Showing 42001 words to 45000 words out of 87059 words
dalilin ta ne na rabu da Ammar. Ta dalilin mahaifiyar sa ne da shi kanshi.”
“Eh amma ita ta fara zuwar muku da matsala a soyayyar ku, zan yi magana da Ammar. Idan na fada masa komai wata kila ya iya budewa dan uwan sa idanu ya gane ko wacece Zahara.”
“Fushi ne zai ja kiyi abinda zaki jagula komai. Kuma nice zaki cutar idan kika yi hakan.”
“Kinsan babu abinda nake so da ya wuce farin ciki kawata. Amma ba zan iya barin yarinyar nan tana yin yanda taso ba.”
“Kiyi tunani ba wai dan kin bata ta ba, Kamal zai dawo gare ki. A'a, saidai ma su kara samun kusanci, dan haka kar ki ce komai, ki jira lokacin da ya dace. Idan nice ke, zan bi abun da nutsuwa. Kiyi kokarin kusantar shi, ki nuna masa kin amince ku cigaba da abotar ku.”
“A'a ba zan iya yin hakan ba. Amma nasan kina da gaskiya... Ya kamata in kara yin tunani kafin daukar wani mataki.”
“No, kiyi kokarin mantawa da komai nake nufi. Idan kika cigaba da saka abun a ranki zai iya zame miki wani ciwo.”
“Salmah matsalar ita ce bana bukatar in manta. Ba zan iya rungume hannuwana ba, ba tare da nayi wani abun ba.”
A BANGAREN ZAHARA
Wannan satin gaba daya, bata samu time din kanta ba, ga aikin office ga kuma shirye shiryen auren cousin dinta Maryam. Ba wani sanin juna suka yi da Maryam din ba. Kasar waje Maryam tayi karatun ta, ta girmi Zahara da shekara biyar. Ta dawo daga karatu a kasar Germany, tazo gaishe da Mama tare da sanar da su maganar auren ta. A nan ne Mama ta gabatar da ita ga Zahara.
Maryam mace ce mai saukin kai, tana hira da Zahara kamar sun dade da sanin juna. Sun karbi numbobin juna, suna waya akai-akai. Ta roki Zahara da ta taimaka mata wajen shirye-shiryen bikin auren. Zahara ba mai son shagulgula bace amma ba zata iya ce mata a'a ba. A daren ranar bikin, ta nemi Zahara taje gidan su ta kwana. Zahara taji dadin hakan, itama Mama tayi murna sosai da Zahara ta sanar da ita. Ko ba komai hakan zai fara sa Zahara ta fara kawaye.
Dan haka Zahara ta shirya yan kayan da zata je da su, taje gidan. Jajibirin biki ne amma gidan cike yake da yan uwa da abokan arziki. Lokacin da Zahara taje, Maryam ta gabatar da ita a wajen kawayen ta Hafsat da Farida. A nan suke fada Hafsat da Maryam a makaranta cen Germany suka hadu. Ita kuwa Farida kawa ce tun ta yarinta. Hafsat kamar Maryam take, akwai raha da sakewa da mutane. Ita kuwa Farida ciki ciki take, bata wani cika son yin magana ba. Sun iya kokarin su ganin Zahara ta sake da su. Har wani lokacin tana dan tsoma bakin ta idan suna hira...
Zuwa karfe sha daya na dare, cacaniyar gidan bata rage ba kuma har lokacin su Zahara basu ci komai ba. Yayin da sauran ke ta surutun su, Zahara da Farida suka yanke shawarar fita waje siyan abinda zasu ci da sauran.
“Ni zan biya kudin.” Cewar Farida tana fiddo kudi yan goma-goma daga cikin jakar ta. Sannan ta kara da cewa
“Zaku biya ni idan anje wajen party gobe.”
“Ai dama rowar ki ba zata bari mu ci mu sa miki Albarka ba.” Hafsat ta fada tare ce musu su biyo mata da ice cream.
Farida sai da taji abinda kowa yake bukata sannan ta cewa Zahara su je. Bakin titin yana da dan nisa da gidan, dan haka dole sai sun dan yi tafiya kafin su samu taxi. Bayan sun dan yo nisa da gidan, Farida tacewa Zahara ta manta id card dinta gida. Zahara tace to bari ta jira ta nan ta koma ta dauko.
