauko wayarsa yayi yana ƙoƙarin kiran Doctor a sace amma wani ya shiga dukan ƙofa da iya ƙarfinsa.
“Waye wannan ke dukan ƙofa haka? Ko akwai wani da kake jira ne?" Ammar ya tambayi Kamal.
Girgiza masa kai Kamal ya yi alamar a'a kafin Ammar ya je ya buɗe.
Kasa motsawa yayi tsabar mamakin ganin mai bubbugar ƙofar cikin wani irin yanayi.
To be continued...
Like, Comment and Share Please.
AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story📖
By Malik al-Ashtar 🖋
CHAPTER 30
I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 30 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”
http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-30.html
Ammar kallon matashiyar matar yake, sosai take a galabaice. Duk da shi da ita basu shiri, yana son yi mata tambayoyi da dama. Bayan abinda ya faru da Afnan, saurin tsorata yake game da irin lamarin. Yasan yanda rayuwa take lalacewa bayan irin haka ta faru.
Kamal ya dawo dauke da ɗan akwatin agajinsa da kuma ƙanƙara mai sanyi ya ɗora bisa goshin Hafsat. Zabura Hafsat tayi kafin ta yarda ya ɗora mata.
“Me ya faru da ke Hafsat?” Kamal ya tambaye ta. Bayan ya ga kamar ta ɗan dawo hayyacinta.
“Bacci kawai nake son yi.. ko zan iya tsayawa nan har gobe?"
“Na fahimci cikin tashin hankali kike, amma ya kamata ki faɗa mana me ya faru da ke, Hankulanmu a tashe suke. Ina tunanin asibiti ya kamata mu kai ki."
Girgiza kai Hafsat tayi kuma ta ƙi ta faɗa musu abinda ya faru. Tasan idan ta faɗi wani abu, zasu ƙara farmakar ta ne. Kawai bacci take son yi yanzu, in yaso kafin gobe ta manta da komai.
Ammar da yayi shuru tun ɗazu, yace
“Abinda ya kamata ace kin yi yanzu shine ki faɗa mana abinda ya faru, ko ba komai kofar gidansa kika bubbuga."
“Ba yanzu ba Ammar." Cewar Kamal.
“Ni kawai cewa nayi muna da ƴancin sanin meke faruwa ! " Ammar ya faɗa.
“Ba ta hanyar nuna rashin tausayi, zai sa ta yi magana ba. Calm down ok?"
Hafsat kallon Ammar tayi kafin ta sadda kai ƙasa. Da a wani yanayin ne zata mayar masa da martani ta kuma daidaita masa zama amma ko'ina na jikinta ciwo yake ba zata iya biye masa ba. Roƙon Kamal tayi da kallo, shi kuma ya yanke barinta ta huta. Wata ƙila ta yi magana gobe. Ya faɗa a ranshi.
“Ok, bari na gyara ɗakin da zaki kwanta." Kamal yace wa Hafsat. Gyaɗa kai tayi tare da yi masa godiya.
“Kai kuma biyo ni." Kamal yace wa Ammar da ya ƙudira sai ya yiwa Hafsat magana, ba wai Kamal bane zai tsayar da shi.
“A'a...ina nan !" Ammar ya bashi amsa.
“Toh yi hankali da abinda kake yi." Kamal ya gargaɗe shi kafin ya tafi.
Koda ya tafi, Ammar ya fara jerowa Hafsat tambayoyi.
“Wa yayi miki haka Hafsat? Kamal matsalolinsa ma sun ishe shi, idan baki faɗa masa komai ba zai shiga damuwa. A halin yanzu baida lafiya kuma ɓoye masa wani abun ba zai taimake shi ba."
Ammar yana tunanin babu abinda zai sa Hafsat magana. Ya damu sosai akan ta, wata ƙila ba wannan bace hanyar da zai nuna mata amma ya damu sosai akan ta. Basa shiri amma ba zai taɓa mata fatan shiga irin wannan halin ba.
“Well... Ok idan baki son faɗar komai zan daina takura ki amma ki sani ina nan idan har kina buƙatar wani abun."
Hafsat har yanzu bata ce komai ba, ba zai taɓa yiyuwa ta yarda da roman bakin Ammar ba. Yayi gwargwadon cutar da ita da zai sa ba zata sake yarda da shi ba. Domin lafiyar jikinta da kuma ta ƙwaƙwalwarta, ƙin yi masa magana shi yafi.
