Showing 111001 words to 114000 words out of 161239 words
bayan na gama na watsa ruwa na koma nayi kwanciyata amma ba bacci nake ba !
Gidan shiru kamar babu kowa ciki sai ƙarar iska irin mai tahowa da ƙasa , a hankali sanyi ya fara saukowa irin mai shiga ƙashin nan , zuwa bayan la'asar sanyi ya sauko sosai wanda yasa mutane suka fara saka rigunan sanyi,
Ni kuma da banda rigar sanyi ina cikin bargo na duƙunƙune , ga azabar yunwa da nakeji na rasa inda zan saka rayuwata , har akayi magrif babu wani labarin abincin rana bare in saka ran na dare zaizo , nasha ruwa har nayi fitsari bansan adadi ba , tun ina daurewa har na fara Allah ya isa a zuciyata...
Tunda nayi magrif ban tashi daga inda nayi sallah ba ina zaune na zabga tagumi kuma ni ba addu'a nakeyi ba , ina cikin wannan tunani naji ƙarar buɗe get murmushin jin daɗi nayi nasan Dikko ne kuma yazo da abinci , tabbas abinci yazo ya kawomin , cike da murna na leƙa ta window kuma wallahi shiɗin ne , sanye da tsadajjiyar baƙar rigar sanyi mai kyan gaske da burgewa tana da farin zif daga gaba , an zageye wuyan rigar da farin ado amma ba irin na mata ba ina ganin dibara ce dan kar rigar ta lalace daga saman wuya , sanye da shuɗin wando da takalmi baƙi amma ba rufaffu bane maɗauri gare su kamar sandals , hannun rigar ya ɗan naɗeshi zuwa guiwar hannu , kanshi babu hula kuma fa gaskiya yayi kyau dake baida ƙiba ko kaɗan amma yana da tsayi daidai burgewa bana zarce misali ba...
Al ' Ameen ke ɗauke da kulolin abinci shi kuma waya yakeyi , ina ganin sun tun karo ƙofar shigowa palon nayi sauri na kowa saman abin sallah na kalli gabas ,
Suna shigowa shi Al ' Ameen ya kunna musu kallo , maimakon ya kawomin abinci sai kawai suka zauna sukaci gaba da kallon kwallo , har akayi isha'e suna zaune kamar asara suna kallon kwallo , inajin maganar Dikko lokacin daya shiga ɗaki mai kallon wanda nake ciki yana cewa bari inyi sallah dai , tsoki nayi tare da cewa andai ji kunya sallah a gida , nima tashi nayi nai sallah dan ina da alwallah ...
Har na gama sallah banji Dikko ya fito ba , kuma naji palon ya fara cika da maza ga dukkan alamu kila gidan dai matattara ce ta maza , tunani na farayi karfa su cinye abinci ban samu ba , tashi nayi na fita ɗan madaidaicin palon na zauna ina jiran fitowar Dikko idan ya manta da ina nan tou ya ganni ya gane ina nan ,
Tunda na zauna ƙarar motoci ke shigowa , hayaniyar sai ƙara sama takeyi maza surutu ga magana babu natsuwa , nafa daɗe ina zaman jiran Dikko bai fito ba , kuma bana so na leƙa babban palon bansan ko su waye a wurin ba , na haƙura da niyar komawa ɗakin da aka ajiyeni naji dai bazan iya kwana banci komai ba yunwa nakeji kamar zan mutu wallahi , dawowa nayi kai tsaye na shiga ɗakin ,
Da sauri ya kallo ƙofar dan yaga waye yake shigowa yana zaune saman abin sallah , murmushi yayi ganina tare da cewa An mata miye ? Ɗan suɓaro baki nayi ina wasa da yatsun hannuna nace dama , sai kuma nayi shiru , ɗauke kallonshi yayi daga gareni yace dama me ? Shiru nayi na kasa magana , shima bai sake magana ba yaci gaba da latsa counter , naci uwar mintuna sha biyar Dikko bai sake kallona ba kuma bai sake magana ba ,
Saida ya gama abinda yake ya ɗauke abin sallar daga inda yayi sallah ya ɗora gefen gado , zuwa yayi zai wuce ya fita dan yayi kamar ma babu ni a wurin ,
Ya kusa fita nace yunwa nakeji , yi yayi kamar baiji abinda nace ba ya fice abunshi , biyoshi nayi a lokacin har ya kusa fita daga palon ya shiga babban palon , nace da Allah nace maka yunwa nakeji nayi maganar a tsiwace , naji ya faɗa tare dayin gaba abunshi ,
Tsoki nayi cikin ɓacin rai na koma ɗaki ina gunguni , shi kuma daya koma kallonshi yaci gaba dayi , sai ihu sukeyi "yan iska kamar mahaukata , amma bana tunanin Dikko yana wurin dan har yanzu ban jiyo maganarshi ba , duk wanda aka ci su sai kuji hayani ta ƙara sama , sai gaddama da magana cikin faɗa² ,
Sai yanzu naji dariyar Dikko yana shigowa cewa ko gobe da fansar kura saidai garin da babu awaki , murmushi nayi cikin yanayin jin kunya nace ashe kaima ka iya karin magana ? A dai² lokacin daya shigo yana dariya ,
Ɗaure fuska nayi kamar ina cikin yanayi damuwa , ko kallonshi banyi ba ya ɓatamin rai ni zai zubowa abinci a gaban bainannasi hmm , ga abinci ya faɗi maganar a daidai lokacin da yake ajiyewa a gabana , kauda kaina nayi na tura abincin na ƙoshi ...