Titin tsit yake, motoci daidaiku ne ke wucewa. Zahara bata tunanin ma zasu samu taxi ko dan sahu da wuri. Allah yasa ma akwai fitilun kan titi in ba haka Zahara zata ji tsoron tsayuwa ita kadai.
Tayi nisa cikin tunani, lokacin da ta fara jiyo kukan yaro. Da sauri ta juya ta hangi wani yaro cikin duhu inda fitilar hanya bata haska ba. Cikin dan tsoro tsoro Zahara ta wai-waiga ko zata ga wani babba da ke tare da yaron amma babu kowa. Dan haka ta karasa wajen yaron a hankali.
“Sannu..” Ta fada cikin tausashiyar murya dan kar yaron ya tsorata.
Yaron ya cigaba da kuka ba tare da ya kalle ta ba.
“Ina wanda kake tare da shi?” Ta tambaye shi, cikin sheshekar kuka yace
“Gi..gida..nake..son..naje...”
“Ina ne gidan naku yake? Kana tsoron zuwa gidan ne kai kadai?”
Gyada mata kai yaron yayi.
“Da kai da wa kazo nan?”
Bai bata amsa ba ya cigaba da kuka.
Tausayin yaron ne ya kama ta, a ranta tace bata san me yasa wasu iyayen basu da kula ba. Ta yaya zasu bar yaro ya fito a irin wannan lokacin?
“Kasan hanyar gidan naku? Ni zan raka ka kaji.” Ta fada da sigar rarrashi. Da jin haka yaron ya fara rage sautin kukan sa, har yayi shuru.
A daidai lokacin Zahara ta jiyo muryar Farida a bayan ta.
“Zahara? Me kike yi kuma a nan? Muje, sorry na dan jima ko."
“Ina zuwa Farida, bari in raka yaron nan gidan su. Yanzu na dawo ! ”
“Wane yaro kuma?” Farida ta tambaye ta cike da mamaki.
Juyowa Zahara tayi da niyyar nuna mata yaron amma babu yaro babu alamun sa a wurin. Ya bace bat.
[03/03 à 05:18] ASHTAR: AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
For more novels https://bit.ly/3Egdy1m
On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485
CHAPTER 15
⚖ HOME OF QUALITIE'S WRITERS ASSOCIATION 📚
Zahara bata taba jin nauyi irin na yau ba. Karasowa tayi a sanyaye ta gaishe su da siririyar murya. Tambayoyi ne birjik a cikin kanta wanda ta gagara amsa su...
“Zo ki zauna 'yata, bari na kawo abin sha.”
Tashi Mama tayi ta nufi hanyar kitchen. Da kallo Zahara ta bita kafin ta yanke shawarar zaunawa domin jin me ke tafe dashi. Karasawa tayi a hankali ta zauna kusa da yayan ta da ta jima rabon ta da shi. Koda ta zauna, suka fara magana. Ji tayi suna maganar zane (art), suna fadar wasu abubuwa da bata taba jin su ba a rayuwar ta. A bakin Kamal, ba abin mamaki bane, domin ganin zanukan dake cikin falon sa, ta tabbatar shi mai son zane ne amma bata taba tunanin yayan ta yasan wani abu ba a harkar zane.
Mama ce ta dawo dauke da jus da ruwa, kama mata Zahara tayi wajen zubawa su Kamal. A yanda take a rikice, addu'a take kar ta barar da lemun. Bayan ta zuba musu lemun, Mama tayi shigewar ta daki. Yayan ta kuma baida niyyar tashi ya barta tare da Kamal. Duk da ba wasu makusanta bane sosai ita da yayan nata, amma kowa a gidan yasan yanda yake bata kariya. Bayan wasu mintuna, ya yanke shawarar basu wuri.
Kamal shan lemun sa yake cikin kwanciyar hankali, ita kuwa na ta kokarin ganin ta sarrafa tambayar da take son yi masa. Jira take har ya gama shan lemun, bai kuwa bata lokaci ba ya ajiye kofin.
“Ya kike?” Ya tambaye ta yana kallon ta.
“Lafiya lau...”
Tayi niyyar yi masa tambayoyin amma kamar an toshe mata baki. Sunkuyar da kanta tayi, domin bata iya jure kallon sa... bare kuma da yace yana son auren ta.
