Showing 99001 words to 102000 words out of 161239 words
faɗa su zaka kawomin a ko wace waya na faɗa maka , yana faɗin haka ya miƙe ya nufo ɗakina...
Da sauri Nana ta ajiye tsintsiya saida tayi masa sannu da zuwa ta fice daga ɗakin , bayanta yabi da kallo zuciyarshi tana ƙisima mishi wasu abubuwa , amma bai ansa sannu da ta masa ba...
Gefen katifa ya zauna kusa dani cike da soyayya irinta mahaifa yabini da kallona mai tattare da tsantsayar soyayya , murmushi nayi nima ina kallonshi nace Babana baka da kuɗine ? Murmushi yayi bai bani amsa ba , nima murmushin na sakeyi kamar yanda yayi sannan na jawo jakata ina cewa ni ina da kuɗi bara na baka...
Ansar jakar yayi tare da rufeta yana mai cewa nifa ina da kuɗi Mamana kinsan mage kota ƙoshi sai ta hari ƙwari , ajiye kuɗinki anjima zan ƙaro miki wasu , ajiye jakar yayi a gefena sannan yace Mamana tun kuna ku hamsin da bakwai har yau an wayi gari kun zama ku sittin ciff,
Tsoki yayi tare da kauda kanshi gefe yace tirr , wallahi da za'a tambayeni abinda nake so a musanya min da tulin "ya "yan nan ke kaɗai zan cire a cikinsu sauran a mayar min dasu daga motocin hawa sai ƙayataccin gidaje , ita kuma matar malam bahaushe ita dai burin ta kawai ta tara taron "ya "ya ita dai a mutu kawai taci gado , tou ban ajiye ba kuma bazan ajiye ba duk wacce ta haifi "ya "yanta taji da abunta ni babu ruwana...
Uhum Babana kenan mugunta kamar mai tsaron gidan yari , wato karya nema ya ajiye idan baya duniya a ci gado , hmm halin Babana saishi kallo nabi shi dashi ga wayyen mutum kisan boko ɗan gayu mai buɗewar ido yana da ilimin boko mai zurfi amma saboda tsabar baƙin ciki ko aikin gwamnati bayayi , tunda yaga ana ruguwar haifar mishi "ya "ya ya daina aiki ya koma caca...
Kallona yayi yace ki ɓoye sirrin mahaifinki koda bana faɗin duniyar nan , ki zama maimin addu'a bayan mutuwa ta ɗaukeni daga kusa dake , ki nunamin soyayya irin wacce nake nuna miki Mamana , ina miki soyayyar da duk duniya bana ma kowa irinta , banajin kunyar kowa idan nayi abinda ban kyauta ba amma Allah ya sani inajin kunyarki Mamana , babu wanda ya isa yasa nayi ko na bari amma idan har kika hanani na hanu , labarin waye Binna kuwa zan faɗa miki ne saboda abinda ya faru dake wanda ba'a san raina hakan ta faru ba , kuma ki yafemin na roƙeki ya haɗa hannayensa biyu tare da ci gaba da cewa kuma bazan sake tafiya na barki ba , ya ƙarasa maganar yana mai min kyakyawan murmushi ....
Riƙe hannunshi nayi tare da cewa kayi alƙawari ? Jinjina kai yayi yana murmushi yace nayi miki alƙawari , nima murmushin nayi tare da cewa nima nayi maka alƙawari Babana bazan taɓa tafiya na barka ba , yayi Allah ya albarkaci rayuwarki Uwar masu gida , da amin na ansa tare da gyara zamana , shima gyara zamanshi yayi sannan ya fara....
*ALIYU MUHAMMAD BINNA...*
Shine cikakken sunan da kowa ya sanni dashi , *BINNA* laƙani ne dana sakawa kaina shi bayan na shiga harkar wasan caca , dalilin binna kuwa saboda tsabagen neman asiri irin nawa , *BINNA* a binne kenan , dan da anyi magana kaza bazai yuwu ba , zance a binne shi kawai , tou idan nace a binne sai mutane suka fara ankara da abinda nakeyi dan haka sai nayi waiwayen damisa na zama Binna kawai dan ɓatar da mutane lissafinsu , sunan yana firgita kowa haka kuma yake bawa kowa tsoro duk wanda yaji ance *BINNA....* tou binna abin tsoro ne abun firgici tashin hankali ne ga duk wanda yasan Binna da irin rayuwar da nakeyi...!
