Showing 105001 words to 108000 words out of 161239 words

Chapter 36 - KWARATA

Start ads

28 Aug 2025

610

Middle Ads

Shima Alaji kiran wayana yayi tayi naƙi ɗauka , ya gaji ya tashi yayi tafiyarshi , shima Umar tafiyarshi yayi gida ,

Ni kuma ina shiga ɗaki saman katifa na faɗa nayi ruf da ciki bansan dalili ba , maganar Dikko yake dawo min a zuciyana , karki sake kiyi mafarkin gemuna , cike da fargaba zuciyata ke cewa kodai Dikko ya gane ina kallon masa gemu ne .... ? Tsoki nayi na gyara kwanciyata ina tuno kyakkyawar fuska Dikko , tunani dai barka tai a zuciyata har bacci ya ɗaukeni....

Da safe Alaji yazo ya kaini kasuwa dan Babana baya nan kuma motana tana wurinshi , siyayya na bada mamaki nayo domin fa Alaji yana da hidima kuma yana da gabata , ya kashe kuɗi duk yanda tunani baya tunani , ko kayan da zan saka wurin partyn zagayowar shekarar aihuwata wallahi masu masifar kyau da tsada ya siyo min abun dai zabburgewa sai wanda ya gani ,

Bayan mun gama siyayya nace masa ya tafi zanyi kitso idan na gama zan kirashi ya ɗaukeni , Alaji yace to saida ya ƙaramin kuɗi ya tafi ni kuma na shige shagon "yan arna da basa gane yare na , na fara faɗa musu abinda nake so amma dan ubansu wai basu gane ba , saida wata rantsatstsar karuwa maiji da iskanci har iskanci yayi mata sign tayi musu bayani , girar ido za'a sakamin akaifa da kuma atach duk gashina saida nasa aka yimin ƙari saboda tsabagen wawanci irin nawa ,

A ƙofar gidanmu kuwa 5:00pm Dikko suka kafe motocinsu , aikawa yayi a kirani amma sai akace masa na tafi kasuwa , maimakon ya tafi sai yace zai jirani har na dawo ,

Duk lokacin da minti ɗaya ya wuce sai Dikko ya kalli agogo ranshi ya ƙara ɓaci , shiru ² babu ni har aka kira magrif , cikin damuwa yace ma Al ' ameen muje zan dawo anjima ,

Tashin motocinsu sukayi gaba ɗaya suka taho , suna fita anguwar mu kuma muna shigowa hannun riga mukayi dasu wato suna fitowa mu kuma muna shigowa ,

Babu abinda na sauko daga mota nace ma Alaji ya tafi sai Allah ya kaimu , sallama mukayi dashi ya tafi ni kuma na shige gida , ina shiga na shirya a gaggauce domin Baban Amisty zaizo , naje kasuwa har nayo kawalcin mace zan haɗasu , itace karuwar da muka haɗu ta tambayeni sana'ar da nakeyi nace mata karuwanci nakeyi , tace ashe tafiyar ɗaya ce ? Nace mata Eh musayar number mukayi har na bata labarin iyayensu Amisty tace suna da mai ne ? { kuɗi } nace sosai ma , shine tace a cikin daren nan in bata aron kowa a cikinsu ita kuma tamin alƙawarin zata ɗaukomin su dukansu a cikin yanayi mara kyau tou shine zan haɗasu , duk da dai malami da mawaƙi da karuwa basu da amana amma zuciyata ta yadda da ita 100% ,

Har ƙofar gida Baban Amisty ya ɗaukeni kuma yanzu ma muna fita Dikko yana shigowa , akace masa yanzun nan muka fita ko bakin titi bamu kai ba , da sauri ya biyo bayanmu ko zai sameni amma bai iskomu ba , ganin baisan ta ina zai samoni ba yasa ya haƙura ya koma ƙofar gidanmu a ranshi yayi alƙawari ko zankai yaushe ban dawo ba zai jirani ,

Daga gidanmu ƙofar soro muka nufa gidansu Mamy ƙarfe 8:18pm mukayi parking a ƙofar gidansu kamar yanda tayimin kwantance , bayan mun tsaya na kirata a waya , babu jimawa ta fito cikin shiga mai ɓatar da hankali , tana isowa ta kama mota ta buɗe ta kashe a gidan baya , shi kuma yaja mota muka tafi , shegen tsoho kenan yace ina muka nufa ne ? Yayi maganar yana kallona ,

Murmushi nayi tare da cewa nifa guzirin dare nayo maka itace zaka tambaya bani ba , kaga ni kullum muna saka rana amma abun bai yuwu ba shine dana ga mai buƙatar ruwa a tsakar rana nace tazo ina da ƙatuwar randa { tukunya } a gidana har yoyo takeyi { ɗiga } kaga kuwa idan har ta riƙe babban kofi a tausayawa ruwan nan domin saita ƙare shi kaf hankalinta zai kwanta , juyawa nayi na kalli Mamy sannan nace a ina zakisha ruwan ne .... ?

