Showing 27001 words to 30000 words out of 161239 words
Murmushi yayi tare da cewa gaskiya ku bata d'aki tabbas muna da masaukin ki a gidan nan, sakaran banza na fad'a a cikin raina nace otiho dakai baka tsan tsiyar nasara ba sai zashi ganin gida, duk shelar da nayi na ce bariki tafini tabbas ka gagara ganewa da gaanin wannan sha ka tafi ne, fuska ta d'auke da mugunta nace mashi idan an bani d'akin kai ka biya kud'in sannan kuma ka bani rance dubu d'ari, tukuicin d'aki zaka kwana biyu kana morewa dani nima daga cikin irin baiwar da Allah ya bani, dubu d'arin ka kuma da kud'in d'aki duk zan baka su idan na fara kasuwa......
Ba damuwa a bata d'akin sama lamba 59 ya fad'a cikin zaguwa, ga *kwartuwar* shi gefe ya manta da labarinta, hawa sama nayi aka nunamin d'akin, makulli aka bani na bud'e na shiga ina shiga na kulle d'akin ta ciki.
Dudduba d'akin nayi bayan na shiga, falo ne sai d'akin bacci madafar abinci da bayi, d'akin bacci katifa ce irin ta "yan bodyn sch, falo tayils ne babu kujeru sai kafet, k'arewa d'akin kallo nayi sannan na koma jikin tagar d'akin na fara kallon yanda *karuwai* suke rayuwarsu.
Ina tsaye na fara tunanin fuskar da tacemin An mata, ina k'ok'arin tunoshi kwalwata ta fara jakkancin data saba, a bayyane nace ki saurara kar kimin haka don Allah rayuwa mai had'ari na kawo kaina ki tausamin ki sanar dani ko waye waccan, kwana biyu kad'ai zanyi nabar gidan nan amma ina so ki sanar dani ko waye shi d'in......
Bugawa zuciyata tayi tare da cewa abokin Dikko ne wallahi, shine ya raka abokin Babanki aka kaiki wurin Dikko....... Kamar kasuwa haka zuciyata da kwalwata suka fara gardama hayani ke tashi daga cikin kwalwata da zuciyata, yayin da kwalwata ke cewa bashi ne ba zuciyata tana cewa tabbas wallahi shine, kyarma jikina ya farayi gaba d'aya d'akin naji yana juyamin, kamar ana jijjiga ni naji anayi dan haka da sauri na dafa bango na zauna k'asa tare da fara karanto duk addu'ar data zo bakina......
Bayan na samu natsuwa ne, na dafa daidai saitin zuciyata da kwalwata sannan nace idan nayi muku wani laifi da Allah ku gafarceni amma ku daina dakushe wa ku barni nayi komai cikin hikima kamar yanda na tsara zanyi. Kuyi hakuri ku daure ku bani gudamwa.
Kwana na biyu a gidan karuwai ina koyon abinda yakaini, safe rana dare wannan d'an iskan yake kawomin abinci, a yanda nayi niya yaune zan tafi amma na fasa tafiya sai naga mai gidan bene....... Wato mai wannan gidan na karuwai.
Da daddare misalin 9:30pm na sauko k'asa na samu wuri daga gefe na zauna banma kowa magana ba haka kuma babu wanda na kalla amma hankalina gaba d'aya yana wurinsu,
Murmushi nayi a lokacin da naji wasu *kwarata* na ciniki, kallarni sama da k'asa kaga zubina ai kasan nafi k'arfin ka kwanta dani kace 1k zaka bani, yo wace kala gareki ni keda bakin masai baku da banbanci a wurina tunda kowa ma zuwa yakeyi ya hau ya kama gabanshi, ina ma laifina da zan baki 1k idan haka yayi miki in bayar idan baki yadda ba naje wurin Umma.
Mai makon naga taji haushi sai kawai tayi dariya tare da cewa shege kenan, to kawo dubu d'in, d'an sosa kansa yayi sannan yace kai nama manta dubun zan siya ma iyalina biredi wallahi kuma machine ina baida mai amma bari dai in bada dari biyar, batayi zuciya ba tace to kawo dari biyar in, bata yayi suka shiga cikin d'akin.....
Tsoki nayi tare da ganin wallan matan aure, kuna gida kwance mazajenku suna nan wurin sakarkarin matan da basu kaiku komai ba, kuna can kuna girman kai da kunyar banza da sakarci aje a yayo cuta a cusa muku babu gari babu dalili.