Malam Muhammad shine mahaifina , Maryam wacce ƙauye yasa ake kiranta da mero itace mahaifiyata , matan malam 2 mero da sahura , mahaiyarmu itace ƙarama kuma dake ta daɗe bata samu aihuwa ba , ita kuma Sahura dama tuni ta kwankwatso ɗiyanta goma sha shidda , hmmm Babana yayi tare da cije haƙorashin na gefen dama ya karkace leɓunansa sukayi sama , jinjina kai yayi sannan yaci gaba da cewa "ya "ya sha shidda saboda haɗama sai kace wata kaza , dan tun kafin a auro Mero tuni Sahura tayi haihuwarta ta gama...
Mu talakawa ne na abin musali , kaf zuri'armu ba'a taɓa samun mutumin daya mallaki kaza biyar ba , kaf kauyen Ƙarara babu mutane masu talaucinmu , bamu gaji arziƙi ba kuma babu wanda yayi shi , kowa dai yanashan azabar talauci yadda ya kamata ,
Malam kuwa wutar talauci data isheshi ya rasa inda zai saka ransa saiya fara aikin tsubbanci , kuma sai Allah ya tallafa mishi domin idan yayi aiki kamar yankan wuƙa wuyar dai kafin yayi ne kawai , cikin ƙanƙanin lokaci sunansa ya fara ketawa yana zagawa kunnen jama'an duniya , yayin da mutane suka fara kiransa mai gobe da nisa...
Nanfa harka ta buɗe dan Allahn yace masa zama , tun abun bai fita ba har mutane suka fara shigowa daga cikin birni suna zuwa wurinshi , a tsabibincin nasa fa yakai maƙura kuma shekarar arziƙin nasa ya tsaya kalmar zama da Allah ya yaddar masa taci gaba da tabbata akanshi....
Malam fa ya fara tara abun duniya , liƙafa taci uban ta da , dan malam ba mutum bane mai rowa dan haka jama'a suka fara saɗaɗowa zuwa gidanmu cin arziƙi , cin nan 3 a yini tou fa idan mutum yazo zaici ya ɗinke har yayi guziri , shi yasa gidan namu kullum ya koma kamar wani gidan biki ko suna...
A lokacin da Mero ta samu cikin farko Sahura kuwa tace ina wuta ta jefata , nan ballin asiri ya fara tashi jefe² tahana mahaifiyarmu zaman lafiya , da ta samu ciki sai ya ɓare , ciwon yau daban na gobe daban , abun dai babu daɗi ,
Su kuwa malam ba abinda ya damesu da harkar da iyalinsu ke ciki burinsu kawai sudai a kawo musu , kullum matan malam basu da aiki sai wanke alluna , ana haka dai har Allah yasa Mero ta samu cikina , tunda Sahura ta lura Mero tana da ciki taci gaba da wurgago subbancinta , haba ina harta isa ? Allah yace saina zo asiri baya tasiri a wannan lokaci sai hukuncin Allah...
Har Mero ta haifeni cikin wahala take da musibar rayuwa , tunda na sako ƙafa duniya dama azababbena aka haifoni , da rana zansha baccina har in gode Allah , amma da zaran an kira sallah magrib na fara kwarara ihu har garin Allah ya waye babu wanda ya isa ya runtsa idonshi kona second a gidan nan saboda kuka na , a haka akayi suna Allah ya cidani da Aliyu , ina wannan masifafen kuka da an kira asubahi kuma zanyi bacci , malam kuwa saida ya rubuce yace abani insha maganin kuka duk ranar da aka bani rubutu kukana sai yafi na jiya , har malam ya haƙura ya daina rubutu ana bani...
Haka Mero ta haƙura taci gaba da rainona duk wanda ya ganta yasan tana tattare da damuwa , tabi ta soye tayi baƙiƙƙirin saboda tsabar rashin kwanciyar hankali , dana fara zama kuwa idan ta zaunar dani zan fashe da wani irin ihu mai firgici wanda dole saita ɗaukeni ta goyani , nadai zama fitinanne ta ko wane sashi ,
Dana fara rai rafe kuma ɓarna harta ƙeta , duk abinda yake na Mero bana ɓatawa amma daga ba ita ba duk abinda na gani saina tadashi aiki , Sahura tace iskanci kesa nakeyi ɓarnar tunda nasan abun uwata bana ɓatawa , da nayi mata ɓarna sai tayita dukana maimakon inyi kuka sai inyi ta dariya...
Abun fa ya fara tayar da kowa hankali , har aka yayeni a nono , iskancina kuma sai abinda yayi gaba , tun ina ɗan firiri na , na iya tsakalo fitina saidai idan ban fita ba , masu kawo ƙara kuwa haka zasu jero layi , wasu a biyasu wasu kuma a basu haƙuri...
Shekarata 3 Mero ta sake samun ciki , amma har ta haifeshi Allah bai sanar da Sahura ba , tashin hankali wanda tayi ba kaɗan ba , amma bata da yanda zatayi dan duk wanda yazo baya komawa sai idan Allah yaso...
