Showing 30001 words to 33000 words out of 161239 words

Chapter 11 - KWARATA

Start ads

28 Aug 2025

583

Middle Ads

Tafiya nayi mai tsayi ba tare da sanin inda zanje ba sannan na tsaya wani shago na samu aron waya, lambar Umar na basu nace da Allah su saka a waya su kirashi, ansa mai shagon yayi yasa lambar ya kira, babu wani b'ata lokaci aka sadani da Umar...

Sultana ce, na fad'a a lokacin da Umar yace hello, Oh kin gama ne ? Ya tambayeni, maimakon na bashi ansa saina kece da dariya kamar hauka sabon kamu..... Meya faru ne ? Inji Umar, saida na gaji da dariya dan kaina sannan nace darasi.

Yau na tabbatar ni bariki ta fini tabbas na tafi na barka, wannan makullin d'akin daka bani ne shine na dawo muku da kayanku, amma zan baka sak'o a wurin Dikko tunda kasanshi , ka fad'a mishi cewa Sultana tace zasu gauraya........ Ina fad'in haka na yanke wayar na mayar da ita ga mamallakinta nayi gaba abuna....

Wata irin zufa ta ketowa Umar mai makon salati sai ashariya, ya fara luk'ak'a zagi tare dayo waje da gudu, yana cewa amma lallai yarinyar nan ni zata danfara, wato wani bazaici abinci yace kai yaci ma ba, wato nine abinci itace bakin ni zakici ki gudu ? Kuma har kike wani cewa mai gida Dikko zaki gauraya dashi ? Kai wallahi idan na yadda shege ne ni, kuma yanzu zan kira Dikkon zaki ci kutumar ubanki, kici dubu d'ari zanci miliyan daga jikinki.

Jikinshi na kyarma ya fara kiran wayar Dikko har ta tsinke bai d'auka ba, k'ara kiranshi yayi bai d'auka ba, ci gaba yayi da kiran wayar babu k'ak'k'autawa, saida ya kira Dikko yakai sau goma sannan miskilin ya d'auka wayar.....

Ya akayi ne ? Shine tambayar da Dikko yayi ma Umar, cikin tausasa lafuzzan shi yace ranka ya dad'e kasan wata yarinya Sultana..... ? Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un Dikko ya fad'a a ranshi lokacin da aka ambaci sunan Sultana,

Me ya faru ne ? Dikko ya tambaya ? Umar yaci gaba da cewa ranka ya dad'e yarinyar nan "yar damfara ce, tazo nan gidan "yanci ne , gidan karuwai suke cewa gidan "yanci, dan idan aka kira karuwai d'in haka abun babu dad'in ji. Shi yasa su gogaggin "yan bariki suke kiran gidan da gidan "yanci.

Wata irin zufa ta tsatstsafowa Dikko amma yayi shiru yana sauraren Umar, ranka ya dad'e kwananta hud'u a gidan "yanci shine yau ashe ta shirya guduwa ta raina min hankali ta ansar min kud'i dubu d'ari akan zata bani tukuici, { zasuyi iskanci } shine ta gudu, wai kuma saboda ta d'aukeni sakarai wai tayomin waya in fad'a maka wai zata gauraya dakai.

Saida Dikko ya goge zufa sannan yace yanzu kayi hak'uri zan biyaka kud'inka, ai ranka ya dad'e ni ba kud'in bane yafi damuna mummunar maganar data fad'a a kanka ne, bayan zata gauraya dani tace maka wani abu ? A , a batace komai ba, amma ina ruwanta dakai ? Tana da dalilinta na fad'in zata gauraya dani, ka fita harkar yarinyar nan zan tura maka kud'inka karka ma sake kace zaka sake tashin wata magana kuma karka sake ka nemeta ,

Umar yace mai gida zafa ta gaura dakai ? Ka kuwa san abinda gauraya take nufi ? Dikko yace ta gaurayo dani d'in ina ruwanka ? Kaine tace zata gaura ko ni ? Shiru Umar yayi, tsoki Dikko yayi da niyar kashe waya, Umar yace ranka ya dad'e nidai idan kaine zaka biya kud'in nan na yafe maka su, Dikko yace ita zaka yafewa bani ba tunda ni banci maka ba, taci albarkacinka na yafe mata, na gode shine abinda Dikko ya fad'a tare da kashe wayarshi.

Miye tsakanin Dikko da Yarinyar nan ? Shine tambayar da Umar yakewa kanshi wanda ya rasa mai bashi amsar tambayar, tou yaushe mai gida ya fara harkar mata ne ? Dariya yayi tare da cewa shegiya duniya mata bala'e ne wato duk musulinci mutum da kawaicinshi babu uztaz babu mahaukaci kowa dai yasan darajar ku, ai dole nake yafe dubu d'ari nasan wasu miliyoyi ne zan ansa, inama zanga yarinyar nan da na tambayeta miye tsakaninta da Dikko.

