Showing 15001 words to 18000 words out of 87059 words
ta, gida zan je.” Ta fada da dan fada fada.
“Ina Zahara, har taci abincin ne?”
“Meye damuwar ka Amar? Bani jakata nace!”
Amar jakar ta ya mika mata domin baya son ta tara masa mutane. Shuru-shuru ce ita wata kila amma idan ranta ya baci ba kyau.
“Muje na raka ki.”
“A'a, i zaman ka nan. Je ka gani idan Zaharaka taci abinci da kyau. Zan iya kai kaina gida, kuma kar ma ka gajiyar da kanka wajen biyo ni.”
Amar da tunanin ko maganar da suka yi dazu ce ta sanya Salmah ke wannan abun, ya yanke shawarar barinta ta tafi tare da bata dan lokaci har ta samu nutsuwa.
A gidan su Zahara kuwa, Mama ce hankalin ta a tashe na ganin sauyin Zahara, yasa ta nemi da malami kuma limamin unguwar da ya taimaka mata. Bayan yazo gidan, Mama ta bashi labarin abinda ke faruwa da 'yarta. Koda ta fara zayyana masa irin sabbin dabi'un da ta tsiro dasu, ya tabbatar da shafar aljanu ce kuma tana bukatar rukiya. Mama cike da farin ciki ta nemi da malamin ya fara rukiyar idan Zahara ta dawo. Malamin ya yarda da bukatar Mama, amma yace ta bashi awa daya zai je gida kafin Zahara ta dawo. Baya bukatar komai, kawai yana son ace Zahara tana nan.
Da fitar malam daga gidan ba'a fi rabin awa ba sai ga Zahara ta shigo gidan fuskar ta dauke da murmushi... Da saka kafar ta cikin gidan, taji wani zafi ya sauka jikin ta, fasa kara tayi tare da zubewa kasa a wurin. Mama ce ta kusan zubewa lokacin da ta tarar da Zahara kwance a kasa bata motsi.
“Zahara, Zahara” Mama ta shiga jijjigar ta domin ta tashi.
Sai da aka dau lokaci kafin Zahara ta farfado, amma tana jin duk jikin ta a mace, kuma wannan karon taji ta dawo a Zahara ta da. Kunyar Mama ce ta rufe ta ganin irin kayan dake jikin ta. Kanta kasa tacewa Mama :
“Zan hau sama.”
Taimaka mata Mama tayi ta mike tsaye amma bata barta ta tafi ba. Zahara kallon Mama tayi.
“Na dan gaji ne, nasan da na samu bacci zan warware.”
“Muje falo tukunna, daga baya kin kwanta ki huta.”
“Saboda me ?”
“Zamu yi bako ne.”
Zahara bata sake cewa komai ba, tabi bayan mahaifiyar ta. Falo suka zauna suka shiga jiran Malam.. Mintuna.. Awanni babu labarin Malam Liman, Zahara da ta gaji da jira ta bingire nan ta shiga bacci. Mama har zuwa goman dare tana jiran Malam Liman da tunanin wata kila wani abun ne ya rike shi. Dole ta hakura ta tashe da Zahara ta raka ta daki ta kwanta.
Washe gari da safe Zahara ta shirya zuwa wajen aiki, ta tarar da kusan duka gidan sun hadu cikin jimami. Tana son ta tambayi meke faruwa amma tana jin kunyar yin maganar a gaban yan gidan su. Ba tare da kowa ya lura da sauyin da ta samu yau ba, ganin kwana biyu sauyin da ta samu na saka matsatsu kaya, yin kwarkwasa da sauran su, amma yau ta dawo kamar da sanye da shigarta wadda take yi a baya kuma ta kasa daga murya tayi magana.
Ba wanda ya lura da ita, domin duka suna cikin alhinin mutuwar Malam Liman da tazo musu jiya.
Zahara sulalewa tayi ta fita zuwa wajen aikin ta. Da zuwan ta cen ta tarar da uban gidan ta. Shi da kullum take rigan shi zuwa, Zahara ta dauka tazo a latti ne, nan ta shiga ba Mr. Amar hakuri.
“Me yasa kike bani hakuri? Nazo da wuri ne yau, da yake akwai abinda zan karasa mai muhimmanci.”
