Showing 51001 words to 54000 words out of 87059 words

Chapter 18 - AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA

Start ads

Ashar   

11 Aug 2025

424

Middle Ads

ina son ganinka.”

“Lafiya meke faruwa?”

“Kowa lafiya, ni ke son ganinka kuma yanzu nake son kazo.”

“Ok gani nan.”

Yana katse kiran, sai ga Afnan ta dawo.

“Mom, Na kira shi amma yace min meeting gare shi mai muhimmanci, ba zai iya zuwa ba.”

“Ok, bani wayar je ki karbo min tea din da nace Rakiya ta hado min."

Debe password din tayi, sannan ta mika mata wayar. Sake kiran Ammar Mommy tayi. A ringing na biyu ya dauka.

“Afnan, wai ba nace miki meeting gare ni...” Bai karasa fada ba Mommy ta katse shi.

“Nice ba Afnan ba, Ammar idan baka zo ba nan da minti goma, na rantse maka sai kayi nadama."

“Amma Mom..” Katse kiran Mommy tayi tareda ajiye wayar kan center table.

Ammar da saurin shi ya shigo gidan, yana tunanin wani babban abu ne ke faruwa duk da jin muryar Mommy kamar ranta a bace yake. Koda ya faka mota, yaga ta dan uwanshi a bayanshi. Fitowa yayi tare da kulle motar.

“Kasan meke faruwa ne?” Ya tambayi Kamal da alamun shima cikin rudu yake kamar shi.

“A'a.. Mom ce tace nazo da gaggawa..” Kamal ya bashi amsa.

“Fatan dai Allah yasa lafiya, domin ni inada meeting mai muhimmanci."

Knocking kofa suka yi, Rakiya tazo ta bude musu. Gaishe ta suka yi ta amsa kamar kullum da murmushi.

Kai tsaye falo suka nufa, inda suka tarar kowa na gidan ya halarta, har da Daddy ma yana nan. Koda Ammar ya hada idanu da Mommy, ta galla masa harara da yasa shi shan jinin jikin sa. Tambayar Afnan yayi da kallo, amma ita ma da alama bata san meke faruwa ba. Sai ma gyangyadi da take yi, amma da Mommy tayi magana da babbar murya tayi firgigit ta tashi.

“Tunda dukan mu mun hadu, zan je kai tsaye akan abinda ya tara mu. Ammar ina son ka min bayanin abinda ya hadaka da Hafsat jiya.

Ammar a ranshi yace «ba dai ta kira ni bane dan ta yimin zancen yarinyar nan.»

“Kin kira ni daga office ne dan ki min zancen yarinyar cen? Kuma fa na fada miki inada meeting mai muhimmanci.”

“Ammar tambaya ta karshe zan maka, me ka yiwa Hafsat?”

A ranshi yace «Me kuma wannan sakaryar tazo ta fada?»

“Fada kawai nasan nasan munyi..."

“Ammar me yasa kake so ala dole sai ka cutar da ni? Ni kake cutarwa idan kana cutar da ita. Kuma kana ja min abun kunya gaban dangin aminiyata. Kana tunani kuwa kafin ka aikata wasu abubuwan ?”

“Amma mom..”

“A'a saurare ni Ammar, wannan ne na karshe da za'a kira ni dan kawo min koken bakin halinka. Shekarunka nawa? Ya kamata kasan ka girma.”

“Idan kana min haka ne domin nuna min jin haushina da kake saboda karuwar budurwarka, to ka sani ina kan bakana. Ka daina ciwa yarinyar nan mutunci, babu abinda tayi maka.”

“Mahaifiyarka na da gaskiya.” Cewar Mahaifinsa. “Yarinyar nan babu abinda tayi maka, banga dalilin da yasa kake wulakanta ta ba. Ba wannan tarbiyar muka baka ba. Abinda kake aikatawa ba wai mutuncinka kadai kake zubarwa ba, har da namu. Bana son irin haka ta sake kasancewa.”

“Ni fa duk wannan ba laifina bane. Me yasa kuke son na aure ta alhali kunsan ba sonta nake ba kuma ba zan taba sonta ba. Zamani ya sauya, an wuce zamanin da iyaye zasu tursasa 'ya'yansu auren dole. Kenan na tsoraci goben Afnan? Ita ma zata yi rayuwa irin wacce nake yi yanzu? Tursasa ta zaku yi ta auri wanda bata so?"

