Showing 3001 words to 6000 words out of 87059 words

Chapter 2 - AMRIYA HATSABIBIYAR ALJANA

Start ads

Ashar   

11 Aug 2025

404

Middle Ads

rana tayi. Inda Allah ya taimake ta yau ogan ta bai zuwa aiki. Tana son ta koma baccin, amma kuma ya kamata taje ta taya Mama aiki. Bayan wani dan yaki da tayi a cikin kanta, na tsakanin ta cigaba da bacci ko ta tashi, daga karshe ta mike ta shiga ban daki. Bayan ta fito ta nufi wardrobe domin daukar kayan da zata saka. Sai dai tana bude wardrobe din, wani abu ya fado kasa. Da yake kayan nata duk a wargaje suke, domin a ganin ta bata da lokacin gyara su, ta duka da niyyar dauko abinda ya fadi ta mayar. Sai dai da ganin meye ya fado a kasa, tayi cak, a hankali ta shiga yin baya baya ganin ta baro bakin wardrobe din, ta ma bar dakin gaba daya, amma tsoro ya sandarar da kafafun ta ta fadi kasa. Kyarma take kamar takarda kuma ko kalma daya mai kama da addu'a ta kasa fita daga bakin ta.

Ba komai bane ta gani face gyalen Amriya da ta bari a bakin kogi, sai dai wannan karon duk ya baci da jini. A hankali ta fara rarrafawa domin ta samu ta bar dakin. Tana son tayi ihu amma ta kasa, tana son ta tashi ta ruga amma gabobin ta sun kasa. Iya kokarin ta take ganin ta saita bugun zuciyar ta, amma ma kamar karuwa yake. Cikin ikon Allah tayi nasarar kaiwa bakin kofar dakinta dake bude, bata san ta yaya ba, hannuwan ta a jikin tawul din dake kirjin ta, a guje ta nufi dakin Mama. Mama tana tsaka da da nadin kayan Abba sai ga Zahara ta shigo a firgice ta fada jikin ta.

Hawaye ne kawai ke ta malala a fuskar ta. Mama kuwa duk ta rude bata san me ya samu 'yarta ba. Zahara ba ma zata iya tuna ranar da tayi kuka a gaban mama ba. Domin a duk lokacin da take da wata damuwar, shigewa daki take ta kulle ta shirgi kukan ta, ba tare da Kowa ya sani ba. Bata taba tunkarar mama da wata matsala ba, dan haka dole wannan karon mama ta shiga cikin tashin hankali.

“Me yake faruwa ne Zahara? Baki lafiya ne?” Mama ta fada tana mai taimakwa Zahara domin ta zauna.

A bangaren Zahara kuwa tana iya kokarin ta ganin ta daina kukan amma abin yaci karfin ta. Goshin ta da jikin ta Mama ta taba dan taji ko zazzabi ne gare ta amma babu, duba ko'ina ta shiga yi ko ciwo ne taji amma Zahara ta rike mata hannu tare da ce mata ta daina.

“Zahara fada mini meke damun ki? Duk kin bi kin rudar da ni. Wani ne yayi miki wani abun?” Mama ta tambaye ta.

Girgiza kai Zahara tayi alamar a'a.

“Toh fada min me ya faru?”

“A.. a dakina..dakina..” Zahara tana kokarin yi mata bayani amma bata ma san ta ina zata fara ba.

“So kike muje dakin naki?” Mama ta tambaye ta tana kokarin mikewa.

“A'a..a'a..a'a kar mu je daki na, akwai wani abu a cen!” Zahara ta fada tana goge hawaye.

“Akwai wani ne a cen? Barawo ko wa?” Cewar Mama cikin tsoro.

“A'a ba barawo ba ne.”

“Kinga zo mu je dakin naki.”

“A'a.. dan Allah bana son zuwa cen Mama.”

“Ina son sanin meke faruwa Zahara. Tashi muje kar ki damu ina nan ba abinda zai same ki.”

Bayan wasu yan dakiku na nazari, Zahara ta kama hannun Mama suka nufi dakin ta. Da zuwan su bakin kofa, da mamaki ita dai Zahara tasan lokacin da ta fita da gudu kofar a bude ta barta amma yanzun a rufe take. Kara kankame hannun Mama tayi, ita kuwa Mama ta balla kofar dakin suka shiga.