Ranar suna data zagayo aka sakawa jariri suna Muhammad , wanda ake kiranshi da ƙarami , ku kuma kuna ce masa Baba ƙarami , haka dai akaci gaba da cakwakiyar rayuwa , har Allah ya kawo wata mace matar wani attajiri malam yayi mata aiki , bayan buƙata ta biya shine ta siyawa malam gida anan cikin garin birnin katsina , a anguwar ƙofan marusa , daga nan muka tattaro mukayo birni !
Shekarar mu biyu da dawowa birni Mero ta ansa kiran mahaliccinta babu jinya haka kuma babu ciwon kai bare na hannu , nasha kuka kamar zan mutu na rashin mahaifiyata , wanda Sahura ko a kwalar rigarta ,
Bayan anyi kwana 3 da rasuwar Mero Sahura ta samu malam ta kitsifa masa ita bata iya zama dani ga iskanci ga rashin kunya ta taɓani ace dan uwata bata raye take azabatar dani , saidai ya raba mana wurin zama ,
Ba tare da nazarin komai ko tunani ba , yace in bar mishi gidanshi dani da ƙarami , haƙuri na bawa malam akan ya bari saiya kamani da laifi , amma fur ya ƙeƙashe idanuwanshi saina bar mishi gida , ina ƙoƙarin barin ɗakin malam Sahura tace sai inzo in tafi da ɗan uwana dan so take gaba ɗaya fitina ta fitar masu daga gida , a lokacin shakarar ƙaramin 2 da wattanni , ni kuma ina da shekara biyar da "yan watanni , haka malam yayi mana korar karnuka , ina kuka na ɗauki ƙarami muka fita daga gidan ,
Ina ɗauke da ƙarami na shiga cikin gari , duk wanda ya ganni ɗauke dashi zaice na mayar da yaron nan bana iya ɗaukarshi , ko sauraron mutane banayi bare na basu ansa , tafiya nakeyi har aka kira magrib , ni kuma a lokacin na isa wata anguwa ita Gambarawa....
Bakin wani shago na zauna na sauke ƙarami dake ta zabgaga kukan gajiya da yunwa , bayan na zaunar dashi naje na ɗauko buta da wani ya gama alwallah ya ajiye na bashi sauran ruwan daya rage yasha , bayan yasha na matsa wurin mai shagon da yake ƙoƙarin buɗewa ya dawo daga sallah nace Baba da Allah ka taimakamin da sadaƙa zan siyawa yaro abinci yaci ,
Cikin hargowa yace ai sai ka buɗe ka ɗauka mishi ɗan barauniya , dama irinku ne masu sacewa mutane abu idan basa nan , wata irin kwanya yaimin tsakiyar kaina harsai da nayi tunanin kaina ya huje , dariya nayi tare ce masa ka nunamin inda zan ɗauka , kuɗi ya fiddo daga cikin aljihunshi kwaci ² shege ɓarawon banza , kallonshi nayi sannan na duma ma kuɗin wawa , kaf kuɗin na kwace na ruga na cicciɓi karami nabi lunguna ba tare da nasan gari ba ,
Biyoni yayi da gudu yana a tara ɓarowa , ƙarami kuma sai kuka yakeyi saboda ya wahala , ganin jama'a na ketowa daga hanyoyi da dama yasa na samu wani zauren gida na sake na rufe bakin ƙarami sautin kukanshi ya daina fita...
Dube ²n su sukayi basu sameni ba saboda haka suka hakura kowa ya kama gabanshi , saida na tabbatar babu kowa sannan na fito naje na samawa ƙarami abinci yaci muka bar anguwar Gambarawa a daren na dawo Qerau da zama....
Haka rayuwa taci gaba da tafiya , ni na saka kaina makarantar allo kuma na samu gidan aiki , gidan aikin suka sakani makarantar boko , haka dai na haɗa abu goma da ishirin , ga karatun allo ga boko ga gidan aiki ga rainon ƙarami ,
A daddafe dai nayi ta dafa rayuwar kuma ban sake zuwa wurin malam ba kuma daga Qerau zuwa Ƙofar marusa babu wani nisa ,
Shima ƙarami daya isa sakawa makaranta boko gidan aiki na suka sakashi , kuma tare dashi mukaci gaba da aikin gidan , daga baya ma suka bamu wurin zama a cikin gidan ,
Na gama secondry sch Bello ya shigo cikin rayuwata , gidan ƙawar matar da muke zaune gidanta itace take aikena gidan ƙawarta gidan kuma a maƙotan gidansu Bello ina zuwa idan aka aikeni nan ya ganni ya liƙemin , yana zuwa gidan da muke zaune yana yini wani lokaci ma har kwana yakeyi , ya shigeni sosai abota mai girma ,
Makarantar gaba da secondry tare da Bello muka fara nidai nayi karatu kuma na fito da sakamo mai kyau yayin da Bello ya faɗa harkar mata , a lokacin kuma ƙarami yana secondry sch aji biyar , bayan na gama degree aka fara neman min aiki , yayin da ni kuma nake neman ƙara faɗaɗa ilimin nawa...