“Daina cakuda mana komai, babu irin haka da zata faru. Mu farin cikin ka ne kawai muke so, mu ga rayuwarka tayi kyau.” Cewar Daddy.

“Ni wannan ba farin ciki bane gare ni. Kuna tarwatsa rayuwar da na shiryawa kaina ne, kuma Mom kin fara min abinda bana jin dadin sa."

“Idan da kayi min biyayya duk da hakan bata faru ba. Ba zan taba kokarin sanya ka alakar da zata bata maka rayuwa ba. Nasan wacece Hafsat, yarinya ce ta gari."

“Kin gani ko? Baki saurare na. Har abada ba zan samu farin ciki da wannan yarinyar ba. Mu nemawa kamfanin su mafita idan har wannan shine ke damunki.”

“Kamal me zaka ce game da dan uwanka?” Mommy ta tambaye shi.

“Rayuwar sa ce, ina ga bai dace ki takura masa ba."

“Daman kai baka taba min biyayya ba, ban ma san me yasa na tambaye ka ba. Bansan me na yiwa Allah ya bani 'ya'ya irinku ba. Idan baka amince da auren nan ba, ka nemi wata uwar ba ni ba.”

“Karima kin fara wuce gona da iri." Cewar Daddy.

“Mom kiyi kokarin fahimtar shi.” Cewar Afnan.

Shi kuwa Kamal bai ce komai ba, sai sauraron su da yake.

“Idan ba zai bi umarnina ba, bana son ya cigaba da amsa sunana a matsayin mahaifiyar sa."

“Shikenan.. tinda.. haka take so." Cewar Ammar.

“Bana son shashanci Ammar!” Cewar Daddy. “Kasan me hakan ke nufi? Kasan illar girman abinda take kokarin yi maka?”

Me hakan zai canza? A halin yanzu alakar shi da mahaifiyar sa tayi kasa sosai. Daga yanzu babu abinda zai dawo kamar baya, dan haka ya shirya sallama shi da zata yi.

Kallon Kamal yayi da tun dazu bai ce komai ba, koda suka hada ido Kamal ya girgiza masa kai alamar kar ya yarda yanke wannan mummunan hukunci. Saidai shi Ammar yana ganin aikin gama ya gama.

Maida kallonsa yayi zuwa kan mahaifiyar shi, suka hada ido. Firgici, tsoro, damuwa da bacin rai.. ne tattare a cikin kallon su.

“Tinda a shirye take na cutu a wannan auren da take kokarin yi min.. nima a shirye nake nayi makokin rashin uwa.”

“YA AMMAR !” Afnan ta kwalla kara tare da dora hannu a kai.

“I want to be free, ban taba samun wani 'yanci ba a tare da ita. I want to be free, nayi rayuwata yanda nake so kuma na auri wacce nake so.”

Shuru Mommy tayi.

“Kana tunanin zaka iya samun wani farin ciki ba tare da sa albarkar mahaifiyar ka ba? Ina mai baka shawara da kayi tunani Ammar.” Cewar Mahaifin shi. “Kamal ka yiwa dan uwanka magana. Kar ka barshi ya bata rayuwar sa. Allah baya tare da wanda tsinuwar mahaifiyar sa ke binshi.”

“Ita ta sallama ni ba ni ba. Allah yana tareda da masu gaskiya. Ban yi komai ba ni, kare kaina kawai nayi.”

“Good.. ka fice min daga gida yanzu. Daga yanzu ban sanka ba." Cewar Mahaifiyar sa tareda barin falon.


“Good, daga yanzu ni maraya ne banda uwa.”

“Ya isa haka..” Cewar Kamal.

Mommy ta fice daga falon, Daddy ya rufa mata ba tareda ya sake kallon inda Ammar yake ba.

“Ka wuce gona da iri.” Cewar Kamal.

“Ina ruwana, su basa ganin adadin yanda nake cutuwa? Eh nine mugun cikin labarin.”

“Abinda ka aikata yanzu, ba komai kayi ba illa kara jagule lamarin. Kuma ina baka shawara da ka bata hakuri gobe ko jibi idan komai ya laba.”

“Ba wani hakuri da zan bayar... I just want to stay alone.”



SARAT

Karfe 12 na dare
A gajiye take sakamakon aiki da ta sha gaba daya yinin yau. Tana shirye-shiryen bacci taji wayarta na ringing. Tayi tunanin ko yayanta ne dake kasashen waje, domin shi kadai ke kiranta irin wannan lokacin. Baccin da take ji ne ya kaurace lokacin da tayi arba da sunan oganta a jikin wayar. Da saurinta ta daga kiran.