Murmushi yayi tare da ɗaukar abinci zai fita , nace kai nifa wasa nakeyi bani nan nayi maganar tare da nuna mishi ya maidoshi gabana , banza yayi ya fice daga ɗakin da sauri na tashi nabi bayanshi amma kafin in fito harya fice ya koma cikin abokanshi yana dariyar mugunta , a ranshi yace daga yau sai kiyi hankali ni ban iya wasa ba kuma ba'amin wasa ,
Wannan rana saidai na kwana da yunwa nasha kukana har bacci ya ɗaukeni bansan lokacin da suka tafi ba ,
Koda safe dakel nayi sallah saboda yunwa duk jikina ciwo yakeyi kamar nayi aikin ƙarfi , bayan na gama sallah na daddafa nayi wanka , na canja kaya sannan na koma bacci ,
Yauma da asibiti ya fara , ya lallashi matarshi kamar yanda ya saba , yau ya samu ya lallaɓata tasha ruwan tea , ya kuma sake tambayarta damuwarta dai tayi masa zurfin ciki har yanzu , dan haka bai wani damu ba ya wuto wurina ,
Yau shi ɗaya yazo babu Al ' Ameen kuma kai tsaye ya shigo ɗakin , bayan ya ajiye kayan da yazo dasu ya kunna fitila yana cewa anya ma kinyi sallah ? Tashi ya faɗi maganar tare da yaye bargon dana lulluɓe , juyawa nayi na kifa kaina saman katifa saboda haushi ya bani jiya sosai ,
Yauma bakijin yunwa bara in tafi , ya faɗi maganar tare da ɗaukar kwandon , cikin fushi nace abinci banza gare ka , ko an faɗa maka yunwarshi nakeyi muma gidanmu sau 3 a rana akeci ka tafi na ƙoshi nasan yunwa baza ta kasheni ba an girma ba'asan an girma ba ,
Dariya yayi tare da zama gefen katifa yace wai nima irin wasan jiya nake miki amma ke naji kalaman naki zafi garesu ai kema da sai kiyi shiru kamar yanda nayi shiru jiya , sai kace dai kina jirana ? Cike da jin haushi na tashi zaune ina cewa jiranka nakeyi kamar yadda ka zanemin rayuwata haka zan zane taka rayuwar babu gudu babu ja da baya ba abinda ke cikin zuciyata face ɗaukar fansa akan ka ,
Murmushi yayi tare da gyara zamanshi sannan ya ɗaure fuskarshi babu wasa a tare da ita ya fiddo siffofinshi masu tayar da tsikar jiki da saka fargaba yace ke har gobe yarinya ce , amma ki sani ya nuna ni tare da ci gaba da cewa wannan tsarin tamkar sautin radio na ne , na ƙarashi na rageshi yadda nake so , kiyi haƙuri burina kaɗan ne amma sanin ya kamata na yana da ƙarfi , ban iya ba kece kika koyamin kinsa na zama kamar wani sakarai sai biye miki nake ina ƙananan maganganu kamar mace , dakamin tsawa yayi tare da zaro idanuwa sannan ya sassauta maganar shi zuwa sauti mai kama da raɗa yace ki kiyayeni kafin na baki hukunci a karo na biyu , azabar yau sai tafi ta jiya zafi , ina nan kuma namijin ne .... 🤫 ya ƙarasa maganar tare da ɗora ɗan yatsanshi a saman bakinshi yace shitt ya rufe maganar da fiddo idanuwanshi da suka ɗanyi ja...