Mi yasa zakiyi haka ? Me zaki tsinta a harkar karuwanci banda wahala ? Me kike so ne ? Me kika rasa ? Kud'i ba damuwa na bane da zan ganki da na wadaki da dukiya har sai kin rik'ajin kyankyan kud'i, k'amshisu ma idan kikaji saiya rik'a tayar miki da zuciya, ke kuma duniyar kike so ? Jinjina kanshi yayi tare da cewa Allah yasa miki natsuwa ki dawo daga rakiyar shaidan. Allah ya had'ani dake Sultana in baki hak'uri in kuma nemi yafiyarki,

Mutane sunamin bahaguwar fahimta, yanda kike kallona ba haka nake ba, kuna min wani tunani na daban bayan ba haka Dikko yake ba,

Duk abinda ya faru tsakani na dake wallahi ina ganinshi ne kamar wasa, banso haka ba, bansan ya akayi nima na koma kamar wani sakarai ba wallahi, Allah ya tsareki fad'awa halaka, idan har kika fad'a harkar karuwanci na cuci rayuwata da zuri'ata da banma fara tunanin auren ba.

Farin ciki kamar in tashi sama yau gani ga naira dubu d'ari, kud'i suna da dad'i gaskiya da farko dai saina ci kaza, sannan na gano wani abu d'aya da maza suke so a tattare da mata, suna san k'osashshiyar mace, suna san tsaftatacciyar mace, suna san mace mai aji suna san mace ma'abociya k'amshi macen data iya soyayya da tattali, ina zan nufa yanzu ? ..........









16/08/2019


Da Allah kuyi hakuri rasuwa akayi min ne kukaji shiru da dad'ewa haka,


Ina ma kowa barka da sallah, Allah ya maimaita mana yasa muna da rabon ganin na bad'in bad'ad'a, amin. Barka da sallah.

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_



*KWARATA*
_{{Kalu bale gareku matan aure}}_



*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_


_Sadaukar wa gareku,_ 👇🏻

*ASMA'U ZAYYAN* _{{ Asmeenat }}_

&

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*



🅿 ------ 10


Lallai idan nayi shiru da maganar nan ban fad'awa mahaifin Dikko ba nan gaba ya gano wani abu lallai zan fuskanci baraza na dagani har mahaifina, kila ma ya kora mu, ya zama wajibi naje na fad'a masa halin da Dikko yake ciki, in yaso zaiyi bincike abinda ya had'ashi da ita yarinyar, Umar yake magana duk abin yazo ya dameshi yana mamakin abinda ya had'a Dikko da mace har take fad'ar zata gauraya dashi.....

Dikko mai zafi akan mata, ya akayi ya koma mai sanyi ? Wuta ne mai tsananin k'unar gaske ga duk macen data matse masa, babu abinda ya tsana duniya irin mata, amma wai shine yake godiya akan mace... Wace ce ita ? Miye tsakanin su ne.... ? Kayi shaye sheyenka ne Umar shi yasa ka manta wace ce Sultana.....

Tsohuwar anguwarmu ta farko na koma, inda Dikko yayi ta siye siyen gidanjen da muke kamawa haya, gida mai sauk'in kud'i na samu na kama d'aki d'aya, bayan na biya kud'in d'aki na tafi kasuwa dan siyo d'an abinda ba'a rasa ba na amfanin yau da kullum.

Na dad'e sosai a kasuwa, saboda duk abinda nasan zan nema saida na tabbatar na siya saboda ni rayuwata ta duniya babu abinda na tsana irin aro, bana san na takura shi yasa zanyi k'ok'ori na bada k'addarata dan na samu kud'i.......

Umar durk'ushe a gaban mahaifin Dikko, hada wani hawayen munafirci kanshi a k'asa kamar sabuwar amarya a daren farko, Dady kuwa gaba d'aya yanayin fuskashi ya sauya zuwa damuwa bayan ya gama jin duk maganar da Umar yazo da ita, shi baya hana Dikko yayi magana da mata bane ko wani abu a , a shi baya so dai ya shiga damuwa har wani abu yazo ya sameshi, kuma idan yayi ma Dikko maganar aure sai yace shi yaro ne a bari saiya k'ara girma, ga Umar kuma yazo ya fad'i k'arya da gaskiya dandai kawai a bashi wani abu, wannan fada ce ko kuwa maulace ? Kallon Umar Dady yayi sosai sannan yace kirawo min shi....