“Hello?”

“Bacci kike?” Ya tambaye ta.

“A'a, a'a kwance dai nake, kana lafiya?”

“Zo ki bude min kofa..”

Rudewa Sarat tayi, jin Mr. Ammar na bakin kofarta. Zuwa tayi bakin kofar, ta leka ta huda ta tabbatar da shine a tsaye. Har yanzu yana sanye da suit dinsa tun na safe, jacket din a kafadarsa, rabin mabbalan rigarshi kuwa a bude, ya bar kirjinsa waje.

Bata gama kare masa kallo ba, ya rungume ta. Bata sani ba ko farin ciki zata yi ba ko damuwar yanayin da ta ganshi ciki. Sai da suka dau lokaci a haka kafin ya sake ta su shiga ciki. Zaune yayi cikin kitchen yana kallonta tana hada masa coffee. Ganin sa take kamar wanda yayi dambe, bata yi gangancin tambayar sa meke faruwa ba.

“Sorry na zuwa da nayi a wannan lokacin.”

“Kar ka damu... da yake ba komai nake yi ba.” Ta bashi amsa.

Coffee yasha ba tareda ya sake cewa wani abu ba, ita kuwa Sarat kallonsa take yanda yake kai kofin coffee a nutse zuwa bakin sa. Ta kasa dauke idanunta daga kanshi, domin ko a wannan yanayin kyanshi take gani. Kasa tsayar da kanta tayi, taje inda yake tareda rabashi da jacket dinsa. Kissing dinsa tayi shima ya mayar mata da martani. Da son zuwa nesa, a hankali ta cire masa riga, ta shiga sumbatar ko'ina na jikinsa, shi kuwa ya tsayar da ita ta hanyar ture ta.

“Ba wannan bane..ya kawo..ni.. Ina son muyi magana ne.”

Kallon sa tayi ta kara tabbatar da yana cikin damuwa kuma ba kadan ba. Hannun sa ta kama ta jashi zuwa dakinta. Tagogi ta bude sannan ta cire masa takalmi. Kwance tayi bisa gado tareda gayyatarsa shima.

“Zo ka huta, komai zai dawo daidai.”

Sai da ya kalleta na wasu yan dakiku sannan ya gyada mata kai. Kwantawa yayi gefenta tareda dora kansa bisa kirjinta. Rufe su tayi da zani, a hankali ta fara shafa shi dan ya samu nutsuwa. Tana tunanin haka ne yake bukata a halin yanzu.. domin bayan wasu yan mintuna taji numfashinsa ya karu alamar yayi bacci.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

For more novels https://bit.ly/3Egdy1m

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 20

⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚


Kwanaki na shudewa babu abinda ya sauya gidan Alhaji Yusuf. Kamar yanda yace, Ammar ya bar gidan iyayen sa ya koma sabon gidan shi da babu nisa da kamfani. Yana ganin abinda ya faru ya gyarashi na wani bangaren, domin ya bashi damar yin tunani akan matsalar shi, ya kan zauna yayi nadamar laifin da ya aikatawa mahaifiyar sa. Amma idan ya tuna yanda mahaifiyar sa tayi masa, sai yaga ba laifin sa bane.

A bangaren Hajiya Karima kuwa, ta kasa gasgata abinda danta yayi mata. Tayi tunanin idan tace zata sallamashi zai ji tsoro yayi abinda take so, saidai tayi kuskure. Mamakinta kasa boyuwa yake, a takaice dai cikin zuciyarta tsoron rasa danta take, wanda shi kadai ne yake sauraronta kuma yake mata biyayya ba tareda wata matsala ba.

Tana jin kamar a dawo baya, ta hana bakinta fadar wadannan kalaman kuma ta shawo kan matsalar ta wata hanyar. Tayi ta kokowa da son kiran dan nata na tsawon makonni amma ji da kai ya hanata kuma zuciyarta na ce mata ai zai dawo gare ta. Jiran da take yi masa kenan a kullum.

Tsawon watanni kenan tana jira amma bata ga inuwar danta ba, babu kuma labarin shi. Hakan ba karamin tayar mata da hankali yayi ba, har ta fara fidda rai. Gashi kawarta na fushi da ita. Babu mai goya mata baya, har mijinta ya daina shiga al'amarin, alhali shine na farko da ya kamata ace ya saka lamarin.