Ƙoƙarin tashi Hafsat tayi da niyyar zuwa ɗaki saidai koda ta tashi tsaye, jiri ya ɗauke ta ta faɗi kasa. Ammar yayi ƙoƙarin kai mata agaji amma kafin ya kai gare ta har ta faɗi. Amma duk da haka ya nufe ta domin ya taimaka mata.
Kama hannunta yayi ya ɗagota koda ta ga ta tashi tsaye kuma zata iya tafiya, Hafsat ta fizge hannunta daga riƙon da Ammar yayi mata. Da mamakin abinda tayi, Ammar ya ɗan ja da baya. Daidai lokacin Kamal ya shigo.
“Me ya faru ne?" Ya tambaye su ganin kallon da suke jefawa juna.
“Sai da na faɗa maka kar ka yi komai." Kamal ya faɗa rai a ɗan ɓace.
“Ai kullum ni ne da laifi." Cewar Ammar. “Kawai fa ni taimako na so yi." Ya faɗa tare da zaunawa bisa kujera...
Kamal taimakawa Hafsat yayi zuwa cikin ɗaki. Tsaftataccen tawul ya kawo mata, sannan ya fiddo mata wasu kayanshi sabbi wanda bai taɓa sakawa ba dan ta saki jikinta. Ya fita daga ɗakin bayan ya faɗa mata ta kwanta ta huta kuma ta kira shi idan tana buƙatar wani abun.
Komawa yayi falo ya tarar da ɗan uwansa na tattarar duk kwaramniyar da ya bari a falon. Zaunawa yayi kusa da shi tare da dafe kanshi.
“Ya subhanallah.. everything is wrong ..." Ya faɗa ƙasa ƙasa.
“Yeah...na yarda. A halin yanzu komai is not really top. Yaya zaka yi da ita yanzu?" Ammar ya tambaye shi.
“Ban sani ba nima gashi gobe wani wuri nake son tafiya da safe, ba zan iya kaita gidansu ba, haka ban yarda da kai ba bare in ce ka kaita."
“Wai da gaske kake? Da gaske kana tunanin zan iya cutar da yarinyar nan?" Ya faɗa da jin haushin maganar ɗan uwan nasa.
“Kalamanka sun fi naushi zafi. Ni shaida ne lokacin da kuka yi faɗa. Wani abu ya faru da ita, bana so ka ƙara mata da naka."
“Na rantse maka nima ina son taimakonta, nasan akwai tsama tsakaninmu amma wannan zancen ba ƙarami bane. Na ɗauki darasi akan Afnan."
“Matsalar ita ce, koda ka so yin abun ƙwarai, ɓata komai kake yi. So ka yi min alƙawarin ba zaka yi komai ba wannan karon. Kawai ina son ka kaita gida ni kuma da na ida abinda zan yi, zan biyo ta gidansu na yi magana da ita ko da mahaifiyarta."
“Hum na ga kamar kuma ka yarda da ni. Daman ni ba mugu bane !"
“Na ji, ina son ka fahimci yanayi ne da za'a yi taka tsantsan da shi."
“Shikenan zan kula nayi maka alƙawari. Kai fa naka matsalolin? Me zaka yi? Idan na fahimta da kyau Khadija tana da juna biyu?"
“Ban sani ba nima abinda ya kamata na yi, amma abinda na sani, ya kamata inyi saurin sanar da Zahara kafin abu yayi tsanani."
“So kana tunanin da gaske akwai wata aljana da ke wasa da ku, me zai hana ka nemi wani malami ko wanda kasan aikinsu ne?”
“Eh zan ga abinda nake iya yi, a halin yanzu ka kula da Hafsat, ni naji da sauran.”
BANGAREN ZAHARA
Zahara har yanzu tana fushi da Maryam tun ranar nan da ta ƙyale ta ita kaɗai tare da Habib. Alhali tayi mata alƙawarin maido ta gida da kanta. Zahara tasan Maryam taimakonta kawai take son yi, amma ita bata ra'ayi da lokacin ƙara faɗawa wata soyayyar. Kuma yanda Maryam take yi, zai sa Habib ya yi tunanin ko itama Zahara tana da ra'ayin sa ne.