Umar ya kira Dikko yafi so a irga amma bai d'auki wayarshi ba, ganin haka yasa Dady ya fara kiran Dikkon da kanshi, shima bai d'auka ba, jinjina kai Dady yayi tare da turawa Dikko sak'o kamar haka....


_Babana idan ka gama abinda kakeyi ka kirani._

Umar kuwa yana tashi daga wurin Dady ciki ya wuce inda iyayenshi suke, a gidan su Dikko Umar da iyayenshi suke zama, suna a k'ark'arshin su Dikko ne, kuma Umar shine mutumin da yayowa Bello jagoranci aka kawoni wurin Dikko, ni da dare na ganshi amma Allah yasa na ganeshi duk da jakanci na, amma shi ya kasa ganeni kwata kwata....

Umar bai dad'e da tashi ba kiran Dikko ya shigo cikin wayar Dady..... Da farin ciki Dady ya d'auki wayar tare da cewa ina ka shige ne ? Ko kana tunanin surukata ne ? Ya fad'i maganar cikin sigar zaulaya, d'an gyaran murya Dikko yayi tare da cewa barka da yini, ya gaishe da Dady dan kauda waccan maganar.....

Ansawa Dady yayi suka gaisa cikin farin ciki da soyayya irin na d`a da mahaifi. Bayan gaisuwa Dady ya tambayi Dikko labarin yarinya da Umar yazo mishi da ita, miye tsakaninsu kuma miye gaskiya labarin ...? Dady ya k'ara da cewa banso soyayya tayi min wasa da rayuwata, domin duk abinda ya tab'a hanci ido ruwa yake, tou duk abinda ya tab'oka ni ya shafa.

Me ya had'aku har take zaginka ? Gyara zama Dikko yayi sannan yace ba komai, kuma ma ai bata zageni ba Dady, duba Babana yaushe ka fara b'oyemin abinda ya shafeka ? Ni zaka juyawa baya ? Me zaka b'oyemi bayan kasan ni bana b'oye maka komai ? Fad'amin abinda ya dameka muyi damuwar tare.....

Shiru Dikko yayi na wasu mintoci yak'i yayi magana, Dady yace kai nake saurare Babana kaji tsoron Allah ka fad'amin abinda yake damunka idan har kana so nayi bacci a daren yau.....

Har yanzu Dikko baiyi magana ba kuma bai kashe wayar ba, Dady ya k'ara cewa ka daiji tsoron Allah ka fad'amin gaskiya k'arya ba halinka bane kuma masu sunan manya basa fad'ar abinda ba gaskiya ne ba, gaskiyar mahaifina da amana irin tashi yasa na saka maka sunanshi saboda kwad'ayin kaima ka zama mai gaskiya da amana kamarshi, kuma ina fatan ka zama mai adalci ko bayan bana duniyar nan..... Ina so ka zama jigo ga "yan uwanka ka tausaya musu ka karb'i damuwarsu ka sakasu farin ciki karka barsu suyi kukan rashin mahaifi, inaji a jikina bazan dad'e duniya ba, nayi kuka kuma na shiga damuwa rashin samun d`a namiji, sai kuma nayi farin ciki a lokacin da Allah ya azurtani dakai...

Idan kaga na damu da nasan abinda yake damunka saboda in d'oraka hanya idan naga zaka sauka daga saman layin gaskiya, ina fad'a maka tawa damuwar ne dan ka gane abinda duniya take ciki.

Me ya had'aka da yarinyar mutane take zaginka ne Babana ? Cikin kame kame yace Dady nifa ba zagina tayi ba, kuma ma yake maganar cewa tana min rashin kunya a ina akayi haka ? Ni ba ruwana da ita sab'ani ne kawai muka samu kuma ma ai abun ya wuce....

Saidai inayin mafarkinta idan ina bacci, inajin damuwa ne idan na tuno da ita, sai kuma inji kamar tana kiran suna na wani lokaci, kuma sai inji kamar tana tare dani, inajin kamar numfashinta a jikina sai kuma shashshekar kukanta tana dai zuwa min sosai a ranaku da dama, shi yasa ma nake d'an tunani, amma bayan haka banda wani damuwa da ita.

Tou soyayya kakeyi da ita ne ? Dady ya tambayeshi, no ba soyayya kawai dai rashin kunya tamin sai nayi maganin bakin tsiwa, kamar ya dady ya sake tambayar Dikko, shiru Dikko ya sakeyi ya kuma rasa abin cewa.

Kai nake saurare, Dady ya fad'a, kwashe komai Dikko yayi ya fad'awa dady amma bai fad'a masa labarin wani abu ya shiga tsakaninshi da Sultana ba, kawai dai yace ya sissiye gidajen da suke haya ne, a haka aka tsaya ba maganar yayi wani abu da ita.