Saidai Hajiya Karima bata san ba rabuwa da danta bane kadai tashin hankalin da zata fuskanta. A safiyar yau, kamar kowacce safiya tsayin wasu watanni, Afnan ta daina zuwa school. Hajiya Karima tayi ta mata tambayoyin dalilin barin zuwanta school, ita da ke da kokari sosai. Amsar da Afnan take bata na damunta : Kawai bana son zuwa ne.

Duk da fadan da Hajiya Karima ke mata, Afnan taki tayi mata bayanin me yake damunta. Hajiya Karima ta fara tsorata da canjin da 'yarta take samu. Ta daina cin abinci sosai, amma sai kiba take yi, batada aiki sai yawan bacci da cin gyada. Halin da har ya janyo hankalin Rakiya mai aikin su. Afnan ta kan yawan ce mata ta hada mata tea da mint domin duk safe zata ce bata jin dadi. Hajiya Karima ta lura da duk yanayin 'yar tata amma taki ta yarda da abinda take tunani.

Saidai yau da safen nan, taga Afnan ta sauko daga sama ta nufo inda take, lokaci guda kuma ta nufi toilet a guje rike da bakinta. Ganin yanayin 'yar tata, Hajiya Karima tabi bayanta ita ma. Tana saka kafarta cikin dakin, karnin amai ya bade mata hanci. Nan taga Afnan durkushe gefen masai tana amaye duk abinda taci jiya.

Yanzu ne ta gasgata abinda take tunani, komai gashi zahiri a idonta, amma taki yarda. 'Yarta juna biyu gareta. Duk da haka sai da ta yiwa Afnan tambayar kamar idan taji gaskiyar ga bakin 'yar tata wani abu zai canza.

“Ciki gare ki?”
Zabura Afnan tayi tareda faduwa kasa, muryar Mommy ta tsorata ta. Dama kwana biyun nan tsoron yin amai take gabanta, yau ma bata ankare bane har ta rutsa ta. Tasan ko ba dade ko ba jima Mommy zata gano gaskiya kuma abin mamaki murnar hakan take. Murna take saboda daga yau babu wata barazana da zata sake fuskanta. Fashewa da kuka tayi yayin da ita kuma Hajiya Karima ke addu'ar Allah yasa mafarki take.

“Mom..” Afnan ta fada cikin kuka tana mai tuna irin ciwon da taji ranar da ta gane tana da ciki. Saidai wannan ciwon ba komai bane akan ciwon sanin uban cikin da ba kowa bane face mjin wacce ta rike ta.

“Mom? Har kina da karfin gwiwar kirana Mommy? Idan da kina daukata a matsayin mahaifiyar ki da ba zaki janyo min wannan abun kunyar ba.”

Afnan kuka take kamar ranta zai fita.

“Please Mom..”

“Please what?” So kike in taya ki murna ko me? Me zan fadawa mahaifiyar ki wacce ta bani amanar ki? Me zan fadawa mutanen da zasu ce ban baki tarbiyar ba domin ba uwa ta gari bace ni? Ta yaya kike son na kalli idon duniya?”

Hawaye ne suka zubowa Hajiya Karima, ta rasa me ke mata dadi. Da abinda ya faru a baya, tayi tunanin koda kowa zai juya mata baya, Afnan ba zata taba bata kunya ba. Saidai ashe irin haka na tafe.

“Goge aman, maza ki same ni a falo!” Mommy ta daka mata tsawa.

Cikin kuka Afnan ta gyada mata kai sannan ta tashi dan cika umarnin mahaifiyar ta. Anyi wannan amma mai wahalar yana tafe. Me zata yi yanzu? Me zata fada? Wannan sune tambayoyin dake yiwa Afnan yawo cikin kai. Tsawon makonni kenan take shirya amsoshin da zata ba uwar rikonta. Ta shirya cewa wani saurayi gareta shedan ya rude su suka aikata abinda bai dace ba. Afnan tana ganin hakan zai zo da sauki kuma zai kareta daga sharrin wanda ake dauka a matsayin mahaifin ta. Saidai yau da ranar tazo, taji batada kwarin gwiwar yiwa Mommy karya domin tasan zata gane karya take mata. Ba yau take zaune a hannunta ba, dan haka ta santa ciki da banta.