Ƙin ɗaga kiran ƙawar tata take yi tsawon kwanaki. Da gaske ne tana ɗan fushi da ita amma wannan ba shine gaskiyar abinda yasa bata ɗaga kiran Maryam ba. Kawai bata da ra'ayin magana da kowa ne. Tana yin kamar komai lafiya amma ba zata iya yiwa kanta ƙarya ba. Komai ba lafiya ba kamar yanda take tunani, ganin Kamal tare da Khadija ya cutar da ita yanda bata tsammani.
Tana jin ƙunyar faɗa ne, amma a daren koda ta zo gida, tayi kuka kamar ranta zai fita. A cikin mota tare da Habib, tayi ta murmushi ga labaransa na dariya, tana bashi amsa wani lokacin har ma tayi ƙoƙarin biye mishi suna hira amma duk hakan ƙarfin hali tayi.
Abinda bata sani ba, Habib ya gani ba a hayyacinta take ba kawai tana pretending ne. Baya son yi mata maganar ne saboda tsoron shiga hurumin da ba nashi ba. Duk da haka yaji daɗin haɗuwa da ita kuma yana so ace ya ƙara saninta kuma ya gano abinda ke ɓoye a bayan Zahara.
“Zahara, ko zaki zo ki ƙarasa wanke kayan nan, na ɗan gaji." Cewar mahaifiyarta ta kan tagar ɗakin Zahara.
Ajiye littafin da take karantawa Zahara tayi. Ta buɗe ɗakin ta bi bayan mahaifiyarta da har ta sauka daga stairs.
Zuwa Zahara tayi ta tarar da kusan Mama ta wanke kayan. Zaunawa tayi ta fara.
Wata ƙila hakan ya taimaka mata wajen rage tunaninta.
Abu ɗaya da ta sani yanzu tana shiga danginta idan ta samu dama. Bata son zaman kaɗaici yanzu dan kar tayi tunanin Kamal dan haka abu na farko da take yi idan ta dawo shine tsayawa cikin ƴan gidansu. A hankali ta fara jin daɗin hakan. Ta fahimci bata da komai da ya wuce danginta toh me yasa zata dinga nesa da su? Nadamar duk lokutan bayan da ta ɓata ita kaɗai tana kuka akan abinda ita ta ƙaƙabawa kanta alhali sauran suna jira ta fara yin takun farko zuwa gare su ne.
Saidai idan kowa ya je ya kwanta, gida yayi tsit, duka tunaninta sai ya koma ga Kamal. Ko tuna nishaɗin ƴan gidansu bai iya warkar da ita daga wannan raɗaɗin.
“Kina da sauri, har kin kusa gamawa?" Cewar Mama da tazo wucewa kusa da Zahara.
Ajiyar zuciya Zahara tayi ta kalli kayan ta ga duk ta wanke su bata ankare ba. Dole zata nemo wani abun ta yi idan ta gama.
“Zan je kasuwa cefane, idan kin gama sai ki tattare kayan da suka bushe ki kai ɗakina. Ni na tafi sai na dawo."
“Zan iya zuwa idan babu damuwa, ina son fita na ɗan sha iska." Zahara tace wa Mama.
Da mamaki Mama ta kalle ta
“Kina son zuwa? Ba ki gaji ba ne?"
“A'a ban gaji ba. Ki bari zan je na yi cefanen."
“Shikenan bari in ƙarasa wankin ni."
Duk abubuwan da zata siyo Mama ta zana mata. Bayan ta gama saurare, Zahara tace wa Mama ba zata daɗe ba zata dawo. Takalmi ta saka da gyalenta ta nufi hanyar fita.
A ƙofar gidan Kamal ne tsaye. Ya tattaro ƙuzarinsa hannu biyu ya zo, amma yana zuwa ƙofar gidan su Zahara ya ƙasa ƙonƙwasawa. Lokaci guda ya shiga tunani.. idan fa ta kore shi? Idan fa bata son ƙara yi masa magana? Komai tayi ba zai ga laifinta ba ganin shi abinda ya yi mata. A cewar shi.
Cikin sanyin jiki ya juya da niyyar tafiya sai ga Zahara ta buɗo ƙofa.
ƁANGAREN AFNAN
Yau Afnan ta tashi a sanyaye. Haɗuwarta da Anwar ta cutar da ita yanda bata yi zato ba. Bata da ƙwarin gwiwar sake tunkarar shi, tasan ba zai yiwu a ce sun ƙara komawa kamar baya ba.