Mr. Amar bai daina azawa kansa tambayoyi akan canzawar shigar sakatariyar sa ba da kuma dabi'unta. Bata iya magana sosai kamar jiya, kuma bata iya kallon sa cikin ido. Kansa ya daure! Tunani yake meke faruwa cikin wannan kankanin lokaci, wannan yarinyar akwai abin al'ajabi a tare da ita.
Zahara godiya ta yiwa uban gidan ta kafin ta nufi ofishin ta da tulin aiki ke cen yana jiran ta. Sai dai ta kasa maida hankali kan aikin domin ta kasa daina tunanin abinda ya faru kwanakin nan biyu da suka wuce. Kwarai, tana tune da komai, tasan duk abubuwan da ta aikata wanda bai dace ta aikata su ba tana cikin hayyacin ta, wani abu ya shiga jikin ta.
Tasan cewa ba kowa bace ta aikata mata hakan face Amriya kuma ko ba dade ko ba jima zata sake dawowa.
AMRIYA
(Hatsabibiyar Aljana)
Love 💞 and Horror ☠️ story 📖
By Malik al-Ashtar 🖋
On wattpad : https://www.wattpad.com/story/270492485
CHAPTER 5
⚖
*HOME OF QUALITIE'S WRITER'S ASSO📚*
_(The Home Of Qualitative Writers That Are Educate Humanities)._
https://www.facebook.com/100495222137315/posts/100496042137233/?substory_index=1&sfnsn=mo
*[📝I.W.A📝]*
Kwanaki da yawa sun shude, Zahara bata sake jin wani motsin Amriya ba, babu wani sauyi da ta sake ji a kanta. Wannan shurun kuwa ba karamin tayar mata da hankali yake ba. Tana son tayi amfani da wannan shurun wajen cigaba da rayuwar ta kamar baya, amma duk lokacin da zata nufi wannan corridor sai taji kamar ana kallon ta. Sai dai ba ita kadai bace ke cikin rudu ba a wannan kamfanin. Uban gidan ta da sauran abokanan aikin ta hankalin su a tashe yake na ganin sauyin da ta samu. Sai dai ba wanda yayi gigin fadar wani abun dan kar su janyo fushin uban gidan su.
A yau, Mr. Amar Yusuf ya shirya wata yar walima a gidan su domin taya kamfani murna kan wata contact da ya samu daga kasar Korea. Mr. Amar ya nemi duk ma'aikatan su hadu a dakin meeting inda ya basu labarin nasarar da suka samu da kuma walimar da ya shirya tare da basu adreshin gidan su. Zahara da tuni ta yanke shawarar kirkiro wani abun da zai hana ta zuwa, taji Mr. Amar yace wajibi ne kowa sai ya halarta.
Bayan duk abinda ta aikata, duk abinda wannan Amriya ta aikata mata, bata jin zata iya zuwa wajen wannan walimar, amma gashi uban gidan ta yace wajibi ne sai kowane ma'aikaci yaje. Kuma ita ce sakatariyar sa dan haka dole idan bata je ba zai gane. Allah Allah take kar budurwar sa taje, domin ba zata iya hada ido da ita ba. Ga kuma dan uwan shi Mr. Kamal, idan ta kai kanta har gidan su, tasan har fitsari zata iya yi a wajen. Irin kallon nan nashi.. har yau yana zo mata a munanan mafarkan ta.
Zungurar ta da taji ana yi ne a baya ya dawo da ita hayyacin ta, ta juya taga Sarat ce.
“Wane irin kaya zaki saka?” Sarat ta rada mata a kunne ta yanda sauran ba zasu ji ba.
Har yanzu suna cikin dakin meeting, duk da an kare meeting din amma basu watse ba kowa maganar walimar yake.
“Toh yaya?” Sarat ta sake tambayar ta.
Kada mata kafada Zahara tayi alamar bata sani ba. Ita ba wasu kaya gare ta, bacin jeans da dogayen rigunan da ba zata iya zuwa wajen walimar da su ba. Dan haka kawai zata yi shigar ta ne kamar yanda ta saba. Zata je ne kawai dan a san tazo.
“Muna iya zuwa muyi chopping.” Cewar Sarat, amma Zahara taki.
“Bakauya ce ke wallahi.” Sarat ta fada tare da jan tsaki. “Toh ni cancarewa zan yi, domin nasan manyan mutane zasu halarci wannan walimar, kuma ni akwai wanda nake hari. Ina son ya fada tarkona.” Sarat ta fada.