Jiki a sanyaye na koma na kwanta , ba tare daya kalleni ba yace tashi muyi break , da sauri na tashi naje na wanko bakina da fuskata nazo na zauna kusa dashi cikin ladabi , shine da kanshi ya zuba komai amma tea ɗin a kofi ɗaya ya haɗa kuma da kofi ɗayan mukayi amfani yana sha ya bani insha in miƙa mishi , cokali ma ɗaya mukayi amfani dashi ,
Ba wani damuwa a tare dashi ko kunya ko irin yaji babu daɗi haka dai , tsakaninshi da Allah hankalinshi a natse yake , har muka gama da kanshi ya tattara komai ya mayar a kwandon ya ɗauka kwandon ya fita , ya daɗe sannan ya dawo ya kwanta a gefen katifa ,
Wayarshi ya ciro yace zo kiga in nuna miki "yan uwana , matsawa nayi kusa dashi amma ni ba kwanciya nayi ba zama nayi , ɗago kanshi yayi tare da bani wayar na riƙe a hannuna yana wuce hotuna , wannan itace wance wannan kaza ce dad ina ne kinga momy kinga wannan itace nake bi mawa , tana aure a gari kaza , haka dai yayi ta wucewa har yazo kan Sadiya yace wannan kuma matata ce....
Kai kalmar namiji yace matata kalmar tana da girma da matsayi , matata saida na maimaita a zuciyata sannan nace ban ƙaunarta har abadan duniya na faɗa a zuciyata , kallona Dikko yayi tare da cewa tayi kyau ko ? Ban sani ba nace masa , baiyi murmushi ba kuma baiyi dariya ba yace kada Allah yasa ki sani "yar rainin hankali ,
Cike da ɓacin rai nace dakai da matarka duk kune "yan rainin hankali munafikai dukanku , tsareni yayi da ido tare da cewa kishi ko ? Ya ƙarasa maganar yana nunani da san yayi murmushi amma ya haɗeshi , tsoki nayi tare da cewa hmmm Allah ya sawaƙe min niko waye zanji kishin a cikinku kai ne ko ita ?
Miƙewa yayi tare da cewa tunda baki son na tayaki fira zan tafi , bazan dawo anjima ba Al ' Ameen zai kawo miki abinci , idan Allah ya kaimu gobe lafiya ki shirya da wuri dan bana san tafiyar rana , yana faɗin haka yayi gaba abunshi....
Abinci rana da dare duk Al ' Ameen ya kawo min , yau babu wanda yazo kallon kwallo ni ɗaya a gida bayan naci nasha na koma na kwanta tare da addu'ar Allah ya kaimu gobe lafiya !
Da safe tun kafin in tashi bacci Dikko yazo , shi ya tasheni tare da ajiye uniform a gefen kati yace maza jiranki nakeyi , kallon kayan nayi sannan na kalli Dikko da yasha manyan kaya hada babbar riga hular kanshi kuwa sai sheƙi takeyi saboda sabinta ko wanki ne ? Koma dai miye sai ka kalli kanka a ciki kayi sakace , kallon ƙafarshi nayi nan ma komai yaji gemu ma dai yasha gyara yana nan dai da jan hankali da yakeyi , gaskiya Dikko haɗaɗɗen namiji ne mai tafiya daidai da zamani , ga kyau ya gayu uwa uba iya saka sutura , Dikko nada burgewa ...
Katse min tunani yayi da cewa kin tsaya kina kallona ! Kiyi maza jiranki nakeyi , yana faɗi maganar yabar ɗakin , cikin kuka na nufi toilet nayo wanka sannan nayo alwalla nazo na fara gafatar da sallah asuba da banyi ba akan lokaci , bayan na gama na shirya cikin kayan makaranta ina kallon kaina a madubi na fashe da wani irin kuka wanda har sai da gaban Dikko ya faɗi...