Me Allah ya rageku dashi ? Me karuwa take dashi wanda Allah bai baki ba ? Naki ma yafi nasu daraja tunda ke ta hanyar bautar Allah zaki mik'ashi kuma Allah ya baki lada, amma matar malam bahaushe tanajin kanta yai mata girma ji takeyi idan ta nunawa mijinta tana buk'atarshi kamar zai rainata, wata ma macen idan bashi ya nemeta ba saidai ayi ta zama a haka, to ya nemiki jiya shekaran jiya kullum har "yar basirar dake gareshi ta kare, ko kuma sai yazo kwanciya dake ki tashi hankalinshi ki tado fitar da kila anyi sati ko wata da yin abu saboda ke kawai za'a kwanta dake, kin b'ata mishi rai yaji gaba d'aya abun ya fita a kanshi ko kuma yayi shi ba cikin natsuwa ba, da kanki kike jefa kanki halakar da babu mai iya fitar dake sai Allah , daga haka sai shedan ya fara doka masa gangar sa ya barki yaje ya nemi na banza, dan babu zuciyat wanda shed'an baya wasa da ita.
Idan kika had'u da muguwar mace sai ta rabaki da mijin fafur ki kasa gane kanshi, daga nan sai ki fara tattara kaya ke a dole kinyi yaji. Idan an tambayeki abinda ya had'aku ki fara cewa baya dawowa gida da wuri, idan kin kawo abinci baya ci, idan kinyi kwalliya baya yabawa, bayan duk kece babban da kika jawo ma kanki wannan damuwar........... Mudai je zuwa zamu gano masu laifin tsakanin matan da mazan su waye masu matsala......
Ina zaune a wurin har 12:30am bai fito ba, tou me akeyi haka har yanzu wanda ba'a gama shi ba ? Duk gorin da yayi mata na had'a mata k'addarar ta da bakin masai batayi zuciya ba.
Lallai bariki bariki ce, mutanen cikinta suma sun barikantu kodai taji haushin abun bata wani nuna mishi damuwa ba, ina nan zaune a wurin har mutumin da nake tunanin mutumin da nake tunanin yana tare da Dikko ya shigo,
Da fito ya shigo babu sallama sai gyara wando yakeyi kamar wani sabon shigar *kwartanci* kallona yayi tare da cewa har yanzu baki bacci ba ? Nima irin yanda naga *karuwai* sunayi idan zasuyi magana nayi, d'an kashe idanuwa nayi cikin sigar bariki sannan nace banyi ba, to me kike jirane ? Kud'in da zaka bani ina so na shiga kasuwa gobe zanyo siyayya kasan jibi nake komawa bakin aiki na......
Murmushi yayi saboda yasan shine farkon layi idan na fara iskanci, kina da account ne ? Ya tambayeni ?Banda shi, to da safen zan baki idan naje wurin mai gida na, Allah ya kaimu nace tare da mik'ewa na fara tafiya cikin *kwartanci* sakaran banza ya bini da kallo, zakaci ubanka idan na gano ku, jibi kamar yanzu kana nan zakayi baccin bak'in ciki dan zan b'ace muku b'at kamar jirgi a cikin gizagizan sararin samani............
07/08/2019
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 9
Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, itace kad'ai abinda Dikko yake ta maimaitawa a cikin wannan tsalelen dare,
Juyi yakeyi sosai a saman gado sai kace macen da ciwon ciki ya taso ta gaba, kifa kanshi yayi a saman lallausan bargon dake kusa da kanshi ya goge hawayen dake bi masa idanuwa.
Allah na tuba..., ya fad'a a bayyane tare da gyara kwanciyar shi, girgiza kanshi yayi , yayin da zuciyarshi da kwakwalwar shi suka hasko mishi abinda yayi ma Sultana, a hankali ya lumshe idanuwanshi na tsawon lokaci sannan ya fad'a a bayyane baiwar Allah baki dace mahaifi ba,
Sai kuma Allah ya jefoki a rayuwar Dikko yayin da nake nemanki, kika zo a daidai lokacin da na d'auki hud'ubar shaidan , Allah ya baki hak'uri kinji, ya k'arasa maganar tare da bud'e idanuwanshi duka da sukayi jajir saboda kuka........
Ko ina kike ? Me kike yi yanzu ? Wane irin bak'in ciki kikeji idan kika tuna dani ? Ki zama mai yafiya a rayuwarki, manta da Dikko ki fuskanci rayuwa, ina nan ke kuma ina ki ke .....?