Cikin wasu yan dakiku Afnan tayi wani tunani cewa uwar rikonta ta gane gaskiya kuma ta yanke zata yi shari'a da mijinta dan ta kwatowa 'yar 'yar uwarta hakkin ta, a cikin tunaninta taga Hajiya Karima na kareta duk da bakin cikin gano cin amanar da mijinta yayi mata.

Mai yiyuwa taso kanta da tayi irin wannan tunanin, amma Afnan tace itama ta cancanci farin ciki fiye da sauran ahalin gidan. Bari dai kar tasa rai da yawa, ba zata taba aikata makamancin haka ba. Ba zata taba tona asirin uban rikonta ba domin idan tayi haka zata wargaza farin cikin ahalin ne fiye da yanzu abun kunyar da ta janyo musu.

Addu'a tayi ta roki Allah yasa komai yaje daidai kan karyar da zata yi akan wanda yayi mata ciki. Tana tunanin wannan karyar da zata yi zata sa uban rikonta ya dena hayke mata.

Tana cikin wannan tunanin, Afnan ta goge aman da tayi, bayan ta gama sai da dan tsaya cikin dakinta domin tattara kuzarinta hannu biyu kafin taje. Tafiya tsakanin dakinta da falo ba karamin tsayi yayi mata ba amma duk da haka sai da ta karasa falon. Ta tarar da Mommy zaune bisa kujerarta, ta buga tagumi daga gani kasan cikin tashin hankali take.

Afnan a hankali ta karasa falon tareda zaunawa kasa nesa da Mommy. Shuru Mommy tayi, shurun da har ya fara bawa Afnan tsoro.

“Tun yaushe kika san kina da ciki?” Mommy ta tambayi Afnan ba tareda ta kalle ta ba.

“Sati uku da suka wuce..” Afnan ta fada cen kasan makoshi.

“Kuma bakida niyyar fada min ko? Tabbas me yasa ma hakan zai bani mamaki? Waye uban cikin, ina son ganin shi yau dinnan!”

“Ya koma kasar su.. a Korea yake.”

“Ko ma a Italy yake, ko a sama ko a cikin ruwa ba abinda ya dame ni, ina son ganin shi cikin kankanin lokaci."

Afnan duk ta shiryawa irin wannan tambayoyin na Mommy.

“Soja ne kuma yana cikin mission ne yanzu, ba za'a iya samun shi ba sai shekara mai zuwa.”

“Dan asalin wacce kasa ne?” Mommy ta tambaye ta.

“Mahaifiyar shi yar Nijar ce, mahaifin shi ne dan Korea.”

“Shine daga ganin shi kika fada mishi ba tareda wata kariya ba, ko tunanin me zai je ya dawo ko? Kina tunanin zaki haife wannan cikin har ki rene shi? Kina tunanin zaki iya kula da abinda zaki haifa alhali ke daliba ce? Da wani kudin kike tunanin kula da shi? Ba dai kina tunani ni zan iya rikon shege, na sai mashi sutura, takalmi da sanya shi a makaranta, na yi masa magani idan baida lafiya, na yi masa duk wani abu da yake so. Tunda kina ganin kin yi girman da zaki je kiyi abun manya, yanzu ai sai ki ji da abinda kika jangwamo. Mahaifin ku ba karamin Allah wadai zai yi miki ba.”

Tayi alkawarin yin karya domin kare mutuncin gidan, amma anya zata iya jure daidai da minti daya a dinga suffanta ta da irin wannan kalaman, alhali ba ita bace mai laifi. Kare mutuncin gidan wani abu ne daban haka tunkarar fushin mahaifiyarta ma wani abun ne daban. Zuciyar ta ba zata juri hakan ba.

Afnan babu abinda ta iya yi face sake fashewa da wani sabon kuka.

“Hajiya ina son fada miki wata magana..”

Rakiya ce mai aikin su ta shigo falon. Tunda take gidan bata taba katse magana mai muhimmanci ba irin wannan, shi yasa Hajiya Karima tayi mamaki domin tasan Rakiya tasan wannan maganar mai muhimmanci ce.

“Rakiya baki ga ina cikin magana da wannan yarinyar bane?”

“Nima maganar ce nake son yi miki.. Nasan ba hurumi na bane amma nasan idan ban fadi abinda na sani ba, ba zan taba yafewa kaina ba.”

Wani kallo Afnan tabi Rakiya da shi. Abinda Rakiya zata fada tasan zata iya rasa aikinta amma dole ta fada ko dan

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login