“Humm Allah ya bada sa'a.”
“Kin tabbatar ba zaki je muje ba? Zamu iya zuwa Ahmad SH Mall.”
“Akwai abubuwa da dama da zan yi, ki huta lafiya.” Zahara ta mike tsaye da niyyar barin wurin amma wani masifaffen ciwon kai da taji yasa ta koma ta zauna da karfi ta yanda tayi sanadin janyo hankalin mutane kanta.
“Zahara, lafiya?” Mr. Amar ya tambaye ta yana mai matsowa kusa da ita.
Da sauri ita kuwa Zahara tayi baya dan kar ya taba ta. Taga irin kallon da yayi mata ganin abinda tayi, hakan kuwa bai mata dadi ba. Bata son ta zamar masa wata matsala ce alhali yana da matar zai aura.
Kara kokarin riko hannun ta yayi, amma ta sake yin tsalle tayi baya.
“Kawai na dan gaji ne, kuyi hakuri dan Allah.” Zahara ta fada tare da ficewa daga dakin meeting din kamar wata barauniya.
Ta tabbatar yau, maganar ta kawai za'a dinga yi a kamfanin. Toilet ta shiga ta rufe kanta na wani dogon lokaci. Wanke fuskar ta tayi, ta dan huta kafin ta dawo hayyacin ta. Daga karshe fitowa tayi ta nufi hanyar ofishin ta, sai dai tana fitowa taci karo da Mr. Amar, jikin ta ya bangaji faffaden kirjin sa. Hakuri ta shiga bashi akan buge shi da tayi ba tare da ta gani ba.
“Kin dan jima, kin tabbatar lafiyar ki kuwa?”
“Eh, amm..nagode. Kar ka damu. Zan je na cigaba da aiki na kafin naje gida.” Ta fada da kokarin barin wurin amma ya riko hannun ta.
Oh please! Ta fada a ranta.
“Akwai wani abu da nake son baki, zo muje ofishi na.”
Kallon ta yake jiran jin amsar da zata bashi, ita kuwa addu'a take Allah ya kawo wanda zai kwace ta. Ba zata iya zama daga ita sai shi a ofishin sa ba. Bata son yayi tunanin ko ita irin marasa kamun kan nan ce.
“Ba zaki wuce minti biyar ba, daga nan zaki iya dawowa kiyi aikin ki.”
Bayan wasu yan dakiku na nazari, ta yanke shawarar bin sa. Suna shiga ofishin taji kamar yau ne ta fara shigar sa. Windows dake kusan a rufe, ga dan duhu da ofishin yayi. Duk da tana tunanin kwalwar ta ce ke nuna mata hakan, amma tana ji a jikin ta mai ofishin nan akwai abinda yake nufi da ita.
Tana nan tsaye kai a sunkuye, Mr. CEO sai da ya dan zagaya desk din ofishin kafin ya zauna kan kujerar sa. Dukawa yayi kasa kafin na dan wani lokaci ya dago hannun sa rike da wata katuwar bakar leda da ya miko mata. Sai da ta dauki yan dakiku kafin tasa hannu ta karba tana mai masa kallon tambaya.
“Naki ne, lokacin da naje Korea bayan mun gama meeting, da na samu dan lokaci, shi ne naje nayi chopping. Da naga wannan rigar, directly da ke na tuna. Shi ne na dauko ta saboda ke. Ki saka ta yau wajen walima nasan zata yi miki kyau.” Cewar Mr. Amar
Ba yanda za'a yi ta karbi wannan kyautar tashi. Yar dariyar yake ta saki kafin tace
“Sorry Sir, amma ba zan karbi wannan rigar ba.”
“Kar ki ce ba zaki karba ba, keda ko ganin rigar baki yi ba. Kuma wa ke maida hannun ma kyauta baya?” Ya fada fuska a daure, da alamar ba zai karbi ledar ba.
“Sir, kayi hakuri ba zan iya...” Katse ta yayi
“Zahara Usman ba zan karbi wannan kyautar ba, zaki iya jefar da ita idan kina so, amma ni ledar nan ba zata koma hannu na ba.” Mr. Amar ya fada wannan karon ransa a bace.