Kofar wardrobe din Zahara a rufe take, kuma babu alamar gyale mai jini a wurin.

“Kin gani babu komai nan.”

Kallon Mama Zahara tayi kafin ta fashe da sabon kuka. Ita dai tasan wannan dakin ba lafiya yake ba, domin ita kadai tasan yanayin da take ji idan tana cikin sa. Ita tasan gyalen nan ta bawa MAMI shi, toh yaya aka yi kuma yazo nan. Mama hankalin ta ya kara tashi ganin Zahara a kasa, kuka kawai take faman yi, ta rasa ta ina zata bullowa wannan al'amarin kuma tasan duk wannan yana da alaka da haduwar ta da Amriya.

Bayan mama ta lallashe ta, tana kokarin tayar da ita suka ji ana konkwasa kofa.

“Bari naje na duba ko waye.” Mama ta fada tana mai cillowa Zahara riga da ta dauko mata daga cikin wardrobe din. “Saka wannan rigar ki jira ni anan.”

“A'a ni ba zan iya zama cikin wannan dakin ba.” Zahara ta fada tana sanya rigar da Mama ta bata da sauri.

“Zan biyo ki mu je tare.” Cewar Zahara tana matsowa kusa da Mama. Sai da Mama ta dan yi jim kafin ta nufi hanyar fita. Ita kuwa Zahara tabi bayan ta kamar wacce aka jona.

Suna saukowa kasa, Zahara ta jira a falo, ita kuwa Mama taje ta bude kofa. Zahara zaune tayi bisa kujera, tana jin kullum gidan kamar bako yake gareta alhali a ciki ta girma. Kullum tana kunshe a daki, koda an hadu kowa na gidan ita banda ita, sai idan Abba ya matsa mata ta fito. Ba wai ganin dangin nata ne bata so ba, a'a idan tana cikin su ne sai tayi ta jin kamar bare ce ita a cikin su. Ko ma dai tare da dangin ko kasancewar ta ita kadai bai sauya komai, kawai dakin ta shi daya ne inda take jinta a tsaro, har zuwa yau da wannan abu ya faru.

Sallama bakin nasu dake kokarin shigowa falon suka yi. Saurin goge hawayen ta Zahara tayi kafin ta amsa sallanar tare da gyara zaman ta.

“Zahara ya kike?”

Muryar MAMI Zahara taji, da sauri ta dago kai kamar wani robot da makirkirin shi ya bashi umarni. Mami ce tare da wata mata wacce Zahara bata santa ba, da kuma wani namiji da zai kai talatin. Zahara, zuciyar ta da take tunanin ta dan samu sukuni, tuni ta cigaba da bugawa da sauri-sauri. Da ka kalle ta kasan a tsorace take. Mami da kullum fuskar ta cikin fara'a take, yau a murtuke take. Tunanin abinda ya kawo su Zahara take.

Ruwa da lemu Mama ta kawowa bakin amma basu da alamar zasu taba wani abun. Da ganin haka Zahara tasan ko ma me ya kawo su yana da alaka da ita. Tun haduwar ta da Amriya babu wani abu dake tafiya daidai. Sosai take da nasanin kula Amriya. Dama hakuri kawai ta bata tayi tafiyar ta gida, da duk hakan bata faru ba.

“Zahara baki ji ana miki magana ne?” Cewar Mama.

Duka kallo ya koma ga Zahara. A daburce ta bayar da hakuri.

“Ba komai kawai ina son jin ko kina lafiya ne?” Cewar Mami.

Kai a kasa cikin sanyin murya Zahara ta amsa da
“Lafiya kalau.”

“Toh madallah, abinda yasa nazo tare da dan uwana Ali da kuma yar uwata Mariya, dan muyi magana ne akan abinda ya faru rannan a gida na.”

Koda tace hakan, Zahara taji idanun Mama a kanta.