Ina gidan karuwai,.... Ina shiga d'akina na mayar da k'ofa na rufe, ya zama lallai na gano waye mamallakin wannan gidan, sannan idan har na karb'i dubu d'ari a hannun wancan garan me ya kamata nayi da ita ne ? Ansar kud'in sune wahala Sultana anso su tuk'una idan suka zo hannu ba'a rasa abinda za'ayi ba, wannan shine shawarar da zuciyata ta fad'amin.
Ajiyar zuciya na sauke tare da hayewa saman "yar k'aramar katifata na kwanta bacci.
Da safe ina tashi sallah asuba nayi, na dad'e ina zaune a saman abin sallah ina addu'o'i na neman tsari d'aukaka farin jini da kuma k'war jini a harkar bariki.
Sai 7:00am na tashi daga saman abin sallah, toilet na shiga nayi wanka, ina fitowa na shirya a gaggauce domin akwai inda nake so naje.
Ina gama shirina na fito sanye cikin hijabina, sai nik'af dana dabkakawa fuskata, ina rufe d'akina mai kirana da irin sunan da Dikko yake kirana yazo.
A k'ofar d'aki muka gaisa daga gaisuwa ban sake masa magana ba naci gaba da rufe d'akina.
An mata ina zakije haka da safe ? Ban kalleshi ba nace zanje wurinka ne dama, murmushi yayi tare da cewa kuma gashi nima nazo wurinki yake nan .?
Babu wani damuwa zamu iya maganarmu anan, mudai shiga daga ciki zaifi ko ? Ya fad'a yana kallo na, gyara tsayuwata nayi tare da cewa kayi hak'uri gaskiya na fito bazan koma ba, yana k'ok'arin bud'e bakinshi yayi magana nace kayi hak'uri da Allah bana san magana tayi tsayo na wuce, ina k'ok'arin tafiya yace d'an tsaya kiji mana.
Tsayuwa nayi ba tare dana juyo ba, am dama cewa zanyi idan kina da hali anjima zamuje wurin Alhaji yace yana san ganin ki, ba tare dana juyo ba nace wane Alhaji ne ? Mai gidan nan, na bashi labarinki shi kuma ya matsa saiya ganki.
Saida nayi shiru na wani lokaci sannan nace wurin k'arfe nawa zamu je kenan ? Yanzu ma dan zaki fita da munje saboda ba'a gida ya kwana ba yana nan bayan gidan nan yana tare da bak'i da sukazo wurinshi manyan alhazawa ne masu kud'i da suka ansa sunansu a kud'i, d'an mugun murmushi nayi a cikin nik'af ina sannan nace tou kai ya maganar kud'in da zaka bani ne ? Suna cikon mota muje, murmushin zalinci nayi irin wanda naga mugu Dikko yanayi sannan nayi gaba abuna ya biyo bayana.
Cikin motarshi ya d'aukeni, muna shiga cikin motar na yaye nik'af ina tare da kallonshi sannan nace niko na tambaye ka mana ? Tambayarni mana ya fad'a a daidai lokacin daya fara tafiya da mota.
Shiru nayi ban sake magana ba, shine ya gaji da shirun yace kinyi shiru kuma ! Ey zan tambaye ka amma ba yanzu ba dan na d'auka ne baka san tambaya da surutu ne kamar yanda nima bana so, amma tunda ka bani izini zan rik'a tambayarka a duk lokacin da tambayar yazo min, amma dai ya sunan ka ...?
Murmushi yayi sannan yace suna na Umar, gyara zama na nayi tare da cewa me yasa Babanku yasa maka suna Umar ne ? Dariya yayi sosai tare da cewa sunan ubangidan shi ne,
Zaici gaba da rattafo min bayani na dakatar dashi ta hanyar cewa barmin bayanin haka nan zan tambayeka wani lokaci, babu gardama ya kame bakinshi ta hanyar yin shiru....
Har muka isa bakin get in gidan babu wanda ya sake magana daga ni harshi, horn yayi mai gadi ya bud'e mana muka shiga, gida ne had'ad'd'en gida na "yan gayu yasha ado da shuke shuke na filawowi, daga gefe kuma wasu irin lafiyayun dawakai ne tsabtatacci kuma k'osashshi aka d'aure sai tattabaru masu kyau wanda suke sauka k'asa lokaci lokaci su kuma tashi sama firrr lokaci lokaci....
Gaskiya dokunan sun burgeni sun kuma bani sha'awa, amma dana tuna da Dikko yana san doki yana k'aunar doki a rayuwarshi sai kawai naji dawakan nan sun fita a raina, saima zuciyata ta fara tunanin taya zanyi in kashe su, domin na tuna cewa Dikko ya fad'a cewa yana san doki ko ba nashi bane, lallai ni kuma na tsani dawakai.. Muje Umar ya fad'a da yaga banda alamar fita daga cikin motar.