“Ok, nagode sir. Allah ya kara budi.” Tayi masa godiya kafin ta fita daga ofishin da saurin ta ba tare da ta jira ya sake magana ba.
Da ta sani da bata bishi zuwa ofishin sa ba. Duk wannan saboda Amriya ne. Ta tsani yanda take yi da ita. Ba zata sake barinta ta dinga amfani da ita ba. Gashi tana saka ta situations wandzma bata iya fidda kanta. Tana jin tsoron abinda zata iya yi mata nan gaba, amma insha Allahu ba zata sake bari tana amfani da gangar jikin ta ba.
“Zahara, sai mun hadu a walimar ko.” Cewar Sarat dake nufar stairs.
“Saratu, tsaya!” Zahara ta kwala mata kira kafin ta kai ga shiga.
“Oh ko kin yanke shawarar zuwa chopping din ne?” Sarat ta fada da tunanin ko Zahara ta sake shawara.
“A'a.” Zahara ta bata amsa. “Kawai ina son na baki wannan ne.” Zahara ta fada tana miko mata ledar hannun ta.
Amsa Sarat tayi ba tare da jira ba, tana tambayar ta meye a ciki. Ba ta jira jin amsa ba, ta bude ta ciro wata bakar kyakyawar doguwar riga. Ita kanta Zahara bata taba ganin riga mai kyau irin wannan ba, amma bata bukatar saka ta.
“Wow... Riga ce.. rigar da take ta wulakanci a duniyar fashion ce. Kin san kuwa irin tsadarta?” A rude Sarat ke tambayar Zahara ba tare da ta sauke idonta daga kan rigar ba.
“Zaki iya daukan ta.” Zahara ta fada da dan karamin murmushi a fuskar ta.
“Tsaya, wai Zahara da gaske kike? Wasa kike mini koh? Kada ki sa min rai idan kin san ba da gaske kike ba.”
“Taki ce Sarat, na bar miki.”
(....)
A hankali baki suka fara cika gidan su Mr. Amar da aka kayatar sosai. Abokai, dangi da abokan aiki duk sun zo amsa gayyata. A wani bangare cikin falon, wasu kawaye ne biyu ke hira ba tare da sun kula da karuwar da bakin ke ta yi ba.
“Karamar yarinya ce, kuma tana da dan hasken fata. Na tabbatar zata zo nan.” Cewar Salmah ga kawarta Khadija.
“Ki manta da ita, na tabbatar tayi hakan ne dan ta tunzura ki. Idan har kika biye mata kina dab da kawo matsala a tsakanin ki da Amar.” Shawarar da Khadija ke ba kawarta kenan.
“Ni ina son Amar ya gane, wannan yarinyar ba mutuniyar kirki bace, kamar yanda take nunawa.”
“Ina kara shawarta ki da ki manta da wannan. Ki yarda da ni ba abinda zai kareki da shi. Ki mayar da hankalin ki kan sirikar ki, kiyi abinda zata yarda da auren ku.”
Tunani Salmah tayi kuma ta gane gaskiya kawarta ke fada mata. Ya kamata ta mayar da hankalin ta ga dangin saurayin ta. Amma tayi alkawarin takawa Zahara birki nan kusa.
A wani bangaren kuwa, Amar ne ke ta lallashin Kamal da yayi hakuri ya tsaya har a kare walimar. Yana son da an ci abinci ya wuce gidan shi. Duk da miskilancin sa amma ya iya zuwa wannan walimar domin karfafawa dan uwan sa gwiwa wajen bayyana Salmah a matsayin wacce zai aura a yau.
“A takure nake ta yanda baka zato yau dinnan. Kasancewar ka nan zata bani kwarin gwiwa sosai. Ba zan iyawa rikicin Mommy ba idan ka bar wajen nan, amma idan kana nan zaka iya mata magana kuma ta amince.”
“Zan tsaya amma bayan dinner tafiya ta zan yi. Ka biyo ni muje tare idan baka son kwakwazon Mom. Idan bata amince ba yau, zata amince wata rana.”
“Idan da hakan na da sauki yanda kace. Well, ba zan tsayar da kai ba. Ai zaka aje Khadija ne gidan su idan an kare?”
Amar ke tambayar dan uwan sa, shi kuwa Kamal bai jin me yake cewa domin shagala da yayi wajen kallon yarinyar da ta shigo.