Cike da bariki tace aishi ruwa ko a tsakiyar hanya shanshi akeyi saidai idan ba ƙishirwar ke damunka ba , amma tunda ni mace ce dole zan matse ƙishirwa har mu isa gida , amma ka daure kar kayi tafiya mai tazara dan lumfashina gaf yake da ɗaukewa , !

Karkata mota yayi ya ibi hanya , muka nufi kwaɗo , har muka isa babu wanda ya sake magana , a ƙofar gida yayi parking shida ita suka shiga aka barni a cikin mota , shigarsu babu jimawa na fara kiran Baban Hafsa inda zamu sameshi ya faɗa mana nace muna zuwa babu ɓata lokaci , Mamy kuma da Baban Amisty bansan abinda ya faru ba , sundai share awa da rabi sannan suka fito...

Bayan sun fito ta buɗe inda nake zaune tace fito mana haka nan , nace kidai shigo muje , Mamy tace nan zamu sauka , fitowa nayi mukayi sallama dashi tare da ƙara tuna mishi sai mun haɗu wurin party yace in Allah ya yadda , yana tafiya muka samu wuri muka zauna , wayata ta ansa ta tura min vidion data ɗauko nashi abundai babu kyan gani ko ya akayi tayi masa dibara ta ɗaukoshi tasa shi sai iskanci yakeyi , a wayana ta tura bayan ta tura ta shiga whatsapp ta turawa Amisty abinda zata faɗa nake faɗa tana rubutawa...

_Salam aminiyata Amisty , Sultana ce ban sani ba ko kin goge lambana shi yasa na baki sani dan kar ki shiga dogon nazari da tunani , kinsan mage bata cin bushiya , idan kuma maciji ya raɓi bushiya noƙe kanta takeyi yana tahowa da ƙarfinshi dan niyar mugunta sai ta noƙe kanta ya soki ƙayoyinta , maciji baya san tabo daga nan sai ya sari kanshi ya mutu , bushiya sai ta fito taci gaba walinta a duniya , tou haka tsaka take mage kaɗai ke cinta ta rayu amma ke in kakaci ta sai sheƙawa lahira , ganin aljanni a siffarshi akwai tsoro da firgitarwa masana ɓoyayyan sirri suna cewa idan kaga aljani a siffarshi kwanakin mutuwar ka ne yazo , nidai naga aljani ban mutu ba kuma naci tsaka ban mutu ba shi yasa na turo miki kema ki gani shin kina da yawancin kwana ko daga yau kwananki ya ƙare ne....?_

Turawa tayi ni kuma na ɗora da voice note cewa kiyi haƙuri kuma kibi sannu ki warware maganganuna kinsan tsarƙesu nakeyi idan kin gani kiba Hafsa ta tayaki gani....

Bayan na tura muka hau napep muka doshi barhim estate acan Baban Hafsa ke jiranmu , shima dai sun shana yadda ya kamata kuma Allah ya bata nasarar ɗauko min mugu , itama Hafsa tura mata nayi da voice note cewa...

Duk gudun kare idan yaga kura ɓoyewa yake domin tsira da rayuwarshi , haka mutum idan yaga abun tsoro kuka yakeyi ya rumtse idanuwanshi , irin haka kikaji a lokacin da kika cire towul in dake jikina..... ?

Ina gama faɗa na sakeshi ya tafi.... , Napep muka hau muka nufo gidanmu , saida aka fara saukeni aka wuce da ita bayan ta shedamin zasu zo wurin shagalin ita da zugar tata ƙawayen , godiya nayi ina ɗaga mata hannu har suka tafi ,

Kallon agogon hannunshi yayi yaga 11:35pm , daga ina nake a wannan daren shine tambayar daya fara ma kanshi kuma bashi da mai bashi ansar tambayar , ni kuma cike da farin ciki na tunkari ƙofar gidanmu sai tsalle² nakeyi na jin ɗaɗi na shige gida abu na ,

Jiki a sanyaye DK yaja motarshi ya nufi gida zuciyarshi tana mishi babu daɗi , amma yayi addu'a gobe tazo mishi lafiya ,

Yau laraba kuma itace ranar da nake wannan gagarumin taro wanda na samu damar gayyato mutane daga sasoshi da dama , tunda safe ake shiga da fice a gidanmu duk inda ka buɗe idonka zunzurutun karuwai ne kawai suke kai koma , wane yaji ga wane waccen taji ga wance , taron motoci ne burjik a ƙofar gidanmu duk wanda ya wuce sai yayi tir da irin matan da dake ƙofar gidanmu !