“Tun ranar ban samu runtsawa ba Zahara. Zuwan ki ba karamin fama min tsohon ciwo na yayi ba. Nasan mahaifiyar ki kuma kema na sanki... ko kuma ince ina tunanin na sanki. Ke yarinya ce mai hankali da tarbiya, wadda bata dagawa ko yaro murya bare babba. Toh tun zuwan ki gidana nake dorawa kaina wannan tambayar. Me yasa kika min haka? Me yasa kika kirkiri wannan labarin Zahara?”

“Mami wai me yake faruwa ne, ku yimin bayani. Me Zahara tayi?

“Asiya ke kamar yar uwa kike gare ni, amma ba zan taba lamunta ba wani naki yazo yamin rashin kunya. Zahara tazo gidana dauke da gyalen da na yiwa marigayiya Aisha kyauta. Tace min taga Aisha ne bakin kogi, kuma ita ta bata gyalen. Kin san wani yanayi na shiga a lokacin? 'yata Aisha ta rasu da dadewa toh me zai sa Zahara tazo har gida na ta fada min haka?”

“Tsaya kina nufin ita Zahara din ce, taje har gida tace miki taga Aisha bakin kogi?” Cewar Mama.

Gyada kai Mami tayi.

“Nasan akwai wani abu da ba mu fahimta ba a wannan lamarin. Nasan 'yata kuma ina da tabbacin ba zata je tayi miki rashin kunya ba ta wannan sigar.”

“Zahara? Mama ta kira sunan ta. Yi mana bayanin abinda ya faru. Ko dai kin ga wata ce mai kama da ita?

“Ai ban ce tasan Aisha ba.” Cewar Mami. “Aisha tun tana karama take hannun mahaifin ta a USA, tana cikin shekara ta 17 ne tazo nan Nijar wajen hutun karatu. Dan haka da wuya su san juna.”

“Zasu iya sanin juna ba tare da mun sani ba.”

“Kai hakan zai yi wuya, kuma wannan ba shi ne zai sa tayi min abinda tayi min ba.” Cewar Mami.

“'Yata.” Cewar Mami da murya mai alamar kuka. “Har abada nasan ba zan sake ganin 'yata ba. Kuma har yau ina nadamar bari da nayi mahaifin ta ya tai da ita. Ban kawo zata tafi ta barni ba haka da wuri. Ta tafi da wani bari nawa, ke da kanki Asiya kinsan ba haka ba nake ba a da. Har abada ba zan manta da ciwon rashin ta da nake ji ba. Bamu wani zauna ba sosai a tare, amma soyayyar uwa akan danta bata jin wani nisa. A gaban idanuna ta mutu, ina cikin ambulance din da ta dauko ta. Mala'ikan mutuwa ya dauki ranta a gaban idanuna. Har abada ba zan manta da kallo na karshe da tayi min ba, kallon da yake dawo min kullum a cikin mafarkina. Asiya ke yar uwata ce, amma ba zan lamunci abinda 'yarki tayi min ba. Ba zan lamunci rashin kunya kiri-kiri akan margayiya ba.”

Zahara ta rasa ta yaya zata fada masu ita bata taba sanin wata Aisha ba. Ba ita taso su hadu da matar nan wacce tace mata sunan ta Amriya ba, kuma take kama da 'yar su da ta mutu da dadewa. Taji tausayin Mami sosai amma ita bata da laifi a ciki. Da gaske ita taga 'yarta bakin kogi dan haka me zai sa tayi karya. Yanke shawarar kawai ta baiwa Mami hakuri tunda babu wani kwakwaran bayani da zata yi masu su yarda da ita. Zata bata hakuri koda kuwa daga ranar ba zata sake yi mata irin kallon da take yi mata a baya ba.

“Zahara kina da abin cewa ne?”

“Mu kawai muna son ta gane cewa bama wasa da irin wannan abubuwan. Bansan me yasa tayi haka ba, amma ya zama shine na karshe.” Cewar dan uwan Mami.

Akwai ciwo a zarge ka akan abinda baka yi ba, amma Zahara ba yanda ta iya dan bata da wata hujjar kare kanta na cewa taga yarinyar jikin hoton nan kuma ma har ta fada cewa Mami ce mahaifiyar ta.

“Kina da abin fada ne? Yi min bayanin meke faruwa dake Zahara?” Cewar Mama.

Sunkuyar da kai Zahara tayi, tana rokon Allah ya kawo mata dauki na wannan yanayi da take ciki. Jin ta take tamkar barewa a tsakiyar kuraye.