“Na sani, da na sanar da ke kafin nazo gidan ku amma kuma bana son ki ki karba ta. Nazo ne kawai na gabatar da kaina gidan ku, domin nuna da gaske nake ba da wasa ba. Abinda kika fada min rannan yasa nayi nazari sosai. Bai dace ki yarda da ni ba, alhali bamu wani san juna ba. Ba zan takura ki ba, domin ki aminta da ni. Nasan kina da tambayoyi da dama, ki sani zaki iya fada min komai. Zan kokarta ganin na amsa duk wasu tambayoyin ki.”
Shuru yayi kafin ya cigaba
“Kuma bana son kiyi tunanin zuwa gidan ku da nayi saboda wata manufa ce ta daban. Idan kina so, ba zan sake zuwa ba, har sai idan ke kika ce nazo.”
Sauraron shi take da kyau kuma ta kasa daina zuzuta kanta kan cewa yayi wannan tattakin ne saboda ita, domin tabbatar mata da gaske yake. Ba zata iya cewa ba ta yarda dashi, amma tasan ba yanda za'a yi ya dinga duk wannan kan abinda baida muhimmanci a wajen sa.
“Me yasa ni? Me yasa sai ni kake son aure?”
“Ba zan iya amsa wannan tambayar taki ba Zahara...”
Tana jin dadin yanda yake kiran sunan ta.. cike da yanga da dadin ji.
“Ba zan iya amsa tambayar ki ba, domin ni kaina bani da amsar ta. Ba zan ce ina miki mahaukacin son nan domin idan na fadi hakan nayi karya, amma kina daukar hankali na sosai. A da ina tunanin hakan a matsayin birgeni kawai kike, amma na gane yafi hakan. Ni ba yaro bane, ba wai dan kina daukar hankali na ba zan yi wata alaka da ke, mu rabu bayan na samu wacce nake so. Addini na yayi min hani da yin hakan. Kina daukar hankali na ne kawai, domin kamar yanda kika ce bamu wani san juna ba. Dan haka zan yi kamar yanda masu cewa soyayya wata aba ce dake ginuwa ta hanyar sanin masoyi, sanin halin sa har ma da kurakuran sa. Dan haka ina son sanin wacece ke kuma idan kema a lokacin kin ga wani abun da yayi miki game da ni. Ki sanar da ni zan zo na nemi auren ki.”
Shuru yayi domin barin ta taji da abinda ya koro mata.
“Of course, idan baki da ra'ayin yin hakan, zan fahimta. Zan ji ba dadi amma zan fahimta, zan yi kokari ganin ban dauki abun da nauyi ba. Ina son kiyi tunani sannan ki fada min abinda kika yanke. Waya ta a kunne take a koda yaushe, zaki iya kira na kowanne lokaci, a lokacin da kika so, zan kasance cikin kaguwar jin amsar ki da sa ran ki amince.” Ya fada da dan guntun murmushi.
A ranta tace, yana tunanin ba abinda zata yi da shi alhali a rikice ne take. Bata san amsar da zata bashi ba, dole ma ta samu nutsuwa tayi tunani.
“Ni zan tafi kafin dare yayi. Kar ki manta, zaki iya kira na a kowane lokaci. Zan zauna zaman jiran amsar ki.” Ya sake tunatar da ita kafin ya mike tsaye.
Mikewa tayi itama da sauri kamar wacce aka sawa remote, tana jiran ya tafi amma ya matso inda take tare da miko mata wani kwali. Hannun sa ta kalla, ta kalli kwalin sannan ta kalle shi.
“Chocolate ce, ban sani ba ko kina son irin wannan abubuwan. Ina son kawai yi miki kyauta ne.”
“Ba zan karba ba..” Ta fada murya cen kasa.
Hannun ta ya kama tare da dora mata kwalin.
“Zaki iya zubarwa, amma ina tabbatar miki chocolate akwai dadi. Ki karba, zan ji dadin haka.”
Karba tayi tare da yi masa godiya. Murmushi yayi sannan yayi hanyar fita daga falon. A daidai lokacin Mama ta fito daga kitchen.
“Ina zaka je? Girki ya kusan kaiwa.”
“Zan dawo wani lokacin Mama, inda nake ne akwai nisa.”