Shi kuma Dikko a safiyar nan tayi mishi babu daɗi dan matarshi aka kai asibiti bata da lafiya sosai , kuma taƙi cin abinci ta rame tayi duhu saboda ciwo da damuwa , hankalin Dikko idan yayi dubu ya tashi da guda ² kallo ɗaya zaka mishi ka gane yana cikin damuwa , ga damuwata ga ciwon matarshi ....

Taruwa akaci gaba dayi duk yaran Baba Ƙarami sunzo gida ya cika taf kuma na duba har yanzu daga Amisty har Hafsa babu wanda ya hau online dan suma suna can suna shirya tasu gadar zaren ,

Komai fa anyi kowa ka gani a wurin shima yakai wani babban shege , sai 6:00 aka fara tafiya wurin partyn , Nana dai bata samu zuwa ba mijinta ya hanata kuma ta hanu , Karima itama bataje ba amma A ` i da Saude tare dasu aka tafi duk yayuna maza da mata sunje ,

Dikko yana duƙe gaban gadon Sadiya riƙe hannunta yayi cike da damuwa yace Sadiya karki kashe kanki don Allah idan baki so na ki faɗamin sai in sahale miki auren nan ki huta , ni ina da damuwa idan naga kina cikin damuwa ko nayi miki wani abu bai miki daɗi ba ne ?

Karkata kanta tayi gefe hawaye suna ci gaba da gangaro mata , zama Dikko yayi gefen gado ya tattaro natsuwarshi fuskar Sadiya ya tallafo da duka hannayenshi yace mene ne ? Ki faɗamin wai meke damunki ne ? Dakel ta ɗaga bakinta zatayi magana a daidai lokacin da wayarshi ta fara ringing , cirowa yayi ya duba , Umar ne dan haka ya ɗauka tare da cewa ina ne..... ?

Bayani Umar ɗin yayi masa , bayan ya gama Dikko ya kashe wayarshi , shafa gefen fuskar Sadiya yayi ina zuwa , yana faɗin haka ya miƙe ya fito daga ɗakin , ita kuma taci gaba da kuka , bayan ya fito yacewa Mom insha zaije ya dawo yanzu , Allah ya tsare tayi masa Al ' Ameen da sauran tawagarshi suka rufa mishi baya.... !

A bakin get suka ɗauki Umar suka nufo inda muke taro , a lokacin anci rabin shagali itama Hafsa ta taho dan ta wulaƙantani tunda gidan Babanta ne , amma tana zuwa labari yasha banban duk wannan taron jama'ar bai hana uban Hafsa rungumeni ba ya yanko cake yana bani a baki , gaba ɗaya wurin aka ɗauki sowa da ihu shi dama Alaji tunda ya ajiye kayan party nace kawai yaje tunda taron mata ne babu maza , kuma yayi tafiyarshi...

Lallaɓawa tayi ta koma da baya ba tare data bari wani yaji koya ganta ba , ihu akaci gaba dayi sakin sauti akayi yadda ya kamata mata sukaci gaba da farantawa sheɗan ,

Hafsa tana fita taci karo da Dikko ya fito daga mota , da gudu ta nufi wurinshi tana kuka cikin kuka ta fara faɗa mishi abinda Sultana tayi mata niko nace danma baki ga vidio ba , number wayar Sultana Dikko ya ansa a hannun Hafsa ya fara kiranta ,

Muna ta cashewa wayata ta fara zurzur dan ba ƙara takeyi ba murzawa takeyi sai kaji sautinta yana shiga maka hannu burbur , ɗauka nayi naci gaba da kwantace ba tare dana jira naji ko waye ba ,

Cikin wata irin murya yace fito gani nan na kasa gane gidan , wallahi banyi tunanin Dikko bane nayo waje , ina fitowa naga Hafsa tsaye da wanda bansan ko waye ba domin ya juya bana ganin fuskarshi sai bayanshi , cike da mugunta nayo wurinta dan a tunani na taga vidio zamu cashe rashin mutunci ,

Saida nazo gabansu na gane Dikko buɗe baki nayi da zumar nayi magana ya wanka min wani irin gigitaccen mari harsai dana juya kamar ranfa saboda karfin mari kafin in dawo hayyacina ya sake wankamin wani firgitacce wanda saida nayi ɗimuwar tunani na dan wallahi a daidai lokacin da zaka tambayeni suna na bansan abinda zan faɗa maka ba ,

Ƙara ɗaga hannunshi yayi zai kaimin wani marin a gigice na riƙe hannun cikin kuka nace yi haƙuri don Allah , a tsawace yace tou shiga mota , har yanzu dafe nake da inda ya mareni na nufi wurin motar da kanshi ya buɗemin na shiga sannan shima ya shigo dani dashi ne a baya , rufe murfin motar yayi Al' Ameen yaja sauran motocin suka biyo bayanmu...