“Dan..dan Allah kuyi hauri, insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.” Zahara ta fada tana share hawayen da suka zubo mata.

Dago kanta tayi dan ta kalli Mami ta nuna mata da tsantsar gaskiyar ta tayi nadamar abinda suke tunanin tayi. Ganin idanun Mami cike da hawaye hakan ya kara karyar mata da zuciya.

“Kiyi hakuri Mami, nasan ba zan iya lallashin ki ba yanda ya dace amma insha Allahu Zahara ba zata sake zuwar miki da makamancin wannan zancen ba. Bansan gangancin me ya kaita yin hakan ba, amma nasan yanzun tayi nadama. Dan Adam ajizi ne, dan Allah ki yafe mata.”

“Shikenan na yafe mata Asiya, amma bana tunanin zan manta nan kusa.”

Har yanzu kan Zahara a kasa yake, jira kawai take su Mami su fita ko ta samu yin numfashi da kyau.

Suna tafiya Mama ta dawo kan Zahara akan dole sai ta fada abinda ya faru. Rokon mama tayi da ta barta ta samu bacci idan ta tashi sai tayi mata bayanin komai. Ba dan mama taso ba ta hakura ta barta taje ta kwanta. A babbar kujerar falon ta kwanta, domin tace babu tsautsayin da zai sake maida ta dakin ta. In har ba solution ta samu akan matsalarta ba.

Bayan kwana biyu, Zahara ta daina jin alamun komai, har ta dan fara sakewa. Har yau bata yiwa Mama bayanin komai ba. Duk lokacin da zata kawo zancen, sai Zahara tasan yanda tayi ta zame. Ba wai bata son fadawa mama bane, a'a tana tsoron kar ta saka rayuwar Mama a hatsari. Kuma ita ba zata juri hakan ba.

Zahara na tunanin abinda kwana biyu yasa bata sake jin wani motsi ba, saboda aikin dake gareta a office, yana mantar da ita wasu abubuwan. Office ba wani wuri bane da take so, amma tafi sakewa akan gida. Ba kamar idan Mr. Kamal yayi tafiya. Zahara tana mugun tsoron sa, ba ma Zahara kadai ba har ma da sauran ma'aikatan kamfanin. Bai cika zama ba a kamfanin amma idan yazo kowa shan jinin jikin sa yake, domin bayada wasa kuma kullum fuskar sa a murtuke take. Zahara kamfanin ma koma mata yake tamkar barikin soji. Tana shan wahala dalilin wannan matar Amriya amma Mr. Kamal yana daya daga cikin dodannin mafarkin ta, domin idan yana a wuri numfashi ma wahalar yi yake mata. Akwai kuma dan uwan shi, wanda ba halin su daya ba, kuma shine ogan su Zahara, wanda ita ce sakatariyar sa, Mr. Amar Yusuf sunan sa, amma suna kiran sa da Mr. CEO. Yana da kirki sosai, kuma kullum cikin fara'a yake, gashi da aji amma duk da wannan ba irin mai daukar raini bane idan abinda ya shafi aiki ne, amma a waje mutum ne shi mai girmama ma'aikatan sa, Ba kamar Mr. Kamal ba da fuska a daure kowanne lokaci. Wani lokacin Zahara har tambayar kanta take anya kuwa ma ya taba dariya.

Yau ma Zahara zaune take a office tana gyaren wasu takardu sai ga Mr. CEO ya shigo.

“Ina kwana Zahara, kin tashi lafiya?” Ya fada yana mata murmushi tare da ajiye jakar shi bisa desk din ta.

Cen cikin makoshi kamar koda yaushe Zahara ta amsa:
“Lafiya kalau...”

“Ba zaki tambayi ya nake ba?” Ya fada yana fiddo wasu files daga cikin jakar shi.

Murmushi kawai Zahara tayi tare da amsar files din da yake miko mata.

“Toh lafiya kalau nake, tunda ba zaki tambaye ni ba. Well, na duba wannan files din jiya sai dai basu cika ba. Zaki iya karanta su sai ki kara abinda babu. Zaki iya aje su wajen ki har zuwa gobe ma. Bana bukatar su yau.”