“Toh Allah ya tsare ka gaishe da mutan gidan.”
“Zasu ji Insha Allahu.” Ya fada tare da nufar hanyar fita. Zahara na biye da shi domin rufe kofa idan ya fita. Lokacin da ya fita, sai da ya juyo ya kalle ta tare da yi mata sai da safe.
“Allah ya kaimu and thanks for chocolate.”
Murmushi yayi mata kafin ya shiga mota. Tayar da motar yayi, har sai da yayi nisa sannan ta koma gida.
Da shigar ta gida, Mama ta shiga kallon tana mata murmushi. Kunya ce ta kama ta tace
“A'a Mama, babu abinda zaki ji...”
“Ban taba tunanin my little girl tana da saurayi ba, kuma kyakyawa dashi. Me yasa baki fada min zai zo yau ba? Da na gama girki da wuri.”
“Lahh Mama ba fa saurayi na bane, kuma bansan zai zo ba.” Zahara ta fada tare da hayewa sama da tunanin ko Mama ta bar zancen, amma Mama ta biyo ta har daki.
“Mama...”
“Ba fa zaki ce min kawai aboki ba ne. Naga yanda yake kallon ki kuma ke baki son kallon shi.”
“Ba wanda nake iya kallo cikin ido Mama.”
Tayi kokarin kare kanta amma dariya hakan yaba Mama.
“Ni dai nasan akwai wani abu tsakanin ku. Me ya fada miki kenan?”
“Please.. Mama ki daina. Bana son yin maganar da ke...” Zahara ta fada tana boye kanta bayan pillow.
“Toh ai baki da kawayen da zaki fadawa. Ni gani nan, zan iya baki shawara. Oya, yarinya ina sauraron ki."
Mama tana da gaskiya Zahara bata da wata kawa da zata iya hira da ita. A irin wannan yanayin ne take nadamar yanda take amma bata shirya irin wannan hirar da Mama ba.
“Zan fada miki komai Mama, i promise.”
“Shikenan, ina jira. Zan je in karasa girkin.”
Bayan Mama ta fita, Zahara ta koma ta kwanta bisa gado, ta shiga juye-juye kamar hakan zai taimaka mata wajen gyara hargitsin dake cikin kanta. A confusing take sosai. Yace yana son relation ta gaske, amma ita bata taba yin saurayi ba, tana da raunin experience a wannan fannin, ta yaya zata fara maganar aure? Shida bama ya cikin tsarin ta, aure da yake karshen list na objective din ta.
Kamal yana birge ta, wannan ko tantama bata da amma bata tunanin zata iya kasancewa matar da yake buri...
A BANGAREN KHADIJA
A yau ta karbi albashin ta, ta shirya zuwa gidan Kamal domin yi masa wata kyauta. Odan dinner tayi daga “Eden restaurant” inda ake soya lafiyayyu kaji. Tana sa ran da wannan kazar, yau ta samu kanshi domin tana tunanin kamar gudun ta yake. Ta sani aikin da yake dole ya kasance busy amma a da yana samun damar kiranta dan jin ya take.
Tayi kewar shi sosai, yana wahala rana ta wuce bata yi tunanin sa ba. Idan ta kira shi baya dagawa sai bayan wasu awanni yake sake kiranta, kuma shima dan yace mata yana wani aiki ne ya sake kiranta. Kiran da ba zai yi ba kenan. Bata san dalili ba, amma a da baya mata irin wannan halin. Dole akwai abinda ke faruwa wanda bata sani ba. Dan haka ta yanke shawarar yi masa bazata.
Salmah har yanzu tana gidan ta, bata jin dadin barin ta ita kadai a gida bare ma yanzu da take cikin wannan yanayin, amma kafin ta fito ta tabbatar mata da babu abinda ke damun ta, ita ma ta taimaka mata wajen zaben kayan da zata saka.
“Bakin abu na yi maki kyau.” Cewar Salmah tana mai ja mata zip din riga.
“Thanks my dear. Rigar tana da tsada, tayi min ne ba yanda na iya dole na siya.” Cewar Khadija.
“Zaki yi kwalliya ne?” Salmah ta tambaye ta.
“Eh amma ba da yawa ba, babu lokaci gaba na. Gashi odan da nayi yana hanya. Me zaki yi bayan tafiya ta?”