Duƙar da kaina ƙasa nayi ina kuka cikin sauti mara hayani jikina sai kyarma yake dan har yanzu marin shiga jikina yakeyi ,



20/09/2019


Jamila Musa ..... 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 36


Duƙiyar ta isheni na ɗago hannuwana na rumgume kujerar da ake kira da mai zaman banza , ta kusa da Al 'Ameen babu kowa akai dan haka na rumgumeta kawai naci gaba kuka ,

Kallon hannuna Dikko yayi idonshi ya sauka akan wayata kawai ya miƙa hannunshi da zumar cirota daga wurina , da sauri na ƙara riƙe wayar gam tunda bana saka ma waya wasu malatsan sirri wanda saini na buɗe da kaina zata buɗe a buɗe take zaka iya shiga duk inda kake so...

Da ƙarfinshi ya fizgi wayar kafin yayi mata kyakkyawan riƙo na fizgeta a hannunshi dan bai kamata ace anga wannan ɗaukar ba bai kamata ba , miƙo hannunshi yayi tare da kauda kanshi gefe yace bani ,

Girgiza kaina nayi alamar a , a , cikin tausassar murya ya matso da fuskarshi kusa dani yace bani wayarki nace , matsawa nayi tare da ƙara saƙe wayar a bayana , shima matsowa yayi kusa dani yace zaki bani ko sai kinci cingom ne ... ?

Cikin kuka nace dan Allah ka shafamin lafiya , kallona yayi gefe da gefe sannan yace ta ina zan shafa miki inyi sauri dan nafi so kiyi lafiya da nisan kwana ya ƙarasa maganar yanamin kallo mai nuni da rainin hankali , nima kallon raini hankali nayi masa amma banyi magana ba ,

Shima shiru yayi bai sake magana ba kuma ya daina maganar in bashi waya , daga haka dukanmu babu wanda ya sake magana har muka zo inda zamuzo , duk sauran motocin a waje suka tsaya tamu kaɗai ce aka buɗe ma get muka shiga , bayan Al ' Ameen yayi parking ya fita daga cikin motar aka barni daga ni sai Dikko !

Al ' Ameen na fita Dikko ya sake taro hannu in bashi waya , cikin kalar ban tausayi na maida hannuwana baya tare da cewa dan Allah kayi haƙuri , ni nace kinyimin laifi ne ? Wayarki kawai zaki bani nace ya ƙarasa maganar cikin kausasa murya yana zazzaro idanuwa ,

Tsoro naji ya kamani sosai dan haka da sauri na miƙawa Dikko wayar , ansa yayi yana mai min ƙwafa tare tare da latso wayar haske ya bayyana , kafin ya shiga inda yake so kiran Amisty ya shigo cikin wayar , badai serving nake da sunan mutum ba lamba ce kawai , dan haka kiran sunan lambar dana ajiye number Amisty yayi sannan ya shafa wayar ya kara a kunnenshi ,

Dafe kaina kawai nayi lokacin da Amisty ta fara watso kalamai masu zafi da ɓatanci akaina sai ta ciko bakinta da ashariya sannan ta luƙaƙamin tare da furta wallahi idonta idona sai takaini kiyama ta dawo , maganganun dai babu daɗi dan har mahaifina ta saka duka dai abun gwananin ban takaici , tana zurara zagin wayar Hafsa ta shigo , amma bai ɗauka ba saida Amisty ta sauka ta kashe wayar , har ya gama waya da Amisty kiran Hafsa daya tsinke sai ta sake kira....

Itama Hafsa ta tata nata rashin mutunci itama a kalaman nata maganganu tayi masu kyaushi itama dai abun babu daɗin ji , idan tayi magana taji Dikko baice uhum ba , sai tace kina jina ko ? Sai yace Umm itama itace ta gaji ta kashe wayarta...

Cikin takaici Dikko ya kalleni tare da cewa fita , ina zanje ? Rumtse idanuwanshi yayi tare da sake cewa fita bana san ganin ki wallahi komai zai iya faruwa ki fita kafin naji miki

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login