Nasiha Dady yayi ma Dikko kamar yanda ya saba, yace yayi ta addu'a, kuma zasu tayashi har Allah yasa ya manta da labarin Sultana a rayuwarshi, godiya Dikko yayi ma Dady sukayi sallama.

Haka kuwa akayi domin dai Dady ya mik'e tsaye yasa ayiwa Dikko rok'on Allah dan shi a tunaninshi Sultana aljana ce, ko kuma mayu ce ko tanawa d`ansa asiri ne, dan haka Dady ya tsaya akan k'afafuwanshi saida ya tabbatar Dikko ya manta da labarin Sultana a rayuwarshi sannan hankalinshi ya kwanta...........

Wannan kenan...........


***

_{ kalu bale gareku matan aure.......... }_


Gidan da na kama haya gaba d'aya gidan matan aure ne babu zawara ko d'aya haka babu budurwa idan bani ba........

Kowa da mijinta daban babu wacce ta had'a miji da wata, abinda na fuskanta da rayuwar mazauna gidan kowa yanayi ma d'an uwansa kallon hadarin kaji ne, babu wanda yake san kowa sai zazzafar bak'in ciki da jin zafi da gasa da kowa yake nunawa abokin zamanshi ido biyu kunne tsaye babu kunya bare kawaici.

Gidan babu katsari kuma bashi da saiti kowa yaga dama shigowa yakeyi, sai a tara dandazon taron mata ayita maganganun sakarci da rashin kamun kai, shi yasa zawarun anguwar da "yan mata wanda suka bushe fitilarsu suka maida gidan dandalin sauke lalatarsu.

Suna da wata d'abi'a d'aya dana lura da ita ta wasan banza, kuma basajin kunyar nuna tsiraici wa junansu, ma'ana kamar irin cire riga da bra a lokacin fira, irin wancan tace amma wance gaskiya kinfi wacce nono, basajin kunya sakin maganganu na sakarci da fallasa sirin mazajensu.

Duk da ni yarinya ce mai k'aranci shekaru a cikinsu na raina musu wayau gaskiya, kuma na d'aukesu wawaye idan naga dama zan basu shawara kuma idan suka d'auka zata musu amfani, amma gaskiya banga dama ba, haggu zanyi amfani da ita dan ni yanzu ba shiriya nake so ba lalacewa itace na zab'a kuma duk wanda naga zai lalace saina kama mishi ya lalace, dan nayi alk'awari saina kafa tarihi a garin katsina, ina so in zama cikakkiyar karuwar da sai suna na ya shiga cikin sahun "yan iska a duniya, dan bazan yadda nayi karuwanci wahala ba.

Kujerata na d'auka na nufi k'ark'ashin bishiyar da ake zaman majalisar, ina k'ok'arin kafa kujerata zan zauna wata zawara tace ke Sultana tashi nan ba wurin zaman yara bane ba kinji.....

Gaba d'aya suka shek'e da dariya tare dayin gud'a, { ayyuri yuri yuriiiiik.... } aka kashe, murmushi nayi tare da ajiye kujerata na zauna, ba tare dana kalleta ba nace dan anyi ciwo an warke ai ba'a ba mutuwa haushi ba, abinda kike takamar an baki nima naci irinshi, tou me za'a b'oyewa ruwa bayan babu inda bai shiga, ansha kuma anyi wanka dashi aikuwa kinga farin wata ba bak'on dare bane ba.

Duk macen dake wurin saida ta kalleni, murmushi nayi irin na "yan duniya tare da d'aga girare na duka nace muci gaba da zance ai abokin cin mushe ba'a b'oye mishi wuk'a.

Sama sama dai akayi firar wannan rana babu wani labarin ci gaba da guda guda kowa ya sab'e duk wanda ba gidan yake ba yayi tafiyarshi aka barmu iyakarmu "yan gidan.....

Bayan sun fashe ne kowa ta tashi ta fara aikin gabanta tunda masu labarin iskancin sun tafi, dan haka sukeyi idan dai ana wannan firar jarabar babu macen dake motsawa, idan kuwa d'anta zaiyi kukan mutuwa bata kulashi.

Maganar sallah kuwa saidai a mik'ata a jimlace, wai sai an gama zance duniya za'aje ayi alwalla lokacin za'ayi azahar la'asar magrib isha'i, wata ma idan ta makara bata tashi sallah asubahi ba, har gari ya waye tou duk wacce ta fito ta samu an fara fira tou wannan sallah sai anjima za'ayi ta, nan mace zata jibge kamar asara ayita kiraye kirayen "ya "yan dan ubanki baza ki kawomin kaza ba,

Saida kowa ya tashi sannan nima na d'auki kujerata nayi d'akina, buta na d'auko nazo nayi

End Ads

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login