Da sauri ya shigo ɗakin fuskarshi ɗauke da damuwa yace a mota zakiyi kalaci , shi a tunaninshi yunwa nakeji , cikin kuka nace ni wallahi bana san makaranta haba Yaya Dikko me yasa zakamin haka abin kunya a ganin a makatanta yanzu ,
Wani irin kallon rainin hankali yayi min daga sama zuwa tsakiya ta yace lallai yarinyar nan kin rainani nine Yayan naki.... ? Baki da hankali ma da Allah ni wuce mu tafi munatane na jirana , hannu na ɗora saman kai ina cewa dan girman Allah ka kyaleni wallahi bazan sake ba , cikin kwantar da murya yace muje tun kafin kiji babu daɗi ,
😭 hijabi na saka nabar kallabin a katifa nayi waje , abun kunya shi ya ɗaukomin kallabin wai hada jakkar makaranta saboda ci baya , waini zan koma makaranta , ina gaba yana bayana har cikin mota , ni kaɗai na shiga baya ya wurgomin jakar da kallabina ya rufe ƙofar ya shiga gaba , Al ' Ameen yaja muka fita daga gidan , kuka naci gaba dayi ina ma katsina kallon ƙauna , tafiya akeyi sosai dan Al ' Ameen yakai mota maleji wurin gudu , kuka na ya ƙaru lokacin da naga an ibi hanya tafiya da gaske babu fashi....... !
22/09/2019
*JAMILA MUSA CE...* 💅🏻
⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_
*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_
*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_
_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻
*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_
&
*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*
🅿 ------ 38
Ƙuramin idanuwa yayi yana kallona ta cikin madubin gaban mota , sai kuka nake ina fyace majina da gefen hijabina , tissue ya wurgomin bai juyo ba kuma bai kalleni ba yace zaki ma mutane shiru haka nan ko kuma dai.... ?
Harararshi nayi cikin muryar kuka nace mara zuciya ko mutum baya harkar ka sai ka shiga nashi mutum ba dangin uwa ba na uba kawai ka shigomin rayuwa , kyakyawan murmushi yayi da gefen bakinshi amma baiyi magana ba , kallonshi Al ' Ameen yayi bakinshi ɗauke da magana , murmushi Dikko yayi tare da cewa manta da labarinta ka ƙaddara ma bama nan bare kayi tunanin munji abinda tace , makaranta dai zuwa babu fashi !
Shiru sukayi su dukansu babu wanda ya sake magana , saidai shi Dikko yana kallona ta cikin madubi idan akayi sa'a muka haɗa ido sai yayi murmushi mai tattare da mugunta , matsawa nayi daga saitinshi dan ya daina kallona , ƙara gyara saitin madubin yayi yaci gaba da kallona , kwanciya nayi na lulluɓe da hijabi naci gaba da baccin dole...
Har nayi bacci na farka bamu isa ba , kuma tafiya Al ' Ameen yake bata wasa ba dan shima kusan irin tuƙin Dikko yakeyi kamar basa san rayuwarsu , ganin har yanzu a hanya muke yasa na sake komawa na kwanta ina mai ci gaba da kuka , jin kukana yasa Dikko juyowa tare da cewa ke miƙomin kunun nan tunda baza kisha ba ,
Cikin kuka nace ina sha , Al ' Ameen yasa ya faka a gefen titi da kanshi ya fita ya ɗauko ruwa a but sannan yazo ya buɗe inda nake ya bani ruwan , yana nufi in kuskure baki na , fita nayi na kuskure bakina na wanke fuskata na koma mota na zauna ,
Ɗan ƙaramin flaks ne na sulba mai kyau cike da kunun gyaɗa tun kafin in fara sha Al ' Ameen ya tada mota ya hau titi yadda ta kamata yaci gaba da gudu , cike da baƙin ciki nake shan kunun , yayi min daɗi sosai ɗan kaɗan na rage na miƙawa Dikko flarks in dan ya ajiye , ansa yayi ya shanye sauran dana rage, a raina kuma tunani nake Dikko ko ƙyamata bayayi yanda yake ɗan gayu mai aji har zansha abu in rage yasha saura na ,
Har muka isa bakin get in makaranta babu wanda ya sake magana , a bakin get Al ' Ameen yayi parking , muna zaune a mota ga dukkan alamu akwai wanda ake jira , bamu wane daɗe ba , wata irin shareriyar mota tayi parking kusa da tamu , wani matashi ne ya fito daga motar yayo wurin motarmu , Al ' Ameen ya sauke gilashin kusa da Dikko , yana isowa Dikko ya miƙa mishi hannu suka kashe ,
Sai kuma aka shiga gaisawa bayan sun gaisa yace ina An matan take ne ? Murmushi Dikko yayi yace gata can baya kuka takeyi , dariya matashin yayi tare da cewa tun daga katsina har bakori tana kuka ? Dikko yace ai bata da aikin yi , dariya matashin ya sakeyi tare da cewa sannu dai za'ayi mata ,
Ba