Ganin dan uwan nasa bai bashi amsa ba, yabi inda yake kallo da kallo, nan ya fahimci abinda ya daukar masa da hankali. Kusan duka kallo ya koma kanta. Tayi masifar kyau a cikin doguwar riga ja da ta hade da fatarta kuma tayi matching da kirar jikinta. Galala maza ke binta da kallo, ta zama tamkar gwal tsakiyar yan kasuwa a kasuwar baje koli. Wannan janyo hankalin da tayi, yasa matan wurin suka shiga kishi da ita, ita kuwa hakan take so.
Lokacin da take gida, tana kokarin shiryawa zuwa wajen walimar da bata kaunar zuwa, lokaci guda kuma taji babu abinda take bukata kamar zuwa wajen walimar. Tamkar wani abu ya shiga jikin ta. Sosai tasan irin wannan yanayin. Amriya ce ta shiga jikinta. Ta sani domin tana jin yadda kirjinta yake mata ciwo, alhali kwana biyu lafiya kalau take. Kokowa ta shiga yi da jikin nata ganin Amriya bata yi amfani da ita ba, amma ta kasa. Domin abinda take dashi yafi karfinta nesa ba kusa ba. Lokaci guda kuma, sai ta manta da kusan komai, babu abinda take tunani da ya wuce wannan walimar.
Da yan kudin dake gareta, ta ruga kasuwa siyan kayan da zata saka zuwa wajen walimar. Amfani tayi da hakan wajen siyo wasu abubuwan, irin kayan kwalliya, kananan riguna da siket, wanduna da kuma dogayen riguna. Bayan ta koma gida, sai da ta kwashe awanni da dama tana kwaliyya kafin ta gama. Har sai da ma ta shiga cikin lokacin walimar, Sai dai hakan bai dame ta ba. Lokacin da ta gama ta fito, taci karo da mahaifinta bai ko gane ta ba. Sai da tayi magana Abba ya gane yarsa ce. Baki ya saki yana kallonta da ganin irin shigar da tayi. Ba kamar matar shi ba, shi dadi yaji ganin sauyin da 'yarshi ta samu. Ita kuwa Zahara bata tsaya wani bata lokacin zagaya gidan gwadin dress dinta ba ta fice domin tuni tayi latti. Tana sanye da takalmin ta masu tsini da kuma yar hadaddiyar karamar jakarta. Dan sahu ta tsayar, tana zuwa ta tarar da Sarat bakin kofar gidan tana kara gyara kwalliyar ta. Tana sanye da doguwar rigar da Zahara ta bata. Tuni Zahara ta shiga da nasanin bata rigar da tayi, domin idan da a jikinta take sai tafi mata kyau, amma mai faruwa ta riga da ta faru. Wata kila kuma hakan ne yafi, ko dan abinda take kokarin shiryawa a yau din.
“Kinyi kyau fa kawata.” Cewar Zahara da kokarin yaba kwalliyar Sarat.
Dago kanta daga madubin Sarat tayi, tare da kare mata kallo sama da kasa.
“Wow, wai da gaske Zahara kece?” Sarat ta fada da mamaki.
“Ni kuwa da kaina. Hadaddiya Zahara.” Zahara ta fada tana wani juyi yanda Sarat zata kare mata kallo.
“Rigata tafi tsada, amma wallahi taki tafi kyau. Gashi kin bata hakkinta!”
“Eh yo ai dole, kyau ne ya hade da kyau. Ke ma ba laifi rigar ki tana da kyau. Daga Seoul ta Kasar Korea take. Mr. Amar ne yace na baki.” Zahara tayi mata karya tana kallonta cikin ido ganin ko karyar tata tayi tasiri.
Kyafta idanu Sarat tayi tare da kara matsowa kusa da Zahara tace
“Tsaya, dan Allah dagaske kike? Amar Yusuf Dan Ladi ya baki ki bani? Kai ban yarda ba.”
“Da gaske nake, ina tunanin kina birgeshi ne.”
“Amma bai taba yimin irin wannan kallon ba. Kuma idan ina birgeshi dagaske me ya hana bai bani da kanshi ba?”
“Mai yiyuwa yana son na mashi sharen fage ne.” Zahara ta fada da dan guntun murmushin munafuncin ta.
“Oh my god, plan dina na yau ya sauya