Cikin damuwa da ɓacin rai yau take, cikin sa'a kuwa Ammar kafin ya fita ya bata haƙuri akan yau ba zai iya kaita ba daman bata son yi masa bayanin dalilin da yasa ba zata je school yau ba.
Ɓata ranar tayi tana ƙoƙarin nazartar darussan da Azima ta bata. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ta ji ana knocking ƙofa. Da mamaki ta je ta buɗe.
“I'm sorry ƙawata amma wlh takura ni yayi sai na kawo shi." Cewar Azima.
“Akan wa kike magana?" Afnan ta tambayi ƙawar tata.
Kaucewa Azima tayi sai ga Anwar ya bayyana.
“Me kazo yi nan?" Afnan ta faɗa da ɗan ɓacin rai.
“Kar ku kashe junanku, ni kun ga tafiyata." Cewar Azima kafin ta juya da ɗan gudunta kamar ɓarauniya.
Afnan cikin matuƙar mamaki take da yasa bata bi ta kan Azima ba.
“Me ya kawo ka nace?" Ta sake maimaitawa.
“Me yasa yau baki zo school ba? Sake ɓacewa zaki yi ba tare da kin faɗawa kowa ba? Yanzu na ƙara tabbatar kin fiye son kanki da yawa fiye da baya."
Ƙasa gaskata abinda ta ji Afnan tayi.
“Wai wasa kake yi? Idan dan ka zage ni kazo, zaka iya tafiya. Dan haka sai an jima ni inada abun yi." Afnan ta faɗa tana ƙoƙarin rufe ƙofa amma Anwar yayi saurin saka ƙafa ya tare ƙofar.
“Haka ne, ai baki iya komai ba bayan guduwa. Ban yi mamaki ba, ban ma san me yasa nazo nan ba!”
“Problem ɗin da nake fama da shi yanzun ma ya ishe ni, ba zan bar wani ya daɗa min da nashi ba. Ka faɗi duk abinda kake so kuma ka yi duk abinda kake so ban damu ba. I have had enough of you all ! Ka zauna nan idan kana so ni ka ga tafiya."
Riƙe mata hannu yayi kafin ta tafi.
“Idan kinada wata matsala me yasa ba zaki faɗa min ba? Me yasa kike maida ni gefe? Na yi tunanin inada muhimmanci a gare ki, nayi tunanin muna tare domin ɗayanmu. Ina ma zaki san irin yanda rashinki ya cutar da ni."
Wannan ne karon farko da Anwar ya bayyana mata haka, karon farko kenan da ya bayyana halin da yake ciki. Ɓoye komai da komai yake ga shi kadai. Afnan tana burge shi ne domin yana faɗa mata damuwarshi kuma ta bashi shawara ba tare da ta bibiyi dalilin damuwar ba...
“Ka fi kowa sanin ba koda yaushe muke bayyanawa juna matsalarmu ba. Na so a ce ka yarda da ni kuma ka cigaba da kasancewa tare da ni ba tare da kayi dogon bincike ba kamar yanda nake yi a baya. Na sha jin zafin rashin faɗamin damuwarka amma a kullum ina girmama ra'ayinka. Amma share ni da kayi jiya, ya nuna min ba zaka iya irin wannan sadaukarwar ga alaƙarmu ba."
Janye hannunta tayi daga na Anwar kafin tace
“Ina son ka tafi yanzu, ba zan ce komai ba na abinda ya same ni. Idan ka yarda zaka karɓe ni ba tare da kaji dalilin da yasa na ɓace ba, zan ji daɗin hakan. Idan ba haka ba... Kasan abinda ya rage maka. Sai mun haɗu school.” Afnan ta faɗa kafin ta rufe ƙofar...
To be continued...
AMRIYA ☠️
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story📖
By Malik al-Ashtar 🖋
CHAPTER 31
I just published Amriyar Hatsabibiyar Aljana Chapter 31 of my story “AMRIYA Hatsabibiyar Aljana”
http://www.ashblogg.com.ng/2022/03/amriya-hatsabibiyar-aljana-chapter-31.html
Bata taɓa tunanin ganin mutumin da take tunani kwana biyu a ƙofar gidansu ba. Abu na farko da ta so tayi shine ta maida ƙofa ta rufe kamar bata ganshi ba. Saidai a daidai lokacin wani ƙwarin gwiwa ya ziyarce ta.
“Me kazo yi nan?" Zahara ta tambaye shi.
Kamal bai san takamaimai abinda zai yi