“Ok...” Amsar da ta bashi kenan.

“Dan Allah ko zaki hado min coffee, dan yau ban samu damar yin breakfast ba.”

“Ok, yanzu insha Allahu.”

“Thank you.” Yace kafin ya nufi office din sa.

Zahara ta mike da niyyar zuwa hado masa coffee, sai ga Sarat, intern ce a kamfanin, ta nufo ta da niki-nikin takardu a hannu.

“Ina kwana Zahara.” Ta fada tana sauke numfashi dakyar.

Amsawa Zahara tayi tana kallon ta.

“Dan Allah ko zaki mika min wannan takardun a dakin meeting? Wallahi yau a gajiye nake sosai.” Ta fada tare da zubawa Zahara su a hannu. Tsabar nauyin takardun kusan faduwa Zahara tayi, Allah yasa kujerar ta ta tare ta.

“Yauwa nagode Zahara, bari naje na dan huta.” Ta juya tana takun ta dai-dai har zuwa stairs. Zahara ta bita da kallo. Tana sanye da wani mini skirt baki kamar na kanwarta, sai kuma wata riga fara da ta fiddo da kusan rabin kirjin ta. Gashin kanta ya sauko har zuwa kafada, yasha gyara, gwanin sha'awa wanda yake ra'ayin shigar kamar irin Zahara, tana yawan rayawa a ranta da tana da kirji kamar na Sarat da ita ma zata dinga sa irin wannan rigunan.

Ba dan Zahara taso zuwa aiken Sarat ba, tayi hakan ne dan kar taga tayi mata ba daidai ba. Daman ta saba yi mata haka, aikin da ya kamata tayi sai ta baiwa Zahara shi, alhali itama tana da nata aikin ba kadan ba. Idan zata bata aikin, zata kirkiro wani abun tace ko kanta na ciwo ko kuma ta gaji. Zahara na son tace ba zata yi ba, amma tana tsoron Sarat ta sakata a layin makiyanta. Bare kuma daman Sarat mafadaciya ce, ita kuwa a halin da take ciki ba zata so ta kara da fadan Sarat ba.

Hanyar dakin meeting din ta nufa, in yaso bayan ta kai takardun sai taje ta hadawa Mr. CEO coffee shi. Tana cikin tafiya a tsanake zuwa dakin meeting, taji wata murya nace mata :
“Wawuya kawai, kin barta tana wani juya ki!”

Da sauri ta tsaya tare da waiwayawa ko zata ga mai maganar amma babu kowa. Kuma abun tashin hankalin zata iya rantsewa wannan muryar iri daya ce da ta Amriya da suka hadu bakin kogi. A ranta tace “Na tabbata kwalwa ta ce ke kitsa min wannan abin.” Haka tayi ta maimaitawa tare da cigaba da tafiyar ta. Bata sani ba ko tsoro ne yasa, amma tunda taji wannan muryar kalar yanayin corridor ta sauya. Corridor dake da haske ga kuma kwalliyar fulawowi da aka kayata ta da ita, amma ta sauya zuwa duhu, har da wata yanar gizo gizo kamar tsohon kangon da aka shekara dari ba'a shiga ba. Yanayin lungun ya komawa Zahara kamar a cikin horror film ko a makabarta... Sauri Zahara ta cigaba da yi, amma wannan karon har da kukan jemagu take ji. Gudu ta fara iya karfin ta, abinda kawai take so a wannan lokacin shine ta fita daga cikin corridor da taga batada niyyar karewa.

Nauyin takardun dake hannun ta suka fara gajiyar da ita. Cikin rashin sa'a, kafar ta daya ta bugi dayar ta fadi kasa tare da takardun. Kokarin tashi tayi amma taji hannu bisa kafadar ta, bata san lokacin da ta kurma uban ihun tsoro ba.

________________________________________

Karshen wannan chapter kenan, ku biyo ni domin jin yanda zata kaya.
AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)

Love 💞 and Horror ☠️ story 📖

By Malik al-Ashtar 🖋

On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485

CHAPTER 2


*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo

*[📝I.W.A📝]*

Kowa a offishin yaji irin karar da ta fito daga corridor, hatta Mr. Kamal da

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login