Sai da Salmah taja dogon numfashi kafin ta bata amsa.
“Da ina tunanin fita, amma ban sani ba.”
“Kizo muje tare gidan Kamal din. Hakan zai dan debe miki kewa.”
“Bana bukatar ganin ko daya daga cikin dangin Ammar kuma bana so na takura ku.”
“Ba fa wajen soyayya zan je ba.”
“Eh amma, zaki iya amfani da wannan damar ki fada masa abinda kike ji game da shi.”
“Bani da wannan kuzarin, yana dauka ta a matsayin best friend din sa ce.”
“Kece kike daukar kanki matsayin best friend. Idan da kin fada masa tun farko da tuni kuna ta shan soyayyar ku.”
“Idan yana sona, da tuni ya fada mini.”
“Ai kin fi kowa sanin shi, kinsan yanda yake da dan shan kai.”
“Banda lokacin da yasan yana san abu.” Khadija ta bata amsa.
“Eh, ai baida budurwa ko kuwa? Mai yiyuwa yana jira ki fara fada ne.”
“Baida budurwa, amma shi ba irin mai jiran nan bane, idan da gaske yana son na zama budurwa sa, da tuni ya sanar da ni. Daina bani fake hope Salmah.”
“Ba zaki samu duk abinda baki gwada neman shi ba, nidai na fada miki.”
“Kafin ki tura ni gun Kamal, ki fara gyara tsakanin ki da Ammar.”
“Daina yimin wannan zancen. Kema kin sani ta kare tsakanin ni da shi. Ba zan so na dawo baya ba. Ke kuwa kar ki yarda ki rasa damar ki.”
_“Tana da gaskiya, babban kuskure ne rasa namiji irin Kamal.”_
Juyawa Khadija tayi da sauri ganin wanda ya rada mata wannan maganar a kunne. Amma babu kowa daga ita sai Salmah.
“Kece kika fadi haka?” Ta tambayi Salmah.
“Na fadi me?”
“Kika ce « babban kuskure ne rasa namiji irin Kamal. »”
“A'a ban fadi haka ba, sai idan mafarki kike dai. Mai yiyuwa kin fadi hakan ne a zuciyar ki.”
A'a.. ita bata fadi hakan ba a zuciyar ta, da kyau taji wata muryar da ta gayi hakan. Ko kuma Salmah tana da gaskiya, mafarkin tsaye ne take.
Daidai lokacin da ta gama kwalliya aka danna kararrawar kofa. Turare ta fesa sannan ta dauki karamar jakarta.
Kazar da tayi oda ce, karba tayi ta biya kudin. Sannan ta nufi bakin hanya, tayi saurin samun dan sahu, ta fada masa inda zai kaita. Ba bata lokaci ya ajiye ta bakin kofar gidan Kamal. Konkwasa kofar tayi, wutar gidan a kunne take hakan ya tabbatar mata da yana nan.
Sautin tafiya taji yana tunkaro kofar. Kamal ne ya bude mata.
“Khadija..” Ya fada da mamaki.
“Ni da kaina.” Ta fada tana murmushi.
“Me kike a nan, daidai wannan lokacin?” Ya tambaye ta.
“Kamar ya me nake yi? Nayi kewar ka ne. Ko bani da 'yancin kawo maka ziyara ne?” Ta tambaye shi.
“A'a, amma ban yi tsamanin ganin ki bane. Ok, shigo.” Ya fada tare da kaucewa dan ta shiga, babu bata lokaci ta shige.
Tasan gidan sosai, dan haka kai tsaye ta wuce falo tayi dare-dare bisa kujera. Komai na falon a tsare yake, kamar yanda ta saba tarar da shi, TV a kunne amma tana tunani yana cikin yin zane ne.
“Na takura ka ko?” Ta tambaye shi lokacin da ya dawo cikin falon, yana sanye da T-shirt da ta fito da kirar shi.
“No, kar ki damu. Ina cikin yin zane ne.”
“Nasan ka tsani a takura maka lokacin da kake zane amma ba zan iya kara kwana daya ba tare da na ganka ba, nayi kewar ka sosai. Ban sani ba ko nice na sa a kaina, amma naga kamar da gaske gudu na kake.”
Da farko dan daure fuska yayi, amma bayan