Fitowa nayi tare da cewa Umar waye yake kiwon dokuna ? Wallahi na uban gidan Alhaji ne, ya bani amsa ne a lokacin da muka fara tafiya, tou shi Alhajin duk kud'inshi kenan yana da ubangida shima ? Na tambayi Umar, Umar yace Eh mana ai ubangidan nashi shine duk wata k'aryarshi, shine ya d'aure masa k'ugu shi ya tsaya masa saida ya tabbatar Alhaji ya zauna saman k'afafuwanshi , gaskiya mutumin kirki ne sosai, da yana harkar mata na tabbata idan na had'aki dashi yarinya kin warke, bake ba talauci, ke bake ba kaf zuri'arku da talauci ya k'are.
Maganar Umar ta k'are ne a daidai lokacin da muka shiga palon gidan, k'aton palo ne mai girman gaske, sai wata irin dakekiyar tv tunda nake a rayuwata ban tab'a ganin tv mai girmanta ba, ko da yake ma ina naje ina na sani a wannan lokaci ? Saifa gidansu Dikko shima naga tashi tv n babba ce amma banda natsuwar gane wacce tafi girma,
Bin palon nayi da kallo, d'an rumtse idona nayi na bud'e tare da k'ara d'ora idanuwana a saman hotunan dake palon, tabbas idan ban manta fuskar Dikko ba wannan shine Dikko, mutumin dana tsana nake san ganin bayanshi komin daren dad'ewa, dan ina sayen gida wa Babana Dikko shine mutum na farko da zan fara sabautawa rayuwa a duniya......
Muje suna ciki, Umar ya fad'a tare da katse mun tunani na, sauke nik'af ina nayi na rufe fuskata sannan nace mu koma gida, zai tambayeni dalili nace kawai mu koma zamuyi magana dakai daga baya. Haba Sultana har mun shigo wuri zaki ce mu koma.... Kallon Umar nayi sannan nace tunda nazo da kaina ai kasan zan sake dawowa ko ? Ina fad'in haka nayi gaba abuna......
Ina fitowa idanuwana suka cika da hawaye, tun ranar da Dikko ya ajiyeni a k'ofar gidanmu ban sake tunaninshi ba sai ranar da Umar ya kirani da An mata, ban sanka Dikko na tsani duk sunan daya fara daga kalmar D insha Allah ni zan zama ajalinka..... Kuma ta hanyar da kabi ka azabtar dani to nima ta hanyar zanbi in rama abinda kamin, yanda ka somar dani ni kuma saina kasheka.... Babana yaci darajar mahaifi na ne shi, zan tara masa dukiya ta hanyar karuwanci zaici yaci bulus amma wallahi kai Dikko bakaci banza ba.....
Fitowar Umar yasa na saita kaina, na bud'e mota na shiga domin ya bud'emin ita tun lokacin daya fito, zakuji dalilin da yasa na fasa shiga ciki, Umar kad'ai yasan fuskata kuma yau ya zamar min wajibi nabar gidan karuwai domin wannan kwanakin sune kwanakin dana iba zanyi a gidan karuwai, na ga abinda nake so na gani, naji na kuma gani nima zanyi gaba dan nima in dogara da kaina.
Muna fitowa yayi hanyar gida nace dakata ajiyeni nan, ina zakije ne ? Ya tambayeni , ban bashi amsar tambayarshi ba nace masa ga makullin d'akina kasa a gyara man, bani kud'in nan zanje in had'o makaman yak'i.....
Miye makaman yak'i kuma ? Ba tare dana kalleshi ba nace ai kasan ba'a shiga gida dole saida sallama, gida ba shara ai baya dad'in zama, na ciki bai san akwai na waje ba idan baya kwankwasa ba, to haka bazai yuwu ba wani yaci abinci yace kai yaci mawa, kaidai bani kud'i kaji idan na dawo zan baka bayani,
Kud'in ya d'auko ya bani, bayan na ansa nace samu wuri ka rubuta min number ka idan zan dawo zan kiraka kazo ka taho dani, yo ina wayarki ne ? Banda waya amma ka rubuta min zan samu aro na kiraka, rubuta min yayi a jikin takarda ya mik'omin, ansa nayi na fita daga motar tare da cewa sai munyi waya...
Saida na daina hango Umar sannan nima na ibi tawa hanyar na shiga duniya......,