Har wannan lokaci banje wurin malam ba , kuma malam bai nemeni ba ni kuma naƙi nemansa dan dama ni nasan inda yake , saida naci gaba da karatu na , na faɗa harkar wasan caca daga nan duk lissafi ya jagulemin , dan duk wannan kangarar da nayi a baya tana da dalilinta kuma a gaba zaki ji ta , dan bayan na baro gida naɗan samu natsuwa , amma shigowar Bello rayuwata yasa na ida ƙwacewa......
16/09/2019
Jamila Musa.....💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 34
*_Fatan na samu kowa lafiya ? Kuyi haƙuri na jina shiru kwana biyu banajin daɗi ne amma na samu sauƙi alhamdulillah ngode da addu'o'in ku a gareni masoyana , gaskiya naga soyayya kuma ngode sosai , na warware zamu ɗaura daga inda muka tsaya , fatan alkairi a gareku masoyana kuyi farin ciki..._*
Shiru Babana yayi ya zubamin idanuwa yana min kallo mai tattare da bayaso ya faɗamin , nima ƙureshi nayi da idanuwa amma bance masa komai ba , shiru yayi yana nazari zuwa can ya ɗago ya kalleni , nima kallonshi nake har yanzu zuciyata dai ta bani kila zai ɓoyemin wani abu ne...
Gyara zama yayi yaci gaba da cewa , zuwan Bello rayuwata yazo min da al'ajabi mai girma , wanda ya kasance bana iya ƙetare maganarsa , idan yacemin inyi zanyi idan yace na bari zan bari ya rabani da ko wane aboki shi ɗaya ne abokina ,
Bello shi ɗayane iyayenshi suka aifa , kuma attajirai ne na gaske , soyayyar duniya sun ɗorawa Bello sun sangartashi yadda ya kamata , saidai ya kashe waccan mota ya ɗauka waccan , ba mazaunin gida bane ba , domin duk kayanshi na sakawa yana cikin motarshi , tafiya yake jira kawai yayi gaba , gashi cikakken ɓarawo domin duk ƙarfin arziƙi mahaifinshi saida ya duƙar dashi ƙasa.
Tun wancan lokacin Bello ya mallaki bantan baƙin biri , daya ɗaurashi duk inda ya shiga idan dai akwai kuɗi hayaƙi ne zai riƙa tashi , da yaga yahaƙi yasan kuɗi ne a wurin zai buɗe kawai ya kwashe yayi gaba ,
Bello mashayi ne , ɓarawo ne , ɗan caca ne sannan tantirin mazinaci ne , idan har ya zuƙawa mace masifa tou duk irin kamun kanta da natsuwarta sai Bello ya keta mata mutunci , baya neman zawara baya neman matar aure sai "yan yara ƙasa da shekarunki , shekaruna kenan ni Sultana , kuma daya biya buƙatarsa ya gama da ita wata zai nema...
Da nayima Bello magana sai yacemin sa'ar caca malaminshi ya bashi , gabana Bello ke zuƙewa kuma gabana yake kwalbewa , ma'ana a gabana yake shawuwa yasha sigarinshi yasha giya da sauran kayan shaye ²n shi...
Ni kuma a lokacin na koma makaranta naci gaba da karatu na , dan zurfafa ilimina dan na fahimci rayuwar idan baka da ilimin zamani mai zurfi tou ka zamo an maido wuta an ɗauke...
Banda isashshen lokaci bansan abinda gida yake ciki ba idan na tafi makaranta , gidan da ake riƙemu akwai ɗiyar mai gidan itama yarinya ce ƙarama lokacin tana js3 ashe itama Bello ya ɗora mata alƙalamin kudirinshi akanta wanda ya fake da soyayya ne ni kuma duk ban sani ba ,
Wallahi babu abinda na sani tunda bana nan , ƙarami ma baya zama gida shima makaranta , Bello idan yazo bama nan zai buɗe ɗaki kawai ya shiga babu mai hanashi tunda abokina ne ,
Wata rana kwatsam ina makaranta "yan sanda suka zo suka tafi dani , tambayarsu na farayi lafiya ? Babu mai lokacina , haka suka sarkafeni